Showing 126001 words to 129000 words out of 281271 words
ban sani ba saboda ba ni da kusanci da ke?”
Ya dago daga jikinta sai ta zauna gefen gado tana hawaye, shi kuma ya zube kasan guiwowyinsa rike da takardun, cikin fargaba da wani yanayi mai kama da firgici ta mika hannu ta karbi takardun tana dubawa sai gabanta ya fadi, tashin hankalinta da damuwa suka karu, abubuwa biyu za su zo ma iyalinta a lokaci daya.
“Ina ka samu wannan Maleek”
“A cikin jakarki, zuciyata ta kasa samun natsuwa tun daga lokacin da Waira ta furta cewar kina ciwo kuma zaki mutu, tun a ranar babu ranar da bana bincike a dakinki, kawai so nake na samu natsuwa ashe wani karin tashin hankalin ne zan tarar, for how long zaki yi ta boye mana wannan Ummi?”
Ta saka hannunta biyu ta rika fuskarsa kuka yake sosai kamar wani karamin yaro.
“Ko wane bawa da irin yadda Allah yake halittarsa da kuma kalar kabubalen da ake aiko masa, i face alot of challenges tun kurciyata har zuwa girma, bana so yayana ko mijina ya fuskanci ko daya, akwai abubuwa da yawa da za su rushe sanadiyar sanin cewar ina dauke da wannan cutar, ina da burika da yawa da nake son cikawa kamin cikar wa'adin da Allah ya dibar min, za ku hana ni yin abubuwa da yawa idan kuka sani, zaku saka ni yin abubuwa da ban yi niya ba, zan cilasta muku yin abubuwan da ba su kuke sha'awa ba, bana son damuwata ta saks shafar wani, bana son na sake saka kowa a damuwa, Maleek kai Musulmi ne, da ciwo ko ba ciwo idan ajali yayi kira dole aje, sanin wannan zai daga muku hankali har nima ku hana ni kwanciyar hankalin”
Ya saka hanayensa duka biyu ya dafe na mahaifiyarsa da suke kuncinsa ya runtse, tun da yake a rayuwarsa be taba shiga tashin hankalin da ya kasa rike kukansa ba irin wannan, ba taba fuskarta bakinciki kai tsaye irin yau ba, kamar zuciyarsa zata tsage gida biyu haka yake ji.
“Da ace na san da zuwan irin wannan ranar, da na roki Allah ya dauki rayuwata kamin yau. Ina kaunarki Ummi fiye da yadda kike tunani, ina son ki fiye da yadda nake son kaina, ki yafe min bakinciki da na yi ta saka ki Ummi”
Ya karasa yana kama hannayenta yayi ta sumbanta kamar marar hankali. Ganin kamar ya rikece ya saka ta kama kanshi ta dora a cinyarta ta sauke yataunta a saman kumatunshi.
“Na ji babu dadi a lokacin, amman zuwan Waira ya saka na fahimci ba a ra'ayin kanka kake min abun da kake yi ba, shiyasa na cilastawa mahaifinka kuma na jaddawa kaina neman maka magani a gurin Allah, na fadada addu'ar da nake har zuwa kasa mai tsarki, kuma na yi da magiya a gurin Ubangijina kalli yadda rayuwa ta zama a yanzu, ka canja Maleek, kana mu'alantarmu kamar ba kai ba, kasan tsawon lokacin da na dauka ina jiran ranar da zaka rumgume ni a matsayin uwa? Ina da burin ganin rayuwarka ta canja Maleek, da ace zan samu aron lokaci zan so samun ganin rayuwarka da iyalinka, kuma na ga hadinkanka ga yan'uwanka”
Ya dago ya kalleta bakinsa na rawa.
“Zaki gani Ummi, duk wani buri da kike da shi a duniya sai na cika miki shi Ummi i promise you, Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un”
Ya furta ya runtse ido yana girgiza kai, be tana jin tsoro irin na yanzu ba, domin abun biyu ya zame masa tsoron rasa uwa, da kuma tsoron rayuwar da zai yi da ita a yanzu a matsayin marar lafiya, ya san abun da zai yi da cinsa ne...
