Showing 315001 words to 318000 words out of 365757 words

Chapter 106 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1444

hard'e a k'irji yana kallon doctor da fad'in  Doctor da raina zan bar wasu ganarmin sirrina? Ku kawo kayan buk'ata kawai .

Doctor daya fahimci Inda zancen Galadima ya nufa saiya murmusa yana cewa  Afuwan ranka ya dad'e .

Hannu kawai Galadima ya d'aga masa, ya juyo suka had'a ido da Munaya ya d'aga mata gira da cizar lips d'insa.

Baki ta tunzuro masa tana yamutse fuska.

Ya d'aga kafad'a da ta6e baki alamar bashida matsala>�7�<���
B&>�#�.



Nurses biyu suka shigo da dukkan abinda ake buk'ata, Galadima Na tsaye ko kallon inda suke baiyiba, idonsa nakan matarsa k'yam, sukam sai satar kallonsa sukeyi, suka ajiye suna fad'in  Gashi Ranka ya dad'e .

hannu kawai ya d'aga musu amma ko tari baiyiba.

Fita saukai cikin takaici, dan sunso yayi musu magana koda sau d'aya ne.



Takawa yay a hankali jikin k'ofar ya Mirza key, sannan ya dawo yana cire link d'in hannun rigar farar shaddarsa da tattarewa zuwa sama.

Suka had'a ido da Munaya tai azamar janyewa cike da kunya.

Murmushin gefen baki yayi yana zama bakin gadon kusa da k'ugumta.

Bottoms d'in jikin green d'in rigar asibitin yafara cirewa a hankali, itadai kunya ta hanata bud'e ido, gashi ya tsareta da idanu, Dan tanajin yanda idanunsa ke yawo cikin jininta, salon daya koma wajen cire bottoms d'in ya sakata dafe hannunsa da hannun haggunta, ta bud'e ido tana kwa6e fuska.

Gira ya d'aga mata, da wani mata salo da kwayar ido.

Babu shiri ta maida idonta ta rufe ruf, tsigar jikinta Na tashi.

A haka dai aka gama cire rigar, yaja bedsheet d'in da ake lullu6a mata a k'afafu ya rufa mata a jiki, sannan ya kuma gyara hannun rigarsa yana tsoma madaidaicin towel d'in cikin ruwan d'umin dake a boket, ya matsa dukda akwai d'an zafi ruwan haka yafara danna mata jiki dashi.

Tanajin zafi, amma kuma tanajin dad'in d'umin ruwan sosai, k'in yarda tayi su had'a ido har aka gama, ya d'auki wani d'an kwalba da mai ke ciki tamkar zaitun, karantawa yay yaga amfaninsa sannan ya zuba a tafin hannunsa yana murzawa, kumajin tattausan hannunsa daya had'u da sul6in mai tayi a k'afafunta, tad'an kuma bud'e ido tana kallonsa. Ganin ba ita yake kalloba saita shagala da kallonsa, babban mutum mai daraja jinin mulki yau shine ke mata hidima irin haka, itako badan kar ace tayi alfahari ba da cika baki da yawa da tace ta more fiye da kowacce mace (=�D�nidai fa bandani, reader's Ku kun yarda harda Ku>�7�<���
@&)?.

Sosai tafara jin dad'in tausar, Dan da salon nutsuwa yake mata, tuni tafara lumshe idanu, hardai barcin yaci galaba a kanta. Sai dai saukar numfashinta yaji a hankali.

Ya kalleta yana murmushi da lumshe idanu, bai bartaba saida ya tabbatar barcin yayi nisa, cikin dabara ya canja mata rigar da suka sakko a kayan domin canji. Ya duk'o ya sumbaci goshinta da bakinta yanajan bedsheets d'in sosai ya kuma lullu6a mata.

Kayan ya maida gefe, ya koma saman kujerar dake gefem gadon ya zauna ya zuba mata idanu, kai kace yaune ya fara ganinta, ya dad'e a haka kafin ya d'auka wayarsa yana dannawa.

A haka Nurses d'in suka masa Knocking, izinin shigowa yabasu, amma sai suka murd'a k'ofar a rufe.

K'aramin tsaki yaja yana muk'ewa, shi yama manta ya rufe. Bud'ewa yay yadawo ya zauna yana d'ora k'afa d'aga kan d'aya da kuma d'aure fuska.

