Showing 147001 words to 150000 words out of 281271 words
abun tashin hankalin zan haifar ba”
“Waya fada miki ba shi da lafiya?”
“Zuciyata ce, na ji bana da natsuwa har sai na zo na duba shi”
“Duk da haka dai, ni da shi duka muna karkashin kulawar Mai gidan ne, be kamata na yanke hukunci ba tare da saninsa ba, ko da kuwa baya kusa balle ma yana cikin gidan saboda yau weekend ne, bari na kira shi ku yi magana tukuna”
Ummi ta amsa mata da kai, zuciyarta na raya mata Mr Bashir ba zai bari ta ga Ameer ba. Mommy ta tashi ta nufi wata kofar sai kuma ta juyo ta kalli Ummi.
“Ke ce matar da aka ce kin ce Ameer ďanki ne?”
“Ba ance ba ne, Ameer ďana ne zan iya tutuya da fadar hakan a gaban kowa”
Ummi ta amsa mata kai tsaye ba tare da ka kalleta ba. Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta fice daga falon. Bayan ficewar Mommy Ummi ta dora jakarta a kan kujera tana ta sake sake a ranta. Ummi ta yi zaman da kai minti ashirin a falon sannan ta ji muryar Mr Bashir kamar daga sama.
“Ban yi zaton na karya daya daga cikin alkawuran da na daukar miki ba, me zai saka ki bada kyautar da zaki dawo daga baya ki tambaya”
Ummi ta juyo tana kallon Mr Bashir da ya tunkarota fuskarsa dauke da damuwa, duk yadda ya shirya yin fada da Zahra da yi mata barazana da duk wani abun bacin rai sai ya ji lagunsa ya karye a lokacin da kalli fuskarta, kwarjininta ya cika idonsa har ya ji kamar yana gudun bata mata rai.
“Ni ban yi zaton zan tambaya ba, fadar gaskiya ko kuma bayyana ta baya nufin canja komai daga alakarku da Ameer, kawai dai ina son na yi duty na a matsayina na uwarsa, ina son na gyara komai kamar yadda na bata”
Mr Bashir ya kalli Mommy bayan ya zauna.
“Ba mu guri”
Ta mike tsaye ta haye sama, sai da Daddy ya tabbatar ta shige dakinta sannan ya kalli Zahra ya ce.
“Wani ya taba kai miki gulmar Ameer ya rasa wani na gata ko kewa daga uwa?”
Ta girgiza kai.
“Aa na kasa jurewa ne, fiye da yadda ka kasa jurewa a yanzu da kake ganin kamar zan rabaka da shi ne, kai kenan balle kuma ni da nake uwa? A ko wane dare ina kwana da kaunar Ameer a raina da kewarsa, na baka amanarsa ne saboda ma gamsu zaka kula da shi, bayan na yi hakan kuma zuciyata ta kasa natsuwa da abun da na aikata, na cutar da wasu domin ba ni kadai nake da hakki da Ameer ba, tsoron hukuncin da zai biyo baya da kuma kurciya a wacan lokacin na cewar idan suka san na siyar musu da jika, kuma ina ganin kiyayyar ďana a cikin idon mijin da nake aure a wacan lokaci shiya karya min guiwar duk wani buri da nake da shi, kai ma zai taba mutumcinka shiyasa na bar komai ya tafi kamar yadda muka tsara, ban yi zaton Allah zai sake dawo da Ameer a kusa da inda zan ganshi ba, sai gashi ya kulla alaka da ďan'uwansa kuma ya zaunar da mu a gari daya, na furta masa hakan ne a lokacin da hankali ya gushe saboda abun da ya aikatawa yarinyar da na yi riko kuma na shayar da ita da nono na, wanda sanin kanka babu aure a tsakaninsu, duk abun da ba mu sani ba, Ameer daman ba son ta yake ba, kawai ya shirya hakan ne saboda ya dauki fansa na gabar dake tsakaninsa da Maleek, sai kuma aka yi daidai da ajali, ya fada mata gaskiya a lokacin da zuciyarta ta kasa dauka har sai da zuciyarta ta buga aka kwantar da ita asibiti, kuma rai yayi halinsa mai ajiya ya karba jiya aka yi sadakan ukun”
“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un
Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un
Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”
Shi ne abun da yake ta fita a bakin Daddy ya cire hular kansa ya dafe kansa, Ummi ta sauke kanta kasa tana hawaye.
