Showing 72001 words to 75000 words out of 281271 words
nan ni kadai ake bari a gidan nan”
Magana ce karama amman sai da ta saka Ummi hawaye domin ita kadai ta san abun da take ji a zuciyarta, Abiey kuma ya gane yarenta, hawayenta kuma suka sosa zuciyarsa hakan ya saka shi zolayarta.
“Abokiyar zama kike so kenan?”
Ta share hawayenta tana hararashi.
“Tab ka ma isa to ka fara din ka ga yadda zan yi da kai”
Sai duk suka saka dariya, ita kuma ya fice daga falon ta nufi Garden, kuka ta samu Waira na yi sosai sai ta mika mata hannu tana mata alama da ta taso, Waira ta girgiza mata kai ta lake kafada. Ta yi mata alamar mari a hannu ta kuma yi alamar dangwarar da Hanne ta yi mata.
“Waya dake ke ki kuma?”
Ta tambaye ta da hannu sai ta nuna cikin gidan, Ummi ta kama hannunta ta jata da karfi ta taso a dolenta suka koma falon.
“Waya mareta?”
Shi ne abun da Ummi ta fara tambaya a lokacin da ta shiga falon, Nimra ta aje wayar dake hannunta.
“Babu wanda ya mareta, waya am mareta?”
“Ita ta fada min”
“Ba wanda ya mareta”
Waira ta taba Ummi ta nuna mata Hanne ta yi mata alama da dangwara ta sake nunata tana tabbatarwa da Ummi ita din ce.
“Hanne ne ta yi miki kika dangwareta?”
“Ni..... Ya ilahi”
Hanne ta nuna kanta tana tambayar Ummi kamin ta karaso gurin Waira ta nuna kanta.
“Ni na dangwareki”
Waira kamar ta san abun da ake fada sai ta daga kanta sama alamar eh, kamin ta juya ta nunawa Ummi Nimra ta yi mata alama da abinci ta kuma yi kakarin amai.
“Ni kuma me na yi?”
“Miyasa kika bata abincin da ta ci ta yi amai”
Ummi ta fada domin ita ta gane abun da Waira take nufi, sai Nimra ta saka dariya ta kama kunneta ta hade hannayenta tana bawa Waira hakuri.
“To yi hakuri, lallai Ummi kin iya maganar kurame”
Ummi ta yi murmushi sannan ta kalli Hanne ta ce.
“Ke ma ki bata hakuri kuma kar hannunki ya sake kawai a jikinta”
Ita ma ta yi yadda Nimra ta yi tana dariya, Ummi ta shiga da ita dakin da aka ajeta ta taya ta cire kayanta domin aman ya taba wani bangare na rigar ta dauko tawul ta daura mata, ta shiga bandaki ta hada mata ruwan wanka ta saka a bandakin ta janyo mata kofa ta fice daga dakin ba tare da ta rufe kofar ba ta shiga dakin Maleek. Abun ka da wanda be son wanka haka Waira ta fara jan kofar bandakin tana son budewa ta fito abu ya gagara daker ta samu ta lankwasa kofar abun ya bude sannan ya fito ganin kofa bude ta fice daga dakin daga ita sai tawul din da take daure ta fara talawa tana dan leke lake a hankali jin motsi a bayanta ya saka ta juyo ta nufi dakin Maleek dake gaban nata, shi ma kofarsa a bude take ta nufi dakin ne ba dan ta san cewa na Maleek ba ne sai dan motsin da ta ji a ciki tana son gani idan Ummi ce a ciki. Lekawa ta fara yi sai ta hango Ummi duke gurin gadon Maleek tana gyara masa, domin ita kadai ya yarda ta gyara masa gadonsa shi ma dan tana kokarin kiyaye abubuwan da baya so na, ba kamar kanensa da idan za su shiga dakin wani lokacin har jan baki sai sun shafa ba, idan ma bata gyara masa ba ya kan gyara abunsa time to time ya fin natsuwa da ya gyara fiye da wani ya gyara masa ma. Ba Ummi kadai Waira ta gani ba har da wata farar mace wacce ta fi Ummi tsawo sosai gashin kanta a yamutse ga manyan idanuwa kamar kwai, farcenta har ya kusan tsawon yatsan Waira, bata da kafafuwa sai doguwar bakar rigar da ke ja mata a kasa bakinta na fitar da hayaki tana goye da yaro sai jijjiga shi take tana hararar Ummi. Da sauri Waira ta nuna inda matar take tsaye ta yi kara Ummi ta kalleta da sauri ta juya a firgice ta kalli inda Waira take nunawa bata ga komai ba sai ta fito dakin da gudu, matar na ganin Waira ta ganta sai ta fitar mata da hakora ta firrrr kamar kamar tsuntsuwa ta dire ta Window dakin dake bude, Waira ta kwala kara ta yi baya da sauri Ummi na kokarin rikota sai ga jini ya fara fitowa a idonta..