Tuni Nurses d'in suka shiga hankalinsu, cikin risinawa d'aya tamasa bayanin zasu canjama Munaya bandejin jikinta ne.

Batareda ya kallesuba yace,  kuyi a hankali, Dan barci takeyi, idan kuma kunsan zata iya farkawa kubarsa saita tashi  .

Kallon juna suka, kowacce tad'an ta6e baki, d'ayar tace,  insha ALLAHU bazata tashiba ranka ya dad'e .

Nanma Kansa kawai ya jinjina musu yacigaba da latsa wayarsa.

Haka sukai wannan aiki a gabansa Dan yak'i fita, data motsa ya zuba musu uwar harara mai rikita hanjin ciki.

Dolensu suka bita a sannu har suka samu kammalawa lafiya, kowacce ta fice a tsorace.............
'<���



ALLAH ya gafartama iyayenmu=�-�=�O�<���







f&RAINA KAMA...!!f&

(Kaga gayya)





Bilyn Abdull ce>��<���





BOOK 3 =�I�<���2� 3�





.................Mud'in mun kasance wasu yankin ahali daga wannan masarauta, sai dai nasan al'ada da ak'idar masarautar ta jima da shafemu daga kasantuwar tsatsonta.

Iftila'in al'ada Nak'in kar6ar d'iya mace a matsayin y'ar farko ga Sarki mai mulki shine silar barin iyayenmu damu kanmu, sarakuna da yawa sun shud'e labarinsu ya shafe tamkar yanda Na Sarki Madou Amadi yazama shud'ad'd'e inna ta share hawayenta, sannan tacigaba da fad'in,  Lokacin da mahaifinmu yake bisa karagar Mulki da k'arfin iko sai ALLAH ya azurtashi da haihuwa ta a matsayin d'iyarsa ta fari. Haihuwata ta girgiza k'arfin mulkinsa matuk'a, Dan Al'adar masarautar shine tilas d'an Sarki Na farko ya kasance d'a namiji, acewarsu d'iya mace rusa masarauta takeyi da tsiyatata, dan ita bata mulki, kamar yanda ake korar duk wani Sarki da matarsa ta haifi y'a mace a haihuwar farko ga mahaifinmu sai bai yuwuba, saboda k'arfin iko da ALLAH ya bashi, anbuga-anbuga yak'i sauka, danshi burinsa ya canja wannan al'adar masarautar, har ALLAH yasa Na cika shekaru 7 a duniya. A tsakaninnan bayyana harmutsi da hayaniyar da taita faruwa 6ata lokacine, Dan mahaifinmu Sam yak'i sauka daga Matsin da suke masa. cikin amincin ALLAH sai kuma ga cikin Rabi'a babu zato, har wannan lokacin babu wani kwanciyar hankali a masarauta, saidai bayyanuwar cikinta yasa akace za'a dakata aga mizata haifa, idan d'a namijine shikenan. Saidai kash, daga lokacinda Rabi'a ta canyara kukan isowa duniya sai masarauta tayi tsitt, Dan kuwa dai kowa yaji macece. Dandanan fa aka tada Sabin bore akan dolenefa sarki ya ajiye a wannan karon, amma mahaifinmu saiya k'i a wannan karonma, danshi burinsa ya canja wannan mummunar al'adar kowa ya fahimci itama d'iya mace tanada tata darajar fa, kufa namijin bai fitaba, domin itama ALLAH ya haliccetane danta bauta masa tamkar namijin, dukansu kuma idan sunk'ibin ALLAH wuta zai sasu, idan sun bishi Aljanna zai kaisu, amma Sam sai suka bijirema dukkan tunatarwarsa, masuma goya masa baya suma sai suka daina, watan Rabi'a 1 kacal a duniya akai mana korar kare daga wannan masarauta dama yankin baki d'ayansa, muna kuka muda mahaifinmu haka muka tafi, mukabar ahalinmu, yankinmu , al'ummarmu. Saboda mummunanr Ak'ida, saidai kuma babu inda muka Sani, Dan haka iyayenmu suka yada zango awani k'aramin k'auye dagacan bakin gari, anan muka rayu tsawon wasu shekaru dahar nakai girman zama minzalin budurwa, itama Rabi'a ta girma, rana tsaka saiga tawagar masarauta wai ankai mata bayanin mahaifinmu baibar wannan yankiba, halan akwai abinda yake shiryawa? Dan bazai yuwu ayi sarki biyu cikin nahiya d'aya ba, sarkin ma da aka d'ora bayan korarmu shima matarsa mace ta haifa, tuni sun korashi, Na yanzunma kuma hakance ta faru, dalilin korarsane ma sukaji labarin mahaifinmu yana a wannan waje tare damu. Korar cin zarafi da akai mana a wannan lokacin tamafi Na farko, Dan alokacin munada wayo muma, munsan zafi munsan d'aci, a wannan karon bama Nahiyarmu ba, k'asar gaba d'aya muka bari, tafiya ta tsawon wattani da yada zango ce takaimu Nigeria, a wahalce a jigace, inda muka samu mafaka a tashar da suke lodin motocin da suke zuwa kasuwanni, makonmu uku a wajen, Dan bamu rasa abincin dazamu ciba iftila'in rayuwa da k'addara ta fad'amin, Wanda muka wayi gari da rashin mai taimakonmu sai wani bawan ALLAH (Malam fharuku kakansu Munaya=��)

