Showing 27001 words to 30000 words out of 281271 words
daya rage ta saka shi a na hagu sannan ta fita kafarta babu talkami daman can bata da su gaba daya ko ma akwai bata damuwa ta saka, wata mahaukaciyar rayuwa take da babu mai burin yin irinta.
Waje ta fito gaba daya ta murza idonta so that ko da akwai kwantsa ta fita ba tare da ta wanke ba, gurin da ta saba zuwa ta ci yayan itatuwa ta nufa kamin ta karasa ta hango mutane sun doso inda take da sauri irin na wadanda aka bawa umarni, ganin haka ya saka taja ta tsaya domin mutanen na gidan Sarki ne dakarunsa ne ba gama garin mutane ba, ko ba a fada mata ba ta san laifi ta yi domin ba kasai Sarkin zai sa a kirata ko zo masa da ita ta sunan su gaisa ba sai idan ta yi laifi.
“Fada ta yi kira, Sarki yace a zo da ke”
Bata ce musu uffan ba, ta kai ta taba hannunsa in 5 seconds ta ga abun da ya faru a fada kamar a gabanta aka yi komai.
“Ban kashe shi ba”
“Mu yan aike ne kawai”
Dayan ya amsa mata, sai ta yi baya baya alamar ba zata je ba, domin zuciyarta bata raya mata komai sai cewar ita ma kasheta za'ayi kamar yadda ta ga gawar saurayin da yayi mata magana jiya a fada matacce. Kai ta girgiza musu alamar ba zata je ba, su kam daman can musu da jayayya ba na su ba ne sai abun da Sarki ya fada, sai suka juya domin sanar da Sarkin yunkurin Waira na cewa ba zata je ba kamar yadda ta yi musu alama. Waira na ganin sun bace sai ta juya ta fara gudu zuwa bayan gari can gurin manyan duwatsun da Eid ya taba kaita, tana gudu tana kuka har ta isa, sai da ta isa ta boya bayan wani dutse tana tuno abun da ya faru jiya, sai ta sake fashewa da kuka, a rayuwarta babu abun da ta tsana kamar mutuwa, domin ta san duk wanda ya tafi be dawo ba, kuma ta san halin Sarki da tsananin hukunci kuma ba ya yafewa kowa musamman idan zalinci ne aka yi. Mikewa ta yi tsaye ta fara tafiya tana sauka ta gafen garin tun tana yi a hankali har ta fara sauri tana hadawa da gudun, duk da ita da kyamar ruwanta sai gata ta saka kafarta ta gafen da ruwan be da yawa ta tsallaka ta fara ratsa dajin dake gurin tana gudu, har da faduwa take ta tashi ta jefa kafarta can ta cire ta saka a nan bata damu da ciwon da ta ji a kafa ba ita dai burinta ta bar garin gaba daya....
EID POV.
Eid dake tsaye cikin fadar yana jiran Dakarun Sarki su dawo tare da Waira da Sarkin ya ce a zo da ita ko ta halin yaya bayan sun shaida masa abun da ta fada. Ya daga kafarsa da ya ji tana masa mugun zafi alamar jin ciwo ko taka wani abu, yana dubawa sai ya ga jini. A take hankalinsa yayi matukar tashi.
“Waira...”
Ya furta numfashinsa na karo da juna, juyawa yayi da sauri domin zuciyarsa na raya masa dakarun sun ji mata ciwo a kokarinsu na kawota, sai tukunyar layun mai cike da kayan tsafi dake fadar ta fado ta fashe, ba shi ba gaba daya yan fadar mikewa suka yi tsaye har Sarki suna kallon tukunyar domin fashewar tukunyar na nufin wani babban lamari. A take Sarkin ya saka a fara bincike abun da ya faru, tsohuwar dake gaban tukunyar ta mike tsaye da sauri ta fara guda da halshe da ya rabe biyu kamar macijiya, ko'ina na fuskarta wuri ne aka yi mata ado da shi ba kuma ado irin na kwalliya ba, ado ne na tsafi domin sai da aka tsafe wurin sannan ta saka su a fuskarta.