“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un”
Ummi ta rika ta da sauri ta rumgume tana ihu.
“Hanne Namra Nimra waye a kusa”
Namra dake dakinta ta riga iso gurin tana ganin jini a idon Waira taja waya ita ma ta fara nata ihun.
“Innalillahi mun shiga uku”
Fitowar Mahmood a dakinsa dake bachi ta yi daidai da haurowar Nimra da Hanne. Karbarta yayi a hannun Ummi tana kiran sunanta.
“Waira... Waira...”
Ta kalleshi daman hankalinta be gushe ba, tsorata kawai ta yi sai kuma hawayen jinin dake fitar mata a ido.
“Mi ya same?”
Ummi ta fada masa iya abun da ya faru da kuma abun da take tunanin ko Waira ta ga wani abun ne, Mahmood ya sake ta, ya shiga dakin yana dubawa da dan tsoro ko zai ga wani abu be ga komai ba.
“Dan Allah Hanne da Nimra a saka mata kaya zan je na shirya na kaita asibiti yanzu nan”
Ummi na rufe baki Maleek ya iso gurin cikin wani irin zafin rai da shi kansa ba zai ce ga daga inda yake zuwa masa ba. Be tambaye miya faru ba sai kallon kofar dakinsa dake bude yayi yana kokarin fahimtar abun da ke faruwa, Waira na ganinshi ta yi saurin tashi ta rike Ummi.
“Daki ta shigar min?”
“Ni ta zo nema”
“Idan ta sake shigar min daki sai ta bar gidan nan, and idan na sake ganinta tsaye a gabana sai na mata dukan da sai ta kusa mutuwa...!”
Magana yake cikin wani irin zafin rai kamar ba shi ba har hade hade hakora yake yana nuna ta da yatsa. Ummi ta tura masa Waira da karfi.
“Gata nan ka kasheta Maleek, idan ka gama da ita ka kashe ni ka kashe kanenka gasu nan”
Waira ta juyo da gudu ta dawo gurin Ummi ta riketa, ba dan ta fahimci abun da Ummi take fada ba sai dan turata da Ummi ta yi a gurin Maleek kuma bata manta shi ne ya mareta ba.
“Are you a gay? Me mata kuka maka? Ba mace ta haife ka ba? A cikina ka zauna Maleek for more than nine months na haife ka na raine ka na ci kashinka da fitsarinka har ka yi wayo ka girma, sai a yanzu zaka ce ka tsani mace, ka tararda yarinya tana zubar da jini baka damu ba sai zancen dukanta kake yi ka kashe ta Maleek sai na san ka haihu, idan ba zaka iya zama da mu ba ka tattara komai na ka bar gidan nan, ai ka yi dukiya ka yi hankali ka gi wayon da zaka iya zama kai kadai a gidanka then move out, ka bar ni ni da yayana mu sakata mu wala, i can live without you Maleek tun da na rayu babu dan'uwanka... Ka je ka rayu da mazan da kake so na yafe ka, na gaji da wulakancinka...”
