Showing 84001 words to 87000 words out of 281271 words
***
Waira na tsaye tana kallon barewar dake ta kiwo ita kadai Ummi ta iso gurin rike da tissue ta dafa Waira, sai Waira ta juyo ta kalleta.
“Kin ce kina so na, amman baki taba hira da ni kin fada min damuwarki ba miyasa? Ina yawan tambayar ina iyayenki suke baki fada min ba”
Waira ta sauke ido kasa.
“Waira bata da kowa, Waira bata san Iyayenta ba, Waira bata san waya haife ta ba, Waira bata ga Babanta ba, bata ga Mamanta ba”
Ta fashe da kuka, sai Ummi ta riketa.
“Wani lokacin barin damuwa a cikin rai ba ya maganin komai, ko da yake fitarwa ma bashi magani, sai dai idan ka fada kana jin sanyi, we all have story to tell, kowa yana da damuwa da burin da yake boyewa a zuciyarsa, Waira na miki alkawari, matukar abun da kika fada gaskiya ne, zan rike ki kamar ƴata wata kila saboda haka Allah ya dubi zuciyata ya yafe min son zuciyar da na aikata a baya, ni ma na rasa farinciki kamar dai, ina da damuwa wacce na boyeta a raina na kasa fadawa kowa, sai dai na san hakki ba zai daina bibiyata ba, tarin dukiya da kayan more rayuwa sun yi kadan su manta da ni kuskuren da na aikata a baya, farinciki a zuci yake na rasa nawa”
Hawaye take sosai tana jin kamar ta samu damar fashe ƙurjin da ya nuna yayi mata tuwa a zuciya.
“Wata kila shaidan ne yake ribantata, amman ina jin son ďana a raina, fiye da sauran ina kewarsa sai kace na taba rayuwa mai tsawo da shi, ina son na hada su guri ďaya matsayin yan'uwa, gabar dake tsakaninsa da Maleek ina son ta wuce na rumgume su biyu a lokaci ďaya, ina son kamin na mutu na roki yafiyarsa kamin ranar da Allah zai tsayar da ni ya tambaye miyasa na aikata son zuciya da abun da nake ganin kamar hanya ce mai bullewa, na manta shi ke kashewa ya raya, soyayya ta rufe min ido a wacan lokaci, ni kawai yarinya ce mai wauta da sakarci a wacan lokacin, hakkin Deen da na iyayensa yana kaina, hakkin Ameer yana kai na, ina son na gyara komai kamin ďan lokacin da ya rage min ya kare, ina son na kyautatawa ďana na fada masa irin kaunar da uwarsa take masa, na roki yafiyarsa, so nake na yi masa gata kamin na mutu amman taya.....?”
Ta rumgume Waira tana kuka, Waira ma kukan take duk kuwa da kasancewar bata fahimta takamaiman dalilin daya saka Ummi take kuka sosai haka ba, kuma take kalaman da bata gane manufarsu ba. Rumtse ido ta yi ta dafa hannun Ummi a kokarinta na fahimta abun da Ummi take fada. Duk abun da suke Maleek na tsaye jikin gilashin windows din ďakinsa yana hangesu, sai dai ko za'a kashe shi ba zai iya fadar abun da suke cewa ba, ko kadam be jidadin hango mahaifiyarsa tana kuka sosai ba, wata kila labarin Waira ne ya taba ta, daman ya san ta da rauni, shi ma da yake dakakken ya ji tausayinta balle kuma ita. Ya cire hannunsa ďaya dake cikin aljihu ya saki curtains din.
