Showing 195001 words to 198000 words out of 281271 words
yana sonta ne ko kuma dai ya fadi haka a yanzu ne saboda kar Ameer ya aureta?”
“Ya kike magana kamar baki san waye Maleek ba, ai shi ni ya gado bashi da wannan zuciyar ko kadan, ina zaton dai Ameer ya fahimci haka ne shiyasa yake kokarin ganin ya shiga tsakaninsa da Waira, kuma be kama ace suna jayayya akan abu daya ba, musamman Ameer da shi ne babba, wannan shi ya zo daga baya bayan ya gama cewa be san yarinyar ba, ba san inda ta fito ba, da ban rike ta na mata gata ba, wata kila da be ganta ya ce yana so ba a yanzu, hausawa sun ce so so ne amman son kai ya fi, kuma da arziki a gidan wasu kara gidanku”
“Ranka ya dade dukansu yayana ne, zan fi kowa farinciki idan dukansu suka samu abun da suke so, amman a yanzu ban san wa zan dauka ba, farincikin ya zame min bakin hadari da na kasa hango haske a ciki”
“Maleek ya Ameer kaunarta, kuma shi ya kamata ya aurenta zai fi sanin darajarta fiye da Ameer, wata kila shi kyauta ne kawai ya dauke shi, ina gudun kar maganar Maleek ta tabbata ya aureta na dan lokaci daga baya ya nemi rabuwa da ita, kin ga ya lalata mata rayuwa kawai, kuma Maleek ba zai jidadin kin bawa dan'uwansa shi kin hana shi ba, ni kaina ba zan lamunci haka ba, kin fi kowa sanin yadda nake goyon bayan yaya a komai”
Ta lumshe ido tana jin wani kalar abu marar dadi na neman karya mata zuciya.
“Amman zamu iya bata dama ta zabi wanda take so, duk kuwa da na san be zama lallai ta san wanda take so din ba”
“Aa haka be kamata ya kasance a tsakanin yan'uwa ba, da ma da wani ne a waje amman ba yan'uwa da suke jini daya ba, me yasa abubuwa suke zuwa min a haka ne? Abubuwa suna zuwa min da yadda shawo kansu zai zama mai wahala a gareni, kullum zuciyata a cikin kunci take”
Ba tare da ta bude ido ba take fadar haka, sai dai haka be hana hawaye samun hanyar fita daga idonta ba.
“Babu wani abun kunci a nan, kawai mu yi addu'a kuma mu ja hankalin kowa a cikinsu, zan yi magana da Maleek na ga idan har zai zan iya canja nasa ra'ayi, na san abu ne mai wahala amman zan gwada, idan na yi nasara kin ga an huta, sai ya barwa Ameer”
Ummi ta bude idonta ta saki Abiey ta nufi hanyar fita tana jin zuciyarta kamar zata fashe. Maleek be cancanci a gabatar masa da wata a matsayin ya so ta ba, domin be taba nuna son wata ba, sai a yanzu, neman canja masa ra'ayi kuma zai iya sakawa ya dawo da rayuwarsa ta baya, ko kuma ya kara rashin fahimtar dake tsakaninsa da Ameer, wata kila kuma yayi ma Ummi guguwar fahimta zai ga abun kamar ta nuna fifiko akan Ameer ne sama da shi. Ba kuma zata iya tunkarar Ameer ta canja masa ra'ayi ba, yadda yake da wahalar tankwaruwa ma ta san abu ne mai wahala ya amince, kuma zai sake kallonta a wata muguwar uwa wadda ta kasa bashi farinciki a baya, kuma ta kasa sama masa shi a yanzu.
