Showing 261001 words to 264000 words out of 281271 words
da Hajiya ta fada masa babu wanda ya fi tsaya masa a rai kamar cewar da ta yi Humairah tana sonsa idan da gaske ne ita din abar tausayi ce domin a yanzu ya fahimci yadda sonta yake, sai dai be yardar son da take masa ya kai wanda yake yi ma Nuwaira ba ma balle har ya fi. Wayarsa ya ciro ya ya shiga bangaren kiran number ta na sama domin idan baya gidan tana yawan kiransa ta tambaye lafiyarsa ko kuma ta fada masa wane abu ko ma ta tambayi yaushe zai dawo. Ya dade yana kallon Number sannan ya aika mata kira, ringing daya ta yi picking cikin nishadi da zumudi.
“Ameer yanzu fa nake ba kawaye na labarinka”
Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba. Jin haka ya saka hankalinta ya tashi.
“Ameer are you okay?”
“No”
“Ka zo ka dauke ni toh sai mu yi magana”
“Ba kararu zaku yi ba?”
“Karka damu, karatun be kai min kai muhimmanci ba, ka saka mood dina gaba daya ya sauya saboda jin ka a haka, kana ina?”
“Ina gida”
“Toh gani nan zuwa”
“No zan zo na dauke ki”
“Okay amman fada min damuwarka kamin ka zo please ka saka ni a tunani, ko Nuwaira ce ta bata maka?”
“Idan na zo zan mu yi magana ba akanta ne kadai ba wannan karon har da Ummi matsalar ciwonta zai haifar min da bakincikin da zan kasa hadewa Humairah”
“Ameer ka zo yanzu please ina harabar makaranta”
“Okay”
*** *** *** *** ***
Suna gama wayar da Ameer ta yi ma kawayenta sallama ta fada musu bata jindadi ba zata iya shiga aji tare da su ba, wasu suka yi mata sannu sannan ta kama hanyar fita makaranta tana goye da fashion bag dinta, sai karamin mayafin da ta rufe kanta kasancewar gown din material ce a jikinta. Tsakanin makarantar zuwa gate din makarantar tafiya ce mai nisa sosai amman haka ta kama hanyar tana tafiya tana tunanin maganar da Ameer ya fada mata, so take ta cilastawa kanta sai ta gano dalilin damuwarsa. Ta isa gate din a daidai lokacin da ya iso bakin gate din shi ma yake kokarin shiga, cikin makarantar shi ya fara ganeta sai ya faka daidai inda take tsaye ya sauke gilashin motar yana kallonta cikin yanayi na damuwa.
“Shigo”
Ta bude motar ta shiga tana kallonsa.
“Me ya faru Ameer?”
Hannu ya saka ya shafa kansa ya kalleta a karon farko bayan ta shiga motar babu abun da ke masa yawo a kwakwalwa sai maganar Hajiya kallonta yake da abun. Jikinta ya mutu bayan Ameer ya gama labarta abubuwan da suka faru babu ma wanda take ji a ciki kamar na ciwon Ummi. Damuwar da ta gani a fuskarsa karara ta saka ta zubar da hawaye.
“Ina son na gama duk wani shiri da ya kamata a gobe jibi zan bar kasar nan na je na ganta”
“Hakan ya kamata, ita a yanzu na san ta yi marmarinka ai, Allah ya bata lafiya, kuma please Ameer ka yi iya kokarin da zaka iya wajen ganin ka cika mata burinta”
“Zan yi hakan Humairah ki taya ni da addu'a, Allah yasa Nuwaira ta ba ni hadin kai”
“Ameen in Shaa Allah zan kara akan addu'ar da nake maka domin ina yi a kullum, Ameer baka sani ba ne kawai amman na fika son ka samu farinciki, farincikinka shi ne nawa, ina matukar son ka samu farinciki, farincikin ka shi ne farincikina a yanzu idan a ganka a damuwa ji nake kamar ba zan sake farinciki ba, damuwarka na jefani a matsala sosai”
Ya kalleta da kyau.
“Why?”
“Saboda kana da muhimmanci a gareni, ina matukar tausayinka a yanzu”
Ya gwada yin murmushi.
“Da can baki tausayina kenan?”
“Ba karya a da kam bana tausayinka sai da ina jin haushin abun da kake yi duk kuwa da kasancewar bana da alaka da kai a wacan lokacin, a yanzu kuma ina tausayin halin da ka samu kanka a ciki”
Be sake ce mata komai ba ya ja motar suka hanyar gida. Yana yi yana satar kallonta har suka isa gidan.
NUWAIRA POV.
Tana jin takowar Namra ta dago kai. Cikin yanayi na damuwar da take ciki ta tambaye ta.
“Yau kuma a stairs kike son zama? Dakin ya miki wani abu ne ko kuma tsoro kike ji?”
