Showing 237001 words to 240000 words out of 365757 words

Chapter 80 - Raina Kama Complete Hausa Novel

11 Feb 2025

1490

Harun ba, domin ni alak'ar wucin gadice ta had'amu, k'iris ma ya rage ta k'are, saidai inason nabama y'ay'ana kamar yanda ka fad'a kariya koda sau d'ayane a rayuwarsu kafin na barsu, dan haka maida wuk'arka a kube, lokacin zareta baiyiba, sometimes kalmar Mahangi da mai hange takanyi kamanceceniya, dan bakowa ke iya rarrabata wajen fasaara ba, amma kalmomine duka masu harshen damo, wani k'alubalen saida tunanin mai zurfi, wata k'oramar ruwan mutanen dake zagaye da ita sukanyi imani bazata balle harta cisu ba, saboda sun yarda sud'in masuntane da kullum suke rayuwa cikin wannan k'oramar, abin mamaki saikaga wataran an wayi gari da mutanen da muhalansu duk wannan ruwan ya had'iyesu, abinda basu ganeba bakowacce irin alak'a bace ake kulla amana da ita, wani farin idan yashiga cikin fari banbance k'arkonsa saidai ALLAH .

Tashi nayi nai shigewata bedroom d'insa.



A fusace shima ya mik'e zai bini, kad'an yarage ya zubda farfesun dana ajiye masa, ALLAH dai ya kiyaye ya shallakesa ya wuce.

Hucin mutum kawai naji a bayana, hakan yasani waigowa da sauri, hannu ya dunk'ule zai kaimin naushi, nai azamar fad'awa saman gadon ina zaro ido waje, a lallai Abu ya girmama, nikuma miye nawa da zai sauke fushinsa a kaina? nai maganar a zuciyata.

Janye hannunsa yayi yana ciza lips d'in sa da k'arfi, idonsa dukya kuma rinewa, ya dunk'ule hannun ya daki d'ayan dashi, muryarsa har rawa take yace,  Miyasa zaki kuma hargitsan tunani ne? Minene laifin Harun shikuma? kuna nufin duk Wanda na yarda dashi shine mak'iyina? Kai impossible wlhy, Munaya wakikema aiki a kaina? ya rankwafo kaina, kaikace cinyeni d'anya zaiyi, saikace zaki yaga bandar nama, da k'arfi yace,  bazaki sanarmin ba saina k'arar da numfashinki ne waishin Ubanwa ke fad'a miki wad'annan maganganun da kike d'aureni dasu a ko yaushe?!!! . Ya k'are maganar cikin tsananin tsawa da k'araji.



Ba k'aramin firgita nayiba, badan karnayi k'arya ba danace har wutar bala'i Nagano a idonsa tana ci, wannan bawa akwai zuciyar tsiya, idan zai zama jami'in tsaro da k'asarmu ta amfanu da yawa.........

Da k'arfi ya girgizani, saboda ganin saboda rainin wayo tunanima na tafi..........

A firgice nace  yi hak'uri zauna zan fad'a maka . na fad'i hakanne dan kawai ina ganin itace mafitar dazan nema ya fasa had'iyeni. a mamakina kuwa saiya tashin ya zauna yana dafe k'irji hawaye nabin kumatunsa.

Tsantsar tausayinsa ce ta kamani, na tashi na d'akko ruwa na dawo kusa dashi na zauna, addu'oi na shiga tofawa a ruwan, yana zaune dafe da kansa, da alama kuka ma yakeyi, dan ajiyar zuciyar da yakeyi ta yawaita.

Saida na gama na dafa ka fad'arsa, tamkar bazai d'agoba saikuma ya kalleni, ruwan addu'ar na basa, babu musu ya kar6a ya shanye, duk da baima san mita bashiba, idanma poison ne dai gara ma yasha ya mutu ya huta.

Mintunansa biyu zuwa uku dasha yafara sauke ajiyar zuciya mai k'arfin gaske, saiya zame kuma ya kwanta, kafin kacemi barci ya saceshi a haka.

nima ajiyar zuciyar nayi ina girgiza kai da share hawayen dake silalomin, ina rok'on ALLAH ya kawoma wannan bawan nasa sauk'i da rangwame cikin gaggawa da warwarewar al'amura.

