Showing 60001 words to 63000 words out of 281271 words
akwai wata daba a tsakaninku, sai dai yadda ka yi mata be dace ba, arziki ba hauka ba ne Ameer muma duk muna da arzikin nan amman miyasa ba ma yin abun da kake yi? Miyasa ka fita dabam a cikin mu? Na kira nan ne saboda mu tattauna akan rayuwar da kuma abun da ya faru tsakaninka da Maleek amman ji abun da ka yi causing? Kasan idan yarinyar nan ta yi maka addu'a sai ta kama ka? Sahoda abun da ka yi mata zalinci ne”
“Yanzu ma ni ne mai laifi kenan?”
“Kullum burinka a bawa wani rashin gaskiya a baka gaskiya, ko da kuwa baka da ita, wannan ba hali na gari ba ne ka canja Ameer”
Yana kaiwa nan ya kara gaba gurin motarsa ya bar Ameer din a tsaye yana binsa da kallo. Ya kusan minti talatin a gurin tsaye sannan ya bude motarsa ya shiga ya dauki hanyar gidansu. Sakon kar ta kwana ne ya shigo wayarsa da number Angel daga bisani kira ya fara shigowa, be kula sakon ba balle kuma wayar da idan zata shekara tana ringing ba zai daga ba. Ya faka motar a harabar gidansu yana tunanin abubuwan da Abdull ya fada masa, so yake ya gane idan da gaske abubuwan da yake bana kwarai ba ne, amman ya kasa ganin haka har yanzu ganin yake ita ta yi masa ba daidai ba, but still ya dan ji babu dadi na watsa mata ruwan da yayi domin zai iya illata fuskarta but ai ita ta janyo ma kanta.
Ta shiga falon yana lumshe ido saboda kamshin turaren wutar da Momy ta turare falonta da shi, yana dalilin ne ya saka yake kaunar matar uban tasa ban da wannan babu wani dalili domin kullum ganinta yake kamar tana nuna masa kiyayya kuma tana tsanarsa saboda ba ita ta haife shi ba. Wanka ne first abun da ya fara yi sannan ya sauko kasa ya ci abinci, then ya koma sama ya bude windows din dakinsa ya tsaya a gurin yana kallon backyard din da Allah ya wadata musu da itacen kayan marmari wani iska mai dadi na kadawa.
‘Ko tana ina yanzu?’
Ya tambayi kansa tambayar da bashi da amsarta kuma be san wanda zai amsa masa ba, ta rayu ko ta mutu ma? Ya za'ayi a gane yan'uwanta wannan ma ya san wani sabon aiki ne, samun kansa yayi da murmushi tuna yadda ta dauke macijin ta rike a hannu ko shi da yake namiji ba ya rikon maciji balle kuma ita da take mace, he thought macijin ba zai iya mata komai ba amman ji yadda ya cijeta har ta suma. Can kuma ya yamutsa fuska tuna yadda take da kazanta a jiki ga wasu bera a hannunta, shi da yake jin ba zai iya rayuwa a gurin da bera yake rayuwa ba ma balle har ya taba shi amman ji ita har rikonsa take.
“Allah kadai ya san garin wannan yarinyar ta fito”
Wannan karon a fili yayi maganar ya zuba hannayesa aljihu yana kallon sararin dake dayan gefen.
ABIEY'S HOME.
Mamaki ne sosai a fuskar Nimra miyasa Ameer zai yi requesting na following dinta? Why? Is he the one ma? Bayan duk abun da ya faru? What now wani abun zai fada mata ko kuma hakuri zai bata? Or maybe ya yarda cewar ba da hadin bakinta aka shirya masa komai ba? Shi din ma ne na gaskiya. Ta shiga account dinsa ta duba da kyau bata gani abu dake nuna fake account ba. Tunani kala kala a ranta at the end ta yanke shawarar karba masa zuciyarta na bugawa da mugun karfe, wani irin yanayi take samun kanta a ciki a duk lokacin data tunkari wani abu daya shafe Ameer, har yanzu ta kasa ganin laifinta kuma ta kasa mantawa ko cireshi a ranta, kamar yadda tausayinsa yake cika mata zuciya bayan kuma ta fishi zama bar tausayi a yanzu domin mahaifinta baya magana da ita saboda abin da ta aikata.
