Showing 141001 words to 144000 words out of 281271 words
motsi an lullube da babban zane. Kowa kuka yake a gidan domin ba su taba dandana zafin rasa rai ba sai a yau, ba ma kamar Namra dake ta kara tana fisge-fisge ji take kamar ace tana da ikon bada kyautar rai da sai ta bawa yar'uwarta.
“Ni kam na yi bakar tafiya, tun da na iso gidan nan bakaken abubuwa kawai suke faruwa, da nasani ban zo ba”
Shi ne abun da Dr Zainab ta fada tana kuka. Maleek ya kalleta yana istijara.
“A'uzubillahi minal shaidanin rajin, Mommy ki daina fadar haka be dace ba, mu fa musulmai ne ko kuka da kuka duk be dace na ba a son ana tsare gawa ana mata kuka”
“Allahu Akbar, yau yata ta canja suna daga Nimra zuwa gawa kaico mai rai”
Ummi ta fada tana kara fashewa da kuka sosai. Maleek da Jabir da Umar ne suka rika gawar aka maida ita a wani empty daki dake kasa saboda idan an haura da ita stairs zai zama aiki, idan kuma aka barta a falon za su tsareta da kuka ne duk da kasancewar falon babba ne mai kamar wata karamar fada. Tun da aka shigo da gawar Nimra a gidan Abiey be fito daga dakinsa ba, kuma ba kuka yake ba sai dai yayi shiru wani abu ya tsaya masa a kahon zuciya... Hoton gawarta da ya gani a asibitin bayan Namra ta kira shi ta fada masa ya rasa yarsa ya doshi asibitin ya ganta a lokacin da aka fito da ita daga dakin da aka shiga da ita domin bata taimakon gaggawa, sai dai ina mai ajiya ya karbi abarsa, mai kira yayi kira babu tsaya, tarin kwararin likotoci ko kayan aikin basa hana mutuwa ko karin wa'adi.
The death of Nimra hit every one of them, domin ba su saka mata ran mutuwa, even though likitan yace za su iya rasa ta, kuma numfashinta ya gagara sauka normal kamar yadda yake. Sai just like yadda mafi yawa mutane suna daukar bugun zuciya kamar baya saurin kisa, but ana haduwa da ajali kuma kowa da silar mutuwarsa. Waya kan waya aka rika kiran Abiey tun daga familynsa na bangaren Ammy har zuwa na Mai Martaba, da na Yesmin amman ya kasa amsa kiran kowa sai na amininsa Sauban. A lokacin da Abiey ya amsa wayar, Sauban ya fara shimfida masa kalaman hakuri da juriya da kuma yadda da kaddara, Sauban ya tunatar da shi abubuwa da dama daga rayuwarsu da baya yayi masa kalamai na kwantar da hankali da saukar da natsuwa. Duk da haka idon Abiey ko kwalla be yi ba balle hawaye. Bayan ya tabbatar masa da gobe zai yi sammakon biyo jirgin safe daga Dubai to Nigeria sannan suka yi sallama. Abiey ya aje wayar ya mike tsaye ya taka yana jin kafarsa kamar ba tashi ba gaba daya jikinsa ma ya sauya as well as zuciyarsa. Ya fito daga bangaren yana jin yadda yanayin gidan ya canja gaba daya saboda rashin yarsa, Nimra ce ta biyu da yafi kauna a cikin yayansa bayan Maleek, domin ita ba kamar Namra take ba da girman kai ko ji da kai, she's very friendly tana zama ta yi hira da shi kamar yadda Maleek ya dauke shi aboki ko ma fiye da haka. Ta kofar baya ya shigo bangaren Ummi ya daga kai yana kallon yan'uwa da suke kusa na garin Abuja da suka cika falon duk kuwa da kasancewar dare ne. Dr Zainab ta fi kowa fahimtar ďan'uwanta tana ganinsa ta san abun da ya kawo shi sai ta fada masa inda gawar yarsa take. Ya taka da kafarsa ya murda kofar dakin ya shiga, sai yayi arba da ita tana kwance a cikin karaga slowly ya karasa kusa da gawar ya sunkuya ya saka hannu ya yaye zanen da aka rufa mata, fuskarta ta bayyana gata kwance kamar ta yi magana amman ba dama, hannu ya saka ya shafa fuskarta yana tuna maganarsa ta karshe da ita a asibiti, ya risina ya sumbance ta sai a lokacin hawaye suka cika idonsa har suka diga a jikin gawar. Yana kokarin mikewa tsaye sai ga Maleek ya shigo da sauri daman baya falon a lokacin da Abiey ya shigo da ba zai bar shi ba.
