Showing 105001 words to 108000 words out of 365757 words

Chapter 36 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1516

Su aunty Mimi dariya suka Sanya, yayinda Galadima yad'an 6ata rai yana fad'in  da tsohuwar Zuma dai ake Magani Momma .

 a fad'arka ba, amma sabuwa ma aitafi aiki da dad'i .

Nidai murmushi nakeyi, Dan wasan nasu ya burgeni, inason ganin family haka cikin farinciki, gaskiya sai sunfi jin dad'in zaman nan fiyema da masarautar sun can.

Gaishe-gaishe aka shigayi, kowa yana k'ok'arin bama Momma labarin yanda biki ya kasance, sai dad'i takeji da sanya albarka, nidai nida Galadima babu mai cewa komai.

Mik'ewa Galadima yayi,  bara nad'an watsa ruwa Momma .

 to afito lafiya Muh'd . ta kalleni nima,  d'iyata tashi kibi mijinki kiyi wanka kuzo ga abinci .

Harya fara tafiya saiya tsaya, juyiwa yayi yana mata magana a yaren daban saniba.

Ta galla masa harara da masa dak'uwa, itama bansan mitace masaba. naga dai ya tura baki yaci gaba da tafiyarsa. ita kuma tace natashi naje.

(Wai ashe cayay mata ai yasa a gyaramin d'akin da zan zauna, shine tamasa dak'uwa tana cewa d'akin safa?, shi idan ance Araba mana d'aki saiya amince?, to tare zamu zauna, shine yakuma cewa ammafa d'akinsa ai ba kowa ke shigaba, tace tasani aii, muje nima sirrinsace ai, shinefa ya tura baki gaba).



Kamar an maken k'afafu haka nabisa abaya muna taka steps d'in benen, har muka isa k'aramin falo mai k'yau, komai farine a wajen, TV ce kawai takasance bak'a.

Falon yad'anyi k'ura alamun ba'a gyaraba (babu mai aikin dake hawa samansa, gashi kuma sunyi tafiya suduka, Momma kuma batada time d'in gyara masa d'aki).

Guntun tsaki yaja yana yamutsa fuska, d'an zaman danayi dashi na fuskanci bayason k'azanta komin k'ank'antar datti yata yamutse fuka kenan, bamu tsaya ananba muka shiga bedroom d'in bayan yabud'e, mayataccen k'amshinsa yana manne da d'akin, sai dai nan d'inma yayi k'ura, waya yazaro yayi kira, ashe Samha yakira, yace  k zoki gyaramin d'aki .

Bai jira cewarta ba ya yanke wayar.

Bance masa uffanba nima nataka nawucesa, bina yayi da kallo dan yaga ina zanje?.

Zanin gadon na yaye duka, nacire rigar filaluwan tareda rumfar da akama gadon, shidai kallona kawai yakeyi, yana tsaye jingine da bango (baiyi tunanin zance zan gyaraba).

Knocking d'in da akayine yabada izinin shigowa, Samha ce d'auke da kayan tsintsiya, ta zubesu a k'asa tana fad'in  aunty kibarsa zan gyara .

Kaina na girgiza nace  barshi Samha, nunamin kawai yanda zanyi, kije kema ki huta .

Nunamin komai tayi, har inda bedsheets suke, tafice a d'arare da zaton Galadima zai hanata yace takoma ta gyara.

Amma saitaji baice komaiba, yama kauda kansa gefe kamar baisan munayiba.

Bathroom nashiga, nazage sosai na tsaftaceshi, Dana k'urarce kawai, duk abinda zaisa toilet k'amshi da tsafta nasakashi, saida naganshi need sannan nafito, ban iskeshi a d'akinba, Dan haka hankali kwance Nagyara bedroom d'inma nagama, nasaka kamshi sosai. falon nafito danufi gyarawa, sainaga Samha harta gama itama tana saka air fresheners masu dad'in k'amshi, da turaren wuta irin namu na gargajiya.

Sannu da aiki namata, itama tamin, Galadima yafito daga wata k'ofa yawucemu batareda ya tankaba, bedroom d'in yakoma.

Kallon Samha nayi nace,  saura wannan d'akin daya fito cikin ko? .

 ai Aunty wannan d'akin dakansa yake gyarawa, babu mai shigarsa duk gidannan inba Momma da Mummy na da shiba .

Cikin mamaki nace  miya sa to? .

 d'akin sirrinsa ne aunty .

Ban fahimci maganarba, bankuma tambayeta ba, ta tattara kayan damukayi amfani dasu tafice tana fad'in  aunty bara naje nayi wanka, dama wankan zanyi yakirani .