Tashi ta yi zaune daga kan kujerar da take kwance ta kalli Mahmood daya shigo falon Maleek na bayansa sannan Abiey dake sanye da manyan kaya idonsa da garin gilashi hular da ya dora a kansa ta zauna das ta masa kyau irin kyaun nan na magidanta masu iyali da hurhura ta fara fitowa ta yi musu ido.
“Sannu da zuwa Abiey”
Ta fada cikin girmamawa da fargabar amsawarsa, ko inda take be kalla ba, ya kalli Mahmood ya ce.
“Je ka kira Umminku, kai kuma ka ce su shigo da ita”
Ya karasa yana kallon Maleek dake wasa da key motar dake hannunsa, Mahmood ya nufi Upstairs dakin Maleek kuma ya juya ya fice daga falon.
Da kuzari Mahmood ya tura kofar falon ya dakin ya shiga.
“Ummi Abiey...”
Ya kara karasa maganar saboda ganin hawaye sharkab a fuskar mahaifiyarsa, sai ta yi wuff ta sauke kai kasa ta kawar da fuskarta daga kallon madubin, ta boye gashin dake hannunta. Jiki babu kuzari ya karasa kusa da ita ya risina har kasa yana kallon fuskarta a nan ta kasa boye hawayenta, ya mika hannunsa ya kama hannunta ya cire gashinta dake ciki ya kalla sannan ya mika hannunsa ya kai gurin kanta ya riko gashinta sai ga gashin ya biyo hannunsa, take na shi idon suka cika da hawaye hankalinsa yayi mugun tashi irin tashin da be taba yi ba, zuciyarsa ta hau bugawa da mugun karfi har fitar numfashinsa ya sauya.
“Ummi mi ke faruwa?”
Ta dauki dankwalinta ta saka sannan ta saka hannu ta karbi hashinta da yake hannunsa.
“Wannan a tsakanin uwa da ďanta ne kawai, bana son mahaifinka ko Nimra Maleek da Namra su ji, ka bar wannan daga ni sai kai sai Allah ka ji ko?”
Binta yake da kallo gaba daya jikinsa yayi la'asar ya kasa gane komai, tana daf da shiga bandaki ya zaburi muryarsa ya ce.
“Ummi zamu je asibiti ko? Ya kamata mu ga kwararen likita”
“Zamu yi magana daga baya”
Ita ce amsar data bashi sannan ta shiga bathroom din, tana kallon kanta a jikin madubi sai ta fashe da kuka Mahmood ya dawo gurin kofar ya tsaya gaba daya ya rasa natsuwarsa, tunani kala kala suke zo masa, wanke fuskarta ta yi ta fito.
“Me Abiey ya ce?”
“Yace na kira ki an zo da yarinyar suna kasa”
Magana yake yana kallonta be san hawaye na sauko masa ba har sai da ta saka hannu ta goge masa, sai ya rumgumeta yana jin kamar ba zai saketa ba, she has to be strong saboda ita uwa ce, ko dan mijinta da yayanta, hakan ya saka ta hana idonta zubar da hawaye ko daya.
“Baka min alkawari ba, babu wanda zai ji?”