“Abiey haba me zaka yi a nan kuma?”
Abiey ya juyo ya kalleshi hawaye na masa zuba idonsa yayi ja sosai kamar wan watsa masa yaji a ciki.
“I'm here to tell na yafe mata duk wani hakki nawa da yake kanta kuma na nema mata gafara”
“Ganinta a haka zai haifar maka da damuwa, damuwarka kai da Ummi matsala ce a garemu”
Abiey ya daga dansa ya mike tsaye, Maleek ya rufe gawar hannunsa na rawa idonsa na kuka ya rika mahaifinsa suka fice daga dakin.
A Daren babu wanda yayi bachi, daga Ummi har Abiey da sauran yan'uwan da suke shakikanta, domin sauran familyns Abiey komawa suka yi gida saboda an fadi cewar sai gobe da 10am za'ayi jana'izarta. Kusan kowa kwana yayi yana nema mata gafara ban da Waira da bata san kalar addu'ar da zata yi mata ba, sai kuka kawai take jikinta na rawa. Babu wanda ya bi ta kanta daman Ummi ce da Nimra masu kulata Nimra ta tafiyarta tafiyar da babu dawowa, Ummi kuma imani da yarda da kaddara ne kadai ya hana ta fita hayyacinta, amman ta yi kukan da ya canja kamaninta ya kusan tashin rashin lafiyarta sai dai bata fadawa kowa ciwon da take ji. Misalin 3am Maleek ya fito waje ya daga dakin da gawar Nimra take saboda ance ba a barin gawa ita kadai, and shi ne mai karfin zuciyar da zai iya zama da ita. Shesshekar kuka ya ji a bayan kujerar da ta saba boya, definitely ya san ita ce a gurin mamakin yadda take ta kuka har yanzu ba ta yi bachi ba. Lekawa yayi sai ya same ta a takure idonta har ya fara duk sanyin ac dakin be hana ta tara gumi ba. Dagowa ta yi ta kalleshi idonta yayi ja sosai fatar idonta ta kumbura, farar fatar fuskarta ta yi ja sosai saboda farar bata bata son wahala, hancinta ma yayi ja. Da hannu yayi mata alama da ta taso, sai ta girgiza masa kai ta kwantar da kanta.
“Taso ki kwanta”
Ta taso tana kuka ta bi bayansa ya san bata son mutane, kuma gidansu yanzu akwai mutane dan haka ya nufi dakinsa da kanshi ya tura kofar dakin ya bude mata. Da kai yayi mata alama da ta shiga ta kwanta, sai da ta daga kanta sama ta kalleshi sannan ta shiga, sai ta kwanta a kasa jikinta na taba gadonsa. Blanket ya dauko ya shimfida mata kan doguwar kujerar dake dakin yayi mata alama da ta koma can, sai ta tashi ta nufi gun ta kwanta ya dauko karamin bargo ya rufa mata.
“Da gaske Nimra ta mutu?”