Inna taci gaba da bada labarin k'yautatawar dasu Innaro sukai musu, har mutuwar iyayensu da aurenta da Abba, Dana mama Rabi'a, da zuri'ar da suka samu harda jikoki, ko kad'an bata fad'i muzanwa ko cin fuska da Innaro taita musuba sai alkairin mijinta da y'ay'anta.

Nanfa kowa ya shiga matse hawayen tausaya musu, hardamu, Dan munji abinda koda wasa bamu ta6a saniba balle tunanin kasantuwarsa, Dama iyayenmu jinin sarautane mai girma irin haka? Amma kullum suka kasance cikin shanye k'ask'anci da gorin talauci Dana ahali, lallai wannan banzar al'ada batada wani abin birgewa.

Shikansa sarkin saidai yay hawayen tausayinsu inna, Yakuma buk'aci su matso garesa, hakama tsohuwarnan rungumesu tayi tana kuka.



Innaro dai anyi zugudim tana kallon ikon ALLAH, Wanda ya girma ya d'aukaka, kunya da d'unbin nadamar Dana Sani sun dabaibayeta tagaza koda kwakwkwaran motsi balle d'aga ido ta kalli su inna, yanzu nan dukkan cin kashi dacin zarafin dataitama su Ai'sha musammanma ita shine zata lullu6e bak'in mugun halinta ta wanketa da alkairin mijinta Dana y'ay'anta? Wace irin k'yak'yk'awar zuciyace da wannan baiwa haka?.



Munsha kukan tausayin su innarmu, sannan munyi murna matuk'a da tarbar da akai musu damu kanmu, Su Abdurraheem dasu Aiyaan, da Aryaan, Ahmad, dake k'anan duk an janyesu, kowa yana d'aukarsu cikeda tsantsar so da k'auna. Saida akad'an lafa sannan Sarki yay bayani cikin nutsuwa da dattako.

 Lale marhabin agareku y'an uwana, kun kafa tarihin da tilasne a yaba muku, Dan babu wasu da suka sake waiwayen wannan masarauta bayan korar da akaimusu, sun tafi ba'a kuma jin labarinsuba ko inda suke. Bak'aramin durk'usar da wannan masarauta waccan Mummunar Al'ada tayiba, mun rasa ahalinmu masu d'inbin yawa, masarauta dake cikeda dangi yau takoma sai tsirarune a cikinta, kunganmu nan dudu iyakarmu kenan muka rage, wasu sarautunma sai hannun jama'ar gari da bayi ta koma, saboda babu masu rik'ewar, haihuwa itace yad'o, mukuma mun nisanta kanmu da wannan yad'on, masarautar nan ta dad'e tana korar ahalinta saboda haihuwar y'ay'a mata, ALLAH kuma yayta jarabtarmu da samunsu a matsayin y'ay'a, bayan shud'ewar marigayi Sarki Madou Amadi sarakuna kusan 20 sun shud'e a dalilin hakan, bamusan duniyar da sukeba, saida mahaifina yahau ya tsaida wannan al'adar gaba d'ayanta, saboda ganin wataran lallai sai kowa dake cikin ahalinmu ya k'are inhar wannan al'adar tacigaba da wakana, muna baku hak'uri, muna kuma Baku hak'uri, a yanzu wannan masarautar ba ita bace waccan da kukasani, mace Nada daraja sosai a yanzu, tanada kima da k'arfin fad'a aji, muna fata bazaku sake nisantarmu ba, zakuzo mu had'a k'arfi da k'arfe wajen kuma samun yad'uwar wannan masarauta  .