Wayarta dake jaka ta fara ringing, amman ta kasa motsawa daga inda take balle ta amsa, kusan sau uku ana kiran wayar bata amsa ba, hannunta hana kan danta tana shafa kansa hankalinma yana gurinsa. Suna a wannan halin Mahmood yayi knocking sannan ya turo kofar dakin ya shigo rike da wayarsa a hannu, jimm yayi jikin kofar kamar mai tsoron karasawa inda suke, tunaninsa be bashi komai ba sai abun da ya faru a dazun a game da Ameer. After taking deep breaths the ya motsa jiki ya shiga cikin dakin, hi pick up some papers da suke gurin, his mind ia tell him maybe evidence ne da za su tabbatar masa da abun da Ummi ta fadawa Ameer a dazun, domin shi ma dai yana jin kamar be gamsu ba, sai dai be mata maganar miyasa ta fadi hakan, da gaske ne ko kuma tana bawa Ameer din tsoro ne? Duk ba bukaci sani ba, abun da yayi shi ne shiru ya bude mata mota ta shigo ya kawota gida.
Sai dai abun da ya ci karo da shi sai ya kawar da wacan damuwar da tunanin gaskiya ne ko kishiyarta, hausawa suka ce sawun giwa ya take na rakumi, hankalinsa be tashi kamar na Maleek ba, domin shi ya san da matsalar, sai dai ganin matakin da take a yanzu ne. Juyawa yayi ya fice daga dakin rike da takardun ba tare ya fada mata abun fa ya kawo shi dakin ba. Kai tsaye bangaren mahaifinsa ya nufa a sitting room ya samu Abiey zaune cikin yanayi dake nuna ransa a bace yake.
“Ina take?”
“Abiey me yasa kake nemanta?”
“Idan zan ga matata sai ka ba ni izini ne?”
“No tun da naji ka ce ka kira sau uku bata daga ba...”
Be karasa ba Abiey ya tari numfashinsa.
“Kuma sai na kira ka na ca ka sanar da ita ina son ganinta ba”
“Ban fada mata ba saboda na tararda da ita a yanayin marar dadi, ban sani ba ko zaka yi mata magana akan abun ya faru ba ne?”
“Ta fada maka ne? Ko kuma an yi a gabanka?”
“An yi a gabana, and think this is more important da kiran da kake mata”
Ya mika masa papers din da suke hannunsa. Kallonsu Abiey yake kamin ya mika hannu ya karba... Kasa duba sauran yayi sai ya dago da sauri ya kalli Mahmood.
“What is this? Na waye?”
“Na Ummi ne, wannan ne abun da take boye mana na tsawon lokaci”
Ya amsa yana kawarda fuskarsa saboda hawayen dake cikin idonsa. A take zuba ya karyowa Abiey.
“Is this a joke?”
“Wa zai yi wasa da irin wannan ciwon mai tsada? Gaskiya ne Abiey”
Abiey ya shiga kansa daga goshi zuwa keya kamar mai alwala, ya mike tsaye ya nufi kofar fita sai kuma ya juyo ya dawo ya zauna jin kamar kafafuwanshi ba za su kai shi ba.
“A ina ka ga wannan?”
“A dakinta, she's with Maleek”
“Lahaula wala'kuwwati illa billah, Ya Ilahi”
“It so hard, why do we have to face this at this age?”
Mahmood ya fada cikin muryar kuka. Abiey ya kalleshi.
“Amman ka tabbatar ta kardunta ne?”
