Showing 132001 words to 135000 words out of 281271 words

Chapter 45 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1221

cikin jaka tana ringing, bude jakar ta yi ta dauko wayar number one of ma su kula da gate din ta ne yake kiranta.

“Wa'alaikussalam”

“Hajiya an wuni lafiya?”

“Lafiya kalau”

“Na kira wayar Alhaji be daga ba shiyasa na kira wayarki, wani ne ya zo da mota yana son ya shigo ciki, na ce wa yake son ganin wai Zahra”

“Waye shi?”

“Bari na tambaye sunanshi”

Tana jin lokacin da yake ta tambayarsa ya sunansa amman yaki yayi magana.

“Musa bar shi ya shigo na gane shi”

“Toh Hajiya”

Ta aje wayar ta nufo falo Waira ta biyo bayanta. Yesmin dake zaune ta dago tana kallon Ummi wadda ta zauna kan kujera idonta na kan kofar falon, juyawa Yesmin ta yi ta kalli kofar sannan ta juyo ta kalleta.

“Ummi lafiya”

Ummi ta daga mata hannu alamar ta dakata. Da wani irin karfi aka murda kofar falon aka turota, daga Ummi har Yesmin da Waira sai da suka mike tsaye suna kallon Ameer da ya shigo falon fuska babu annuri, kai tsaye ya nufo inda Ummi take domin ba kallo kayan alatu suka kawo shi ba balle ya tsaya bata lokaci. Tsaye yayi a gabanta kamar without any rest yana mata wani irin kallo da ya fi kama da tsana. Waira ta saki baki tana kallon Ameer da mugun mamaki shi kam ko ganinta be yi ba domin baya ganin kowa a falon sai Ummi kadai daman zuwan nata ne. Yarfar da hannu ta fara yi tana son ta tuna sunansa ta kasa amman tabbas ta gane shi, abun ka da mai son mutane ta ga wanda ta sani sai jin yayi an shiga tsakanin shi da Ummi an rumgumeshi da karfi. Yana kokarin saka hannu ya ture kowaye ta dago kai shi kuma ya sauke nasa kan kasa dan ganin wanda ya yi masa wannan kasadar. Murmushi take masa mai sauti hakoranta a washe, lokaci daya ya gane wacece ita, ya tuna inda ya fara ganinta, alakarta da gidan ta tuna masa cewar ita ce yarinyar da ya saka a motar Nimra, daman Nimra ta fada masa yarinyar tana gidansu, a yanzu ya gane duk ganin da yake mata a gidan take. Yesmin ta fisgeta ta jefar da karfi kan kujera.

“Baki da hankali daga ganin mutum zaki tashi ki rumgume shi?”

“I know him i know him”

“Idan kika taba shi sai na kusa kasheki. Kai.. Ya zaka shigo cikin falo ka nufi uwar masu gida kai tsaye ko baka da hankali”

Ta fada tana kallonsa kamar yadda yake kallonta cikin bacin rai, shigarsa da yanayinsa be yi mata kama da mahaukaci ba, balle ta ji tsoronsa kama yayi mata da marasa tarbiya yan tijara.

“Yesmin stay out of this please, Ameer me kake so?”

Ummi ta fada sai ya dawo da dubansa gareta.

“Shaida abun da zai saka na yarda da abun da kika fada”

“Ribar nawa zan ci idan na yi maka karya? Na san wannan abun zai iya kai ni gidan yari idan har karya ne, to akan me zan yi haka? Ina da yaya mata kuma Allah ya ba ni mata idan ba ni da hujja ba zan yi haka ba, idan aka auna jinina da naka na tabbatar results daya zai ba da, ba dukiyar Mr Bashir nake kwadayi ba nima Allah ya rufa min asirin da zan iya yin komai... Amman jira ni ina zuwa”

Ta nufi stairs da sauri dakinta ta fara shiga ta bude wardrobe dinta, sai da ta fara kokarin sauke akwatin sannan ta tuna Maleek ya dauki jakar, da sauri ta fito dakinta ta shiga dakin Maleek akan gadonsa ta tararda jakar wasu takardun a watse wasu kuma be taba su ba, wadanda be taba din ba ta dauka tana dubawa har ta kai ga evidence din da take son nunawa Ameer ya sauko da sauri ta iso inda yake ta mika masa. Kallon envelop din yayi ya kasa mika hannu ya karba, kamar wanda aka cewa makomarsa ce a ciki.