Dagashi har yaran tausayi suke bani, nayi zurfi a tunani wayarsa tayi ring, kamar zan share saikuma Na tuna maybe Momma ce, tashi nayi zuwa inda wayar take, aikam dai itace, nayi picking jiki a sanyaye, dan tunanina kota gamajin komai, amma sainaji sa6anin haka, da y'ar raharta ma tace,  Muh'd duk hidimar sunance haka? .

 Uhm Momma bashi bane nice .

 a'a d'iyata kece? .

 eh Momma, kuna lafiya? ya jikin Abie? .

 Alhmdllh d'iyata, ya k'arfin jikinki kema? ina yaran? .

Gabana ya fad'i, Na had'iye wani yawu da k'yar, cikin in ina nace,  lafiyar kowa k'alau Momma, shima y... yana barcine .

Dagacan Momma ta murmusa tana gyara zama a harabar asibitin, dan batason Abie yaji wayar da zatayi, tace,  humm d'iyata kema 6oyemin zakiyi kenan? yanzu koda mutuwa yaran sukayi dashi kansa kowama saiya shiga fargabar gayamin? .

Na had'iye yawu dak'yar,  kiyi hak'uri Momma, ki gafarcemu https://2gnblog.blogspot.com/.

 Bakumin laifin komaiba ni, hakan da Muh'd yay shine dai-dai, dan lokaci yayi dazai daina zama jiran sak'on mak'iya ko zuwansu, shine yakamata ya fita farautarsu domin kawo k'arshen komai, na yarda dake 100% Munaya, nakumayi imani insha ALLAH kece zaki sauyamin yaro daga k'uncin dayake ciki zuwa farin ciki, tamkar yanda Na fad'a miki tun farko karki ta6ama Muh'd sanya ko nuna tsoronsa, lokacin dazaki kwantar masa dakai kizama kowacce irin mace a agidan mijinta har yanzu baiyiba, kada ciwonsa yasakaki fargabar fad'a masa gaskiya, rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne, ko ayanzu Muh'd yabar duniya bazanyi bak'in cikiba, domin ya nuna musu shi jarumine, kuma ya haifi wad'anda zasu iya zama magadansa su sauya komai koda ba'aso, nanda kwanaki biyu komai ya gama lafawa ki tabbatar kin masa maganar tafiya wanka gida, wannan shine target d'inmu Na k'arshe akan rayuwar zaman aure na dindin, kowacce irin birkicewa zai miki akan bazaki jeba, kema ki birkice masa, dan nasan abinda yafaru zaisashi dagewa akan yaran bazasuyi nesa dashiba, idan kuma har aka cigaba da tafiya a haka, kowane irin dana Sani zai iya biyo baya . Momma ta share hawaye dake kwarara a idanunta, taci gaba da fad'in  ALLAH yayi miki albarka Munaya, dake da abinda kika haifa, yanda kikamin biyya wajen k'autata kar6ar Abu mai wahala (duk da bani na haifekiba) kema ALLAH yasa y'ay'anki sumiki biyyaya fiye da wannan, ALLAH yasaka hannu adukkan lamarinki keda mijinki da sauran y'an uwansa, nusar dashi abinda duk baki gamsu dashiba shine zai rage ma zuciyarsa baraza, dan tarawar yagani a lokaci d'aya shine mafi had'ari Munaya, zuciyarsa zata iya bugawa a lokacin, kiyi hak'uri nasan bak'yajin dad'in zama da Muh'd ko kad'an, domin ni kaina mahaifiyarsa wataran gaza gane kansa nakeyi, amma inaji a jikina akwai sauyi maiban mamaki dazai zo ya rusa komai, ki sameshi fiyema da yanda kikeso, ALLAH yayi muku albarka, idan ya tashi ki kirani naji ya jikin nasa .