“Ga suna a jiki Abiey? Kuma ko bayan takardu ni na dade da sanin wannan ciwon saboda na tana tararda da ita a daki gashin kanta na cirewa, amman ta hanani fadawa kowa, ina ta ajiyar wannan abun a raina kuma yana ci na, ko wane duba idan na yi mata da ciwon nake mata shi”
Abiey yayi shiru yana tunawa lokutan da yake yawan ganin gashinta a gadonsa sai tace maskin dare ne yayi mata aski, the ciwo da take da yanayinta, da yawan bashi results din cewar Likitoci ba sun ce hawan jini ne sai Ulcer, sai a yanzu yake fahimtar he make a big mistake da ya fifita aikinsa da wasu abubuwa be tsaya ya kula da yadda matarsa take gudanar da rayuwarta, how comes yana mijinta ace be san ciwonta? Ta ya be fahimci halin da matarsa abar kauna take ciki ba tuntuni.
“Amman da ka sani ko a boye ne sai ka sanar min, akan me za a boye irin wannan ciwon? Ko hiv take dauke da shi ya kamata na sani balle leukemia kasan hadarin wannan cutar?”
“Ita ta bukaci kar na fadawa kowa, ni ma kuma sanin da na yi be wuce shekara da wani abu ba”
Abiey ya dafe kansa ya runtse ido yana jin duniyar na juya mishi. Can ya dago yayi ma Mahmood alamar ya fita da hannu.
AMEER POV.
Barin gidan yayi gaba daya bayan ya fito bangaren mahaifinsa, tunani kala kala akan maganar karshe da ya tarar Daddy na yi a waya, be gamsu da abun da ya ji yana fada ba. Ta dayan bangaren kuma zuciyarsa na ta son ya tattauna akan kalaman Ummi. Tuki yake yana tunanin kiran Hajiya Jamila duk kuwa da mahaifinsa ya ce kar ya kirata, but he need to ask her few questions, wata kila ita da Ummi sun san juna if not Ummi ba zata ambaci sunanta ba. Be ankara ba ya ji an bugu bayan motarsa da karfi a lokacin da ya karyo kwana, a take ya faka burki, daman mai nema a duhu balle an haska masa, da dai shi ya bugu motar wani ba zai tsaya ba, amman tun da tasa motar aka daka dole zai duba. A fusace ya bude motar ya fito wanda hakan yayi daidai da fitowar Jabir a tasa motar dake bayan ta Ameer.
“Sorry please amman kai ne mai laifi domin baka duba ba kawai ka hau babban titi”
“Oh Really saboda titin na Ubanka ne? Ni da motata zaka fada min ban duba titi ba? Baka tukin hankali ka yi shaye shayenka sannan ka fada min maganar banza....”
“Amman dai daga ganinka baka da tarbiya, daga magana sai ka fara zagin mutane...”
Jabir ya mayar masa a fusace yana nunashi. Ameer zai yi magana idonsa ya sauka akan Waira dake zaune gaban motar ta runtse ido sosai ta dafe kunnuwanta tun a lokacin da motarsu ta bugu da Ameer. Wannan ne karo na biyu da ya sake ganin kyakkyawar fuskarta a garin Abuja, at first ba zai manta ba a school bus ne, sai kuma a nan sai dai ya kasa tuna a inda ya fara ganinta, wata kila kuma kyauta ne yake rudarsa har yake ganin kamar ya santa. Kamar an masa allurar kwantar da tarzoma haka ya rasa duk wani kuzari da zafin zuciyar daya fito da shi da zimmar yin fada da wanda ya bugar masa mota. Yadda yake kallon Waira ya saka Jabir juya ya kalleta ya juyo ya kalleshi sai suka hada ido, Ameer be sake ce masa komai ba ya juya ya nufi motarsa ya shiga. Da kamar mamaki Jabir ya koma ya shiga motarsa yana rufe gambun sai Waira ta kara firgita ta kamkame kanta jikinta ya fara rawa.
“Hey ba fa hatsari muka yi ba bude idonki”
Ta girgiza kai alamat ba zata bude ba, har Jabir yayi baya yaja motar suka wuce bata bude idon ba.
“Gida nake so”
Ta fada tana son yin kuka, daman can bata gama wankewa daga tsoron mota ba, gashi kuma yanzu sun bugu motar wani.