Wai miyasa tuntuni bata kula da alakar dake tsakanin Maleek da Waira ba, da a yanzu haka duk bata kasance ba, da yanzu ta san yadda zata bullowa lamarin, zuwan Ameer ya dauke hankalinta daga komai har bata ganin wata alaka sai ta Ameer da Waira, shi kuma ya cancanci farinciki daga gurinta a yanzu, ta dayan bangaren kuma ta san Abiey fada kawai yake amman ba zai bar vangaren dansa ya zabi Ameer ba, wadda suke yi ma kallon makiyinsu saboda abun da ya faru da Nimra, ga kuma salsalar rashin jituwa dake tsakanin Deen da Abiey, Deen din ya tafi amman Abiey ya kasa jefar da wannan gabar da kiyayyar wata kila shi ya saka har yanzu bw taba tambayar lafiyar Ameer ko kuma zuwa duba shi a bangarenta, tun da Ameer ya sako kafa a gidan Abiey be taba maganarsa ba idan ma ta yi magana ba zai ce uffan ba har aci a sude.
“Wayyo Allah....”
Ta fada tana jinginawa da corridor ta sulale kasa tana kuka marar sauti, gaba daya abun ya rikice mata, ta rasa na dauka ta rasa na zubarwa haka ma ta rasa yadda zata bullowa lamarin.
WAIRA POV.
Tana gama kallon Sallah a wayar Ummi sai ta aje wayar akan gadon Ummi, daman kamin Ummi ta fita dakin ta karbi wayarta ta shiga gurin da Ameer ya nuna mata, kuma a yau ta ji bata sha'awar kallon komai sai Sallah, daman yadda take ganin suna yi a gidan abun na burge, ta wani bangaren kuma tana kallon abu kamar wahala ne a gareta.
Tana aje wayar ta nufi gurin da Ummi take aje a carpet dinta ta dauka, ta dauko dankwalin Ummi na atamfa dake kan gado ta riko carbi ta fito ta sauko kasa. Bata damu ta fuskanci alkiba ba, domin bata san miye haka ba, kuma bata taba ganin kowa yayi sallah a falon ba balle ta kula da inda ake kallo idan za'ayi sallah, dama a cikin dakin Ummi ta san inda zata tsaya ko ta shimfida yayi daidai da alkiba. A falo kam sai ta shimfida carpet din ya fuskanci gurin plasma ta nada dankwalin a kanta ta rufe gashinta, bata damu da yadda rigar jikinta bata sauko mata har kasa ba ta rufe ido tana tuna yadda macen da ta kalla take yi, da kuma yadda take yawan ganin Ummi tana yi da Nimra idan suna sallah, har fa motsa baki take ba dan ta san abun da ake fada ba, ita dai motsa baki kawai take saboda ta ga Ummi na yi, har lokacin kuma idonta a rufe yake. Tun daga sama Maleek ke kallonta yana saukowa a hankali ya iso inda take zaune tana zaman tahiya, bata san raka'a nawa ke magariba ko isha'i ba, dan haka ta kara ra'a uku bayan ta yi biyu. A lokacin da ta gama sai ta zauna ta yi sallama kamar yadda ta ga Ummi tana yi, duk abun da take Maleek na tsaye bayanta yana kallonta fuskarsa da murmushi, wani irin kimarta da girmata da kwarjinta ga haibarta suka cika masa zuciya. Jin kamshin turarensa ya saka ta juyo suna hada ido sai ta yi dariya ta rufe ido, sautin dariyar da yadda ta kalleshi ta rufe idon da ta yi suka ruda shi har ya nufi kujerar dake gefenta ya zauna yana mata wani irin kallo da shi ma be san yana yi ba.
“Sallah nake yi”
Ta fada ganin yana kallonta, sai dai hakan be saka ya dauke idonsa daga barin kallon ba sai ma jan hankalinsa da ta yi da sautin muryarta mai dadi sauraro ya zuba idonsa akan bakinta yana kallon yadda take motsa shi a hankali tana sake nanata masa Sallah ta yi.