“Shaidata tana nan, kuma ka tambaye duk abun da kake so zan amsa maka...”

Cikin nauyin jiki tana zuciya ya karba ya bude, takardar yarjejeniya ya fara cin karo da ita kalar wadda Hajiya Jamila ta bashi, abun da ke rubuce a can shi ne a rubuce a nan babu banbanci har kwanan wata. Daga kasan takardar kuma hoton mahaifinsa ne da ya kara gasgata masa cewar tabbas shi ba ďan Mr Bashir ba ne. Domin kamanin dake jikinsa da fuskarsa su ne a jikin hoton banbancin wannan hoto ne da ya dade shi kuma yana a tsaye ne a zahiri. Zubewa yayi kasa guiyoyinsa ya fashe da kuka ya rumgume hoton a kirjinsa.

“Me yasa zaki yi haka? Me na yi miki?”

Dukawa ta yi tana kuka

“Baka min komai ba Ameer, ban aikata hakan saboda son zuciya ba”

Ta mika hannu zata taba shi sai ya daka mata tsawa da zai da ta zabura.

“Don't touch me”

“I won't i won't”

Ta rike hannayenta da sauri.

“I'm sorry Ameer na san ban kyauta ba, amman ban aikata hakan da nufin bana son ka ba dole ce ta saka”

“Da kina so na, da baki siyar da ni ba tun farko, kuma da baki bari na rayu a gurin wani da yake amsa sunan Ubana ba, da soyayyaa bata barki kin kai wannan lokacin ba tare da ni a kusa da ke ba”

“Wallahi soyayyar ka bata bar ni na samu farinciki da kwanciyar hankali ba, a kullum da kai nake wuni na kwana a zuciya, ina tunani a wane hali dana yake ciki”

“Ni ba ďanki ba ne, you have never been my mother and you will never be, kin san abun dariyar? A kullum sai na yi ma mahaifiyata a addu'a, saboda Daddy ya fada min cewar ta mutu, kuma haka zan cigaba da yin addu'ar har a yanzu, domin har yanzu uwata a mace take, ta tafi kenan ba zata taba dawowa ba, ki bayyana gaskiya a yanzu saboda ki sake ruguza rayuwata, me yasa ba ki bar ni na cigaba da kallon mutumen da ya tsaya min a matsayin Ubana ba?”

“Saboda ina son na farantawa kowa kamin na mutu, na tafi ana yabawa ba a bini da bakar addu'a ba, ina son an roki gafarar kowa Ameer?”

“Har da mahaifina? Ba zaki taba samun wannan damar ba, ba zan taba yafe miki ba, kuma ba zan taba kallonki a matsayin uwata ba..”

“Mahaifinka yana kaunata Ameer, da ace yana raye da baka isa ka fada min wata magana marar dadi ba, ban aikata hakan dan bata ran kowa ba, idona a rufe lokacin bana ganin kowa sai mahaifinka rayuwarsa kawai nake son na ceto”

“Yana kaunarki, amman ke baki kaunar ďansa baki son jininsa, shiyasa kika zabi rabuwa da shi, why me? Miyasa baki siyar da Maleek ba?”

Kamar daga sama suka ji muryar Abiey yana amsa tambayar da Ameer yayi.

“Saboda Maleek ubansa mai arziki ne, Ameer kuma an siyar da cikinsa ne saboda a nemawa Ubansa magani”

Duk kallonsa suka yi, Ameer ya ji ina ma be zo duniya ba, da be ga wannan bakar ranar ba a rayuwarsa. Ya girgiza kai ya kalli Ummi yana murmushi.