“Da ace Ameer ya aureta, ko sun aikata wani kuskuren laifin waye? A yanzu ma da ta rasu laifin waye? Kai ma uba ne ka bude zuciyarta ka kalli yadda zaka ji idan hakan ya faru da kai, Maleek da Ameer gaba suke da junansu bayan kuma su yan'uwan juna ne, idan na fadi na mutu a yau wace amsa zan bawa Allah? Na aikata abun da na aikata ne saboda ina tunanin mahaifinsa zai rayu, na aikata saboda ba ni da mafita, talauci ne silar komai a yanzu kuma ba arzikinka nake so ba, so nake na gyara komai ina da wasu yayan kuma mai arziki nake aure a yanzu idan har saboda kudi ne to me zai saka na yo haka? Me na rasa? Ina ta kokarin kaucewa amman kaddara ta rubuta haka, shiyasa har Nimra ta gabatar mana da Ameer a maysayin wanda take son aure, bayan shi yar'uwarta Namra kuma ta gabatar mana da ďan likitan da yayi min hanyar ganin Hajiya Jamila wato yayanta a matsayin wanda take son aure, me ka gani shim ke kamata mu bawa kaddara damar rubuta abun da ta tsara akan mu ba? Idan na kauce wannan to abun nawa ya zama son kai, dan Allah ka ba ni dama ni ma na wanzu a rayuwar Ameer ya kalleni a uwa kamar yadda yake kallonka a mahaifi”
Ummi ta karasa tana saukowa daga kan kujera ta zube kasa kamar zata roke shi. Sai yayi saurin mikewa tsaye ya girgiza kai.
“Ameer be yi lalacewar da uwar da ta haife shi zata duka ta roki wani abu ba, idan har wani zai tsuguna ya roki wata alfarma to ni ya dace na duka na yi miki godiya kuma ya roki Alfarmar ki bar Ameer ya cigaba da zama a matsayin ďana, dan Allah koma ki zauna”
Ummi ta tashi ta zauna kan kujerar, Mr Bashir ya zauna a karo na biyu yana kallon fuskarta tausayinta shimfide a fuskarsa.
“Allah ya mata rahma, hakika ban tarbiyar da Ameer da wata kalar tarbiyar makamanciyar wannan ba, sai dai rayuwa da kuma jarrabawa babu ta inda bata zuwa, ni kaina halayen Ameer sun jefa ni a cikin damuwa kala kala, sai dai be kara min komai ba sai kaunarsa, a da ina ganin kamar kin yi hakan ne saboda ki yake ni, sai dai a yanzu na fahimci ba mu isa mu yi ma Allah wayo ba, kuma Ameer deserve to know the truth, My condolences”
“Ameen”
Ummi ta amsa tana share hawayenta.
“Sai dai idan zai yiyu ki yi hakuri ganin Ameer ba zai samu a yanzu ba, ba dan ina nufi gina wani abu a tsakaninku ba, domin kin min komai kin rufa min asiri a lokacin da makiya za su min dariya, gaskiya kika fada bayyanar cewar Ameer ba ďana ba ne a yanzu babu wanda zai ji sai idan mun so ya sani, amman a wacan lokacin da hakan ya faru da na sha kunya da kunci matuka, kin min kyautar ďa sukutun da ya hana ni kewar rashin haihuwa, ko a haka kadai kin cancanci na yi miki komai a yanzu, kin aikata abun da kika aikata saboda ki ceto rayuwar mijinka na farko, sai dai hakan ya gagara saboda rai baya tsayawa dan wata rai, kuma kin hakura kika danne abun da kike ji ranki saboda farincikin mijin da kike aure a yanzu, maddallah da ke Zahra hakika ke mata ce ta gari”
Ummi ta sauke ajiyar zuciya tana sanyi a ranta na saurin fahimtarta da Mr Bashir yayi domin ba ta yi tsammanin zata same shi haka cikin ruwan sanyi ba.
