Showing 66001 words to 69000 words out of 365757 words

Chapter 23 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1466

ne yayi muguwar fad'uwa lokacin daya d'ora idansa akan k'afarta, sake had'e rai yayi , kana ya cigaba da tafiya,

yana tafiya tana binsa a baya,

har suka zo gaf da isa class d'in,

Kai ya d'an jinjina tabbatarwa da yayi class d'in sa zata shiga , hankalin shi na kan laptop d'inshi, hannunshi mai yin typing d'in ya d'an d'aga shi saman kafadarshi ta yadda zata gani, sanan ya had'e doguwar yatsarsa ta tsakiya da babbar yatsarsa ya kettasu sau d'aya ta yadda ya bada sauti, sannan ya had'e yatsunsa biyu ya kad'asu kamar mai buga fiyano ya mata nuni data tsaya inda take karta biyoshi,

batare daya juyo ya kalle ta ba bai kuma tsayaba yaci gaba da takunshi zuwa cikin class,

Itako Sanah bata gane abinda yake nufi ba,

dan haka taci gaba da binsa a baya,

Kai ya jinjina tare da yin gutun murmushi, mai dauke da alamar zaki gane kurenki,

kana ya cigaba da tafiya har suka k'arasa cikin class d'in,

Sanah tazo zata wuce mazaunin d'aliban, *"Keeh"* kamar daga sama sautin muryarsa ya ratsa shirun daya ratsa ajin,sai sautin takalminta dake amsakuwa, shirune ya sake ratsa ajin duk sunsha jinin jikin su, ita kuwa Sanah kai ta d'ago ta kalleshi ,Amman bata ga fuskarsa ba dan baya ya bata, sai gashin k'eyarsa da ta tsurawa ido ganin shi a kwance lub sai wani lauyewa a yayi ya bi k'eyan nashi yana Shek'i, tana cikin nazarin da me tayi mishi ta kuma jiyo muryarshi na ratsa ajin baki d'aya taji tajiyo muryarsa nacewa yana cewa, *"kneeling down,"*

ya fad'a still bai jiyo ya kalle ta ba,

juyawa tayi bayanta taga babu kowa sai ita kad'ai,

cikin mamaki ta kalli bayansa dan ita a iya saninta tasan ba'a saka Patick a jami'a.





Cikin mamaki ta kuma kallan bayansa,

batare daya jiyo ba taji yace *"ko bazaki kiyi bane?"*





Muryar dataji ta daki dodon kunnenta,

tasa gabanta mugun fad'uwa a razane ta kuma kallan bayansa,

babu damar taga fuskarsa saboda ya juya mata baya,

a hankali Sanah ta d'an zumb'uri baki kana tayi kneeling down d'in,

gaba d'aya students mamaki ya gama cika su,

duk da sun san halinsa, sun tabbatar zai iyin abinda ma yafi hakan,

dan sun san mari ko dizgi abu ne mai matuk'ar sauk'i a wajensa,

amma basu tab'a ganin yasa wata ko wani kneeling down ba,

sai yau kuma daganinta new comer ce,

students suka rink'a yin dogon wuya suna l'eka ta,

jin muryarsa ta fara explanations yasa duk suka shiga hankalinsu.



Sanah na nan har ya gama lecture tana ta zumb'ure-zumb'uren baki,

Cikin k'asaita ya fito zai tafi , ganin ya wuce ta gabanta amma bashi da niyyar ce mata komai,

yasa ta cewa *"Sir to ni wuni zanyi a nan ne? "*





Tsayawa yayi cak a inda yake,

kana ya juyo da fuskarsa a hankali ya zuba mata ido,

had'i da hard'e hannayensa a k'irji,

mik'ewa Sanah tayi batare daya bata umarnin tashi daga kneeling d'in ba,

kanta durk'ushe tana kakkab'e siket d'inta,

tana yin magana k'asa-k'asa, "eh wato kai zaka fece gidanku ni kuwa in zauna a nan, sai kace baiwar gidan ku ko, hegen k'eya! da nad'edd'en gashi."

dan ita a tunaninta ya tafi shiyasa ta d'anyi halin, baki ta murgud'a tare da mik'ewa tsaye,

d'ago kan da zatayi, keda wuya sexy eyes d'inta,

suka sark'e cikin na *SIR MOLI* dayake tsaye hard'e da hannuwa yana kallan ta..................