Bata jira nayi magana ba ta yanke wayar, da alama kukane yaci k'arfinta. nima saina fashe da kukan ina kallon Galadima, insha ALLAH zan cikama baiwar ALLAHr nan burinta, koda ace mun rabu dashine, dan maganar gaskiya bazan iya rayuwa da mutum murd'ad'd'e mara yarda irin Galadima ba, labarinsa kawai kukeji, amma halinsa saika zuna dashi, Mara hak'uri zai iya gundurarsa ne cikin awanni biyu kawai, dan zaka dinga kallonsa a matsayin mai wulak'anci ko dizgi, girmankai da sauransu. Na sauke ajiyar zuciyarsa ina maida kallona ga Abdurrahman dake motsin tashi, nasan dukansu saisun tashi inhar d'aya ya tashi, saina lalla6a na kwanta kusa dashi na saka masa nono a baki.





********************



Har akayi la'asar Galadima bai farkaba, Nuren yazo shida Sauban, da Saleem har sau biyu suka iske yana barci, hakama Mom da inno da mama Fulani. Gashi su inno 4:30pm zasu wuce ma, laraba tazo tama yaran wanka, dan tuni sun farka, Nima nakumayi sannan naci abinci, kaina ciwo yakemin sosai, dan haka Sauban yafita ya samomin Magani nasha na kwanta, munyi sallama dasu Mom, zasu dawone kawai idan Galadima ya farka kafin su tafi. yaran kam duk d'insu suna can an kaima papi su tun d'azun.

Nidai barci yay awon gaba dani, daga nankuma bansan wainar da aka cigaba da toyawa ba a gidan.





*******************



Bayan la'asar kad'an Galadima ya farka, ganin shi kad'aine a d'akin ya tashi zaune bakinsa d'auke da addu'ar tashi barci, jin k'irjinsa yayi sakayau yasaki babu nauyin kamar d'azun, saidai abinda ba'a rasaba, yatashi zuwa bathroom yay wanka da alwala.

Sallan zuhur da la'asar ya rama, tareda addu'ar neman sauk'i akan wannan lamari da samun k'arfin zuciya, dolene saiyayi yak'i da dukkan abinda zai zama makamin barazana a agaresa inhar da gaske aikin zaiyi, falo ya fito bayan ya kimtsa, zamansa da mintuna baifi 2 ba saigasu inno.

Basu jira isoba suka shigo, a zatonsu yana bedroom yana barci, sunsan Munaya kuma tana d'akinta tana barci tunda daga can suke. ganinsa a zaune ya saka fuskar kowannensu fad'ad'a da murmushi. Shidai kallonsu kawai yake d'ai-d'ai.

Inno ta mangari kansa tana fad'in  ja'iri baka sanmu bane halan? .

Hannunta ya rik'e yana kallonta, cikin maganarnan tasa ta k'asaita yace,  Inno wai ina zakuje ne? .

 inda muka fito mana . Inno tafad'a tana zama kujerar kusa dashi.

 saikace wad'anda ake kora? .

 A'a wazai koremu nida gidanmu, komawar dai ne yafi cancanta, dan takawa ma yace a gaisheka basai ya shigoba, zakuyi waya, idan ka murmure kaje yana nemanka .

 To shikenan ALLAH ya tsare hanya, mun gode sosai da sosai .

 Amin inno tafad'a tana shafa kansa ta ciga da kwararo masa addu'oi shida matarsa da yaransu, falon kowa tana amsawa da amin, itama mom tayi nata.

Yace,  mom hada ke wai? .

 eh mana Sameer, zaman mi zanyi to? tunda ALLAH ya iyakance komai cikin sauk'i, nanda y'an kwanaki kuma basai na zagayo naga masu jego ba da jikin naka, a dai dunga kulawa sosai, gasu laraba nan da bayi 2 anbar muku, dukdai wata kulawa insha ALLAH zasu taimaka wajen badata akan yaran, dan yakamata dukkan bayi da kuyangin sashen nan naka ka sallamesu kawai .

Kansa ya jinjina mata alamar amsawa.