“Na gode, amman me yasa ba zaka bar ni na ga Ameer ba?”
“Saboda ni mahaifinsa be, duk wani abu da zai jefa Ameer a damuwa bana sonsa, kwanansa biyu babu lafiya, abincin kirki baya iya ci, ko aiki baya fita kuma ina tunanin duk saboda faruwar wannan abun ne ya haifar masa da damuwa, yau ne muka samu ya dan sake har ya fita harabar gida yana dan hutawa, ina tsoron kar ganinki ya dawo masa da damuwa ko ya haifar masa da wata matsalar domin har yanzu be gama fahimtar rayuwar da kika bijiro masa da ita ba”
Ummi ta yi shiru, bata son takurawa domin ita ma din kamar shi take bata son damuwar Ameer idan har ganinta zai haifar masa da damuwa yo zata iya hakura.
“Daman dai na zo na duba lafiyarsa ne, ssboda zuciyata ta kwadaitu da son ganinsa, tun da na ji lafiyarsa Alhamdulillah wannan ma kadai abun farinciki ne a gurina”
Ta mike tsaye ta dauki jakarta.
“Ka taimaka min gurin shawo kan yaron nan dan Allah, ya yafe min abun da na yi masa”
“Ba zamu iya cilasta shi ba, amman a hannu zai fahimta mu bashi lokaci”
Ta amsa masa kai sannan ta ce.
“Na barka lafiya”
Binta yayi da kallo har ta fice sannan ya girgiza kai ya sauke ajiyar zuciya.
AMEER POV.
Tun a safiyar da ya raka gawar Nimra makabarta ya dawo gida zazzabi ya rufe shi, be sake lafiya ba sai yau shi ma kuma ba wadatarsa ta yi ba, ya dai samu kuzari ba kamar kwana biyu da yake wuni da zama a daki ba, har sai da Daddy ya kira Family Doctor su ya duba shi ya rubuta magani aka siyo masa ya sha, abinci sai Mommy ta matsa masa ya ke dan ci, ko kuma Daddy ya saka a kira shi bangarensa su ci abincin a tare duk yadda Daddy yake jans ada hirar duniya saboda ya sake ya kasa yin haka, idan kuma ya dauko masa zancen Ummi sai kawai ya tashi ya fice ya bar Daddy. Sai dai ya tashi jikinsa da dan sauki bama kamar da yamma nan da ya sha energy drink. Kewar Nimra da tunanin rayuwarsa da yayi ta baya kamin komai ya lalace ya saka shi fitowa yana ta yawo a compound din gidan, kamin daga karshe ya tare a garden da yar sarewarsa yana busar dake deba masa kewa da kadaici. Vest ce a jikinsa sai Jean baki da talkamin da suka fi kama da silifas. A tsaye yake yana busar a tsakanin ruwa swimming pool da kujerun da aka ware na kwanciya a huta. Be sararba ya ji an rumgume shi a baya ana kuka. Cak ya tsaya da busar yana sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa da mugun karfi, bugawar da be taba jin irinta ba, bugawar da ta wuce kima, har take neman danne numfashinsa. Da sauri ya juyo sai yayi arba da kyakkyawar fuskar da zuciyarsa ke raya masa be ga wata macen da ta fita kyau ba on earth, hawaye ke mata zuba jikinta rawa yake bakinta na motsi kamar ta yi masa magana kuma ta kasa furta komai, kanta a sama tana kallonsa domin yayi mata tsawo sosai kamar yadda Maleek yake mata kasancewar ba wata mai tsayi sosai ba sai dai kuma ba zaka kirata gajera ba.