Kaina kawai na iya d'aga mata, saman kujerar na zauna shiru ina nazarin maganarta, miye kuma ma'anar d'akin sirri? nashiga k'ololuwar nazari banyi zaton time yawuce hakaba, k'afata yad'an shura, nad'ago idona ad'an firgice na kallesa, haryayi wankan yana sanye cikin jajayen kaya na Adidas, sun masa k'yau sosai.

Juyawa yay zai sauka k'asa yana fad'in  kitashi kije kiyi wanka .

Bai jira cewata ba ya sauka.

Nima saina tashi nayi yanda yace, d'akinsa sosai ya had'u gaskiya, harma bansan Yaya zan fasalta mukuba, nasan farin Abu namai tsaftane, lallai yanada tsafta, daga bedroom parlour zuwa bathroom nashi komai farine, bedroom d'inne kawai keda d'an sirkin Golden kad'an-kad'an shima.

Nidai ina wanka da d'unbin tunani, haka kawai naji kwad'ayin son Shiga d'akin sirrin nasa.

Koda na fito saina saka zani da riga na atanfa, ban shafa komaiba na d'auki turarensa na saka saboda neman magana=��. ina tsaka da saka turaren Samha tashigo kirana.

Ajiyewa nayi na d'auki gyale nabi bayanta.



Falon k'asa muka sakko, inda aka shirya abincin saman wata lallausar darduma, duk suna a zaune har Momma, kusada Galadima daketa cin abincinsa ko kallon mutane bayayi Aunty Mimi ta nunamin wai na zauna.

Kamar nafasa kuka haka naji, Sauban dake gefen haggunsa yace,  auntynmu har yanzu amarcin bai k'are bane? kin shige d'aki kinyi bulum .

Murmushi kawai nayi na k'asa ce masa komai, dan yabani kunya gaskiya, nakula kuma yanada yawan tsokana, aunty Mimi kam dariya tayi, yayinda Samha tarufe baki tanayin tata.

Momma tamasa dak'uwa,  o kai Sauban ALLAH ya shiryeka, kowama bazaka d'agama k'afaba? .

Dariya ya kumayi yana satar kallon Galadima dayay tamkar baya wajen, yace  to ai gaskiya nafad'a Momma. dan ALLAH aunty ba haka bane? .

 gaskiyarka fa Sauban . Aunty Mimi ta fad'a tana dariya.

Momma tace  barsu kinji my daughter, ci abincinki .

Kai na jinjina mata cikeda kunya.

Galadima dai har yanzu baice k'alaba, baima d'ago ya kallemu ba.

Haka muka ci abincin nidai duk a takure nake, kamar yanda yafara cin abinci haka yarigamu kammalawa, tashi yay yabar wajen, yakoma can saman wasu kujeru guda biyu ya zauna, laptop d'in dake saman table d'in wajen ya d'auka ya kunna, da alama shiya ajiye kayansa.



Bayan mun gama duk muka mik'e, kowa ya hau shirin zuwa asibiti duba Abie, time d'in barcin sane shiyyasa ma Momma tasamu tataho, jakadiya kawai aka bari a wajen, itama a waje, da yake in time d'in barcinsa yayi kowa fitowa yake daga d'akin a barsa shi kad'ai.



Galadima saboda aikin da yakeyi yace muyi gaba shima zai taho.

Momma tace  to matarka ta zauna ta jiraka, mudai mun tafi .

Kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru, cigaba yayi da aikinsa harsuka fice, jinai kamar nace nidai zan bisu kawai. Amma na makaro, dan harma sun fice abinsu.

Ganinai tsayuwa ta isheni, shikuma d'an latsin baice na zauna ba, sai kawai naje na zauna d'ayar kujerar dake kallon tasa, nima na d'ora k'afa d'aya kan d'aya tamkar yanda yayi. nayi gefe da kaina cikin basarwa.

Daina danna System d'in yayi, ya d'ago idanu yana kallona, yayinda yake Murza hannunsa na haggu daya d'ora guywar a hannun kujera hannun yana sama, yinai tamkarma bansan yana kallona ba kwata-kwata.

cije lips d'insa yayi kad'an, ya janye idonsa ya maida ga system d'in, aransa yana mamakin izzar yarinyarnan, tabbas data fito gidan sarauta da anga mulkin tsiya.

Falon shiru babu kowa, tunda kuyangin suka gama hidimarsu duk suka koma 6angarensu dake can baya.

Kusan mintuna 40 yagama abinda yakeyi, laptop d'in ya kashe sannan ya mik'e, batare da ya kalleni ba yace  muje .

Saida na d'an ja wasu seconds sannan na mik'e, saidama ya juyo ya kalleni, dan har yakai k'ofar fita.