“Sallah ce kawai Ameer ya fada min yadda ake yi, kuma na ganin a wayar Ummi, yau na ji ina son na yi shiyasa na yi, amman kai ma kana yin sallah? Ban taba gani ba Ya Maleek”
Still motsin bakinta yake kallo, kamin ya maida duban akan eyes dinta da dagon hancinta, wata kila sallah da ta yi ne ko kuma ya ga ta yi ne ya kara mata haiba da kyau a idonsa, har yake jin kamar bata taba burgeshi ba sai yau. Ganin yaki amsa mata sai kallonta yake ta saka ta kwanto da kanta tana leken fuskarsa.
“Ya Maleek”
Can cikin kwakwalwarsa yaji sautin kiran sunansa da ta yi da wata irin siga da yake jin kamar wani be taba kiran sunansa a yadda ya kamata da dadi ba irin yau, matsawa ta yi kusa da shi da gangan ta hura masa iska a cikin ido domin ta ga kallon da yake mata ta gani idan tana ganinta da gaske ko kuma binta ne kawai yake da kallon. Iskar bakinta na isa a fuskarsa kai tsaye ta zarce a idonsa ragowar ta ziyarki hancinsa kamshin bakinta ya daki hancinsa, slowly ya lumshe ido sai tattausan murmushi ya biyo baya. Ita ma murmushin ta yi ta matsa baya.
“Sorry”
Ya bude idon ya kalleta still murmushi yake mata kamar ba shi ba.
“Sorry for what?”
“Na hura maka iska mana, to na ga ina ta fada maka sallah na yi amman baka ji ba, sai kallona kake yi”
“Sallah da kika yi ne, abun da ya bani mamaki kuma ya faranta min rai na ji kin burge ni, shiyasa har na kasa dauke idona daga barin kallonki kin yi abu mao kyau Waira, baki taba burge ni ba irin yau”
Ta kai hannu ta taba zuciyarta dake bugawa da karfi, cewar ta burge shi ya fi komai yi mata dadi, ashe akwai ranar da zata burge shi? Akwai ranar da Maleek zai sake mata fuska haka kuma ya fada mata kai tsaye cewar ta burge shi, a take ta ayyana a ranta cewar kullum sai ta yi sallah domin tana bukatar ta cigaba da burge Maleek, burinta ya zame mata kamar Ameer ta yadda bata tsoron komai akansa kuma zata iya wasa da dariya da shi kamar yadda take yi da Ameer.
[7/26, 9:41 PM] My S Line: 64
Ta mike tsaye tana nade carpet din.
“Kullum zan dinga yin Sallah”
“Hakan yana da kyau, amman ba za a amsa miki ba har sai kin musulumta”
“Me kenan?”
“Kin bar addininki kin shiga na mu”
Ta yi shiru for some minutes sannan ta zauna a kan kujera tana fadin.
“Zan yi tunani”
“Kina da wannan yancin, babu mai miki dole”
Maleek ya amsa mata da murmushi sannan ta kalli stairs ya kalleta.
“Dare yayi ki shiga ki kwanta so that ki tashi da wuri, gobe akwai school”
Ya rausayar da kai shagwabe ta ce.
“Ummi nake jira ta zo ta hada min tea sai na sha zan kwanta”
“Ba ta ce ki rika hadawa da kanki ba?”
Ta bata fuska tana zuba shagwaba ta ce.
“Da dai ayi min”
Ya tabe baki kadan ya mike tsaye.
“Let me help”
Ya nufi kitchen din ya shiga ya hada mata tea ta dauko mata cake ya dawo falon tana zaune saman kujera ya mika mata.
“Karki ci cake din da yawa saboda zaki kwanta karya saka ki ciwon ciki”
Ta karba.
“Thank you”
Ta sauko kasa ta zauna ta fara ci, a kokarinsa na hana idonsa abun da suke son kallo ya ciro wayarsa ya shiga dannawa. Waira sai kallonsa take tana tuna furucinsa na dazun da ya fada nata cewar tana burge shi, kuma gashi a yanzu ya hada mata tea, ba wannan karon farko da ya taba hada mata tea ba amman this one is special ita kanta tana jin haka, ko dan hado mata da cake da yayi kuma ya kawo mata har inda take zaune, kana ya fada mata kar ta ci da yawa saboda kar cikinta yayi ciwo.