“Ummin na miki alkawari babu wanda zai ji”
Ta yi murmushi sannan ta nufi kofar fita daga dakin dake kusa da kofar bathroom din, ta bude ta fito a hankali take takawa har ta sauko kasa, yadda ta samu yarta Nimra zaune a saman kujera kanta a kasa ta kasa sake jiki da mahaifinta sai ta bata tausayi, kusa da ita ta zauna ta dafa Nimra ta kasa dagowa saboda idonta na cike da kwalla. Zaman Ummi da kamar minti daya Maleek ya shigo falon ya rike kofar falon Police din dake dauke da Waira ya shigo da ita zai ajeta kasa Ummi ta yi saurin cewa ya dorata akan kujera, bachi take amman tufafinta na rumgume a hannunta da kuma yar takardar da Dr Shuraim ya bata, dayan da baya ciwo dayan kuma an nade shi. Kallo daya Maleek yayi mata ya dauke kai be sake kallon inda aka aje ta ba, ta tsaya jikin kofa domin baya jin shigowa cikin falon ma.
“A kai su BQ za a kawo musu abinci yanzu sannan mu yi magana”
Cewar Abiey yana bawa Maleek umarni cewar akai police din da suka mata rakiyar a BQ, sai da yayi musu bayanin da Dr Shuraim yayi musu akan ciwonta da yanayinda ta kuma kalar abincin da take ci ya ba shi takardar magani da file dinta na asibiti sannan ya fice. Ummi ta taso ta karasa inda aka kwantar da ita a dayan set din na kujera tana kallonta kaminnta kai hannu ta taba ba, tausayin yarinyar ya kamata ga ta dai a fuska y matashiyar yarinyar ce ga kyau ga fari tana bachin a tsorace domin ta takure jikinta da yadda mai hankali zai iya fahimtar bata natsu da halin da take ciki ba, ta kai hannu ta taba zoben da yake wuyanta ta fara kokarin zare takardar hannunta sai ta Waira ta kara rikewa hakan ya saka Ummi bata takura ba cewar sai ta ga ko miye a cikin takardar ba.
“Asibiti za a kaita?”
Ummi ta juyo ta tambaya tana kallon mijinta.
“Sai ta farka tukuna, yanzu dai a ina za'a aje ta?”
“Akwai extra daki dake tsakanin Maleek da Namra, a nan ya kamata a ajeta ko kuma dakin su Nimra”
“Aa daga zuwan yarinya ba san wace iri ba ce sai a hade ta da yayana?”
“To zan iya kaita dakina saboda ba zai yiyu a aje ta BQ ba duba da yanayinta da kuma ciwonta, ya kamata ace ta samu kulawa kuma ta haka ne zata sake jiki da mu”
“Ban yarda da kwanta dakin yayana ba zan yarda ta kwanta dakinki? You're more important to me”
Juyowa ta yi ta kalleshi sai ta yi murmushi.
“Yau kuma?”
“Kullum ma, ke kika jamyo duk abun da nake furtawa ko yake faruwa ai, kamin na ga yayana wa na fara gani ba ke ba?”
Da murmushi yayi furucin kamar yadda ita ma murmushin yake shimfide a fuskarta. Duk abun da ake Mahmood na tsaye jikin Stairs ya kasa karasa saukowa kuma shi be hau sama ba, idonsa na kan mahaifinyarsa duk wani motsi nata yana idonsa.
“Mahmood zo ka shiga da ita dakin dake kusa da na Maleek”
Sai a lokacin ya sauko ya saka hannu ya dauke ta cak ya haura da ita sama. Abiey ya mike tsaye yana fadin.
“Ki saka mai aikinki ta kai musu abinci, CP yace su zo nan kai tsaye ba sai sun shiga office dinsa ba, nima kuma yunwa nake ji”
“Yanzu zan saka ta kai musu, daman tun dazun muka gama shirya komai, ni kuma i will serving my King”
Girgiza kai yayi ya fice yana dariya, sun saba irin wannan wasan amman faruwa abubuwa ya saka sun rufe babin wadandasu abubuwa da dama. Sai da ya fice sannan Nimra ta dago ta kalli Ummi.
“Har yanzu Abiey fushi yake da ni”
“Zai sauko yata, dole zai daina fushi da yarsa, ki bashi lokaci Abieynku yana daukar zafi akan abubuwa amman yana da kyakkyawar zuciyar mantawa kuma ya yafe, sai dai ba a nan take ba”
Ummi data karaso kusa da ita ta kai hannu ta taba ta.