_Aunty AISHA ALIYU GARKUWA_

_kina tambayar inda nakai miki Sir Molinki to gashi nan na maido miki abinki_







~To fans masu tambayar ina nakai Sir Moli na b'oye har tsayin six years, gashi nan ya dawo~

~sai a cigaba da gashi a d'ora daga inda aka tsaya~





*_Typing=���_*







*_HASKE WRITERS ASSO...=ء�_*

_(Home of expert and perfect writer's)_









*_f&RAINA KAMA......!!f&_*

_{Kaga gayya}_









*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







=�I�<���1� 9�





.......Kallone ya koma sama yayinda kuyangin suka shigo cikin gidanmu, na d'akima tuni sun fara rige-rigen fitowa, baba k'arami da fitowarsa kenan daga sashensa yak'araso ga kuyangin, domin tambayarsu daga ina haka?.

Baiwa d'ayace tabashi amsa da fad'in basu kad'ai bane, masuyin bayanin suna waje.

Fita yayi sukuma suka ajiye kayan gefe suka kuma fitowa domin kwaso sauran.

Muna falo a zaune inna lami ta tsaremu sai mun sha romon wani nama da aka dafa k'anana, sai yatsine fuska mukeyi saboda rashin dad'in naman. shigowar Ahmad da Aryaan da gudu yasa mama Rabi'a tambayarsu lafiya?.

Ahmad yace  mama wlhy bak'ine da akwatina da yawa suka shigo .

Gaba d'aya muka zuba masa idanu, kafin wani yay masa tambaya a cikinmu mukajiyo sallamar baba k'arami.

Innarmu ce tamik'e domin fitowa, ganinsa da manyan mutane cikin alk'yabbu yasata fad'in  baba k'arami bak'i mukayi? .

Cikin washe baki yace,  wlhy kuwa maman biyu  .

Itama murmushine shinfid'e a face nata, tabasu hanya suka shigo falon, duk suka zazzauna.

Muduka muka durk'usa muka gaisasu, yayinda suka kuma gaisa dasu innarmu cikin mutunci.

Fita baba k'arami yayi yasa yaa Anas ya kunna Gen..... dayake babu nepa. Shikuma yakuma fita da hanzari domin nemawa wad'annan bak'i masu bazata kayan tarba, bayan yakira Dady da Abba ya Sanar musu.

Kaf matan gidanmu suka shigo, kowa yanason jin daga ina kuma.

Mukam d'akinmu muka koma muda su Ayusher muna hasashen bak'i daga ina haka? da gani dai kasan jinin sarautane, ko kad'an ban kawo Galadima a rainaba ma, dan narigada Na shafe labarinsa ni.



Suna cikin gaggaisawa da matan gidanmu saiga innaro tashigo, kai kace an wurgotane. baki tarik'e tana fad'in  o ni Marwanatu, manyan bak'i irin wad'annan surasa gurin sauka sai 6angaren Ai'sha? kuko bayin ALLAH daga ina haka?  .

Su aunty Mimi basu fahimci zancen taba, dan haka duk sai sukayi d'an murmushi, matan gidanmu kuwa kowacce tayi k'asa da kai dariyar mugunta Na cinta, Innarmu dai bata tankaba, hakama mama Rabi'a, sai inna lami ce tace,  yo inna in banda abinki waka hana rana fita idan lokacin fitar tata yayi? .

Kallonta innaro tayi zatayi magana baba k'arami yashigo da sallama, su Yaa Anas na biye dashi da kayan ciye-ciye nik'i-nik'i, bayan sun ajiye suka gaishesu cikeda girmamawa suka fita.

Zama baba k'arami yayi suka sake gaisawa, sannan yace,  kufayi hak'uri, mukam duk kun sakamu a duhu wlhy .

K'asaitaccen murmushi aunty Mimi tayi, domin dama papi yamata bayani akan komai na 6oye musu dasukayi. ta gyara zamanta sosai  Alhaji daga masarauta muke, munkuma zo kawo kayan k'anwatane Gimbiya munaya .