Gyalena na maida saman kai nabiyo bayansa, a k'ofa na iskeshi tsaye, na fito shikuma ya daddana wasu madannai agefen k'ofar, Ashe wai security yasaka.

Ranar farko danaga yayi tuk'i da kansa, dogarin dasuke gate suka bud'e mana muka fice.

Tunda muka tafi ba Wanda yayma wani magana, shi yanata deriving d'insa nikam ina kalle-kalle abuna, mun Isa katafaren asibiti mai k'yawun gaske, inma badan sunanba da saika d'auka wani wajen shak'atawa ne, asibitin ya had'u gaskiya, har ciki muka shiga bayan security sun mana 'yan tambayoyi dakuma gaisawa da sukayi, naga alamar sun sanshi sosai, amma duk da haka saida akai searching d'inmu.

Abin ya birgeni gaskiya, inda aka tanada domin parking ya tsaya, ya kashe motar sannan muka fito kusan a atare, bai tafiba saida na zagayo, muka jera zuwa ciki, yanata gaisuwa da jama'a, ina mamakin yanda ya iya yarurrukansu, nikam dai saidai da turanci nake gaishesu, kuma ba kowaba.

Mun fara zuwa office d'in wani doctor, suka d'an tattauna akan cigaban da aka samu na jikin Abie, mun gaisa dashi yaymana murnar aure, murmushi kawai nayi, sai Galadima ne ya amsa masa.

Daga nan muka shiga d'akin da Abie yake jiyya, iyalansa su aunty Mimi duk suna zagaye dashi, nidai a raina danaga d'akin nace oni kamar ba Asibitiba?.

Tunda muka shigo fuskar dattijon dake kwance a gadon ta fad'ad'a da murmushi, kallo d'aya namasa naga kamanninsa dana hoton d'akin Galadima na Nigeria.

Gabansa muka k'arasa, Galadima ya durk'usa yarik'o hannunsa, nima saina durk'usa ina gaidashi da Hausa.

Momma ce tazo ta kamani na tashi, cikin wani yanayi tace,  d'iyata ai Abban naku baya iya magana kinji .

Da sauri na kallesa, ya sakarmin murmushi, sai kawai na mayar masa hawaye nabin kumatuna domin tausayi, duk kallona sukeyi sukam, harda Galadima.

Kuma zamewa nayi na durk'usa a gaban gadon, cikin rawar murya nafara jera masa addu'ar samun sauk'i wajen ubangiji. duk suna amsamin da amin.

Murmushi yakasa barin face d'in dattijon, Wanda k'aunata take shigarsa har zuciyarsa, Momma takuma d'agoni a karo na biyu ta rungume tana lallashina.

Galadima ya had'iye hawayen dake Neman zubo masa shima, yafara gaida Abie dake murmushi, da ido ya nuna masani wai ya lallasheni mana.

Sai Galadima yayi murmushin jin kunya yana susar k'eya.

Murmushi Abie yayi sosai, har hakwaransa na bayyana.



Ban ta6a jin tausayin Galadima ba sai yau, dama haka suke cikin tashin hankali? Lallai dan ba'aga dariya a fuskarsa ba ba laifi baneba, nama yabama k'ok'arinsa yanda yake zirga-zirga tsakanin Nigeria da nan d'in.

Ahaka akaita firar dani bana fahimta, danshi Abie da idanu yake maganar.

Bamu baro asibitinba sai dare sosai, a can mukayi salloli dacin abinci.

Mun taho muka baro Momma a can, jakadiya ma ta biyomu, dama Momma kad'ai ke kwana a wajensa, shima ba kullumba, dan wasu ranakun basa bari a kwana dashi, a sati sau uku take kwana a wajensa.





**********



Tunda muka baro asibitin tsohonnan ketamin yawo a zuciya da ruhi, sai cud'awa nake da kwancewa, inason jin labarin masarautar su Galadima gaskiya.



Yanzun ma iza k'eyarmu aunty Mimi tayi muka wuce d'akinsa, muna zuwa bathroom yashiga, kusan mintina 25 saigashi yafito, da Alama wanka yayi, harya sauyo kayan barci aciki, dama da abinsa yashiga.

Nima tashi nayi nashiga da nawa masu kauri a hannu. Wankan nayi da shirin barci, sannan nasako hijjab na fito.

Saman gado na iskeshi yawani barbaje a tsakiya, alamar baya buk'atar wani ya hau.

Na ta6e bakina, a raina nace koma bakayi hakaba ai bazan ta6a had'a makwanci da kaiba, aikin banza kawai, naja tsaki a zuciyata.

Saman sofar d'akin na hau na kwanta, inata tunanin Abie da ma tsalarsa.



Kasa daurewa nayi, na kallesa nace,  wai miye matsalar Abie (kamar yanda naji suna fad'a) .