“Yar autar mata, ta so ki fadawa Hanne ta kai baki abinci da abun sha”
“Toh”
Ta amsa sannan ta tashi tare da wayarta ta fice daga falon, Ummi kuma ta nufi dinning...
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: *W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
21
After ya nuna musu BQ sai ya samu guri a cikin set din cushion din da aka jera a Balcony ya zauna, yana tsala wayarsa. Har Hanne ta gama ziyar kaiwa bakin abincin da abun sha Maleek ba dago ya kalli gurin ba, Mahmood ne ya fito daga falon yana kallon harabar gidan zuciyarsa cike da tunani kala kala kamin ya kalli gurin da dan'uwansa yake zaune ya nufi gurin. Ajiyar zuciya ya sauke hakannya sakan Maleek dubansa domin ba kasafai Mahmood yake barin wani abun ya dame shi, kusan shi da Namra a gidan babu wanda zai ce ga damuwarsu, Namra saboda bata sake jiki da kowa ciki har da Ummi da yar'uwarta Nimra, komai yake cinta sai dai ta barshi a cikinta, shi kuma baya barin damuwa ta kusance shi ma balle har ya damu da ita, idan ma akwai damuwar kenan, babu abun da suka nema suka rasa a duniyar nan hakan ya saka damuwa nesanta inda suke.
“Are you okay?”
“I hope so”
Ya amsa yana kallon harabar gidan, Maleek ya cigaba da danna wayarsa.
“Tunani nake yadda rayuwa zata zama idan babu Ummi”
Mahmood ya fada ba tare da ya kalli inda Maleek yake zaune ba. Cak Maleek ya tsayar da taba wayar ya dago kalli Mahmood.
“Baka da hankali? How could you say that? Kasan abun da ake nufi da babu Mahmood? Rasa ta fa kenan mutuwa, ta ya zaka fadin irin wannan maganar?”
Mahmoud yayi murmushi yana kallon Maleek, da ya mike tsaye rai a bace.
“Wannan ranar ba zata zo ba Mahmood idan kuma ta zo to ba zata same ni da rayuwa ba, ban taba mafarkin rana zata zo da zan saka kafata a cikin gidan nan ace Ummi bata nan ba, ban san me ya zo kanka ba ya kamata ka yake shi ka nemi tsarin shaidan daga wannan mummunan tunani naka i hate nonsense”
Ta zazzaga masa magana sannan ya saka kafarsa sai fice daga gurin sai kuma ya juyo ya kalleshi.
“Ko wani abu kanji Mahmood?”
“No ban ji wani abu ba, kawai zuwan yarinyar nan ne ya ba ni tausayi ta rabu da iyayenta, ya saka ni tunanin mu idan muka rasa Ummi ya zamu ji irin yadda muka saba da ita?”
“Ku da kuka saba da ita kenan, ya kake tunanin ni da ka kasa kebewa da ita ko da tsawon awa daya ne? Balle har na raba jikinta na rumgume ta a matsayin uwata? Baka tunanin ina jin zafin haka Mahmood? Mi yasa zaka min irin wannan maganar? Why?”
Ya karshe maganar muryarsa na karkarwa irin na wanda rauni da bakinciki ya dade a zuciyarsa.
“Bana nufin bata maka rai...”