Innarmu da mama Rabi'a Na hawaye suka amsa masa da insha ALLAH.



Zayyana muku farincikin daya cigaba da gudana 6ata lokacine, mun shige cikin dangin mahaifanmu munata warkajami, kulawa ake bamu ta musamman da birgewa, aranar aka canja mana masauki Na musamman dayafi wancan k'awatuwa da komai, aka zuba mana hadimai masu hidima, su Abba kam ko ganinsuma bakayi, gagarumin biki Na musamman aka shiga shiryawa Na murnar dawowar su innarmu. Kai lallai munashan kallo, kukadai najin dad'i da farinciki mun shashi, INA y'an gidanmu? Suzo suga abin al'ajabi daban mamaki, innaro dai baki ya mutu murus, saima dukta tsangwami kanta a cikinmu, aiko mukaita zuba mata habaici muma, Dan ganin su innarmu yama gagareta gaba d'aya, sun shige cikin y'an uwansu tamkar dama ciki suka taso, duk wannan hidima batasani mantawa da kewar mijinaba, musamman da Saurayin jiya yafara takurani da kallon tsiya har a ranar, nikuma ban daina antaya masa hararaba, saida nagaji nake sanarma su Munubiya, suma sukace ai duk hakan yake musu, itadai Munubiya tasamu tayi maganinsa ta hanyar mak'alk'alema mijinta, dukda kuma suna tare da Yaa Marwan d'in duk inda yasa k'afa, hasalima Yaa marwan ya koma sashensa gaba d'aya. Daganan tasamu lafiya, saiya koma kanmu ni da Ayusher, dukda wani lokacin yakan Gaza banbantamu ni da Munubiya, inhar baya ganta tare da yaa Marwan bane, itakuma Ayusher ta fini jiki, musamman ma ramar danayi ta jiyyar Dana sha, ita kanta Munubiya tafini jiki a yanzu. Gashi su Abdurrahman sun gagareni d'auka balle nima Na fahimtar dashi inada aure, inkin gansu a wajena shayar dasu zanyi, tokuma bazan iya hakan agabansa ba.



Wannan saurayi dai d'ane ga Sarki, Dan shine magajin masarautar ma yanzu.

_________





Muna zaune awata rumfar Bunu a washe garin da muka cika kwanaki buyu a masarautar, ranarda za'a gudanar da bikin dawowar su innarmu, zaune muke da wasu y'anmata kusan 8 masu kama damu, duk kuma bazasu wuce sa'annninmu ba, saidai wane ya girmi wane da wata 1 ko biyu, hira muke cikin so da k'auna juna, da d'okin kasantuwarmu ahali d'aya.

Suna bamu labarin yanda bikin al'adunsu ke gudana irinsu bikin sallah dana aure, muma muna basu namu, saidai maganar gaskiya ni hankalina ya rabune gida biyu, rabi garesu rabi ga Galadima.

Munubiya ce ta lura da hakan, ta d'an ta6ani Na juyo Na kalleta.

 Sweetheart mike faruwane wai? .

Cikin marairaicewa nace,  Munu Galadima mana, yakamata yajini koda a wayane, kinga anama mahaifinsa Magani, baikamata ace koyaya bana bibiyar lamarin Yaya lafiyarsaba, karyaga kamar ban damubama .

Cikin gamsuwa tace,  zancenki gaskiyane, shiyyasa kike burgeni wajen hangen nesa, inaga yakamata mu nemi sim card mu saya .

Naji dad'in shawararta, Dan haka muka tambayi y'an matan.

'Daya a cikinsu mai suna Badeera tace,  yanzunan kunason yin amfani da waya shine bazaku kar6i namuba? Amma bamuji dad'iba gaskiya, Ashe bamu zama d'ayanba kenan? .