“Babu abun da zai sake faruwa fa, kuskure ne kawai aka samu, shi ya shigo gurin da karfi be duba ba”
“Aa ina son gida gurin Ummi please”
“Shikenan bude idon to”
Ta girgiza kai gani take kamar hatsarin za su sake yi.
“Idan baki bude idon ba ba zan maida ke gida ba, that's the rule”
Ta bude idon kadan ta kalli titi sai ta yi saurin maida idon ta rufe, bata bude ba har sai da ta ji ya faka, a kokarinta na tantance inda take ya saka ta bude idon, wani katon shopping mall ne da ya ji ado tun a waje.
“Zauna a nan ina zuwa”
Ya bude motar ya fita, this time around hankali kwance take kallon gaban mall din. Be dade ba ya fito rike da leda, side dinta ya bude ya dora mata ledar saman jiki. Kamin ya zagaya ya shiga motar har ta bude ledar few abubuwa ne a ciki, chocolate, biscuits, sai wani katon milk candy dake cikin gwangwani mai kyalli kamar an watsa masa zinari.
“Na ki ne you can eat, dan dana na ji akwai dadi”
Ba ko wane kalar abu take ci ba, dan haka bata taba komai ba sai chocolate shi ma saboda rubutun chocolate ne a jiki, tasan ba irin wanda ta saba ci ba, sai dai a yadda ta fahimta ko wane chocolate yana da dadi sai dai dandanonsu ya babanta. Bakinta ta saka a take hakoranta dake da kaifi suka yanke mata ledar sai ta yaye ledar daga sama ta fara ci a hankali.
“Akwai dadi?”
Ta daga masa kai, bata san rowa ba dan haka ta gutsura rabi ta mika masa. Yayi murmushi yana girgiza mata kai
“Sha abun ki ni bana shan kayan zaki”
Ta rike da dayan hannunta idan ta ci na hannu dama sai ta ci da hagu, shi dai be ce mata komai ba har suka isa gida kamar yadda ta bukata, ba tare da ya je inda yayi niya ba.
[6/24, 4:36 PM] My S Line: 42
A gurin ya tsaya yana kallon motar su Jabir har ya ja suka wuce, sannan ya faka tasa gefen titin. Daman fitowa kawai yayi daga gidan ba dan yana da gurin zuwa ba. Sosai ya zurfafa a tunani yana son gano inda ya san Waira ko ya taba ganinta amman ya kasa, kallon da yayi mata a mota ma yanzu ya ki ya fita idonsa, sai da yayi da gaske sannan ya iya focusing akan abun da ya kamata ace shi ne a gabansa ba tunanin kyaun wata yarinyar da bata san da zamansa ba, kuma karamar yarinyar kanwar kanwarsa ba ma babbar mace ba. Ac motar ya kara sannan ya dauki wayarsa dake aje a inda ya saba aje ya yi dialing number Ammynsa. Kiran farko bata daga ba haka ma na biyu da na uku sai da yayi mata na hudu sannan ta daga.
“Ameer my son how are you?”
“I'm good Ammy”
Ya kai hannu ya rage ac jin kamar baya bukatarshi kuma.
“Ammy wani abu nake son na tambayeki, i don't want you to lie to me, kin san na yarda da ke, karki rushe wanann amince da ke tsakaninmu, kuma karki dubi Daddy ko ni ki fada min abun da ba gaskiya ba please..”
“Mene ne haka zaka tambaye ni Ameer?”
“Daddy ya kira ki?”
Ta yi jim kamar mai son ya canja mata tambaya.
“Eh ya kirani”
“I know na tambaya ne saboda na tabbatar zaki fada min gaskiya ko akasin haka, seriously bana son ki fada min abun da ba gaskiya, idan kika min haka zai yi wuya mu sake shiri da ke, you know how much i love you ko? Kin san ke na kallo kamar uwata right”
“Ni din ma uwarka ce Ameer, tambaye ni duk abin da kake so na maka alkawarin zan fada maka gaskiya”
“Akwai wata mata da na hadu da ita dazun, ta fada min maganar ban da da maganarta ba sai dai kuma sunanki da ta ambata ta ce na aje na tambaye ki idan kina raye ya saka na ji kamar akwai kamshin gaskiya a ciki....”