Wani irin fada Ummi take masa ko'ina ana jin muryarta idonta har ya kade yayi ja sosai, su kansu ba su taba ganin bacin rai da fadanta kamar haka ba, ta fisge hannu Waira da karfi ta nufi dakinta da ita. Nimra da Namra suka bi bayan Ummi Mahmood ma ya rufa musu baya, aka bar Maleek shi kadai a tsaye, Hanne ma sauka ta yi da sauri kasa. Daker Maleek ya cira kafadarsa ya shiga dakinsa ya maida kofar dakin ya rufe ya jingina da kofar ya rumtse ido sai hawaye suka sauko masa ta gefen ko wane ido, ya jinke hannayensa sosai. Ya dauki lokaci a haka sannan ya bude idom ya nufi inda keys dinsa suke ya dauka ya fice daga gidan gaba daya.
Mahmood na shiga dakin, Ummi ta dakatar da su daga yi mata wata magana da ta dangancin Maleek.
“Kar wani yayi min wata magana akan Maleek, and i meant it, enough is enough na gaji kowa ya tafi gurin sha'aninsa, Mahmood je ka shirya mu kai yarinyar nan Asibiti, Namra wuce ki tafi gurin aikinki, and you Nimra ki sama mata tufafin da zata saka zan shiga na yi wanka”
Haka ta rabawa kowa aiki sannan ta shiga bandakin, kamar yadda ta umarta haka kowa yayi, ba ma kamar Mahmood da ya san condition dinta shi ya tsoron tashin hankalinta fiye da komai. A falo ya fito ya zauna yana jiran saukowarsu, Namra tuni ta wuce gurin aikinta Nimra kuma ta taimakawa Waira ta saka wando da riga domin su ne kadai suka yi mata a cikin tufafinta shi ma wandon dan yana gajere ne sai ya saukowa Waira saboda tsayinta be kai na Nimra ba. Ummi ta fito da shirinta suka wuce tare Mahmood da be samu tsayawa ya karya ba a ranar, daman Abiey tuni ya fice daga gidan bayan sun yi sallama da Maleek da ya dawo bangaren Ummi a dazun da abubuwa marar dadi suka faru. Sai ya rage Nimra ce kadai a gidan, hakan ya bata damar shiga bangaren Abiey ta shiga har dakinsa tana bincike inda yaks aje abubuwansa ta har ta samu sa'ar gano inda keys din motar ta yake ta dauko ta fito waje ta bude motar tana duba ko'ina. Har da addu'a take Allah ya sa ta sarewar saboda ta farantawa Ameer rai, can kasan kujera ta hango abu mai kamar akwaiti da sauri ta dauka tana budewa sai ta yi arba da abun da ba dan ta ganta a hannunsa yana busa ba da ba zata iya kiransa da sarewa kai tsaye ba, saboda ya sabon samfur ne. Da sauri ta fito motar ta rufe ta maida key din inda ta dauko shi ta dawo dakinta ta dauki hoton sarewar ta turawa Ameer sannan ta boye box din a karkashin gadonta.
AMEER POV.
Ya aje wayar yana murmushi ya cigaba da saka maballan rigarsa.
“Good Girl yanzu sai zancen haduwa zan yi wannan wasan da kyau”
After ya gama sakawa ya sake daukar wayar ya mayar mata da amsa.
