Showing 165001 words to 168000 words out of 365757 words

Chapter 56 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1512

mai ji da mulki da kud'i ta fito, kallo d'aya zaka mata ka tabbatar tagama samun duniya, cikin tsantsar tink'aho da homa take zuk'ar iska tareda taku d'ai-d'ai irin na manyan mata.

Cikin sauri aka bud'e mata k'ofar gidan ta shiga guard d'inta na take mata baya.

A tsakkiyar tsakar gidan taja tunga, sai hura hanci takeyi tana harare-harare.

d'aya a cikin guards nata yace,  ma'am nan shine d'akin da yake .

Batace uffanba taci gaba da takawa d'ai-dai har zuwa k'ofar d'akin, hannu ta d'aga musu alamar su dakata. Dukkansu baya sukaja domin cika umarninta.



Zaune yake a kujera an d'ad'd'aureshi, kallo d'aya zaka masa ka tabbatar a galabaice yake.

Shigowarta baisa ya d'aga kai ba balle ya motsa, yasan dai bazai wuce k'artan dasuka kawosa wajen baneba. sai dai jin k'amshin turaren mace yabashi mamaki, hakanne ya sakashi d'ago idanu domin tabbatar da yaren hancinsa.

Bakinsa na rawa yace,  Wacece ke? .



Bata bashi amsaba, saima kujera data ja irin wadda yake kai ta dinning ta zauna, k'afa d'aya ta d'ora akan d'aya tana wani cika da batsewa.  yaro baka isa sanin ni wacece ba, Sai dai cigaba da 6atamin aiki zai sakaka sanina .

Murmushi Muftahu yayi, ya d'ago idanunsa yana mata kallon rainin wayo,  Saninki dama aikin banzane a gareni, aikin ki kuma da kike ik'irarin ina 6atawa duk da ban sanshi ba, kisa a ranki yanzu ne na fara 6atawa, saiki shirya nunamin ke d'in wacece? .

 hahaha, yaro baisan wutaba saiya taka .

 Humm, wuta bata san yaroba saisu k'ulla .

 karan farauta yaushe uban gidan naka yafara koya maka irin izzarsa haka? .

 Kinsan zama da mad'aukin kanwa aishi ke kawo farin kai .

 lallai zan had'a da kanwar da mad'aukin nata duk na koyar dasu darasi. Shi kansa Sameer d'in baikai darajar karen gidana ba balle kai yaronsa .

Murmushi Muftahu yayi,  Uhmm sai yanzu na fahimta, sai dai zan tunatar dake abinda kika manta, Wanda kikeyi danshi baima San da zamanki ba, kinga ashe ihu kikeyi bayan hari.......... .

 hhhhhhhh! Abin dariya, inbai fahimta ba ai zai fahimta lokacinda sak'on sunana da gawarka suka isa a gareshi, yanda ban haifi magajin masarautar gagara badauba, zeenah bata isa haihuwar magajinta ba wlhy .

Idanu Muftahu ya tsura mata, sai yanzu yafara hango kamannin d'aya daga matan tsohon Sarki Abie da suka bar masarauta bayan shekaru biyu da fara jinyarsa, bashida wayau a time d'in, Dan dagasu har Galadima bazasu wuce 7-7 year's ba, saida suntaso sunji labarin bijirewar matan a lokacin da za'a tafi da Abie India, dama shekaru biyun da suka zauna basu ta6a saka hannu a jiyarsa ba, sai Momma keta fama...........

Marin da aka zuba masane ya sakashi dawowa daga dogon tunanin daya tafi....

 tunanin mi kakeyi Karen farauta? .

Jajayen idanunsa ya zuba mata, sai kuma ya kwashe da dariya, saida yayi mai isarsa sannan ya dakata tareda tsuke fuska,  ina tunano mummunan fuskarkine, in banda abinki miye na kishi da abinda kika bari da kanki? nasan dai Momma ba itace ta hanaki haihuwa ba ai, inason kisan ni ban isa kare Galadima ba dama, amma kulum cikin kariyar Wanda ya haliccesa yake, a tunaninki 6ata sunansa da kikayine ke nufin bazai mulki masarauta mai d'unbin tarihi da girmaba? kinyi kuskure babba wlhy, Dan kinsaka kanki a ramin damisa. duk ranarda Galadima ya gane kece kika saka amasa 6atanci a jarida wlhy saikinyi nadamar rayuwarki..........

