Showing 57001 words to 60000 words out of 281271 words
tsaye. Ya nufi gurin da ta zubar da kayanta ya dauka ya mika mata ta rike da hannun da baya ciwo, shi kuma ya rike wuciyar hannun ya jata suka fice daga falon, binshi kawai take kamar wata igiya har ya isa gurin motar da suka shigo dazun, a tsoro ya kamata jikinta ya fara rawa a taken hawayen na jini suka fara mata zuba, shi kanshi yayi mamakin ganin hawayen jini a idonta. Bude motar yayi ya dauko tissue ya goge mata hawayen, hakan nan ya ji yana sha'awar rumgumarta saboda ya kwantar mata da hankali, ba dan yau kadai ba har da gobe dan ya san da mota za aje da ita Abuja. Rumgume ta yayi yana shafa bayanta alamar rarrashi, yanayinsa sai yayi mata kamar na Eid da baya son kukanta. Bata san lokacin data kankameshi ba ta fashe da wani irin kuka mai karfi, jikinta na bata rabuwa zai yi da ita, bata san yaushe zata sake ganinsa ba, haka kuma bata san hannun da zata fada ba, bata san waye zai fahimce kamar shi ba. Dagota yayi ya duba idonta a yanzu din ma hawayen jinin ne, ya dauko wani tissue ya goge mata sannan ya bude mata front seat, wani irin dauke numfashi ta yi ta kalleshi, sai ya dafa kafadarta zai shigar da ita sai ta rufe ido gam jikinta ya fara rawa, hannunsa ya saka ya bude mata idon tana kallonsa sai ya girgiza mata kai, bata fasa hawayen ba, shi kuma be fasa goge mata ba har ya zaunar da ita cikin motar, sai ta ki yarda ta zauna a inda ya zaunar da ita ta sulale kasa ta matse kanta ta zauna a inda ya kamata ce kafafuwanta ne a gurin. A hankali ya rufe motar saboda kar ya daga mata hankali ya zagoyo ta dayan side din ya shiga ya saka maganinta da tufafinta a back seat ya kunan motar a hankali ya fara tukawa kadan kadan har ya fice daga gidan. Ganin ta ki daina hawayen kuma ta kasa rufe idon ta kasa daina kallonsa ya saka yayi mata murmushi ya mika hannunsa ya rike hannunta.
Tausayi take ba shi sosai, ya san zata san wahalar rayuwa a inda zata je, idan ma ta rayu kenan idan kuma ta mutu fa? Kamar yadda mahaifiyarsa tace? Ko kuma yadda yake zargin tsafi za'ayi da ita? Tafiya yayi mai nisa har sai da fita unguwar, gidansa incomplete building ne, be gama ba balle yace ua tafi can ya kwana ba kuma zai iya kwana a hotel ba, gashi baya jin zai iya kaita gurin police din a yanzu idan wani yayi kokarin keta haddinta fa? Yadda take da masifar kyaun nan zata iya jan hankalin wani ya ji yana sha'awar yin alfasha da ita. Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya dauki hanyar gidan nasa da yake ginawa gimbiyarsa dake Abuja, da kansa ya fita ta bude gate din ya shiga da motar sannan ya dawo ya rufe gate din, fita yayi ya zagaya side din da take ya kwantar da kujerar ya dagota ta dora masa ya share mata hawayen, babu haske a gidan a dole ya bar hasken motarsa a kunne ya kunna na wayarsa. Ita dai kallon gurin kawai take ya dauko carpet ya shimfida a gafenta ya zauna kasa ya jingina jikinsa kusa da kujerar da take zaune saboda ta samu natsuwa. Be daga daga gurin ba har sai da aka yi sallah Isha'i be sha wahala samun ruwa da bula ba saboda akwai rijiya a gidan, kuma akwai butocin da masu aiki suke amfani da su su yi sallah ko kama ruwa a duk lokacin da aikin ya kawo su, da kansa ya bude rijiyar ya debo ruwa ya zuba a bukatar yana juyowa sai ya ganta tsaye bayanshi, murmushi kawai yayi ya zauna bakin rijiyar yayi alwala ta sake biyoshi har inda ya aje carpet din dake ta zauna a kasa tana kallonsa har ya gama Sallah. Rikata yayi ya maida ita cikin motar ya rufe, sannan ya zagaya side dinsa ya shiga ya zauna ya rufe bayan ya kwantar da kujerarsa. Juyowa ta yi tana kallonsa sai ya sakar mata murmushi, be ce mata uffan ba ita ma ba ta iya magana da yarensa balle ta fada masa abubuwa da yawa dake son bawa wani labari. Sai karfe tara Hajiya Hajara ta kira wayarsa da gangan yaki daga wayar har sai da ta yanke sannan ya saka ta plane mode, ita dai kam ban da aikin kallonsa babu abun da take har bachi ya dauketa daman a gajiye take kamar wanda ta yi yakin duniya. Bachi tai sosai sai dai ta yi shi a takure saboda ba gado ba ne kuma ba tabarma ba, a cikin mota ne duk yadda ta so ta wala ba zata samu haka ba, bata farka ba sai da ya tashe ta da kanshi, sai ta bude idon a hankali ta kalleshi sannan ta tashi zaune. Fitowa yayi da kafafuwanta ya rike hannunta ya kaita inda zata yi fitsari ya aje mata buta, yana juyowa sai ita ma ta juyo bata saba sarki idan ta yi fitsari ba balle ta gane cewar fitsari yake nufin ta yi. A kokarinsa na fahimtar da ita ya saka hannunsa a daga rigarta ya dukar da ita, sai ta fahimci manufarsa, mikewa ta yi tsaye sai ta juyo ta kalleshi, ganin hakan ya saka ya juya baya sanin idan yayi nisa zata iya cewa ba zata yi fitsari ba. Tashi ta yi ta zo gabansa ta tsaya tana dage sai ta saka hannunta daya ta rufe masa ido daya, a take rufe idon gaba daya yana murmushi, ta daga hannunsa ta kai gurin kunnensa, sai ya saka hannu biyu ya rufe kunnensa.