A yanzu kam baya bukatar tuna inda ya santa ko ya ganta, ya fahimci wacece ita tun a karon farko da yayi arba da ita a gidan Ummi, sai dai siffarta gaba daya ta canja sam ba zaka ganta a yanzu ka ganta a can baya kuma ka ce mutum daya ne ba, sai dai kamanin da suka zo daya.
“Me kike so?”
Ya tambaya sai ta rumgume shi ta fashe da wani kukan, rayuwarta ta baya ta tuna mata, rumgumar da ta yi masa ta farko ta rumgume shi ne ba dan tasan waye ba, a yanzu ta gane Ameer ne hakan ya bata gwarin guiwar sake rumgumeshi domin a gurinta ba laifi ba ne, kasa motsi yayi har sai da ta gaji da kukan ta dago kanta.
“A ina ka iya wannan busar? Waya koya maka?”
Wannan ne karo na biyu ta ji yayi busar bayan busar da yayi a cikin dajin lokacin da take boye. Yawo yake da idonsa a fuskarta kamar mai kirga abu.
“Ya aka yi kike magana? Waya kawo ki nan?”
“Ka fara amsa min ni”
“Wani ne ya koya min”
“Wani wa?”
“Baki san shi ba, waya kawo ki nan?”
Amsa mata yake yana tambayarta idonsa akan kyakkyawar fuskarta mai daukar hankali ko kyabtawa ba yayi, wani irin kallonta yake kamar zai cinye ta, irin kallon nan dake tafiyar da hankalin mai yinsa ya mantar da shi a inda yake da duk wata damuwa da yake ciki.
“Ya aka yi kika zama haka? Ya aka yi kike iya magana yanzu?”
Ya kama hannunta yana dubawa, ko tabo babu balle alamar cizon maciji.
“I have so many questions for you Girl, you change alot, kamar dai bake ce yarinyar nan ba”
“Ni ma ina da tambayoyi da yawa”
Ta amsa tana fisge hannunta daga riko da yayi mata.
Ya dafa kansa ya daga sama.
“Oh my God”
Gani yake kamar ba ita ba ce, a lokacin da ta yi masa magana a gidan Ummi hankalinsa ba akanta yake ba dan haka be yi realize duk wani abu da ta fada ba, shi dai ya san ta rumgume a sa'ilin da kasa rabata da jikinsa kuma ya kasa ce mata komai har sai da Yesmin ta fisgeta a jikinsa.
“Ya Maleek ya kawo ni”
Ya dawo da kansa kasa ya kalleta.
“Fada min waya koya maka wannan busar?”
“Me yasa kike son ki sani?”
“Saboda mutum daya yake wannan busar, wani be isa ya ko yi yadda ake yi ba, kai ya aka yi kake yi? Ina Eid?”
“Eid..? How do you know him?”
Ya tambaya yana karin hancinta. Kamin ta amsa masa ya nufi hanyar fita Garden din tunawa da yayi ta fada masa Maleek ya kawo ta, me Maleek zai kawo ta yi me yasa ya kawo ta? Ta fada musu tana da alaka da shi ne.
“Ina Maleek din yake?”
“Yana can waje”
Ta nuna gate tana biyo bayansa, da sauri ya nufi gate din ya bude ya fita. Maleek na tsaye yana kallon wasu gidajen, zuciyarsa cike da haushin Ameer, saboda Ummi kawai ya tsaya nan ba dan ita ba da babu abun da zai tsayar da shi a kofar gidan.
“What now? Me ka zo yi?”
Ameer ya fada yana daga bayansa tsaye, Maleek na jin haka ya saka hannayensa aljihu ya cigaba da kallon da yake, sai yayi kamar be san da mutum bayansa ba.
“Are you here to celebrate?”
Maleek ya bawa banza ajiyarsa, domin ya san idan har ya juyo yayi masa magana to ba zai fada masa mai dadi ba, shi a yanzu baya ma son ganin Ameer din da idonsa.
“All those years kana min kallon wani kalar mutum na dabam right? Saboda kansan gaskiya, boye gaskiyar me ya haifar? Da ace na san gaskiya da ban yi soyayyar karya da kanwarka ba”
Sai a lokacin Maleek ya juyo.