Kallonta kawai yake ya rasa kalar amsa da zai bata, ya san ita ma tana jin kamar ba gaske ba ne, abun it's so hard to accept. Be ce mata komai ba ya nufi kofar dakin ya fice yaja mata kofar. Downstairs ya sauko yana kallon gurin da Nimra ta gi yawan zama, kitchen ya zarce kai tsaye ya kunna tap ya tara cup ya sha ruwa, sai ya ji su da daci. Ya aje cup din yana kallon harabar gidan da komai yayi tsit, da cije bakinsa ya girgiza kai idonsa suka sake cika da hawaye. Immediately ya baro kitchen ya dawo dakin ya zauna yana da Nafilar dare.
Washe gari aka yi mata sutura, aka yi mata Sallah kamar yadda addinin musulunci ya shar'anta, sannan aka dauketa zuwa gidanta na gaskiya wato final destination. Hauka ce kawai Namra da Ummi ba su ba, amman sun yi kuka har hawayen suka kafe musu. Duk dauriyar Abiey sai da ya fashe da kuka a lokacin da aka zo sakata kabarinta. Har sai da aka rike shi Maleek kuka Mahmood kuka duk wani na kusa sai da yayi kuka a lokacin da suka rufe Nimra...
______________
Allah ka jikan Mahaifin, shi ne first gawan da na fara arba da ita a rayuwata. Please include him in your prayers Allah ya lullube kabarinsa da Rahma ya yafe masa. Tabbas mutuwa akwai ciwo💔😭
[7/4, 8:48 PM] My S Line: 47
*Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
“Abun is some how, amman taya aka dauki tsawon lokaci haka babu wanda ya fada maka?”
Ya juyar da fuskarsa dayan gefen yana kallon wani bangare na dabam.
“I think Daddy yana kokarin kare ni, domin ta ba shi ni kyauta, kuma ya rika ya rike ni ya so ni fiye da yadda yake son kansa, idan kuma yana son kwanciyar hankali dole ya bar magana ta kasance a rufe”
“Wata kila ita ma tana da dalili na aikata haka fa farko, kuma a yanzu ba ba zata rasa dalili da ya saka ta bayyana maka ba”
“Bata da wani dalili Humaira, kawai ina tunanin mijinta da take aure a yanzu ya nuna cewar baya so na, shiyasa ta aikata hakan ko kuma tana tsoron talauci, a yanzu kuma ban san dalilinta na bayyanawa”
“Ameer...”
Ta kirashi sai ya juyo ya kalleta.
“Ban taba ji, kuma ban taba ganin uwar da ta dauki cikin ďa wata tara ta haife shi kuma tace bata sonsa ba, ko da kuwa ďan nan ta hanyar zina aka same shi balle kai da aka haifa da hanyar sunna, kuma irin ku da suke nisa da iyayen kun fi komai shiga rai, dole akwai wani abu mai karfi da zai saka ta aikata haka, saboda ka aje duk wani abu da kake ji a zuciyarka ka fuskance ta ka tambaye dalilinta na aikata maka haka, wata kila zata baka gamsasshiyar amsa”
“Bana ma som ganin fuskarta a yanzu, bana son komawa gida, gaba daya na rasa me ke min dadi”
“I hope alakarka da Daddynka ba zata canja ba”
Ya girgiza.
“Ba zaki fahimci abun da nake ji ba Humairah, i wish bayan na mutu hakan ya faru”
“Mahaifiyarka bata kyautar da kai a gidan marayu ba, bata jefar da kai a hanya kamar yadda wasu iyayen suke ba, bata bada kai inda za ka sha wahala ba sai a inda aka nuna maka gatan da ko mahaifinka na gaske iyakar abun da zai yi kenan, please Ameer ka dubi wannan abun da idon Rahma”
“You take her side saboda mace ce yar'uwarki”
“No ina fada maka gaskiya ne, kuma ita ta fika zama abun tausayi, wata kila da zaka tambayi labarinta da zaka ji bata da laifi abun da ta aikata”
“Kalli yadda alaka ta kullu tsakanina da Nimra da ace ta kai na biye a yadda ta so na mun gudu mun yi aure yaya kenan? Ashe ma kanwata ce it hurt so bad, all this while Maleek yana kallona wani sakare saboda ya san komai”
Ya daki sitiyarin motar da karfi har sai da Humaira ta zabura.