Dawowa ta yi ta yi fitsari a inda ya nuna mata Hankali kwance, bata jin kunyar aga cikinta ko wani bangare na jikinta, sai gabanta da kirjinta, daman a gurinsu kirjin mace da kasanta ne a abun kunya a gurinsu, shiyasa gurin kawai suke damuwa su rufe, a gurin namiji kuma kasan ne kawai abun kunya, wannan na daga cikin dalilin da ya saka mazan garin basa damuwa da saka riga ko tufafin da zai sitirta jikinsu. Bata yi tsaye ba ta mike tsaye ta ja wandonta sannan ta dawo gabansa ta tsaya, shi ya ji cewar ta gama ya bude ido, juyawa yayi ya dauko butar ya mika nata yana mata alamar yadda zata gage cewar ta wanke fuskarta da baki, sai ta girgiza kai daman wanke baki ko fuska idan an tashi da safe ba al'adarta ba ce, yana daga daga cikin abun da ta tsana. Juyin duniya yayi Waira ta ki yarda ta wanke bakin nan nata daga duniyar kazanta, shi kan mamaki kawai yake daman haka take fama da kazanta ko kuma koya mata aka yi. Mota ya saka ta sai ta sake zaunawa irin zaman da ta saba idan ta shiga mota ta zauna a kasa, ta rufe ido bata dago ba har ya isa gurin masu siyar da fruit kasancewar da safe be samu wasu abubuwan ba, sai lemu da abaya ya siya mata, ya sake shiga motar yana sauke ajiyar zuciya. Sai a lokacin ta bude ido saboda ta ji kamshin abaya. Zobensa na azubarfa ya cire ya mika hannu ya dauko rigarsa ta yaga ya saka zoben yayi mata sarka da shi ya saka mata a wuya, sannan ya dauki diary sa da biro yayi rubutu akai ya mika mata, ta karba ta rike. Ya ja motar suka nufi CID office, fita yayi ya zagaya gefenta ya fito da ita ta dauko maganinta da kayanta ya mika mata kayan maganin da ledar kayan marmarin daya siyo mata kuma sai ya rike ya rufe motar yaja hannunta sai taja ta tsaya tana kallon gurin, a gurin ya barta ya shiga ciki yayi musu bayani sannan ya bukaci mai uniform din gida ya zo ya rikata kuma kar a shiga da ita gurin saboda zata tsorata sosai. Haka kuwa aka yi dayan ya cire uniform dinsa ya saka kayan gida bayan Dpo ya ba shi umarni saboda kawo ta da Dr sai da yayi musu karyar cewar Tiyata zai shiga kuma yana tsoron kar azo daukarta ba shi kusa. Dr Shuraim ya mika masa maganin sannan yayi masa bayanin abubuwan da take ci, sannan ya mika mata ledar fruits din ya nuna kanshi yana gabatar mata da sunanshi.
“Sunana Shuraim, sai wata rana”
A nan ta saka hannunta mai ciwo a kirji ta nuna kanta.
“Waira....”
“Waira....”
Ya maimaita sai yayi murmushi ya mike tsaye yana nata waving, zuciyarsa na masa babu dadi, ji yake kamar kar ya rabu da ita, kuka ne kawai be yi ba amman sai da idonsa suka cika da kwalla, he thought za ta yi ihu tace zai ta biyo shi, sai ga tsabanin haka ta tsaya a inda ya barta tana kallonsa babu kuka babu hawaye sai dai ta ki dauke ido akansa har sai da ya shiga motarsa sannan ya saki ledar fruit din dake hannunta. Tana jin kewarsa ta fahimci fada ake masa tun jiya hakan ya saka bata takura cewar dole sai ta bishi ba, tunanin zai tafi ya barta ya saka ta manta da tsoron mota take, tana kallonsa har ya fice daga harabar.