“A'a dazun da Ya Maleek zai fita na tambaye shi jikin Ummi be fada min ba, ina jiran ya dawo ya fada min ne”
Ta fadi hakan ne kawai dan ta kare kanta amman ba dan son jin ciwon Ummi kadai take jiran dawowarsa ba har da daukin ganinss da take yi. Namra ta sauke ajiyar zuciya ta zauna kusa da ita.
“Baya son ya fada miki ne saboda fadin ba shi da dadi Nuwaira, ni ma da ace akwai yadda zan ji na hana kaina jin abun da na ji akan ciwonta a dazun da na yi, amman ban isa na yi hakan ba”
“Bata ji sauki ba?”
A take idon Namra ya cika da hawaye.
“Saukin dai muke fata a yanzu...”
Tana bata labarin tana kuka Nuwaira ma kukan take daman abun da ta dade tana tsoron faruwarsa kenan bayan ta gano ciwon Ummi. Kuka sosai take na tashin hankali har ta fi Namra daga murya daga karshe ma Namra ce ta koma tana bata hakuri ta kwantar da ita a kafadarta. Suna a wannan halin Abiey ya shigo bangaren yana sanye da nasa tufafin bachin, kallo daya zaka masa ka san akwai damuwa sosai a tare da shi domin damuwar ta kasa boyuwa a fukarsa.
“Me ya faru?”
Ya tambaya ganin Nuwaira na kuka sosai Namra na rarrashinta ita ma tana kukan.
“Na fada mata abin da ka fada min ne a dazun”
Abiey ya sauke numfashi a hankali.
“Toh ya za'ayi, dole sai hakuri, Nuwaira zan iya magana da ke a yanzu?”
Jin haka ya saka ta dago ta dube shi, sai ta mike tsaye ta fara saukowa, Abiey yayi ma Namra alama da ta ba su guri da ido, sai ta tashi ta haye stairs din ta shige dakinta. Abiey ya samu guri ya zauna ya zubawa Nuwaira dake kokarin ganin ta saita kanta ido, ita ma sai tausayinta ya kama shi domin ita ta rasa duka uwa da uba a age dinta, kuma matar da ta zame mata uwa tana kokarin tafiya ya barta.
[8/18, 12:15 AM] 🦋-🦋: 82
“Babu abun da zamu yi sai hakuri, ki cigaba da yi mata addu'a In Shaa Allah zata samu sauki”
Ta amsa masa da kai tana share hawayenta.
“And dalilin zuwa a nan saboda ke ne, dazun Alhaji Bashir mahaifin Ameer ya same ni da maganar aurenku da Ameer ya son idan kun daidaita kanku mu kuma sai mu shiga ciki, domin ina son na hade aurenku da Namra da kuma Maleek da Mahmood saboda kawai na faranta ran Ummi, likitoci sun ce idan akwai wani abun da ya muke da buri ko kuma ita take da buri to mu aiwatar mata da shi a yanzu, domin ciwon nata kara tsanani yake”
A take tashin hankalin ya rufe Namra, wani irin faduwar gaba da fargaba da bata taba samun kanta a ciki ba ya rufeta, bata san wani abu gumin tashin hankali da sarkewar numfashi ba sai a lokacin, kamar ta bude baki ta cewa Abiey bata son Ameer kuma ba zata iya ba, domin yana da girma a idonta kuma baya wata magana mai girma bata taba hadasu haka ba, gani take kamar idan ta musa masa zai ce bata kyauta masa ba ne.
“Nuwaira”
Ta kasa amsawa kuma ta kasa dagowa ta kalleshi sai hawaye suke mata zuba kanta na sarawa a take zazzabi da tsanyi suka rufe ta.
“Nuwaira ina son ki bude bakin ki amsa min abun da zan tambaye ki, karki ji kunya ko nauyi na, karki cuci kanki kuma karki cutar da kowa, ki fada min abun da yake ranki, Shim kina son Ameer?”
Ta dago jajayen idanuwanta ta kalleshi hawaye na mata zuba ta girgiza kai alamar aa bakinta har rawa yake saboda kukan dake cikinta.
“So na aure nake magana kina son Ameer zaki iya aurensa ki zauna da shi? Idan baki sonki ki amsa babu wanda zai miki dole domin ke ma amanace a gurinmu”
Abiey ya fada mata a kokarinsa na fahimtar da ita, sai ta girgiza kai.
“Toh shikenan, amman kin tabbatar baki son shi? Kuma ba wani ya cilasta fadar hakan ba?”
Ta daga masa kai da sauri.
“Akwai wanda kike so a yanzu? Wanda zaki iya gabatar mana? Domin a al'ada da addininmu wanda kika kai a yanzu, kin kai munzalin aure, kuma addinin musulunci ya bawa mace zabar wanda take so, ba a yarda a aurawa mace wanda bata so ba, akwai wanda kike so?”