Bayan Hannu tasaka ta bugi bakinsa, gefe yay da kansa yana murmushi, ga jini na zuba a gefen bakin, dayake hannunsa a d'ure suke.

Tace,  kafin ni nayi nadamar kai ne da shi zakuyi, Dan yanda kake a tarkona shima yanacan a cikinsa, wawa kawai, kai aboki mai gaskiya ko? zan shayar dakai mamaki, domin saikaga gawar Sameer a gabanka kwance kafin kaima kabishi baya .

Dawo da kallonsa yayi gareta yana murmushi,  miyasa kika tsorata tunban k'arasaba, Galadima maruci ne, kuma kainuwane, gashi dakalin majina, kina hawansa zamewa zakiyi wlhy, ina tausaya miki yayinda tunaninsa ya waiwayo kanki, Dan yanzu aikin manyanki ne a gabansa ba nakiba, d'ana masa tarkonki kuwa tamakar kin tado damisane daga barci, hakan kuma fitinace babba a gareki da shi kansa Karen farautar taki Harun, tirrr da zuciyarki, ni kaina danasan ma kece bazan 6ata lokacina wajen bibiyar ki ta hanyar Harun ba, amma banyi bak'in cikiba, ko babu komai na ribantu da abubuwa masu yawa, domin ta silar hakan na had'a auren sunna, gashi harda ribar ciki, magajin Galadima Sameer kenan.......

A fusace ta d'aga kofin glass zata kwala masa.

Yace,  relax relax mana giwar mata, ai bangama fad'aba OK? ba kince zaki kawomin gawar Galadima ba sannan, to miye kuma na fusata haka da wuri?, ni ina kuma tabbatar miki indai Galadima ne zaizo, daga lokacinda yasan ina nan tabbas zai zo, banza karyar farautar wasu, na tabbata k'arya kikeyi ba aikin kanki kikeba kema, sakaki akayi, lallai ke farashinki ya fad'i k'asa, matar sarki mai fad'a aji irin Sarki Saifudden Ce ta k'are ahaka? Abin kaico abin jaje, tirrr .

Dariya ta kwashe da shi tana tafa hannaye, saikuma ta matsa gabda Muftahu tana magana cikin kunnensa  lallai bayan Sameer akwai magajin sa a gagara badau ashe? .

 oh sai yanzu kika fahimta ashe? .

 karen Sameer zaka mutu kaida uban gidan ka, saina saka wannan zuciyar tasa ta buga wannan shine k'udirina .

 hhhhhhh abin dariya, kudirin wasu dai, danke naki bamai muhimmanci baneba, tunda kuka kasa saka zuciyar Sameer bugawa a lokacin da k'uruciya da rashin sanin kansa ke damunsa, miyasa kuke tunanin zata buga a lokacin da yagama tanadar makaman yak'insa, ranar shiga filin daga kawai yake jira, nagaji da tattaunawa dake please .

 kaima kace wani Abu yaro, Dan haka mu zuba, kwana uku kawai zakaga gawar Sameer a gabanka!!!!! .

Bata jira yabata amsaba ta fice daga d'akin, tareda jan k'ofa da k'arfi.

Idanunsa kawai ya rintse. Baya tsoron makircinta, amma yana tsoron na Harun, dan Galadima ya rigada ya yarda da Harun 100%, bazai ta6a kawo zai cutar da Shiba. Waige-waige yashiga yi, yasan babu wani abunda Galadima zai iya bibiya tare dashi.

Da sauri ya girgiza hannunsa saboda tunowa da agogo, jin agogon tare dashi ya sakashi lumshe ido yana ambatar Alhamllh. Matsala d'ayace baya ganin agogon, saboda hannunsa yana a baya ne. Amma dukda haka zai gwada idan za'a dace.