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: *W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
20
A gurin ta risina tana kuka dafe da fuska, coworkers dinta suka rika bata hakuri dayar ta rikata ta kaita restroom ta wanke mata fuskarta.
“Wai miya hada ku?”
Bakin ciki da masifa irin na Humaira sai ya yana ta fada mata komai, da zarar ta bude baki ta yi magana sai ta fashe da kuka, ta girgiza kai, ta san ita talaka ce mai nema a karkashin wasu saboda ta taimaki iyalinta, amman hakan ba zai saka ta dauki wulakanci ko kaskanci a gurin kowa ba, bata taba wulakanta wani ba, hakan ya saka idan aka wulakanta ta abun yake mata ciwo.
“Da gaske shi dan mai gurin nan ne?”
Shi ne kawai abun da ta iya tambaya, tana dafe zuciyarta saboda bakinciki dake taso mata.
“Bana jin haka, ni ban ma taba ganinsa ba sai yau”
Ta lumshe idonta hawaye na sauko mata kamar ba gobe, fitowa ta yi daga gurin ta dauki katon hijab dinta ta saka, ta dauki yar karamar jakarta da take sako tarkace a ciki.
“Humairah ba zaki tafi da abincin ba?”
Ta juyo ta kalli kawarta Muneera, tun da ta kama aiki gurin bata da kawa irin Muneera sun shaku sosai kusan duk wani abu daya shige mata duhu ita take nema shawara ta warware mata. A ka'ida idan za su tafi gida suna raba abincin daya rage a gurin ne, mai gurin ya fada musu idan har an raga abincin to su raba tsakaninsu kowa ya tafi da shi gida, saboda ba a dumamane abincin da safe idan kuma aka bar shi nan zai lalace ne kawai. Duk wadanda suka yi duty dare ana kaisu gida ne da motar gurin, saboda fadin garin Abuja wasu a kusa suke ba, Mr Bashir yana musu haka ne a kokarinsa na kyautatawa kowa a zaman da suke a gurin, ana canjin duty idan wadannan sun yi da safe na sati sai a canja wasu su yi na yamma ko dare ko rana, kana ana canja su daga wannan gurin zuwa wani dabam.
Kai ta girgiza mata alamar ba zata tafi da shi ba, saboda bakincikin abun da aka yi mata a yau ya rufe mata ido bata iya ganin komai, daman can haka take ba kasai take jan mutun fada ba, amman ko harararta ka yi ba zata kyale ba. Muneera ta matso kusa da ita ta rumgume ta ganin har lokacin hawaye take.
“Wai miya faru ne Humairah me kika masa?”
“Akwai wata hanya ta kai kara”
Ta tambaya so take ta kai kararsa idan har da gaske dan mai kamfanin ne ya kamata mahaifinsa ya san abun da ďansa ya aikata mata. Arzikin ďaya bata kone ba amman har yanzu fuskarta zogin zafin tea take da kuma marin da ba a taba yi mata ba.
“Idan ma akwai ai ba za a masa komai ba, dan mai gurin ne fa?”
“Da gaske dan mai gurin nan ne?”
“Eh ance shi kadai ya haifa namiji sauran yayanaa duk mata ne, shiyasa yake juya kowa yadda ya ga dama, ya taba zuwa gurin sau daya a lokacin da na kama aiki a nan, yadda kika san be ga mutane ba haka ya shigo ya zauna yayi abun da zai yi ya fita, be yi ma kowa magana kuma babu wanda ya isa yayi masa, a nan nima aka fada min cewar na kiyayeshi dan Mr Bashir ne, mahaifinsa ya fi shi kirki kowa ya san mahaifinsa mutumen kwarai ne amman shi kam hmmm”
“Wannan ne karo na biyu da ya wulakanta ne, akwanan baya na taba zuwa kamfaninsu yin wani abun, kallo daya yayi min yace ba su bukatar irina, na ji babu dadi domin be karbe ni da kima ba, yanzu kuma ya sake wulakanta”
“Hakuri zaki yi, a duk lokacin da kake nema a gurin wani dole ne sai ka yi hakuri”
Ta share hawayenta ta juya ba tare da tace komai ba, ta ficw daga gurin da direbobin gurin suke aje motocinsu, wanda ya saba kai ta ne ya taso sai ta tsaya jikin bus din tana jiran isowarsa.
“Humairah lafiya kike kuka?”
“Wani ne ya mare ni ya watsa min tea a fuska”
“Saboda me? Waye shi? An hukunta shi?”