Kusan kowa dake falon saida ya waro idanu waje, domin jin furicin aunty Mimi, wasuma zuciyar tasu kad'an tarage tayo tsalle waje.

Aunty Mimi bata damu da yanayin nasuba tacigaba da fad'in  kuyi hak'uri fa, nasan nakuma sanyaku a wani duhun, mai martaba sarki Abdul'fatah da maimartaba sarki Jalaludden Abubakar, sune sukazo Neman auren yarinyar Ku Munaya wa d'ansu Galadima Muhammad Sameer Saifuddeen Abubakar, sun 6oye muku kansune saboda wani dalili, amma sun aikomu da sak'on ban hak'uri a gareku, yanzu dai mun kawo kayan lefen Munaya ne gasunan .

Jin jina kai kawai baba k'arami ke iyayi, bakinsa yakasa rufuwa saboda d'unbin farinciki da al'ajabin dake dank'are a zuciyarsa, yanzu nan daman manyan sarakunane agabansu a wancan karon sukazo Neman auren d'iyansu, lallai sun godema ALLAH dabasu aikata wani Abu Mara k'yauba agaresu, lallai ya yarda kwarjinin mulkine yasakasu mik'a Auren d'iyarsu ga mutanen dabasu saniba.

Ai su madam innaro sai aka zauna k'asa babu nauyi, muryarta har zuga take tace  ranki ya dad'e wai gaskene saboda ALLAH?, kokuwa wasa kikeyi? .

Murmushi aunty Mimi tayi, sannan ta kalli su Ummu hasheem da suma suketa murmushi, kallonta ta maido akan innaro,  hajiya kaka mizaisa muzo muyi muku wasa irin wannan akan magana mai muhimmanci irin ta aure, tabbas maganar nan gaskiyace, munama fata gobe idan ALLAH ya kaimu iyanzu Munaya tazama d'aya daga cikin zuri'ar masarautar gagara badau .

Innarmu da mama Rabi'a juna suka rungume suka fashe da kuka, yayinda innaro tamik'e ta callara gud'ar data jawo hankalin tawagar jama'ar 'yan biki, sai kawai tashiga taka rawa.

Dariya sosai tamaba su aunty Mimi, shi Kansa baba k'arami dariyar yayi yana girgiza Kansa da mamakin innar tasu mai kayan arzik'i Dana tsiya.

Matan gidanmu kam ba'a magana, kowacce tayi d'if takasa koda kwakwkwaran motsi, kowaccensu jitake tamkarma tafasa ihu take a nan.

Muryar gwaggon halimatu na rawa tace  wai da gasken dai Munayar gidan sarauta zatayi aure? .

 kwarai kuwa .  innaro tafad'a tana mata wani kallo,  jikata sai gidan sarauta, masu bak'in cikin kuma sai a mace .

Lallai maganar innaro tadaki zukatan dukkan matan gidanmu, Sanin halin innaro da baba k'arami yayi saiyace duk afita abama bak'i waje susha koda ruwane.

Jiki babu kwari sukaita Jan k'afa suna fita Su da danginsu 'yan biki da gud'ar innaro tajawosu shigowa. bak'in cikin kuwa k'arara a fuskokin wasunsu, maman su yaa hameed tayi taga-taga zata fad'i saida aka taryota.

Gwaggo Safiyya tace  lallai jama'ar gidannan yau ake *RAINA KAMA KAGA GAYYAFA* duk Wanda kake Kallon bai kaiba to tabbas watan watarana shine zai kereka, babu ruwan arzik'i da mugun gashi, Wanda yace shine to tabbas bashi baneba .



Su Ayusher suka shigo suna gumtsa mana, kallonsu kawai nakeyi amma badan na gaskataba, munubiya ta rungumeni ta fashe da kukan dad'i, kallonta kawai nakeyi nakasa koda motsi, to murnar Auren shekara d'aya zanyi? Kokuwa murnar Ashe galadimane mijin nawa? bawani can da ban ba kamar yanda muketa hasashe?.