“Yau dandanon azabar rai ta tabbata ga mai butulcewa Sarki, mai gudu ya bar garin tsafi, mai yunkurin karya dokokin garin Garuk, yaryaryar...... Karkarkar.... Farfarfar Waira ta gudu kafarta ta taka wata kasar da ba ta garin nan ba, hancinta ya shaki iskar da ba ta garin Garuk ba, lelelelelelelelelelelelelelelele hasara ta tabbata ga tsatson Kusan....”
Tsohuwar na maganar Eid na jin zuciyarsa na rawa kamar zata fado tsabar tsoro da zuwan labarin ba ga tatatan, a take ya ji yawun bakinsa sun kafe kansa ya fara tsawa, kamin ya ji kamar bakinsa ta bugu wani abu, sai jini ya samu hanya. Hannu ya kai ya taba bakin ya duba sai ya ga jini, ya juya da sauri sai Sarki ya daka masa tsawa.
“Waira ta tsallake iyaka, babu wanda zai je ya dawo da ita, babu wanda zai taro ta, wannan doka ce, ita zata dawo da kafarta”
Sai da suka fadi kasa kamar za su masa sujada domin girmama umarninsa da nuna tsantsanr biyaya a gareshi, ban da Eid dake tsaye yana kallonsa domin ya san hukuncin da Sarki ya shar'anta idan har ta bar garin kasheta za'ayi.
AMEER POV.
Ko da aka yi azahar ya bar garin Abuja, gudu yake kamar wanda baya son ransa, yana overtaking any how irin shi ya shiryawa mutuwa a yanzu saboda mahaifinsa ya bata masa rai. Sai da ya isa Kano sannan ya rage gudun da yake, ya shiga wani Shagon siyar da kaya dake bakin hanya, yana dubawa ko zai samu tufafin da za su masa, wani kallo tsana yake yi ma tufafin domin ba a'adarsa ba ce saka tufafi mai karamin kudi, duk wani abu da karamin mai arziki ko talaka zai iya sakawa sai ya ji cewar ba sa'arsa ba ne. Hakan nan dai ya daure ya siya kayan da suka ci kudin da ya kai 20k riga da wando, sannan ya fito ya shiga wani Babban shago ya siye biscuits da lemu sai ruwan da ya san za su ishe shi har ya isa inda zuciyarsa zata raya masa.
“Ina zan samu Carpet a nan?”
Ya tambaya daker domin mutane haushi suke ba shi, wani yayi masa kwatacen inda zai samu carpet dai ya nufi can ya siye karamin Carpet domin ba su da na sallah, shi kuma be ji zai iya sallah da na Nimra da ya gani a motar ba, domin be dan waye yayi sallah da shi ba.
Cikin garin Kano ya shiga ya sauka a wani babban Hotel da dollars yayi amfani ya kama daki, bayan ya bada key din motar Nimra da sunan a bada masu wankin mota na Hotel din su wanke masa ita saboda kyamar ta take tun da ya kamo hanya, duk kuwa da kasancewar be ga wani abun kazanta a ciki ba, sai dai taba sitiyarin da Nimra ta yi shi kuma ya bata yana jin kyamar kansa domin be san iya abun da ta taba ba kamin ta tuka motar bayan ita be sani ba ko wani ya tuka motar ma. Yana shiga tufafin jikinsa ya fara cirewa ya shiga be yarda ya taba tawul din dake Hotel din ba, shi dama be tana amfani da kayan kowa ba sai na shi, idan zai yi tafiya be san wahalar neman komai ba sai dai a hada masa, har Hotel ko gidan da zai zauna nema masa ake, haka ya shiga dakin wanka yadda zai kai hannunsa ya taba shower ma wani abun kallo ne, domin kyamar komai yake na Hotel saboda sanin da yayi kowa zai iya zuwa ya kama dakin ciki har da kare da akuya da tinkiya ko jaki.