Hak'uri muka basu, Maryamu ta d'oramin wayarta a jiki tana fad'in gashi kiyi kiran duk Wanda zaki kira, bara a sanarma Yareema issifa yasa akawo muku.



(Nayi amfani da namune saboda wasu dalilai, yarenmu ba d'ayaba Dan haka abubuwan da suke fad'a bazai zama d'aya da namuba, to amma Raina kama anginashine bisa wani bigire daban, zanyi amfani da iya abinda Na sani, Dan ban zurfafa bincikeba gaskiya, ALLAH yasa zaku fahimceni=��>��<���).



Da mamaki nace,  waye hakan? .

Cikin dariya sukace magajin wannan masarautar mana, Wanda kike k'orafin ya dameku da kallo .

Baki nad'an ta6e cikin mamaki, nace,  To wai Issifa sunane? .

Nanma dariyar sukayi, Dijahma tace Youseefa kenan fa.

Nace,  tab, sunayenku kukam wasu iri wlhy, nidai bara kuga naje Na nemo mijina .

Dariya duk suka sanyamin.

Natashi zuwa cikin masaukinmu. d'akinmu Na shiga, Na lalubo wayata a handbag wadda tunda mukazo suka zama marasa amfani agaremu.







**********



A 6angaren Galadima kam suma Alhmdllh, Abie yanata samun kulawa ta musamman ga Dr Erfan Fahad, Dan da iya k'yautatawar yakema Abie abu, kodan sanayyar dake tsakaninsa da Galadima wadda saidaga baya ya tuna wanene Erfan Fahad d'in, sunyi karatun addni wajen malami d'aya a time d'in bazasu wuci shekaru 9 ba, har lokacin da suka kai 17years shi Erfan Fahad iyayensa suka d'aukesa daga wajen Sheaik Mu'azzam Abdul-aziz, saboda zasu koma Kashmir a lokacin, dama aikine yakawo mahaifinsa India, tundaga nan basu sake had'uwa ba sai yanzun, lokacinda Sheaik Mu'azzam Abdul-aziz ya rasu shi Dr Erfan Fahad yazo gaisuwa, amma basu had'u da Galadima ba, a sanann shikuma yana k'asarJapan karatun shekara 2 daya kaisa, saida ya dawonema yakejin rasuwar malamin nasu, gaisuwa kawai yaje yayma iyalansa yaymusu alk'airi mai yawa.

A kullum Dr Erfan Fahad da Galadima cikin hirar tuna baya suke, balle da Dr Erfan Fahad ya d'ebo masa wasu hotunansu suka gani, nanfa suka kuma rikicewa da labari, suna hirar sauran abokansu da rashinjin da sukayi a makarantar.



Rabonsa da jin Munaya tun randa suka tafi, suna gab da shiga Niger sukayi waya, daga nan basu sake ba, sosai yake kewarta, duk ya damu, kwana biyu kawai dabai jitaba, har Dr Erfan Fahad saida ya fahimci yana cikin damuwa, Dan Dr Akash da Dr Ajay sun koma India kan aikinsu.

Amma Galadima yace masa babu komai, Dr Erfan Fahad bai yardaba, Dan haka ya damesa da tambaya, doledai Galadima ya sanar masa.

Aiko ya tasashi gaba da tsokanar wai yace dai soyayya kecin zuciyarsa ba wani abuba, to yarage damuwa, yasan itama laila d'in nacan cikin damuwar rashinsa.

Murmushi kawai Galadima yayi, Dan yafara sabawa da yawan tsokana irinta Dr Erfan Fahad, akoda yaushe yanzu suna tare, idan kin gansu ba tareba to yashiga aikine, yakanbar Galadima a Office, Dan har yanzu ba'a shiga wajen Abie, awata na'ura suka sakashi dake taimakama ga66ansa motsawa a hankali, saboda allurar da ake masa duk bayan awanni 12, a koda yaushe saidai Galadima ya lek'ashi ta Window idonsa yakan cika da hawaye, Dan lallai ALLAH ne kawai zaima Abie hisabi dasu Alhaji Lawan tanderu bawai Alk'alin duniyaba.

Su Momma sunso zuwa amma Galadima ya dakatar dasu, Dan bayason suzo su d'orama Dr Erfan Fahad nauyi, shikuma maganar gaskiya a tsakaninnan aljihunsa yayi k'asa,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login