A gurguje sukad'an kuma tattaunawa da kwantar masa da hankali suka fito, dukda yaso musu rakkiya suka dakatar dashi. Abincin da mom ta zuba masa takumace yamata alk'awarin zaici ya dage yaci sosai, sannan Sauban daya dawo rakkiyarsu d'auke da y'an uku shida bayinnan biyu yabashi magani yasha, kar6ar Amaturrahman yayi, Sauban kuma na zaune dasu Abdurraheem yana musu wasa wai dole sai sunyi dariya, (nace,  aiki jaa kenan, inba dariyar k'udaba ta jarirai idan suna barci keyi aiko ka dad'e baka ganiba Uncle triplets=��).



Galadima ma madai yatsansa d'aya ya saka cikin hannun Amaturrahman yana wasa dashi, dukda idonsa a lumshe yake ya jingina kansa da kujera, maganganun Munaya na d'azun kawai yake nazari dalla-dalla.

Ana cikin haka Samha tayi Knocking, Sauban yace ta shigo, saida ta gaida Galadima damasa ya jiki.

Ya amsa mata batareda ya kalleta ba, tareda tambayarta Khaleel fa?. Tace,  yana 6angaren Ummu hasheem .

Baice komaiba, itama ta k'araso ta d'auki Ammaurrahman data rik'e yatsansa gam tak'i saki..

d'agowa Galadima yay yana kallon yarinyar, Samha dai dariya takeyi, har Sauban shima ya farga da abinda ke faruwa ya shiga tayata. Galadima ya zare yatsansa yana murmuahin gefen baki da lakatar hancin Amaturrahman.



Har Magriba suna nan sun shashance akan yaran, yayinda Galadima ke zaune yanata cud'awa da tantancewa, lokaci-lokaci yakan kallesu dagasu har yaran. Tunda ya tambayesu Munaya sukace tasha Magani tana barci bai sake tambaya ba.





********



Ban tashiba saida suka fara kuka, a time d'in har magrib tama wuce, nagama shayar dasu na lek'a Galadima, na iske doctor jalal tareda Dr Yaseen da Akash Wanda yake shirin komawa gobe, sai Muftahu da Nuren.

Muka gaisa dasu suka kuma tambayata jikinsa? na Amsa musu da Alhmdllh. fitowa nayi na barsu, da aka kawo mana abinci ma can nace akai musu, Sauban yazo ya kwashi yaran bisa Umarnin Galadima, doctors zasu kuma duba lafiyarsu.





&&&&&&



Tunda Harun ya fita saiya kira wata Number lokacin daya k'arasa d'akinsa, dukkan abinda ya faru ya labarta mata, daga can tace k'aryane bahaka akaiba, ita an sanar mata lallai da Galadima aka kar6o yaran, babu wasu police, amma itafa kamar tafara saka alamar tambaya akan wannan ficikar matar tasa.

Harun yace,  haba dai, wannan y'ar yarinyar mizata iya, akwai dai abinda bamu saniba, yanzu dai kibari zamuyi maganar daga baya, zand'an bincika yarannan danni na lurama kamar ba wad'anda muka saka bane sukayi aikinnan? .

 sunefa gaskiya, abinda dai na lura dashi sun had'a aikin da wasune, shiyyasa suke 6oye mana Kansu, tunda kaga mudai baiwarnan bamu muka sakata ba, amma shi namijin yana cikinsu, nasan sunyi luff ne sai k'ura ta natsa su fito .

 ok shikenan to, zandai sake bincikawa, dan Sameer yanada wayo, shiyyasa naso bugar cikinsa akan batun, amma wannan shegen k'asaitar tasa ta rainin hankali ya hanashi tankamin, sai matarce ke bani amsa ..

 karka damu zamu sauke masa shine ai ...............
'<���











>�#�abin dariya, ku a naku zaton yaranku sun 6oye Kansu be?, to suna hannun Galadima, lafiya kawai muke jira ya samu ya yagalgalasu kuma ya cafkoku munafukai=�D�=��.