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: 28
Ta saki Ummi da sauri ta daga kai ta kalleta, a take ta mance da kalar nata damuwar, tausayin Ummi ya kamata, tsoro da mamaki suka bayyana a fuskarta. Ummi ta yi kasa ta zauna tana kukan data kasa controlling din kanta, Waira ta bita suka zauna a gurin sai dai ita ba kuka take a yanzu ba, mamaki ne ya kusan kasheta da kuma tausayi. Ganin dukansu jiran mutuwa suke yi. Ummi da ta zo da tissue da sunan ta sharewa Waira shawaye sai gashi Waira ta dauko tissue tana sharewa Ummi hawayenta. Cikin karfin hali Ummi ta yi murmushi ta karbi tissue ta share hawayenta, sannan ta mike tsaye Waira ma ta tashi tana kallon Ummi da wani irin kallo da take jin kamar ace yana iko da damar yaye mata damuwarta ta kawar mata da komai, domin ta rike ta kamar yarta bata taba nuna mata kyama ko hantara a iya zamanta a gidan ba, tana ganinta a ciki yanayi na damuwa sai dai ba ko yaushe ba, domin tana kokarin boyewa saboda yayanta da mijinta, hakan ya saka bata taba kokarin netso ta shiga duniyar tunaninta ta hango rayuwar da take boyewa a cikin ranta ba.
“Ummi... Waira tana tana son Ummi”
Ta fada tana kallonta, wani sabon babin kallon tausayi ta budewa Ummi da zarar ta kalleta sai ta hango abun da ta gani daga rayuwarta. Ummi ta rike fuskarta tana dariya.
“Ummi ma tana son Waira, amman ba haka ake cewa ba, kin kasa iya hausa daidai har yanzu, saboda baki bude baki ki yi magana idan ana hira, cewa zaki yi Ummi ina sonki fadi na ji”
“Ummi ina sonki...”
“Yauwa Yata yar albarka”
Ummi ta rumgume ta tana murmushin da kusan ya zame mata a dole a kowa ne wuni da dare, domin mutane suna ganin zahirinta ne baďininta kuma ita kadai ta san abun da take ciki. Sun dade a haka sannan ta riko hannunta suka dawo cikin falon. Yammaci ranar har dare Waira kusa da Ummi ta rayu kamar yadda ta saba wai dai wannan ya kusanci ya fi na baya, ko ina Ummi ta motsa idon Waira na kanta. Dr Zainab suka tattauna maganar yadda Ummi take ganin ya dace da Waira sai dai bata yanke hukunci ba har sai ta ji daga bakin mijinta. Bayan Sallah Isha'i aka sake gabatar musu da abincin da Hanne ta girka, Ummi kuma ta damawa Waira madara da kankara kamar yadda ta saba mata a kowane dare. Tana gama sha ta kwanta akan doguwar kujerar tare da yin matashin kai da cinyar Ummi, Dr Zainab ce ta sauko sanye da gown marar nauyi sai hula a kanta tana rike da wayarta, Juwairiyyya da Yesmin suna dakin Nimra tare da yar'uwarta suna ta hira, Mahmood kuma ya fita tare da Jabir da dan lukuti wato Umar, Maleek ne kawai a Falon sai Ummi da suke kallon wani documentary da ake a Al Jazeera, Hanne ma ta shige BQ bayan gama aikinta a bangaren Ummi domin babu abun da ta rasa a sashenta sai dai kadaici da take fama da shi wani lokaci, kasancewar bata tare da kowa sai ita kadai kanta, da kuma karamin tv da Abiey ya saka mata da startime ta kama channel din da take so a ko wane lokaci. Ummi da Maleek ne kawai ke kallon sai kuma Gwaggon su Maleek wacce ta sauko a yanzu ta zauna tana latsa waya, Waira kam Ummi ce tv ta, daman can kallo ba burgeta yake ba, farkon fara ganin mutane a tv ya tsorata daga baya ta saba sai dai hakan ba saka ta saki jiki ta dauke shi da muhimmanci ba ko wani abun burgewa ba, har yanzu tana kallon wani abun na rayuwarsu dabam da ya sha banban da nata, akwai abubuwa da yawa da bata waye da su ba a tsawon zamanta a gidan, wasu abubuwan kuma basa burge ta, har gobe tana marmarin rayuwarta ta baya kamar yadda bahaushe ya ce sabo turken wawa. Lokuta da dama Ummi zata shigo falon ta tarar kowa yana zaune yana kallo ko taba waya ita kuma hankalinta yana can wani gurin dabam, ko kuma ta boya a bayan kujera ta kwanta idan bata son zama a cikin mutane, shi ma kuma sai idan Ummi bata kusa kamar idan ta leka bangaren Abiey ko kuma wata fitar ta kama ta, ko kuma tana kitchen tana girki.