Ban iya ta6uka komaiba wata k'yak'yk'yawar budurwa tashigo, daka ganta kaga wadda Hutu yagama ratsawa, babu shakka zamu iya zama sa'anin juna da ita, fuskarta d'auke da murmushi tace,  to ina amaryar Uncle Sam d'in? .

Feena ta nuna ni da hannu itama tana murmushi.

Gadon ta hayo batareda jiran abata iziniba, ta mik'amin Chocolates guda biyu tana kuma fad'ad'a murmushin nata.

Cikin mamaki muryata a sanyaye na girgiza mata kai nace  yar uwa namiye? .

Hannuna takamo tasakamin tana 'yar dariya,  inji Uncle Sam yace nabama matarsa, sunana Samha, d'iyar yayar Uncle Sam  .

Duk da mamakin daya cika zuciyata, hakan bai hani mata murmushiba, nace  nagode Samha .

Tad'an langa6e kai alamar itad'in shagwa66iyace tace ,  zan dai fad'ama Uncle Sam kin gode, lallai Uncle ya iya za6en k'yak'yk'yawar sarauniyar gagara badau mai jiran gado insha ALLAHU .

dariya su Bilkisu sukayi, nidai nakasa cewa komai, sai d'an murmushi danayi.

Ta dafa munubiya takuma fad'in inason twins sisters arayuwata, dan ALLAH nima kuna sona? .

Yanzun kam kasa daurewa nayi, nima saida na dara kamar yanda su munubiya ke dariyar, nakula ko kad'an Samha batada girman kai irinna 'ya'yan sarauta, sannan tanada surutu gaskiya .

Cikin shagwa6a ta langa6e kai gefe,  ALLAH da gaske nake kubarmin dariya, ina addu'ar ALLAH yasa nanda wata 9 aunty ki Haifa mana twins muma .

Amin su Ayusher suka amsa atare.

Matsowa tayi kusa dani tafara mana hotuna, nidai nakasa ma magana, lallai Samha akwai rawar kai, ta tubure da shagwa6a wai sainayi murmushi kamar yanda munubiya tayi, tanason taje tabama Galadima tagani kozai iya banbancemu. Babu yanda na iya dole na murmusa akayi, sannan mukayi gaba d'aya.

Bata bar d'akinba saida mama Rabi'a tashigo kiranta zasu tafi, aikam kamar tayi kuka, dan bataso tafiyarba, sai dai tace anjima zasuzo wajen brothers and sister's event.

Har k'ofar gida su Ayusher suka mata rakkiya, dan lokacin su aunty Mimi harsun fita, sunso ganina amma sukayi shiru kar aga kamar dawata manufa sukayi hakan, sun hak'ura tunda dai insha ALLAH gobe ina cikinsu.

Basuci komaiba dai a kayan da'aka jibge musu sai ruwa, dan haka baba k'arami yasaka aka bisu dashi mota, yace inhar ba wai bazasu iya cin cimar tamu bane to dan ALLAH suje dashi koda bazasuci ba su bada.

Godiya sukayi, suna mai yaba halaccin wannan gida mai cikeda karamci, dukda dai sunkula akwai lauje cikin nad'i gameda wannan family d'in, musamman yanda wasu suka kasa 6oye hassadarsu, aunty Mimi ta murmusa a zuciyarta tana fad'in Ashe ba masarautar mu kawai baceba keda irin wannan kitimurmurar ta family.

Mukulin farar motar da aka zubo akwatinan suka dank'ama baba k'arami sukace ta amaryace.

ai yanzu kam rasa abin fad'a baba k'arami yayi, yak'agara 'yan uwansa su dawo suga wad'annan tarin baiwa da hikimar ubangiji da yayma d'iyarsu, wadda akulum ake ganin mahaifiyar yaran a k'ask'ance acikin gidan, sai gashi tazama *RAINA KAMA.....*



Bak'i na tafiya gwaggo Safiyya tasaka aka baje manyan tabarmi a tsakar gida, aka fiddo akwatinan domin kowa yagani, makwafta duk sun shigo suma kam dan kar ayi babusu.

Gaba d'aya gidan yacike da shewa da hayaniya, tun anama irga kayan har aka bari, saibi da idanu, 'yan bak'in ciki kam sun kume waje guda, sai kukan zuci, wasuma kasa daurewa sukayi suka bar wajen.