“Matsala ta da kai kenan, kai ba shaye shaye ba, sai surutai kala kala, ka san mun rasa Nimra kenan? Amman kake tsaye a nan kana fada min magana marar kan gado? Saboda ka zama ďan Ummi sai na yi celebration?”
Maleek ya kara takowa ya isa daf da Ameer.
“No na ji ba dadi ne saboda Ummi bata cancanci ďa kamar kai ba, arrogant, wanda be iya komai ba sai son kai da wulakanta mutane, Ameer har duniya ta nade ba zan manta cewar kai ka yi silar mutuwar Nimra ba, kuma ka gode Allah Ummi tana tare da kai, ka ci albarkacinta saboda ka zama daga tsatsonta, if not Wallahi da sai na saka nadamar da sai ka yi nadamar haihuwarka da aka yi”
Ameer yayi murmushi.
“Kai kasan waye ni Maleek ba yi wani wanda zai saka ni nadamar ba, sai dai idan na ga lokacin nadamar yayi na yi dan kaina, ka ce Ummi bata cancanci ďa kamar ni ba, sai kuma ga shi ta hada jini da ni? Ya aka yi?”
Fitowar Ummi ce ta saka duk suka kalleta, tana ganin yadda suka yi kirko kiro ta san ba lafiya ba, sai dai ganin Ameer da ta yi ya kawar mata da damuwar sanin dalilinsu na tsayuwa har suna fuskantar juna kamar abokan gaba.
“Ameer ďa na, i just come to check on you”
Ta kai hannu ta taba shi sai ya kauce ya matsa baya, ya dauke fuska.
“This should be the last time da zaki zo duba ni, ba ki ba ni kulawa a lokacin da nake bukatarta karki ce zaki yi kokari yi a yanzu”
Maleek ya watsa masa wata uwar harara yana jin kamar ya shaki wuyansa. Sai dai shi mutum ne dake kokarin danne abun a zuciyarsa dan haka ya budewa Ummi mota.
“Ummi shiga muje”
Ummi ta kalli Motar sannan ta sake kallon Ameer cikin wani yanayi mai kamar na tsoro ko fargabar zuciyar Ameer ta ce.
“Akwai abubuwa da yawa da ya kamata ka sani, ka ba ni dama na bude maka komai Ameer”
Ya tari numfashinta.
“Bana bukatar sanin komai”
Ya juya sai kuma ya juyo.
“Sorry for the lost na ďana daga cikin yayan da kika fi kauna, Allah ya mata rahma”
Ya sake juyawa zai shiga cikin gidan, sai Waira ta bi bayansa.
“Ke”
Maleek ya kirata, ta juyo kamar a razane.
“Ina son zan tambaye shi wani abu ne”
Ta fada muryarta na rawa. Maleek ya bude mata ido.
“Shiga mota”
Ta kalli Ameer kamar zata fashe da kuka ta zagaya gurin motar da Maleek ya bude ta shiga.
“Sai anjima Ameer, na gode”
Ummi ta fada sannan ta shiga motar, sai gashi ya juyo yana kallonta har ta shoga motar Maleek yaja suka bar gurin. Kansa ya daga sama hawaye suka zubo masa ta gefen ido.
[7/7, 10:21 PM] My S Line: 49
“Ummi magana kawai zan yi da shi, wani abu zan tambaye shi”
Waira ta fada tana girgiza hannun Ummi, so take Ummi ta cilasta Maleek komawa gidansu Ameer ta yi masa tambayoyi abubuwan da take son sani da kuma wadanda suka shige mata duhu.
“Ummi ki ce ya koma”
Duk magiyar da take Ummi, Maleek be ce komai ba har sai da suka faka compound din gidan.
“Ummi please ki ce Ya Maleek”
Juyowa yayi ya watsa mata harara sannan ya bude motar ya fita, ya budewa Ummi ta fito tare da Waira. Abun ka da mai na ci sai ta sake rokon Ummi ba Maleek umarni