“Na gane, tsiya kike gudu, shiyasa da kika samu wani mijin kika watsar da ni, kika tara wasu iyalin? Toh miyasa yanzu kika ruguza tawa rayuwar? Da ace da kika haife ni kashe ni kika yi da na huta ganin wannan ranar, kin cutar da ni ba ki cancanci a kira ki uwa ba, na ga soyayya da kauna daga gurin wadanda ba jinina ba, ya kike son na yi rayuwa a yanzu? Farincikin da nake ne yake kona miki rai?”

Ummi ta kasa cewa komai sai kuka take, ya mike tsaye rike da takardun ya nufi kofa har ta ya kusa fita ya juyo hawaye na masa zuba cikin ihu ya ce.

“Kin san zafin da ďa yake ji idan uwarsa bata sonsa? Da ma gidan marayu suka hai ni, siyarwar ita ta fi min zafi...”

Ya juya ya fice, kai kawai take iya girgiza masa domin kuka ya ci karfinta ta yarda bata ko iya magana. Abiey ya rikota ya nufo inda take ya rikata.

“Ya isa haka, and this is the last zuwan da yaron nan zai yi a gidan nan, domin ba zan dauki ya shigo har cikin gidana ya fadawa matata magana marar dadi ba”

Ummi ta kwanto jikin Abiey tana kuka ta dafe zuciyarta, Yesmin ma kuka take duk da kasancewar a yanzu ne ta fahimci abun da yake faruwa, Waira ma kuka take tana kallon Ummi.

“Me yasa bana da tunani, me yasa ban yi tunanin zuwan irin wannan ranar ba Abiey? Ameer zai iya shiga wani hali, ba zai yafe min ba na shiga uku..”

Shi ne abun da ta iya furta tana kuka sosai kamar zata rusa ďakin.

“Zai yafe miki amman ba a nan kusa ba, dole sai kin jure kin zama jajirtacciya, and i promise you zan yi iya kokarin da zan yi na gyara mun gyara duk wani abu da kika bata”

Ta runtse ido tana girgiza kai, zuciyarta na wani irin zafi kamar an watsa mata tafasasshen talge a ciki.






____________________

Allah sarki Ameer 😭 ni dai duk ya fi ba ni tausayi, taya kana rayuwa da iyayenka rana daya ace ba iyayenka ba ne. Wayyo Allah, ku dauke zancen jindadi ko da wahala ake sha a tare wannan kallon da kake musu a matsayin iyaye canja shi ne abu ne mai wahala, and the most painful part yana zaton uwarsa ta mutu ashe tana raye a kusa da shi........

Ni daman can team DEEN ce yanzu ma ina bangaren ďansa AMEER, gaskiya Zahra baki kyauta mana ba 🥺😏
[6/29, 9:08 PM] My S Line: 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 𝐧𝐚 𝐦𝐮𝐤𝐮 𝐛𝐚𝐫𝐤𝐚 𝐝𝐚 𝐒𝐚𝐥𝐥𝐚𝐡.
𝐅𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐤𝐮𝐧 𝐲𝐢 𝐒𝐚𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐥𝐚𝐟𝐢𝐲𝐚, 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚 𝐦𝐚𝐢𝐦𝐚𝐢𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐲𝐚 𝐤𝐚𝐫𝐛𝐢 𝐢𝐛𝐚𝐝𝐮.
𝐀𝐦𝐞𝐞𝐧🥰


*Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*


44


Kamar mashayi haka Ameer ya isa gaban motarsa sai budewar ya gagareshi, saboda rashin kuzari da kuma rawar da zuciyarsa take wadda ta haifar da jikinsa zazzabi. Jinginawa yayi jikin motar ya kife kansa wasu kalar hawayen sauko masa wadanda be san daga ina suke fitowa ba. Sai dai ya san a rayuwarsa be taba kuka da bakinciki da jin tashin hankali a lokaci daya kamar yau ba.
Meyasa ma ya zo duniya? Akan me rayuwarsa zata yi tsayin da zai ga wannan bakar ranar a yau? Da ace ya mutu kamin yau da yafi masa domin be sam komai ba. Matar nan kullum addu'a nake mata ina jin na rasa wani gurbi na uwa, ina jin abubuwa da yawa da ace tana raye ba zan aikata ba ko na rasa ba, ashe tana raye, ta kuma san ina raye amman ta kasa zuwa duba ni ta kasa nemana sai a yanzu da ta shirya tarwatsa rayuwata, me zai saka ya zubar da hawaye? Akan macen da bata cancanci zama uwa a gareshi ba? Wani bangare na zuciyarsa ya karanta masa, a take ya ji kukan ya yanke masa, kuzarin da ya rasa ya taho da gudu ta yarbe shi, fa sauri zazzabin ya bar jikinsa. Sai ya bude mota ya shiga yayi reverse, yanayin yadda yake tuka motar har ya fice be nuna yana cikin tashin hankali ba, duk kuwa da kasancewar hakan ya kasa boyuwa a fuskarsa.
Tafiya mai nisa yayi kamar zai fita garin Abuja, kawai be san inda zai tafi ba, ya tafi gidansa ya kebe shi kadai? Ya kama hotel ya zauna? Or yayi ta driving har ya gaji? Ya rasa na zaba atsakanin abu ukun da zuciyarsa ke lissafa masa. Sai dai definitely ya san baya bukatar zuwa gida a yanzu, ji yake kamar ba zai jure kallon Mr Bashir a matsayin wanda yayi adopted dinsa ba not his biological father, duk rayuwar da suka yi a tare duk wahalar da Mr Bashir ya sha a kansa ace ba mahaifinsa ba ne? Ya dauki nauyinsa ya rike shi tsakani da Allah all this ahi ba mahaifinshi na gaskiya ba ne? All this wealth da ya tashi a ciki ya ga Mr Bashir na juyawa har ta kai shi ma ya isa sarrafa wani abu daga ciki, ba mahaifinsa ba ne? Yadda yake sakar masa kudi da duk wani iko da gata still he's not his biological father? Even for once Mr Bashir be taba nuna masa cewar shi ba ďansa ba ne. Ya cire shi a kowace kalar rigima ya bashi damar aikata duk abun da yake so ya daure masa gindi still ba mahaifinsa ba ne? Zuciyarsa ce ta buga da mugun karfi abun da kwakwalwarsa take kalato masa ya fi karfin tunaninsa, wani hudu bakincikin mai zafi ne ya rufe masa kirji. A take ya ji babu wanda yake bukatar gani kamar a lokacin kamar Mr Bashir, kamar mahaukaci haka ya taka burki ya juya motarsa tsakiyar titi he just got lucky titi babu manya motoci a lokacin, ko da ma akwaisu ya shirya yin haka domin jin yake kamar rayuwarsa bata da amfani a yanzu. Sai da ya kusa isa gidan then ya sake jin bana bukatar shiga cikin gidan ba dan an masa laifi ba, rauni zuciya yake kusantoshi a duk lokacin da rai ya rasa masa ganin fuskar Mr Bashir. Faka yayi nesa da gidan ya fito waje ya tsaya yana kallon motar kamar mai tunanin abun yi? Jin kamar numfashi zai gagareshi ya saka shi bude motar ya dauko ruwan gora ya daga kansa sama ya kafa gorar a bakinsa ya fara shan ruwa kamar rakumi, ragowar kuma ya daga gorar sama suka zubar masa a fuska suka jika jikinsa musammansa ma kirjinsa dake masa zafi kar an watsa masa tafasasshen talge a ciki.

“As Simple as that you just look in to my eyes kika fada min cewar ke ce mahaifiyata? Akan me? Me yasa ba zata bar wannan ya cigaba da zama a sirrin ba?”

Ya tambaye kansa wasu hawayen ya cika idonsa?

“Ina take son na rayu? So take na tsani duniya? Me jindadin rayuwata ya tsare mata?”

Ya sake tambayar kansa a karo na biyu, yana jifa da empty gorar ruwan dake hannunsa.