“Calm down please ba lallai ace ya sani ba, maybe su ma ta boye musu”
“Amman Humaira ya zan kalli duniya da wannan?”
“I think zaka cigaba da zama a matsayin dan Daddy ita dai ta yi subutar baki ta fada maka gaskiya, kuma ina son ka kalli abun da budaddiyar zuciya please”
“Okay na kalli abun a yadda kike son na kalla, then what zai canja abun da ta yi? I don't even know my real father, sunansa ban sani ba ya rayuwarsa take ina yan'uwansa suke duk ban sani ba, wannan kadai ba abun bakinciki ba ne? Yanzu ne duniya zaka min dariya ashe duk abun da nake takama ba na ubana ba ne”
Ya dafe kansa.
“Na mahaifinka ne mana, shiyasa na ce ka kalli abun da budaddiyar zuciya, saboda ka fuskance ta tattauna da ita ka yi mata tambayoyi, kuma ka san yadda za ku bullowa abun saboda samun mafita, bayyana wannan abun wani abu ne na sirri da be kamata kowa ya ji ba, kuma za ku iya rufe wannan abun a tsakaninku”
Ta kunna wayar hannunta ta duba agogo.
“It getting dark ya kamata na shiga gida kar a fara nemana”
Ya gyada mata kai.
“Please keep reciting Hasbunallahu Wani'imal Wakil, aka samu sauki In Shaa Allah”
Nan ma dai kan ya gyada mata yana ta kallonta har ta fice daga motar da ke bude. Duk wani tsana da ta yi masa da kiyayyarsa da take ji a ranta sai ta ji abun ya tafi, tausayinsa ya cika mata zuciya, yadda yake rayuwa yana alfaharin da cewar Mr Bashir mahaifinsa ne ace a yanzu ba shi ne ya haife shi ba, abun dai kamar a shirin film ko littafi, domin abu ne da be cika faruwa a zahiri ba. Tsaye ta yi tana kallon motarsa har sai da ta daina hangoshi sannan ta juya ta koma cikin. Ba shi da wani gurin zuwa da ya wuce gidansu, daman idan bashi a office yana a gida ko kuma yana tare da abokansa, sai dai a yau jin yake baya kaunar kwana a gidan. Saboda haka ya nufi gidansa, fakawarsa ke da wuya a harabar gidan kiran Daddy ya shigo wayarsa, sai da yayi kamar ba zai daga ba sai kuma wata zuciyar ta hana shi kin amsa kiran Daddy.
“Hello”
“Kana ina?”
With serious voice Daddy yake tambayarsa.
“Ina gidana”
“Gidanka? Yaushe ka fara zama a gidanka?”
“Na kan zo sometimes da rana, yau kuma ina jin zan kwana a nan ne”
“Saboda makiyanka suna cikin gidan daka saba kwana?”
“No Daddy no har abada, kawai dai ina jin gidan kamar ya matse ne, ina jin wani yanayi marar dadi idan na tunkari gidan”
“Shiyasa na ce ka bar abun nan ya zauna a sirri, domin har yanzu baka mallaki hankalin da zaka iya controlling kanka da zuciyarka, me zai saka ma na yarda a gidanka kake? Kuma idan a gidan kake waya san iya abun da zai biyo baya? Zaka iya illata kanka ko ka illata wani, ko kuma a zo a yi maka wani abun”
“I can controlling myself, Daddy ni ba karamin yaro ba ne zan iya kula da kaina, sanin gaskiya ba zai kara min komai ba sai kwarin guiwa da sanin waye ni, bani da halin wulakanta kowa a yanzu, mutanen da nake ganin kamar na fi, wata kila sun fi ni komai, i need to know su waye familyn mahaifina, waye shi, wata kila ni din ba dan kowa ba ne, na ci mutuncin mutane da dama, saboda ina jin cewar na fi su, ashe ba haka ba ne”
“Ko a yanzu ka fisu Ameer, fada maka gaskiya ba zai canja matsayinka da duniya take kallonka da shi ba, ba kuma zai saka na tashi daga mahaifinka ba, babu abin da zai canja, sai dai idan butulce min zaka yi, ina son zan samu Zahra mu tattauna wannan maganar a barta ta zauna a sirri, kuma har yanzu Ameer shi kadai ne ďa namiji da Mr Bashir ya taba haihuwa, babu wanda zai fika gata da jindadin rayuwa i promise you this”
“Mahaifin Maleek ya fada min, saboda rashin kudin aiki aka siyar da cikina, kuma bayan siyar da cikin Ammy ta fada min Zahra ta kyauta da ni a gareka, wata kila saboda tsoron talauci ne ko Daddy? Akwai abun da ya fi wannan zafi? Kana ganin zan iya aje wannan abun na manta da shi?”