*_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*=�-�=�O�<���

*_typing=���_*





=ء� *_HASKE WRITERS ASSO....._*





*_f&RAINA KAMA.....!!f&_*

_(Kaga gayya)_







*_Bilyn Abdull ce>��<���_*







~Book 2~ =�I�<���2� 9�





..............Harmun kwanta zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason naje naga halin da yake ciki, Dan koda su Nuren suka wuce ban komaba, sakkowa nai daga kan gadon, laraba dake a tsakar d'akin kan katifa tace,  ranki ya dad'e lafiya kuwa? .

Banason ta kalli abun da wata manufa, dan haka nad'an murmusa,  uhmm iya inason duba Abbansu ne, ban saniba koyasha maganinsa kafin ya kwanta .

 eh lallai hakan yanada k'yau, badan ma jego ba ai bai kamata ya kwana shi d'ayaba .

 aiba shi kad'ai baneba iya, Sauban ne zai tare dashi  .

A to hakan yayi.



Bance komaiba Na kar6i gyale wajen Samha Na saka na fita.

Masarautar tayi tsit, da alama kowa yasamu nutsuwa a sashensa, ban tsaya knocking ba na shige kawai, a falo na iske Sauban zaune yana kallon ball, cikin tsokanar da ya iya yace, aunty gimbiya kin kasa barcine? .

Nayi murmushi,  yaa Sauban matarka taga ta kanta wlhy .

Dariya yayi kawai, nikuma na wuce abina.

Saida nayi sallama kusan uku banji an amsaba, saina shige kawai. Zaune na iskeshi a bakin gado ya jingina da fuskar gado, hannunsa d'auke da Qur'an yana karatu a hankali, idonsa cikin medical glasses, gakuma system a gefe itama a kunne. naji dad'in yanda na sameshi, Addu'a da karatun Qur'an babban jigone dake wanke zuciya da damuwar d'an Adam (duk lokacin da ranki ya 6aci d'auki Qur'an ki karanta koki saurara, wlhy zakuji sassauci mai yawa).

Har zan juya na fita sai naji yay gyaran murya, juyowa nayi na kallesa, har yanzu dai karatunsa ya keyi. na dawo na zauna a bakin gadon ta d'ayan gefen, shikuma ya cigaba da karatunsa, kusan mintuna 6 kafin ya rufe Qur'an d'in ya ajiye, ya cire medical glasses d'insa shima ya ajiye yana kallona, ko kad'an fuskarnan babu walwala, nuni yamin da inzo.

Ban musaba na tashi nadawo 6angaren inda yake, zama nai d'an nesa dashi kad'an.

Ya lashe le6ensa da cizarsa kad'an yana hard'e hannayensa a k'irji.

Muryata can k'asan mak'oshi nace,  yaya jikin? .

Kansa kawai ya jinjina min cikin lumshe ido, sannan ya motsa baki kamar zaiyi magana saikuma yay shiru, saida yaja wasu seconds sannan yace,  Munaya!? .

 Na'am . Na amsa ina kallonsa da janye idon lokaci d'aya saboda ya tsareni da nasa.

Huci yad'an furzar, ya cire hannayensa daga k'irji yana gyara zama,  Nayi nazaci sosai akan maganganun ki na d'azun, nakuma fassarasu aji-aji, na fahimcesu a yanda tawa fahimtar take, so a wannan karon rok'o nake miki na k'arshe akan ki fad'amin abinda kika sani, ni d'an Adam ne, ban isa cewa komai na sanshi a rayuwaba ko na iyashi, sai abinda Ubangiji yaso in sani kawai, Munaya ada ba haka rayuwata takeba, mutumne ni mai yawan raha dason nishad'i, amma daga lokacinda nafara sanin kaina da matsalar mahaifina sai komaina ya canja, nazama mutum mai yawan rashinson magana, nafison kullum na kasance ni kad'ai a kuma ke6antaccen waje yay murmushin takaici sannan ya cigaba da fad'in  Bawai hakan Na birgeni baneba ko a San raina, saboda Ina shiga k'uncine, amma banida za6in daya wuce hakan. nasha wahalhalu Na rayuwa kala-kala kafin na tsaya da k'afafuna, zuciyata ta bushe namance daga wane tsatso na fito,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login