___________________________





Yau na kasance cikin farin ciki, saboda gani tsakkiyar 'yan uwana, dukda ma zazza6ine mai zafi ke nuk'urk'usata, amma kewarsu ta hanani gajiyawa, mun bud'e babin fira a tsakkiyar falon mama Rabi'a, duk abinda akayi bana nan shine ake labarta min, yayinda Nima nake basu labarin India da nuna musu hotuna.

Haka mu kai wannan yini cikin farin ciki da annashuwar kasancewa da junanmu, musamman ma ni da 'Yar uwar tagwaicina da k'addarar aure ta tilasta mana nisantar juna, ji muke tamkar mun shekara ba'a tareba. Kowannenmu k'ok'arin ganin farin cikin d'an uwansa yakeyi.





_____________





Tunda Galadima yabaro gida dasu Aryaan saiya wuce wajen wani hutawa dasu, ya yawata dasu sunata farinciki, yayinda shi kuma yake biyema shirmensu dan d'auke musu kewar mahaifiyarsu, yana son yara, shiyyasa ko yaushe Khaleel d'in aunty Mimi zakigansa manne dashi, sa'annin Khaleel dasu Aiyaan kuwa zai iya zuwa d'aya.

Cikin lokacin k'ank'ani suka saki jikinsu dashi.

Daga nan plaza ya nufa, haka kawai zuciyarsa keta tsikara masa zancen 6atan Muftahu, dukda k'ok'arin wofantar da lamarin da lamarin da ya keyi.

Waya ya d'auka ya shige danne-danne, alamu sun nuna masa wayar Muftahu na cikin masarauta, kenan bai d'auki wayarba, yad'an murmusa kawai yana cije lips, yayinda idonsa ke kansu Aiyaan da Saleem yazo d'auka suje wajensa danya huta.

Bye suka masa, shima ya d'aga musu hannu yana murmushi.

Suna ficewa ya sauke ajiyar zuciya tare da mik'ewa tsaye. zagayen office d'in ya farayi hannunsa goye a baya, a wannan karon bazai ta6a k'yale Muftahu ba, dolene yayi wani Abu akansa, dama yana d'aga masa k'afane domin son ganin gudun ruwansa kawai, yanzu kuma lokacin yayi dazai San mi yake k'ullawa...........
'<���









*_Duk Wanda yaga ban amsa massage nashiba yamin afuwa, cakwakiyar network tasani clearing charts d'ina batareda na dubaba, tun around 3:47pm nayi posting amma yak'i tahowa._*





Dan haka ina gayyata kowa gobe a court, zamu shiga shari'a ni da network ne=�D�.



Wad'anda suka ga basa ganin posting d'ina gaba d'aya a satinnan duk aikin network ne=�D�.













*_ALLAH ya gafartama iyayenmhiyayenmu=�-�=�O�<���_*

*_typing=���_*





=ء� *_HASKE WRITERS ASSO....._*





*_f&RAINA KAMA.....!!f&_*

_(Kaga gayya)_







*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







~Book 2~ =�I�<���1� 3�





...............Muna tsaka da hira saiga Aunty salamah tazo, daga ni har Munubiya da Ayusher rungumeta mukayi.

Cikin tsokana ta ture Munubiya da Ayusher tana fad'in  ku matsamin, kullum Ku ina ganinku, kewar gambo nakeyi .

Gwalo na shiga yi musu, mama Rabi'a da Feena namana dariya.

Bayan mun zauna Aunty Salamah ta shiga yaba canjawar danayi tanamin shak'iyanci, nanfa su Munubiya ma suka samu abinyi, sosai suka tasoni gaba sai mama Rabi'a ke kareni.

Can muna tsaka da hira takamo hannuna tana fad'in  zo nabaki wani sirri nan autana .

Mik'ewa mukayi inamasu Ayusher gwalo, yayinda suma suka tubure basu yardaba sai an bada sirrin dasu. da k'yar muka samu muka shige d'aki muka kulle.