Kasancewar su Ayusher duk suna can nashige toilet d'inmu nashiga raira kuka, nifa bammasan yanda zan fasalta muku yanda nakejiba wlhy.





&&&&



A 6angaren sister's d'ina kam su Safara'u harda kukansu, fauziyya ce kawai ta nuna farincikinta, dan har d'aki tashigo ta rungumeni tana ALLAH ya sanya alkairi.

maganar tashin hankali ga jama'ar gidanmu ba'a magana, sunma rasa yanda zasu masalta lamarinma, maman yaa hameed data kasa hak'uri saita saka masifa da zage-zage wai ai munafurcine su abbanmu suka shirya, wannan zancen k'aryane akwai magana a k'asa, 'yan koranta ma irinsu momy Hadiza suna tayata.

Nanfa gidan ya hargitse da hayaniya, kowa da abinda yake tofawa, innaro dai Abu biyune ya dameta, farinciki dakuma damuwar abinda tayita ma innarmu shekara da shekaru, yau kuma gashi ALLAH ya d'aga darajarta, ita dawanne ido kuma zata kalli Ai'sha.

Babu Wanda ya tanka a 6angaren innarmu, saima farinciki dasu mama Rabi'a ketayi abinsu, inna lami kuwa da aunty salamah sunata callara gud'a dawasu acikin matan anguwarmu, hakanne yakuma harzuk'a su maman Safada'u, suka murje idanu sunata zuba tsiya, danginsu na tayasu.

Innarmu dai tana daga cikin d'aki abinta, sai zuba murmushi take tana sharar hawayen dad'i, yau kokad'an rashin mutuncin 'yan gidanmu bai 6ata rantaba, saima wani farin ciki dasuke sakata.



>�#�>�#�

Maganar sisters and brothers event kam ai bai yuwuba yau, dan gidanmu gaba d'aya a harmutse yake, ga 'yan anguwa sunata turuwar zuwa ganin kaya harda mota.

Nikam ma zazza6ine yagama rufeni tunda nagama kukan, duk wannan kacaniya da akeyi ina cikin bargo k'udundune, su munubiya kam sunacan tsakar gida sun kasa sun tsare akan kayan gudun masu suruf bahana=��>�#�.

Da k'yar aka tartare kayan aka kaisu falon baba k'arami kasancewar magriba ta gabato, sai bayan isha'i su Abba da Dady suka gani, ranar Abbanmu shima saida yayi kukan dad'i, ALLAH Sarki Ai'sha, nagodema ALLAH da wannan babban al'amari yashigomin ta 6angaren tsatsonki, kema yanzu k'ya samu 'yancin kanki agidan mijinki, 'ya'yanki zasu samu 'yanci a gidan mahaifinsu, dama akance ka yarda da k'addara kakuma godema ALLAH a yayin da ya jarabceka, Ashe sharrin da akama d'iyarsa zai zame mata alkairine, sun had'ata da babban mutum domin 6atanci agareta dashi kansa Ashe zai zama sanadin alkairi a rayuwar yaranne, dan yasan inba dan wannan abin yafaruba ina Galadima zai ga munaya har iyayensa sunema masa aurrenta? hikimar ubangiji yawane da ita, yakan jarabeka domin kankare zunibinka, kokuma danya d'aga darajarka ta inda bakayi zato ko tsammaniba.







&&&&&&



Labarin tarbar mutunci dasuka samu tuni ya karad'e masarautar, wasu kam dariyama abin yabasu, ina wata tarba dazasu samu ga talakawa fak'irai. suna dai fad'ane dan kar amusu dariya.

Mama Fulani koda labarin yaje kunnenta saita ta6e baki tana murmushi k'asaita, Wanda ita kad'ai tasan fassarar kayanta.



Tsaf yagama shiryawa zaije sashen da aka sauke abokansa a cikin masarautar, dan babu damar saukesu a 6angarensa, saboda angama masa gyara tsaf amarya kawai ake jira, su aunty Mimi ma dasuka kai lefe sun Sanar da amaryarsu kawai suke buk'ata, basai su Abba sun wahalar da kansuba wajen kaita da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login