Time to time Maleek yake jefar Waira da kallo a sace, yana mamakin me Ummi ta fada mata take ta mata wannan kallon a yau, ya san ta saba da kallon mutane har sai mutum ya sargu, ba ma kamar Ummi sai dai wannan karon kallon da take yi mata ya so yayi yawa ko ma yayi. Suna a wannan halin ne Dr ta dauko labarin rayuwar waje wacce ta sha banban da Nigeria kasancewar gidan jaridar suna tattauna abun da ya shafi Africa ne, yadda ake bin doka da order da kuma yadda komai yake a tsare can take ta ba su labari, can jefi Maleek yake sako bakinsa yana fadar wani abun da ya sani a lokacin da Karatu ya kai shi kasar. Shigowa Abiey ne ya tsinke musu hirar waje da suke, annashuwar dake fuskarsa na farincikin ganin yar'uwarsa kuma macen da yake mata kallon uwa abokiyar shawara wacce ke share kukansa tun a wacan lokaci ya saka Ummi jindadi, domin bata da farinciki a yanzu sai an mijinta Abiey. Tsokanarta ya fara yi yana dariya sosai kamar ba shi ba, har buga kafa yake kasa tsabar nishadin da yake ji a yau. Sai da suka yi rabin hira sannan Juwairiyyya da Yesmin suka sauko suka gaishe shi domin ba su san shigowarsa har sai da Ummi ta kwalawa Namra kira. A bangaren ya cire babbar rigarsa ya aje domin yau ko marmarin part dinsa haya yi tsabar murna da farincikin ganin yar'uwarsa, Ummi ta daga kan Waira da ta yi bachi ta aje a kan kujerar a hankali sannan ta tashi ta dauko masa abincinsa ta jera masa komai a inda yake zaune. Abun ka da ďan'uwa cin abincin da Dr Zainab ta yi a dazun be hanata karawa a yanzu da ďan'uwanta yake cin nasa ba, hira suka sha sosai har kusan sha ďaya na dare Ummi tun tana saka baki ana yi da ita har ta fara jin bachi, sai hamma take tana murza ido.
“Toh Sarkin bachi ya fara kawo ziyara ko? Har yanzu baki daina bachi da wuri ba, na dauka duk kin watsar da ragancin nan ai”
Karaf Abiey yayi tare numfashin yar'uwarsa yana shigarwa matarsa.
“Doctor yadda Zahra take da juriya ko ke zaki iya ba a yanzu, duk fa yawancin aikin gidan nan ita take yi, ko bata ti girkin kowa ba sai ta yi nawa saboda ban son abincin kowa sai na matata da uwata kin kuma sani, ai tana kokari ma, da ke ce da yanzu kin yi bachi, ko kin dauka na manta yadda kike ne?”
Dariya ta saka ta girgiza kai, yadda yake tsokanarta sai ka rantse ita ce kanwa shi ne yaya, ko kuma ka yi zaton yan yaya da kanwa ne ba yaya uwa ďaya ba. Maleek ya tashi ya fice daga falon yana murmushi daman ya san halin Abbansa idan yar'uwarsa na kusa baya raga mata kamar yadda ita ma take masa idan ta tashi ramawa. Ummi bata bar falon ba sai da ta kira Mahmood ganin shiru shiru be dawo ba gashi har dare ya fara lulawa.