A bakin gado muka zauna Aunty slamah ta sauke ajiyar zuciya tana kamo hannuna cikin nata, serious nima na zama na maida hankalina gareta.

Tace,  Munaya! Aiki yatafi yanda ya kamata, saidaifa labarin ya canja daga yanda kike zato, Muftahu ba munafuki baneba .

A matuk'ar razane naja baya ina ture hannunta daga cikin nawa,  Aunty kinsan mi kike fad'a kuwa? Anya yaranki Muftahu suka kama? .

Hannuna ta kamo tana murmushi, kinga zauna, shiyyasa na saka aka d'auki komai dan kema ki gani da idonki .

Zaman nayi kuwa, ita kuma tayi 'yan latse-latsenta a iPad d'inta ta mik'omin. kar6a nayi cikeda fargaba, da kaina nayi playing d'in video n, tun daga fitowar Aunty salmah daga mota har shiganta cikin gidan zuwa shigarta d'akin, tsayarwa nayi na kalli Aunty ina dariya,  kai Auntynmu kinfa iya Acting wlhy, wanifa saiya d'auka da gaske irin mugayen hamshak'an matan nanne .

Dariya Aunty Salamah tayi,  wlhy koni dai nayi mamakin dakewata, bakiga sai wani hura hanci nakeba, sukuma su Ameer saikace guards d'in irin manyan mutanan nan .

Dariya mukayi, sannan nakuma playing na cigaba da kallo.

Shigar Aunty Salamah d'akin da tattaunawarsu da Muftahu. gaba d'aya jikina yayi sanyi, zuciyata sai wani tsitstsinkewa takeyi, idona cike da kwalla nace,  anya gaskiya Muftahu yake fad'a Aunty Salamah?, wlhy da gaske fa shine ya saka mana desire tablets, inhar bada wata manufaba miyasa yay haka?, kumafa ni banta6a ganin wani alamar rashin gaskiya ba ajikin Harun .

Murmushi Aunty Salamah ta yi, ta dafa kafad'ata tana fad'in,  Munaya mugu bashida kama, Ai Muftahu baisan nid'in ba matar sarkin bace ta gaske, mizaisa ya za6i 6oyemin? yanda yanuna akan k'yamar matar sarkin tabbas akwai mai mugun hali a cikin su da gaske, kinga ai kince bakiga fuskar wanda kika kama yana wayarnanba a bayan window d'inki randa kuka iso .

 Eh hakane, ban ganiba, maganganun kawai naji .

 to kin gani, kifa tuna kuma firar da kika ta6aji Galadima nayi a asibiti shida aunty Mimi. wad'annan alamomin sun nuna akwai wata a cikin matan Sarki dakeda hannu a ciki, maganar Harun kuma idanu zamu saka masa tamkar yanda mukaima Muftahu, dan ayanzu idan mun saki Muftahu zakiga sun cigaba da takun sak'ar datafi ta da zafi, dan nariga da nasaka rud'ani a zuciyar Muftahu cewar zamu kashe galadima, tabbas ta wannan hanyar Harun zaizo hannunmu. Maganar Galadima kuma har yanzu karki fara kwantar masa da kai, dan kwantar da kanki zai d'arsa masa rashin aiminci a kanki, ke dai kinsan halin mijinki ai yanzu, kinkuma fi kowa sanin yanda yakamata ki cigaba da tafiya da shi .

Insha ALLAH Aunty zan cigaba da k'ok'ari nakuma gode da gudunmawarki akanmu, sai dai akwai matsala, dan na lura agogon hannun Muftahu kamar akwai wani sirri a cikinsa, dolene a daren yau a fitar da Muftahu daga gidanan, zanma sarkin mota bayanin yanda zai taimakeku a maidashi masarauta kamar yanda yaymana aikin d'akkoshi, shima Galadima zansa ido akansa saboda tsuntsune shi nai azabar wayo .