‘Idan ba zaki iya zuwa can ba, then mu hadu a Galadimawa inda muka taba zuwa it's a safe place babu wanda zai gan ki kuma yanzu nan zan tafi sai kin iso’
Tana gama rubuta mata amsar ya kashe data shi ya saka wayar aljihu ya dauki abubuwa da ya san zai bukata ya fice daga dakin. Sai da ya zabi motar da ta yi masa sannan ya saka kanwarsa ta dauko nasa key motar a bangaren mahaifinsa ya karba ya hau ya kama hanyar Galadimawa. Ya isa in time saboda yayi abun da ya saba wato gudu da mota, ya ki ya kunna data shi balle ya ga abun da Nimra zata fada masa so yake ya cilasta ta baro gidansu zuwa inda yake bukatar ganinta so that ya san idan ya fara tasiri a zuciyarta ko akasin haka, yadda ta nuna masa ba zata iya zuwa gurin da suka saba haduwa da farko ba ya nuna tana tsoron yan'gidansu sun ganta kenan kamar yadda ta fada masa cewar idan mahaifinta ko wani ya gani bata san iya hukunci da za'ayi mata. Yana zaune cikin motarsa ya hango yarinyar da suka yi fada a gurin aikin mahaifinsa an sauke ta a wata motar da bata gurin aikin ba, 206 Saurayi a ciki yana sanye da kananan kaya kamar yadda Ameer ma ya saka kananan kayan, ita kuma tana sanye da rigar gurin aikin sai skirt ta dora after dress sai mayafin rigar da ta yafa tana rataye da jakarta daya hannunta na rike da bakar farar ledar dake dauke da rubutun kamfanin. Bude motar yayi ya fito ya nufi inda take tana tafiyarta a hankali.
“Miye a cikin ledar nan?”
Ta tsaya sai ta juyo ta kalleshi kamar ba zata ce komai ganin shi ne, sai kuma ta daure ta ce.
“Abinci ne?”
“Hmmm-uhmm wato kin yi sa'a ba a koreki ba bayan fadan da kika yi da ni, and now sata kike mana a gurin ko?”
Kalmar sata ta bata mata rai, sai dai mai nema baya fushi kamar yadda Kakarta ta fada mata dole ta hakurewa wani abun.
“Aa ni ban taba sata ba, mai gurin ya amince mana mu rika diba idan ya rage ko kuma idan mun san babu shi a gida”
“Oh Really i will ake him then, but before that bari na fada miki wani abu karki sake saka rigar kamfaninmu kina yawo da ita samari na dauki kala kala kuna iskancinku idan an gani sai ace a karkashin mahaifina kike aiki, and consider yourself a matsayin korrriya a gurin nan”
Ta daka masa tsawa domin kalmar iskanci da ya jefeta da shi ya bata mata rai.
“Sai me? Idan ka koreni rai ka acire min? Kuma ni ba yar iska ba ce ban san miye iskanci ban hada hanya da shi ba, amman kai ka sanshi saboda aikinka ne abun da kake yi ne, kuma ka bakar shegiyar shinkafar ku nan ka dauka ka tafi da ita”
Ta jefa masa shimkafar, har ta juya ta fara tafiya sai kuma ta dawo ta iso har inda yake ta kama hannunsa yaja kamar wani yaro haka ya rika binta har cikin unguwar ta shiga da shi har cikin gidan ta tsaya da shi kofar dakin ta bude kofar dakin.
“Ga gidan mu nan ka ga dakin da nake rayuwa nan, idan ka iya ka kore ni a nan din ma, sannan ka raba ni da duniyar gaba daya, sai na san ka kai tsohon shege, idan baka gode ni'imar Allah ba zaka godewa zabarsa, ba dai ka zabi wulakanta bayinsa ba saboda ya daukaka ya baka abun da bayinsa suke nema a karkashinka? Ka ji tsoron karshenka”
Wadanda suke cikin gidan suka fito suna kallonta da shi, Mamanta ma ta fito da sauri tare da kakarta dake lullube da zane zata fita bara.
“Miya faru Humaira?”
Mamarta ta tambaya sai Humaira ta fashe da kuka ta shige falon ta bar shi a gurin tsaye. Kakarta ta taso ka iso inda yake tana kallon fuskarsa da wani irin kallo kamar zata cinye shi.