“Ga mu a hanya, Jabir ne ya debe mu nesa kin san ya kwana biyu be shigo garin ba, amman dai mun kusa isowa gida”
“Toh Allah ya kawo ku lafiya”
Ya ake wayar kusa da inda Waira take kwance ta dauki babbar rigar da Abiey ya cire tare da jakarsa ta nufi bangarensa, ko minti uku bata yi da shiga ba, ya shigo yana cire agogon hannunsa tare da kiranta da sunan da ya saba kiranta tun kurciya har yanzu da girma ya zo, soyayya bata canja ba balle ya sake mata sunan da har gaban yayansa idan ya kama yana kiranta da shi.
“Hiayatee ya gidan?”
Ya aje komai a muhallinsa sannan ta juyo tana taya shi cire rigar dake jikinsa ta dauko masa bathrobe ya saka, sannan ta shiga ta hada masa ruwan wanka.
“Yau ka yi latti dawowa, na yi zaton zaka dawo da rana ma saboda zuwan Aunty Zainab”
“Na so na dawo, amman aiki ya rike ni Wallahi”
“Ya dai kamata ka huta Abiey, yaranka sun kawo yanzu wani abun za su iya maka shi, by the time ka kawo tsufa hutu ya kamata ka samu, muma iyalinka mu samu time dinka”
“Wani abun dole ne sai ka yi da kanka, ko da na so na cire hannuna abokam kasuwancin ba za su bari ba, amman dai komai lokaci ne”
“Kullum haka kake fada, kuma lokacin tafiya yake yi baya jiran kowa Abiey, lokuta da yawa ina jin son kasancewa da kai amman baka da time sai dare ko kuma da safe kamin ka fita, akwai abubuwan da ya kamata ace kana saka ido akansu a gidan amman rashin zamanka baya bari, nima kuma ba kullum nake son kasancewa da yara ba”
“To zamu duba, abun da Hajiya take so shi za'ayi dole, zamu aje abun da zai aju wanda ya kamata a rage kuma za mu rage, har ma da wanda za a bari In Shaa Allah”
“Toh Allah ya bada iko”
“Ameen Allah ya miki albarka”
Ta yi murmushi ta bude wardrobe ta fara ciro masa pajamas, shi kuma ya shiga bathroom din, kamin ya fito ta feshe su da turare ta dauko masa maganinsa na ciwon kafafuwa da yake sha ta aje masa tare da ruwa. Sai da ya shirya ya sha maganin sannan ta fita ta koma bangarenta ta hado masa coffee, a lokacin babu kowa falon sai Waira dake bachi da kuma Plasma dake kunne. Bangaren mijinta ta dawo ta kawo masa coffee da ya saba sha tun can baya ta mika masa kana ta zauna kusa da shi tana labarta masa labarin Waira. Tunanin namijj ba ďaya da na mace ba, haka zuciya ma ta mace ta fi tausayi da saurin yarda. Hakan ya saka Abiey be yi saurin amincewa da labarin da Ummi ta ba shi ba, ba Ummi yake karyatawa ba, Waira ce lamarinta ya ďan daure masa kai.
“Amman ta ya aka yi kika tabbatar gaskiya ta fada miki?”
“Kasan ba tun yau ba, na sha yi mata magana akan garinsu da abun da ya shafi rayuwarta bata fada min komai, idan ka lura bata da sakewa irin yadda ya kamata, kusan kullum a tsorace take bata da walwala, kuma yanayinta sai ya rika min kamar mai tunanin wani abu, wata kila tana tsoron fadar garinsu ne, kar ace za a maida ita”
“Maida ta kam dole ne”
“Tace kasheta fa za'ayi”
“To ya kike son ayi mata?”