‘Saboda ka taba Malee ne, kuma ka taba Nimra su ai yayanta ne da take matukar kauna’

Zuciyarsa ta amsa masa tambayarsa da amsar da zata fi gamsar da shi. A take ya girgiza kai yana kara gamsuwa da hakan, domin a lokacin da duk wannan be faru ba, bata nuna cewar shi danta ba ne, a yanzu ya yarda da maganar Hajiya Jamila cewar bata sonsa, kalli yadda wanda ba ubansa yake nuna masa kauna fiye da iyayensa, kalli Hajiya Jamila ma yadda take sonsa. Tabbas da ace Ummi ma tana sonsa ko da tabin haka ne da bata barshi ya tashi a hannun wani yana masa kallon ubansa ba. Yanzu ya duniya zata kalleshi? Taya zai fuskanci mutane? Alfarmar da yake samu ta mahaifinsa zai rasa a yanzu, korar wanda yake so da bawa wanda yake so aiko ko mukami ya fita a hannunsa a yanzu, mutanen da ya wulakanta saboda yana jin cewar shi dan Mr Bashir ne ya za su kalleshi idan suka ji? Mutuwa ce kawai be yi ba a lokacin amman komai na duniya ya taru ya tsaya masa cak a lokacin. Yana kallon wayarsa na kara ya kasa dagawa kuma ya kasa kashewa. Yana tsaye a gurim har aka kira sallah Magariba, that's what he can't afford to miss, sallah in time, wannan ne a abun da ya saka shi shiga motarsa duk kuwa da kasancewar ba kiran sallah ya ji ba, domin unguwarsu tafiya ce mai nisa tsakaninsu da massallaci that's why kowa yake yin masa masallacin a gida, for masu kula da addini kenan, wasu kuma babu ruwansu da gina Masallaci, though he's muslim App ya gane Magariba ta yi saboda kiran sallah da app da ya fara. Yana fara tukin wayarsa ta kara ringing sai ya kalli inda wayar take aje, number Hajiya Jamila ce take kiransa da sunan da yayi saving number ta wato Ammy with heart emojis. Ya amsa kiran and put the phone on speaker.

“Ameer kana ina? Ka daga min hankali, na kira mahaifinka yace min baka gida, shi ma yana ta kiranka baka daga wayarsa ba? Please Ameer ka san muna matukar kaunarka, mu ba kamar Zahra ba ne, idan ka shiga wani hali ko ka illata kanka zamu shiga uku ba, ba zamu iya bearing rashinka ko shiga damuwarka, dan Allah karka jefa kanka a matsala please we love you kuma ka sani, sanin gaskiya ba zan saka mu canja maka komai ba, ba zai canja cewar kai ďan mu ba ne, sai ma kaunarka da tausayinka da suka karu a zuciyarmu”

Cikin kuka take fada masa hakan, shi ma hawayen yake yana jin tausayinta da kuma na Mr Bashir da kansa a lokaci daya.

“I promise you ba zan jefa kaina a halin da hankalinku zai tashi ba, i will control my temper, i will take care of myself”

“Thank you, please pick up your phone call your dad ka yi magana da shi”

“Does he know kin fada min gaskiya?”

“No kawai na kira wayarsa a saboda na kiraka baka daga ba, sai ya fada min shi ma ya kira baka dauka ba kuma na san ya damu”

“I already reach home bye”

Ya yanke kiran ya jingina jikin motarsa, this is the first time da ya taba tsayawa haka a gate din gidansu peacefully ya danna horn yana jiran a bude masa. Yaja motar kamar marar lafiya ya shiga yana ta kallon bangaren da mahaifinsa yake. Calmly ya faka motar ya bude ya fito ya bar wayarsa da takardar da Zahra da bashi tare da hoton ya nufi Garden. Tun da yake a rayuwarsa be tana kunna fonfon Garden yayi alwala na sai yau, saboda yana matukar kyamar gurin, kasancewar ma'aikatan gidan suna yawan zuwa gurin diban ruwa idan babu a fanfon masallaci. Damuwa ta mantar da shi dokokinsa na ware kansa da yake a masallaci yana sallah a one place ba tare da hada kafada da sauran mamu ba, sai gashi a sahun gaba, wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login