“Ameer ka dawo gida ka kwana, bana son ka je ko'ina”
Daddy na fadar hakan ya yanke kiran be tsaya jiran abin da Ameer din zai fada ba, domin ya fahimci Ameer din yana son jan maganar ta yi tsawo kuma ba lallai ya fahimci abun da yake kokarin lurar da shi a yanzu ba. Aje wayarsa ta yi daidai da sauwa hawaye a babban mutum kamar Mr Bashir ba tare da ya kalli Mommy dake gabansa ba ya ce.
“Jamila ta lalata min duk wani abu da shirya, ko da yake ba laifinta ba ne ita kadai har da Zahra, yanzu sun kirkiri tazara tsakanina da wanda na fi kauna a duniyar nan, kuma sun yi nasara shiyasa bahaushe yace tsintacciyar mage bata mage, da na san wannan ranar zata zo da ban karbi wannan kyautar da Zahra ta yi min ba tun farko”
Cikin yanayi mai ban tausayi Mommy take kallon jagoranta nata idon na kwarar da kwalla ta ce.
“Ka yi hakuri, haka Allah yake ikonsa idan ya zo, da ace ya so da dauke Ameer zai yi gaba daya ya mutu, ba ku san abun da zai faru gaba ba, dan Allah ku bar jayayyarsa, masu iya magana sukan ce ba a jayyyar ďa da miji, idan aka yi jayayyarsu tafi suke su bar masu jayayyar”
Mommy bata taba sanin cewar ba shi ya haifi Ameer ba sai a yanzu da komai ya lalace. shakuwarsu da yadda kaunar Ameer take a zuciyar mijinta take tunawa sai tausayinsa ya kamata. Tun da ya aureta be taba zancen mahaifiyar Ameer da ita ba idan ma ta dauko masa sai yace mata baya son maganar a dole take kawar da zancen domin ita macece mai matukar son farincikin mijinta yana ďaya daga cikin dalilin da ya saka take nunawa Ameer kauna, domin ta lura yana matukar kaunar Ameer ya kuma tabbatar mata da hakan tun kamin ya aureta.
“Baka taba kuskuren aikata wani abu da zai nuna Ameer ba ďanka ba ne, ko da wasa baka son bacin ran Ameer, Wallahi a rayuwata ban ga wani uba da ya nunawa ďansa gata fiye da yadda ka nunawa Ameer ba, lallai duniya zata girgiza idan labarin nan ya fita”
Tana fada tana kuka, ita ma tausayin Ameer din take jin cewar be sani ba sai a yanzu, kara ma Daddy ya san da sirri amman ya boye saboda farinciki ďansa, amman Ameer fa? Dare daya da wuni aka ruguza masa komai.
“Wata kila da Jamila bata aikata abun da ta aikata tun farko ba, da ba mu jefa yaron nan da kanmu a matsala kamar haka ba, ina tsoron kar ya shiga wani hali”
“Jamila ai dole ta fada masa gaskiya, saboda ta bata alakarku, na yi imani ba zata tado maganar kai tsaye ta fada