A lokaci daya ya jero mata tambayoyin.
“Ance dan mai gurin nan ne”
“Ameer ko? Zai aikata kuwa ai bashi da hali ko kadan miya hada ku?”
A cikin motar ta iya labarta masa abun da ya faru, ciki har da kudurinta na son kai kararsa a gurin mahaifinsa. Direban ya saka dariya.
“Idan ma be koreki daga gurin nan ba, kin yi arziki ai ba shi yake kula da komai ba, akwai masu kular masa, ko da ace email dinsa suka samu ba zama lallai shi yake kula da mail din ba, idan kuma kin je gidansa be zama lallai abarki ki shiga ciki, domin akwai masu gadi da yawa a gidan”
“Shikenan ya sha banza kenan?”
“To ya zaki yi”
“Toh Allah ya isana, Allah ya hana shi farinciki duniya da lahira, yadda ya ci amanar marainiyar Allah ka saka shi cikin damuwa”
Direba dai sai dariya yake, ya san Ameer be kyauta ba, sai dai lamarin Humairah ne abun dariya domin bata barin ta kwana sai gashi kuma an kai inda ba zata iya ramawa ba. Har ta bude motar ta fita bata daina masa Allah ya isa ba da bakar addu'a, sai da ta yi tafi mai nisa sannan ta shiga isa gidansu dake cikin kwana, irin gidan nan ne da ake na yawa a bada haya wanda saka zamu falo da daki biyu lo daya sai toilet a cikin dakin, gurin girki kuma sai an fito wajen, yawancin gidajen duk kabilu ne ke hayarsu da kuma masu sana'a a garin abuja kamar masu siyar da nama ko wasu aikin da suke tare da iyalinsu.
Ta shiga gate din ta nufi kofar dakinsu ta buga Kakarta ta taso ta bude mata, sai ta shiga ciki ta rufo kofar, sai da kanenta suka tashi zaune suna kallonta tausayinsu ya kamata domin kullum ita take zuwa musu da abincin sai sun ci sannan su kwanta yau kuma bata riko komai ba sai hawayenta da ta kusan kararwa.
“Lafiya kike Humairah”
Ta zauna saman kujerar roba dake dakin tana jin wani sabon kuka na sallamo mata.
“Mutumen da na fada muku cewar ya wulakanta ni saboda na je neman abu a kamfaninsu, shi ya watsa min ruwan zafi na tea a yau kuma ya mareni”
“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un”
Maihaifiyarta ta furta tana tasowa ta fito daga cikin dakin da take zaune tana sakar zaren olu. Cikin kuka ta fada musu abun da Ameer yayi mata. Hawaye ya fara saukowa a idon Ummanta.
“Allah ya isar miki Humaira Allah ya saka miki”
Kakarta ta amsa sannan ta dora mata da dogon sharhi.
“Ameen duk mai nema daman dole yayi hakuri, kuma wata rana sai labari dole sai kin jure, kuma tun da kin ga halinsa sai ki yi taka tsantsan, kin san da aikin nan kika dogara muma kuma da shi muka dora sai dan baran da nake ina samu, dole mu yi hakuri kamin Allah ya kawo mana mafita, idan Allah ya sa kika gama karatunki kika samu aiki ai mun warke, amman kamin ki kao ga wannan dole mu hakura da halin da muke ciki, mai hakuri mawadaci ne wata rana, kin ga wannan saurin fushin naki da daukar zafi, ga nacewa ki ce sai kin rama idan aka yi miki abu ki tattara shi ki aje a gefe, ki rika hakuri da rayuwa, idan ba haka ba fitina zaki janyo mana, Humaira ke marainiya ce karki manta da wannan baki gata sai na Allah”
“Ai wanda yake da gatan Allah shi ya fi kowa gata, Wallahi ni sai Allah ya isar min, ba zan yafe masa ko kabarinsa na balbala da wuta”
Ta tashi ta shige dakin da suke kwana ita da kanenta.
AMEER POV.
A lokacin da ya fito daga cikin zuwa yayi ya tsaya jikin motarsa not knowing what to do, har lokacin ransa a bace yake, a gurin Abdull ya same shi shi ma fuska babu annuri yake kallon abokinsa da mamakin yadda yake da zafin zuciya da daukar komai da girma.
“Wani lokacin ina mamakin yadda Allah ya halicce ka Ameer, wannan halinka sam ba shi da kyau, yanzu me yarinyar nan ta yi maka da zaka mareta ka watsa mata tea mai zafi a fuska? Idan wani abun ya same ta fa?”
“Ba damuwata ba ce, kai baka ji abun da take fada min ba? Ni tsararta neda zata kalleni ta fada min maganar banza?”
“Amman kai ka shiga sha'aninta ai, kuma a yadda na fahimta daman