“Miyasa Daddy zai min haka”
Ya fada yana jin duniyar ta juye masa gaba daya saman ya dawo kasa, kasan kuma ya koma sama, yamma ta zama kudi arewa ta zama yamma, ransa be kara baci ba sai da ya shiga wankan ya tuna be siyo soap ba, wani mugun tsaki yaja ya ji kamar ya fashe komai dake cikin bathroom din, a dole ruwa kawai ya watsa ya wanke jikinsa yayi alwala ya fito ya saka tufafin da ya siya ya bar nasa a gurin ya dauki kudin da rikonsu dole kawai suka zame masa da Atm ya saka aljihu sannan ya dauki wayar da Nimra ta bashi, Hotonta ne shimfide saman screen din wayar tana murmushi ta sha kwalliyar zamani har ta sauya kamanni. Samun kansa yayi da tsayawa kallon hoton sannan ya saka wayar aljihu ya dauki ledar biscuits dinsa da lemu ya fice daga dakin.
A dole gurin hutarwasu ya tsaya bayan ya fito Masallaci yayi sallah, sai da aka gama wanke motar aka goge sannan ya shiga, ya kama hanya, be bar garin Kano ba sai da ya siya Soap da yawa ya wasu abubuwan bukata ya zuba a motarsa, shagon da ya siye kayan ba su karbi dala ba sai ATM ya ba su suka cire kudinsu, sannan ya kama babbar hanyar fita daga Kano ba dan ya san garin da zai tafi ba. Yana tukin yana cin biscuits da lemun da ya siya, not his regular biscuits da lemu sai ya ji tas din wani iri ba irin wadanda ya saba ci ba, sai dai ba laifi wannan ma yana da dadi.
Hakan wata zuciya ke raya masa ya koma garin Kano ya shige gidan Hajiya Jamila yayi zama, sai kuma ya ji ba zai iya ba, a ganinsa ita ma ai saboda mahaifinsa ya santa, after that kuma zata iya fadawa mahaifinsa cewar yana gurinta, a yanzu be bukatar wani abun da ya shafi mahaifinsa. Driving kawai yake heading to Katsina ba dan yana da kowa a garin ba, ba dan kuma ya san kowa ba, Impact ba dan yana sha'awar zuwa garin ba sai dan ba shi da gurin zuwa.
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
_Na Khadeeja Candy_
🔟
Namra ta matsa kusa da ita ta karbi wayar ta duba hoton, sai gata suna kallon kallo ita da Nimra, sai a yanzu Namra take tuna ta sha ganinsa a media amman how come ta ganshi a fili bata gane shi ba. Nimra ta yi baya ta zauna saman kujera ba tare da tace komai ba, Namra shiru ta yi gudun kar ta furta abun da zai saka jefa yar'uwarta cikin matsala, domin idan Ummi ko Abiey suka san cewar ta bashi motarta za su yi mata fada sosai.
Ummi da wani abu mai kama da kashi ya tsoki kahon zuciyarta saboda ambatar sunan Ameer da na mahaifinsa da Mahmood yayi ya saka ta kasa zama ta kuma kasa motsawa zuciyar sai ciwo take mata.
“Ummi”
Namra ta kira sunanta ganin yadda ta tsaya kamar hoto, da sauri ta kalli Namra irin kallon kamar bata cikin hayyacinta, wani abu take ji mai kamar kuka kuma ba kukan ba, ba zata iya kiran da damuwa ba, haka kuma ba almara ba ce, wata kila mamaki take na sunan da ya zo daya, wata kila kuma wani bangare na zuciyarta gaskiya yake fada mata cewar Ameer dinta ne. Ko shiyasa Abiey yace a bar magana sun yi solving matsalar da mahaifinsa.? Daker ta iya tara yawun bakinta ta jika makoshinta sannan ta juya ta cira kafarta da take jin kamar ta shekara bata taka ta ba, ta fara tafiya.
“Ummi lafiya”
Mahmood ya tambaya domin hankalinsa yana gurinta, Nimra kam nata hankalin yana can gurin wani tunanin na dabam.