“Jika na, ka yi hakuri idan wani abun Humaira ta yi maka, kai namiji ne, karfi da zuciya da fushi ba daya ba, a inda ta nuna maka a nan muke rayu, bata da kowa sai Allah marainiya ce ubanta ya rasu kuma da aikinku da dogara da shi take biyan makaranta tana mana hidima har ta yi ma kanta wani lokacin, mahaifiyarta bata sana'ar komai ni kuma kakarta bara kawai na iya, dan Allah karka koreta karka mata wani abun ka yi jinkan na kasa da kai, duk wanda ya nema a gurinka lallai dan ya san kana da shi ne, ka fi karfinmu nesa ba kusa ba, amman karka bari sherin shaida da zuciya su rinjaye ka, ka yi hakuri dan Allah...”
Ta duka har kasa tana bashi hakuri idonta dake cike da hawaye suna kallon fuskarsa, ba shi kadai take gani ba zubun fuskar da tsarin hallitar da tsayin take ganin kamar na ďanta ďa ďaya tilo da ya rasu, Kamar har ta so ta yi yayi sai dai wannan ya fi ďanta manyan ido da kyau da fadin kirji. Baya baya yayi ba tare da yace komai ba ya juya ya fice daga gidan cikin rashin kuzari, yana jin wani abu marar dadi a ransa.
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: *W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
25
Cikin motarsa ya dawo ya zauna yana ta kallon mutanen dake wucewa, ya duba duba hannunsa daidai saitin inda ta rika wutsiyar hannun ta ja zuwa cikin gidansu. Isowar Nimra ya saka shi sauke gilashin motarsa yayi mata horn, sai ta fito motar Ummi ta nufo inda yake rike da Box din ta saka mask a fuskarta tare da katon bakin gilashi, bude motar ta yi ta shiga ta zauna ta cire mask din da glass.
“Na karya dokar da Abiey ya saka min, kuma na karya alkawarin da na yi ma Ummi”
Ya kalleta a lokacin da hankalinsa da kuma tunaninsa suka dawo kanta.
“Wace doka?”
“Na yi ma Ummi alkawarin ba zan sake haduwa da kai ba, ita ta bukaci haka kuma na yi mata, Abiey kuma yace ko sunanka kar ya sake jin a gurin mu, yanzu kuma na fito ba tare da sanin kowa ba na zo nan”
Ya taba baki.
“Just”
Ta kalleshi.
“Just ne kawai?”
“Yeah don't tell me this is the first time da kika yi breaking rules din gidanku, yanzu fa an waye ba komai zaka aikata ka bar iyayenka su sani ba like this”
Ya kwanta jikin kujerar da take ya sumbanci gefen bakinta.
“You can't tell them same one kissed you”
Ya rika hannunta ya murza a hankali.
“And you can't tell them someone hold your hand, akwai abubuwa da yawa ba zamu fadawa iyayeba amman muna aikatawa, an waye yanzu Nimra muna wani zamani ne da muka fi iyayenmu wayo da iya sirranta abu”
Rawa jikinta yake, ba rawa ta tsoro ko fargaba ba, rawa irin da macen da namiji be taba rika hannunta ba ya fara a yanzu, wani abun take jin mai kamar faduwar gaba tana ji tana gani numfashinta na son sarkewa, so take ya janye hannunta daga rikon da yayi mata domin har yanzu murza mata yatsun yake amman ta kasa. Kiss din da yayi mata ma ta aje shi a wani ma'auni na dabam. Ta kasa kallonsa sai yawo take da idonta a titi.
“Ga... Ga.. Sarew... War...”
Ta samu kuzarin mika mishi bayan ta yaki zuciyarta. Be saki hanninta ba sai ya saka dayan hannunsa ya karba yana hadawa da hannunta ya rike, sai kuma ya daga hannunta ya sumbanta.
“Na gode sosai sarewar tana da muhimmanci a gareni”
Wannan karon ka ta samu kuzarin fisge duka hannayenta.