Sai da ya fara bata labarin abun da ya faru tsakaninsa da Maleek duk kuwa da ya san Daddy ya fada mata komai, sannan ya dora da abun da ya shiga tsakaninsa da Nimra zuwa yau da Ummi ta fada masa wannan maganar.
“Me kika sani game da ita?”
“Ameer”
Ta kira sannanshi a a hankali, sai ya amsa yana duban agogon hannunsa.
“A ina kake?”
“Ina kan hanya”
“Tuki kake?”
“Aa”
Ya amsa tare da bude motar ya fito.
“A tsaye kake”
“Eh yanzu na fito mota”
“Nemi guri ka zauna”
Ya koma cikin motar ya maida gambun ya rufe gabansa na faduwa.
“Akwai wani makami ko wani abun da zaka iya yi ma kanka rauni a kusa da kai?”
Ya juya ya kalli wukar da ya dauko daga restaurant, wadda ya firgita Humaira da ita.
“Eh”
“Matsar da shi”
Ya kai hannu ya dauki wukar ya bude motar ya fita ya jefar da ita sannan ya dawo cikin motar ta saka wayar hands-free ya lakata a mazaunin ta dake cikin motar.
“Done”
“Yarona akwai ruwa kusa da kai”
“Akwai ruwa a motar Ammy just go on”
“Matar da ta fada maka haka fara ce?”
“Fara ce sosai”
“Sunanta Zahra right?”
“Ban san asalin sunanta ba, amman dai Ummi Nimra take kiranta”
“Ita da mijinta yan asalin garin Kano ne?”
“Nimra ta taba fada min haka”
“Wani labari zan baka da ya shafi rayuwata, kuma ya gurbata zamana da mahaifika, ya nisanta ni da kai”
Ya gyara zamansa a cikin motar.
“Ina saurarenki”
“Mahaifinka ya taba baka labarin shekarun da muka dauka ba mu haihu ba?”
“Ya fada min”
“Amman be fada maka miyasa ya rabu da ni ba?”
“Har yau be fada min ba”
“Ameer na kwashe shekarar da ta kusa goma a tare da Mr Bashir, Allah be bani haihuwa ba, na yi iya yadda zan iya ta bangaren asibiti na da hausa amman Allah be bani ba, sai a yanzu na gane ashe ba a rubuto ni cikin wadanda za a rabawa kyautar yaya a duniya ba, yan'uwan mijina suka tsangwame ni, ni ma kuma na matsawa kaina, idan na ga yaya kamar na sace nake ji, ko kukan jariri naji sai hankali ya tashi, Ameer akwai kunci da damuwa matuka a zuciyar uwar da bata taba amsa sunan uwa a bakin jininta ba, ni kadai na san irin kuncin da mace take ji a lokacin da take sha'awar dandana azabar zafin nakuda da dawainiyar daukar ciki. Hankali ya tashi matuka a lokacin da mahaifinka ya gabatar min da magana aure, ina ta jin tsoron kar wata ta zo ta haihu ya juya min baya, duk kuwa da kasancewar ban ga alamar haka a tare da shi ba, a lokacin idan na hana shi aure ban masa adalci ba, kuma yan'uwansa ba za su kyale ba, ina ji ina gani aka daura masa aure sai zuciyata ta kasa hakuri har na fara bin bokaye, duk mace da ta shigo sai a fitine ta ta kasa zaman auren, a haka har ya auri mace hudu dayar har bari ta yi amman ban barta ta zauna ba, sabida jna kaunar mijina sosai. Daga baya na samu wani likita ya ba mu shawarwari akan hanyoyin da zamu bi mu samu haihuwa, a ciki akwai dashen kwan haihuwar, bayan ta tabbatar mana da cewar ni da shi duk bama da matsala zamu iya haihuwa a duk lokacin da Allah ya so, sai na kasa hakuri shi kuma ya ki ya amince