“Ya Maleek”
Ta kira sunansa a hankali tana cin cake din, sai ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba.
“Huhmm mmn”
“Me yasa yau kake min kirki?”
Ya kalleta sai yayi murmushi.
“I already told you saboda na ganki kina sallah ne”
“Haka ma Ameer ya ce he can't wait ya gan ni ina Sallah”
Ba tare da tunanin komai ba ta fadi haka tana dariya, sai ta ga murmushi dake fuskarsa ya gushe fuskarsa ta zama kamar wanda be taba murmushi ba. Ganin hakan ya saka ta mike tsaye sai kuma hakan yayi daidai da shigowar Ummi a bangaren tana tafiya kamar wanda bata son zuwa. Waira ta mikawa Maleek cup din tea din.
“Gashi thank you”
Ya kalleta kamar yace ki aje a kasa mana ko ki kai kitchen sai kuma ya ji ba zai iya fada mata ko daya ba, ya samu kansa da mika hannu ya karba ya sunkuya ya aje juyowar da zai yi ya kalli inda Waira take kallo sai ga Ummi ta iso gurin tana kallonsa Waira kuma na fada mata, Maleek ya hada mata tea kuma ta yi sallah, halin da Ummi take ciki ya saka bata maida hankali akan abun da Waira take fada mata ba.
“Yayi kyau, shiga ciki ki kwanta dare yayi”
“Okay good night”
Ummi ta kai hannu ta shafa kanta ta tsayar da hannunta daidai fuskarta tana shafawa fuskarta dauke da murmushi mai wuyar fasssara. Maleek ma mamakin yadda Ummi take kallon Waira yake, at first yayi zaton ko saboda ta yi sallah ne, sai dai jin bata yi magana ba ya saka shi kawar da wannan tunanin ga kuma idanuwan mahaifiyarsa da ya gani da alamar kuka, damuwa ma ta kasa boyuwa a fuskarsa.
“Good night sweetheart, sleep tight”
Waira ta dan yi murmushi sannan ta kalli Maleek ta ce.
“Good Night Ya Maleek”
“Good night”
Ya amsa mata sannan ta nufi stairs rike da dankwalin Ummi da carpet da kuma carjin da ta dauko bata ja ba. Maleek ya bita da kallo har ta haye sama, Ummi kuma ta ke ta kallon Maleek tana karantar abun da Abiey ya fada mata a fuskarsa ta ce.
“Ban taba tsayawa na lura da abun da ya kamata ace na gani ba, shiyasa zuciyata bata tana ayyana min kana son Waira ba....”
Dum-dum-dum yaji wani irin bugawar zuciya da karfi, kamar wanda aka jefowa aradu haka ya ji saukar maganar a kunnensa, ya juyo da fuskarsa daga barin kallon Stairs ya kalli Ummi dake kallonsa with emotional, shi dai ya san be fadawa Abiey yana son Waira ba, kuma be shi ba sonta yake ba to how comes Ummi ta fahimci abun a baibai? Abiey ya fadi haka ne saboda ya toshe duk wata hanya da Ameer zai bi ko kuma shi ma ya masa tsabanin fahimta ne? Sai dai abun da ya kasa yi shi ne karyata cewar baya sonta, ba dan saboda kar ya karyata Abiey dinsa ba, kawai sai dan baya da kuzarin karyata haka ko da kuwa Abiey ne a gabansa a tsaye yake shimfida masa fahimtarsa. Bashi da wannan kwarin guiwar na karyata cewa baya son Waira, kuma ba dan yana sonta din ba, kawai dai yana ganin kamar idan yayi haka ya rage mata kima da daraja.