“Na'am”
Ummi ta amsa sannan ta juyo ta kalleshi gaba daya a rikece take irin rikicewar abun da kake tsammani ko tsoron ya faru, irin rikicewar wanda hankalinsa ke daf da gushewa, ba kuka take ba sai dai kana kallon fuskarsa kasan akwai tashin hankali a zuciyarta da fargaba.
“Lafiya”
Ya sake tambaya hakan ya hanyo hankalin Namra gareta, Hajiya Zahra ta kasa cewa komai kallonsa kawai take amman hankalinta da tunaninta suna wata duniyar ta dabam, ba tare da ta sake ce masa komai ba ta juya ta fara takawa suka bita da kallo har ta haye sama ta shige dakinta. Sai ta maida kofa ta rufe ta nufi gadonta ta zauna kwakwalwarta na tuna mata da abubuwan da suka faru a baya, yayin zuciyarta take soyuwa da kuskuren da ta aikata. A hankali Namra ta turo kofar dakin ta shigo rike da jakar Hajiya Zahra da wayarta da ta bari a falo.
“Ummi ga wayarki da jaka”
Wannan karon tana dagowa sai hawaye suka sauko mata, a sanyaye Namra ta ake jakar saman gadon ta zauna kusa da ita.
“Ummi lafiya?”
Sai ta yi saurin share hawayenta.
“Tsoro nake kar..... Kar.... Kar... Yaron ya sake yi ma Maleek wani abu....”
Ta fada ba dan komai ba sai dan ta kawar da tunanin Namra akan hawayenta.
“In shaa Allah ba zai sake ba, ko da ba a hukunta shi ba ai ya tsorata da yadda aka dauki abun da muhimmanci kuma kin ji har mahaifinsa ya kore shi”
Ummi ta juyo wasu hawayen na taruwa a fuskarta ta rike hannun Namra.
“Toh idan ya fada wani halin fa, nuna min hotonshi Namra”
“To koma minene ai shi ya jawa kansa, kuma hukuncin da mahaifinsa yayi zai saka dole ya kiyaye gaba”
Ta fada tana daukar wayar Ummi ta shiga google ta kama hotonsa ta nuna Hajiya Zahra. Hannu biyu Hajiya Zahra ta saka ta karba kamar wanda aka bawa sakada, gabanta na wani irin bugawa da ya wuce kima kanta har sarawa yake, hotuna ne da yawa a zube ko wane da kalar style dinsa, hannunta na rawa ta saka yatsanta ta taba daya sai ya bude a babban hoto, zaune yake akan kujera ya saka kananan kaya wando da riga ya dan karkata fuskarsa kadan ya kalli wani wajen dabam. Kamanin Deen ta gani zube a fuskarsa ciki har da hade rai da haske.
“Da gaske sunansa Ameer? Kuma dan Mr Bashir ne?”
Ta tambaya.
“Ummi gashi ma kina gani a rubuce”
Namra ta amsa mata tana kallonta, sai ta daga kai ta sake girgizawa. Tun tana kallon hoton da kyau har ta koma bata ganin komai sai duhu hannu ta saka ta fara shafa wayar.
“Namra Hoton ya bata, dawo min da shi na sake gani”
“Ummi ai kin jika wayar da hawayenki ba zaki iya gani ba”
Sai a lokacin ta san hawaye ne ya rufe mata ido take ganin duhun. Hannu ta saka ta share amman suka ki tsayawa tana kokarin ganin bata yi kuka a gaban Namra ba amman abun ya ci tura har sai da ta fashe da kuka mai karfi, ta saki wayar hannunta ta saka hannayenta ta rufe fuskarta.
“Subhanallahi Ummi lafiya?”
A take hankalin Namra yayi matukar tashi, sai ta rumgume mahaifiyarta tana rarrashinta, can kuma ta sake ta mike tsaye ta fice daga dakin da sauri, bata dade ba ta dawo dakin tare da mahaifinta Nimra da Mahmood suka shigo daga baya Maleek ya shigo dakin ya tsaya jikin kofa ya rumgume hannayensa, yana kallon Namra dake fadawa Abiey abun da ya faru.