Shiru yamin, harma na zata yayi barci, sai can yacemin  ciwone dai kawai . daga haka yaja bakinsa yay shiru.

Nima shirin nayi, dan bakuma nida abin fad'a, musamman yanda yabani amsar.

Nidai zan iya cewa barcina na daren ranar rabi da rabine, kewar 'yan uwana da bak'unta, gakuma matsalar babansu Galadima data k'asa Barin zuciyata.

Da asuba narigashi tashima, na fito toilet bayan gama d'aura alwala na iskeshi zaune bakin gado dafe da kai, k'ala bance masaba nad'au abin salla na shinfid'a, tashi yayi ya shiga bayin yana Jan tsaki a zuciyarsa, Shifa wlhy dukya takura, yasaba zamansa shikad'ai a d'akinsa, yanzu duk anzo an cika masa=�D�.

Haryaje k'ofar toilet d'in yadawo baya, doguwar riga ya d'auka ya shige, saida yay wanka da brush sannan yayo alwala yafito sanye cikin jallabiya blue.

Turare yad'an fesa sannan ya d'au key d'in mota yafita, Ashe inda yake zuwa sallan can gaban gidanne, kuma daga sallar asuba yake wucewa asibiti ya kar6i Momma tataho gida itakuma, duk ranar weekend haka yakeyi, yanzu kuwa yana cikin hutune.

Da yake ina sallah yafita, banyi zaton yafita kenanba, bayan na idar saina d'an kwanta, maganar d'akin sirrinsa ce taita cin zuciyata, namik'e nafita, saida na lek'a falon k'asa naga babu kowa sannan nadawo, cikin tantama na murd'a k'ofar d'akin, sai naga ta bud'e, banyi zaton hakaba gaskiya, musamman danaji an kira d'akin dana sirri. (bakisan ya manta bane bai rufeba Munaya=�� dan harda security a d'akin).

'Dakin k'aramine bashida wani girma, gaba d'aya bangon d'akin zagaye yake da hotuna, sai Computers guda hud'u da kuje d'aya gabanta akwai deck's babba, wanda duk Computers d'in akansa suke, sai pens da yawa cikin wani d'an Abu, gefe kuma k'aramar loka Ce ta glass cikeda takardu, gakuma tarin wasu takardun kashi-kashi da akayi kamar files a seman decks d'in, matsawa nayi jikin bangon nafara kallon picture's d'in, hotunan mutanene daban-daban, harda wasu manya dana Sani a TV, mafi yawa yayi rubutu a k'asan kowanne photo, bana fahimtar rubutun gaskiya, danhaka nacigaba da kallon picture's d'in kawai, harda na mama Fulani,=��

=�1�

Kutu melesi hotona fa jama'a a d'akin sirri, naga idi, nakaranta rubuntun k'asan yafi sau goma ban fahimci komaiba, saiwasu lissafi-lissafi kamar mai rubutun Mathematics=�+�.

Na Muftahu nagani a k'arshe, abinfa ya d'aure minkai, mu kuma ni da amininsa Muftahu miya kawomu d'akin sirri=�F�<���?.

Agogon d'akin na kalla naga 7am tayi, da sauri nafita gudun karya zo ya sameni.

Na rufe k'ofar a hankali nakoma bedroom d'insa, ajiyar zuciyata na sauke ganin bai dawoba.

Zama nayi na zabga tagumi ina tunanin ma'anar wad'ancan pictures d'in dana gani, danma a tsorace nake, ban nutsu tsaf naganiba>�&�<���
@&.



Ban sauka k'asaba saida 9am tayi agogon k'asar, na iske su Samha suna breakfast, harda Momma, na durk'usa har k'asa na gaidasu itada aunty Mimi, cikeda fara'a suka amsa.

Momma tace  ai nayi zaton barci kike, shiyyasa na hana a tadoki .

Cikeda kunya nace  a'a na tashi tun d'azun .

Aunty Mimi ta zaunar dani kusada ita, Sauban ya had'omin komai na breakfast d'in.

Yanzun ma a kunyace naci abincin, kunyata na burge Momma sosai.



Bayan mun kammalane Momma ta kama hannuna muka shiga d'akin ta, a bakin gado ta zaunar dani itama ta zauna, anutse ta kira sunana.

Hakan yasani maida hankalina a kanta nima dan nakula magana mai muhimmanci zamuyi da ita............
'<���









*_tofa, mi Momma zata fad'ama Munaya kuma?._*>��

















*_Ya ALLAH ka gafartama Iyayenmu=�-�=�O�<���_*

*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���2� 9�





........... Munaya taimakona nakeson kiyi akan mijinki .

'Dagowa nayi na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login