 Hakan yayi Munaya, ALLAH ya cigaba da bamu nasara, insha ALLAH zamu gano komai, ALLAH dai yabama Abba lafiya, yasa mu fahimci komai cikin sauk'i, akan Galadima kuma kici gaba da k'ok'arin da kikeyi Fiyeda da, dan dolene saimun samu had'in kansa kafin musan komai, ALLAH ya ku6tar damu baki d'aya, dan kina dai ganin yanda suka maida Abba .

Hawayen da suka ziraromin a kumatu na share, cikin Murmushin k'arfin hali nace,  insha ALLAH Aunty Salamah, domin raina da farin cikina fansane akan mahaifina, kuma zuwa yanzu Auren Contract bai damuna, sai dai bazan 6oye mikiba aunty Salamah wannan cikin shine damuwata a yanzu, inaji ina gain zan haifishi na barsa inda yafi k'arfina, bansan wace rayuwa zaiyiba a wannan gidan da kowa zuciyarsa takeda k'arancin imani, Aunty Salamah gidan sarauta tsantsar matsalace kawai, bazaki fahimci hakaba saikin tsinci kanki a ciki, Aunty dan ALLAH ki amince na zuba da cikinnan .

 munaya waishin miyasa bakida hankaline? to idan baki saniba wannan cikin shine zai zamemiki tsanin mallakar cimma nasara, kuma ta hanyarsane kawai zamu samu had'inkan Galadima domin fidda Abba daga wannan matsalan da Ku kanku ahalinsa, kina tsammanin koda Abba mutuwa yay masu farautar rayuwarsa zasu barku Ku6utane? Dolene saisun samu abinda suke nema koda ace dukkan gidanku zai k'are, bak'ya tunanin aurenku yana cikin abinda yakuma hasala zukatansu, a zatonsu Abbanki yasamu damar had'a kan mijinkine, ya ina jinjinama fik'irarki ke da munubiya kuma zaki 6ata shirin, karma ki bari 'Yar uwarki taji maganar zubda cikinnan, wlhy zaku samu Matsala ne babu ruwana .

Munaya ta share hawayenta,  shikenan Aunty Salamah nabar maganar insha ALLAH. Amma a yaran nan masu mana aiki bak'ya tsoron wani yaci amanarmu? .

 komai zai iya faruwa, domin amana tayi k'aranci a rayuwa, tunda yau gashi Harun yafito cikin masu cin dunduniyar Galadima, amma ki kwantar da hankalinki, su duka ukunnan da kike gani amintattunane, kuma Saleem ya saka mana idanu sosai a kansu .

 to Alhmdllh aunty, ALLAH kamana jagora .

 amin dai, saikima Munubiya dukkan bayanin da mukayi, ki bata itama ta gani, zuwa gobe zan aiko Bilkisu ta kar6a min, kuma ki fad'a mata yakamata ta koma gidan ta, dan gaskiya aiki bazai cigaba da yuwuwaba tana gidannan, saboda kinga ba ita kad'ai baceba, yanzu haka randa zaku zo da zamu kama Muftahu wlhy nasha wahala wajen nemanta naji kokin iso? dan ta tabbatar min inhar kin iso k'asarnan saitaji a jikinta, amma naita kiranta batayi picking ba, ashe wai wayar na hannun Feena .

murmushi nayi nace,  sorry sweet auntynmu, insha ALLAH zata koma gobe .

 shikenan, bara na wuce to .

 to Aunty ngd sosai, ALLAH ya bada ladan zuminci, ammafa gaskiya kinci zalin muftahu da yawa .

Dariya tayi sosai,  kibari kawai, nima wlhy ina marinsa tausayinsa Na ratsani, insha ALLAH zan nemi yafiyarsa zuwa nan gaba, ALLAH yasa ya yafemin dai .

 hhhh zai yafe miki aunty ai duk cikin aikine .



Mun rakota har tsakar gida, su Munubiya na tsokanarmu wai nad'an sammusu sirrin suma.

Daga ni har aunty Salamah dariya mukayi kawai.

Bayan dawowarmu na turama Munubiya massage akan taje tagani itama.

Sai da taja wasu times sannan tamik'e tana fad'in bara tad'an watsa ruwa. duk muka amsa da to saita fito.







**************************







Su


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login