“Ummi ta cika daukar komai da girma, ko karamin abu ne sai ta dauka ta saka a ranta”
Maleek ya fada, duk a tunaninsu saboda abun da ya faru ne take kuka ban da Abiey da ya san dalilin kukanta.
“Ku fita waje bari na yi magana da ita”
Fita suka yi daga dakin cikin damuwa, ko a tsakaninsu wani ya shiga damuwa damuwa suke da Matsalarsa balle kuma uwa kamar Ummi. Sai da suka fice sannan ya zauna kusa da ita ta kalleta da duba na tsanaki da natsuwa ya ce.
“Wannan kukan duk na minene? Na fada miki an yi solving matsalar nan komai ya wuce, kuma na miki alkawari iri haka ba zai sake faruwa ba”
Sai a lokacin ta samu damar dago kai ta kalleshi da jajayen idanuwanta.
“Abiey ka san yaron nan?”
“Ni ban taba ganinsa ba”
“Amman kasan mahaifinsa?”
“Aa na dai yi magana da step mother dinsa”
Ta hade kuka daker.
“Mahmood.... Mood.... Ya ce dan Mr Bashir ne kuma yan Kano ne”
“Eh haka ne, mun yi magana da ita kuma ta tabbatar mana cewar ba zai sake ba”
Ta kai hannu ta dauki wayarta ta bude ta nuna masa hoton Ameer, karba yayi ya duba.
“Oh shi ne wannan yaron kamar mai natsuwa, Allah ya shirya na fadawa Maleek kar na sake ganinsu tare”
“Ranka ya dade Ameer ne, Ameer..... Ameer...”
“Wane Ameer kuma?”
Gangan yayi mata haka saboda ya kawar mata da tunanin da take.
“Dana Ameer...”
Wani irin deep breath Abiey yayi taking sannan ya ce.
“Kina da wani ďa bayan Maleek da Mahood?”
Hajiya Zahra ta kalleshi da duba na irin wanda yake son yayi wasa da hankalinta ya juya tunaninta.
“Ameer ďana na farko da na fara haihuwa, ďan da na haifa da Deen, ka kalli fuskarsa sunansa da sunan mahaifinsa”
Wani irin kallo Abiey yake mata mai kama da harara zuciyarsa ta hau bugawa da mugun karfi.
“Wata kila ba ki gane ba ne”
“Na gane shi Ameer ne Wallahi, ta ya zan auri ubansa na haife, na kwana da shi a raina na tashi da shi har yau tunanin Ameer be bar raina ba kuma ka fada min cewar ban gane ba, wannan ďana ne Abiey jinina ne, ka daina canja min tunani Abiey mu ba yara ba ne”
Mikewa yayi tsaye ya daka mata tsawa da sai da ta zabura.
“Kin gane shi saboda har yanzu kina rike da shi da ubansa a ranki, na dade da sanin cewar Mr Bashir yana garin nan tare da Iyakinsa sai dai ban san akwai alaka tsakanin ďansa da Maleek ba, da ban bari abun ya kawo haka ba, ni da ke mun dade da rufe babin Deen da duk wani abu da ya shafe shi, ďa dai kin riga kin siyar yana da rayuwarsa da iyayensa a yanzu, yana da dangi da yan'uwa, ba san ki ba be san da labarinki ba, so this should be the last time da zaki sake yin maganar Ameer a gidan nan, kar son zuciya ya saka ki rusa rayuwarsa da ta wanda kika bawa, karki ruguza farincikin Mr Bashir da shi kanshi Ameer din, and mafi muhimmanci yarana ba su san da wannan maganar ba, ba su san ma kin taba auren wani kamin ni ba, karki kawo mana wani bakon al'amari a gida, na fi son yayana fiye da kowa karki tashi hankalin yayana...!”
Yana kaiwa nan ya kabe rigarsa ya fice daga