“A barta ta zauna a nan tare da mu kawai, gudun kar mu maida ita mu jefata a matsala”
“Hajjaju ai ko zata zauna tare da mu, dole ne sai mun san inda yan'uwanta suke, dole ne mu san garinta da kuma dalilin da ya saka suke son kasheta, ko kuma kina tunanin haka nan kawai za su kasheta ba tare da wani abun ba,? Ko da tana da gaskiya ya kamata mu ji gaskiyarta, kuma idan har zata yarda ta fada mana garinsu ai ba mu kadai ko kuma ita kadai zata tafi ba sai tare da jami'an tsaro, bayan haka kuma za mu sake kafa shaida a gurin jami'an tsaron saboda su san duk abun da yake faruwa ko da wani abun ya taso”
“Ba zan hana a fadawa police ba, amman dai zuwa garinsu ai kamar tona mata asirine idan ma yan garin ba su san inda take ba, ka ga mun bude musu hanya sai su aikata mata abun da suke so, kuma fa ta fada ma Jabir iyayenta sun rasu bata san iyayenta”
Ya kai hannunsa ya dafa kafadar matarsa a kokarinta na saitata a hanyar da yake ganin za au bulle musu.
“Madam, ki zauna da ita ki yi hira da ita cikin hikima ki yi mata tambayoyi ki saurari labarinta ko iya ta nan zamu gane gaskiyarta kuma mu fahimci halin data fito, sannan na sha miki magan akan nunawa yarinyar addini amman baki kula da wannan”
Ya aje cup din dake hannunsa.
“Na kan nuna mata tallar addini ne kawai ban fara mata ba, kuma ka san ba ayi ma mutum dole a addinin musulunci”
“Na sani, amman yanayin mu'amalarki da ita da kuma yadda kika nuna kyaun addinin shi zai saka ta ji tana sha'awar shiga, ya kamata ki rika nuna mata wasu abubuwan”
“Zan yi kokarin yin haka”
“Toh Allah yayi miki albarka, ya bada iko Hajiyata”
“Ameen”
Ta amsa da murmushi, sannan ta mike tsaye tare da daukar cup din tana fadin.
“Bari naje na duba Aunty Zainab”
“Duk ke kadai wai aikin gidan nan be miki yawa ba? Ya kamata dai a kawo miki mai taya ki gaskiya”
Domin kawai ya tsokane ta yayi maganar, sai ya yi sara akan gaɓa ya sosa mata inda yake mata kaikayi.
“Kamar kasan abun da yake raina kenan Wallahi, kawai na rasa ta ina zan fara maka maganar ne”
Dariya yayi
“Kamar gaske, mata ai basa son abokiyar zama balle ke da na san ki da kishi”
“Kishi ai na yara ne ranka ya dade, yanzu mun wuce wannan kuma har ga Allah ina son ka karo wata saboda ka samu mai maka wasu abubuwan ko da bana nan, kara ka saba tun yanzu abun zai fi maka sauki”
Ba fahimci yarenta, hakan ya saka shi nitsawa a duniyar zoyalarta da yake.
“Kuma idan na tashi kawarki zan auro”
“Ai ba ni kawar da bata da aure a yanzu, a dai duba mai mutunci wacce zata son yayanka”
“Hauka kenan ban yi aure da kurciya ba zan yi shi yanzu da furfurata a gemu, yayanki ma ai ba za su bari ta zauna lafiya ba, ke din dai ke ce Allah ya bar min abata har mutuwa ya sa ke za ki min wanka”
Ummi ta yi murmushin da ita kadai ta san abun da take sakawa a ranta sai kuma Allah.
After like 30 minutes da barin Ummi da Abiey bangaren, Mahmood ya dawo gidan tare da Jabir da Umar, ba su shiga bangaren Ummi ba sai suka tsaya a dayan side din da mostly idan aka yi baki a nan suke sauka saboda wadatar gurun kuma an samar da komai a ko wanw ďaki. A waje suka ci na su abincin na dare dan haka ba su damu da leka bangare ba Ummi ba. Maleek kuma be fito daga dakinsa ba sai karfe ďaya saura, ya sauko sanye da nasa pajamas din, Plasma dake kunne ya fara nufa ya kashe, yana juyowa Waira na farkawa sai ta tashi