Fuuu ya fice daga gurin be tsaya sauraren abun da Mahmood zai fada ba, baya jin komawa ya cikin gidan hakan ya saka shi nufar Katon Garden din dake gidan, Garden da aka kawata da itatuwa da fulawoyi ta ko'ina ta bangare daya kuma an yi Swimming Pool, an jera kujeru a kusa da gurin, ta dayan gefen dama kuma kebantattun tsuntsaye ne da aka yi musu muhalli na dabam, sai barewar dake ta kiwonta a gurin wani decoration na busashen itace. A hankali yake takawa har ya isa gurin da tsuntsayen suke ya bude yar wayar da aka kewasu da ita ya shiga cikin garden din, guri ya samu a gurin kujerun nan da ake na siminti ya zauna yana kallon yadda wasu suke tashi wasu na sauka. Wayarsa dake hannunsa ya bude Gallary ya shiga can wani gurin ajiyar sirrin ya kamo hoton mahaifiyarsa inda take zaune tare da Abiey aka yi musu hoto Tan murmushi har koranta sun bayyana. Yatsansa yakai ya shafa saitin inda take a jikin hoto yana jin wani launi marar dadi na masa yawo a zuciya. Shi ne kadai abun da yake iya, ya kalli hotonta ko ya shafa amman a fili ba zai iya zama yayi shawara ko hira da ita ba, ba zai iya kai hannu ya taba taba jikinta a matsayinta na mahaifinyarsa ba, ba zai iya kebewa daga ita sai shi na tsawon awa daya ba, tun da yayi wayo ya mallaki hankalin kansa be san wata rana da haka ta taba faruwa a tsakaninsu ba, sai dai duk da haka Ummi bata taba juya masa baya ba, bata taba jin ta tsana shi ba, tana kokarin ganin ta ja shi a jikin sai ta ga hakan ya gagara sannan ya saka masa ido ta daina kokarin kebewa da shi a cilas ko taba shi, sai ma taimaka masa da take na yadda zai rayu ba tare da yan'uwansa sun shiga rayuwarsa sun bata masa rai kamar yadda baya bukata ba.
Shi dai ya san ba tsanar mahaifiyarsa yayi ba, domin bata yi masa abun da zai saka ya tsane ta ba, idan ma ta yi masa dole ya so ta saboda ita din uwa ce, balle kuma bata yi ba, sai dai ya tsabarsa da mata ne ya saka ita din yake kaurace mata saboda ita ma tana daya daga cikin jinsin matan. To miyasa ya tsani matan? Why? Shi kasan ba zai iya fada ba, be yi soyayya ba balle yace yaudararsa akai yi, be zauna da matar uba ba balle yace ta cucheshi. Sai da aka kira Sallah magariba sannan fito daga gurin, a harabar gidan ya hadu da Ummi ta nufo Garden tana kallonsa.
“Mahmood yace min kana Garden tun dazu gashi Magariba ta yi baka san iya abin da zai sauko ba”
Cike da kulawa irin ta uwa take masa magana, lafiyarsa ce abar damuwarta a yanzu. Ya dan dauke kai daga barin kallonta ya kalli kasa.
“Ina taba waya ne ban ankaro lokaci yayi ba sai da na ji kira, bari na je na yi alwala”
Ya amsata yana tafiya sai ta juyo ta biyo bayansa domin inda sabo ta saba da halinsa. Yana gaba tana bayansa har suka shiga falon kai tsaye ya nufi Upstairs ita ma stairs din ta nufa domin gabatar da nata alwalan, daf da zai wuce dakin da Waira take ciki ya shiga nasa dakin sai gata ta fito da gudu daga dakin da yake bude kicibis suka yi da Maleek bata tsaya komai ba ta rumgume shi ta rike da mugun karfi.....
Duk wani abu mai rai da motsi a cikin jikinsa sai da ya tsaya cak, ciki har da bugun zuciyarsa da numfashinsa.
Ummi ta rufe baki daga bayansa da take tsaye domin ta ga abun da ya faru, Nimra da ta biyo bayanta da gudu ma ta tsaya cak ta zaro ido. Shisshikar kuka kawai Waira take tana kara rike shi ba dan ta san waye shi ba ita dai gurin boya da cuto kawai take nema. Ganin ya rumtse ido ya ya cige baki ya saka Ummi ta nufo inda yake da sauri ta banbare hannun Waira har da mai ciwon taja ta baya, a lokacin ne wani abu mai kamar ba suma ya ziyarce shi sai ya ji wani uban jiri da rawar jiki na neman kamashi