“ Tsawon rayuwata wannan ranar nake jira, ranar da zaka gabatar min da wata mace a matsayin wadda kake so, ko kuma ni na gabatar maka ka karba, ba tare da ka musa min ba, sai dai abun ya zo min da inda ban zata ba, a wani yanayi da ban yi tsammani ba, ba zan ga laifinka ba, haka ma Ameer ba shi da laifina ne da ban maida hankali na kula da abun da idonka yake a kai ba”
Sai a lokacin Maleek ya samu baki magana domin a dazu jin yayi kamar Ummi ta daure shi da tsarkoki.
“Ba komai ne laifinki ba Ummi, ki daina dorawa kanki laifi babu abun da kika yi a nan”
“Da ace na zama Jarumar uwa kamar sauran iyaye mata, da na dade da lura da haka, da komai ya zo da sauki”
Maleek ya matsa daf da ita sai ta kwanto saman jikinta.
“Mahaifinka ya fada min abun da kake ta boyewa, ban yi zaton abun zai zo da wuri haka ba, kullum addu'a da buri na ga ranar da zaka canja, i wish i could...”
Sai kuka ya ci karfinta. Wani abu ya ji na rashin dadi, irin wanda ki wane dan kwarai yake ji idan uwarsa tana kuka. Sai yayi unkurin fada mata shi ba son Waira yake ba sai kuma ya ji ya kasa, wata kila farinciki take da hakan din ma da Abiey ya fada mata, sai dai shi ya san baya son kowa a ransa. Dan haka ya rumgume yana jin wani sanyi irin na wadda uwarsa take raye da kuma kaunarta a zuciyarsa da tausayinsa. A yanzu ya tabbatar hi miss alot na rashin samun damar rabar jikin mahaifiyarsa da sanin danuwarta tun da dadewa.
“Dare yayi Ummi ya kamata ki samu wutawa”
Ta dago daga jikinsa ta kalleshi sannan ta sauke kai ta nufi hanyar stairs jiki babu kwari. Da kallo ya bita har ta haye sannan ya zauna yana tunanin maganar, a sirance ya yi murmushi ya shafa kansa, be san me yasa abun yake saka shi nishadi ba, saboda Abiey yayi amfani da shi ne ko kuma saboda za a hanawa Ameer ita ne? Abun dai is just funny to him kuma be san dalili ya mike yana murmushin da ya kusan komawa dariya ransa fes kamar an masa albishir da wani abun farinciki. Wayarsa ya ciro ya rika ta da hannu biyu ya shiga message dinsa ya turawa Abiey sako.
“Abiey ban ce ina son yarinyar nan ba fa, me yasa ka fadawa Ummi haka zata yi zaton saboda Ameer ya ce yana sonta ne”
Silly Emoji Abiey yayi masa reply da shi ba tare da yace komai ba, a nan ma Maleek murmushi yayi ya nufi kofar fita daga falon, harabar gidan ya fito gurin motoci ya tsaya yana ta kallon taurarin dake samaniya, yana jin kamar bashi da damuwa ko daya. Can kuma ya sauke kai yana tuna sallah da ya tarar Waira na yi a dazun abu ne mai kyau domin haka na nuna sha'awarta ga addinin musulumci ne. Wayarsa dake hannunsa ya taba ya shiga sashen hotuna ya kama hotonta da ya dauke ta tana bachi yayi ta kallo kamar ba gobe.
A daren Ummi kasa bachi ta yi saboda tunanin da ya zame mata biyu ta rasa ina zata bullo, wane zata dauka wanne zata aje. Sai kusan asuba ta samu runtsawa asuba na yi kuma ta farka ta yi sallah ta fito dakinta kamin ta kawo kasa ta hango mijinta dake kokarin hauro stairs din.
“Na san baki yi bachi ba yau, zaki takura kanki da tunani ne kawai na raya haka saboda ba zo kin kwanta a bangarena ba”
Kamin ta karaso inda yake har hawaye ya cika idonta.
“Ba ni da sauran karfi a yanzu Abiey, dukansu yayana ne, ban san wa zan goyawa baya ba, a zan iya zaba a