A al'adarsu bata sun kunya a yayin zaben miji ba, amman sai ta samu kanta da kasa amsawa Abiey wannan tambayar, wata kila tana jin tsoron yadda zai kalli abin ne ko kuma tana tsoron reply din da Maleek zai mata ne.
“Bude baki ki min magana idan akwai wanda kike so idan kuma lokaci zan baki ki yi tunani zan iya miki haka, amman dai ina son ki sani ina son cika burin Ummi ne”
Jin haka ya bata gwarin guiwar amsa masa ba tare da ta dago kan ta kalleshi ba.
“Tun a can garinmu an daura mana aure da Ya Maleek amman shi da Ameer sun ce ba auren gaskiya ba ne sai an sake daurawa”
Abiey na jin haka ya fahimci inda ta doso, domin ta yi masa magana ne da halshen damo, bata fito fili ta fada masa abun da take nufi ba, wata kila tana tsoro ne ko kuma tana jin kunya.
“Eh haka ne, dole ne sai an sake daura muku aure na musulunci, yanzu dai idan na fahimta Maleek kike so kenan?”
Abun ka da wanda ba bahaushen mutum ba sai ta daga kai tsaye tana kuka.
“Eh amman zai iya min fada, shi baya so na nindai ba zan auri Ameer ba, Ya Maleek nake so”
“Ta kwana gidan sauki, daina kuka yarinya zan yi magana da shi idan ya amince shikenan idan kuma be amince ba shi ma ba zan masa dole ba kamar yadda ke ma ban miki dole ba”
Ta amsa da kai sannan Abiey ya mike tsaye ya nufi bangarensa, tsoron kar Maleek ya dawo ya same ta a falon ma ya saka ta shige dakin Namra ta kwanta kwanan dole, amman bachi ya ki daukarta sai ta da dare ya raba. Washe garin Abiey ya labartawa Maleek abun da ya faru tsakaninsa da Nuwaira bayan na gama fadawa Daddy yadda suka yi a waya, Maleek sai ya rasa me zai yi farinciki ta fadi shi take so, ko bakincikin dan'uwansa Ameer ya rasa? Domin ya lura Ameer yana son Nuwaira sosai sai dai ba su isa su yi mata dole ta so abun da bata ra'ayi ba.
“Amman Ameer zai ji wani iri idan ya ji, zai shiga damuwa”
“Ina kyautata zaton zai fahimta, kuma idan har ya sauya a yadda ni da kai muke gani zai yarda ya karbi wannan kaddarar ne”
“Amman Abiey abun is some how ta ya zai kalleta a matsayin matata?”
“Ta yadda zaka kalleta a matsayin matarsa da ace abun da yake nema ya samu, idan baka ra'ayinta kai ma ba zan maka dole ba kamar yadda ban mata dole ba, zaka iya gabatar da wadda kake so sai mu bincka iyayenta da tarbiyarta kamin lokaci ya kure mana”
“Zan yi tunani akai Abiey, a bani kwana biyu”
Daga haka ya mike tsaye ya fice daga falon, ji yayi baya bukatar ganin kowa sai Nuwaira a lokacin dan haka ya nufi bangaren Ummi, yana shigowa ta ganshi sai ta saki kular hannunta ta juya zata bar falon da gudu, cikin hanzari da jarumtaka ya sha gabanta sai ta duke ta rufe kanta, tunanin take zai mata fada ne ko ya fada mata magana marar dadi akan abun da ta yi, domin bata da masaniyar yana sonta ko akasin haka all what she knows is ita dai tana sonsa. Dukawa yayi gabanta ya kalleta gabansa na bugawa da mugun karfi, har lokacin kuma ya kasa faricikin ya kasa bakinciki kuma ya kasa ganin laifinta haka ma yana ganin babu hujjar da zata saka ya zargeta da kin Ameer.
“Me ye na rufe idon?”
“Fada zaka min?”
“Saboda kin san abun da kika yi baki kyauta ba ko?”
“Ni dai kawai na fadi abun da yake zuciyata ne”
Ta amsa da muryar dake nuna alamar tana daf da fashewa da kuka, har lokacin kuma bata yarda ta dago ta kalleshi ba. And now murmushi ne a fuskarsa sometimes tana abu kamar wata yar 6 years.
“Me yasa baki son Ameer?”
“Ni dai kawai bana son shi da aure?”
“Sai wa?”
Ta ki yarda ta amsa masa, har ya gaji da jira ya mike tsaye ya rumgume hannayensa yana kallonta.
“Ba fada zan miki ba tashi tsaye”
Ta ki ta mike tsayen kuma ta ki ta dago kan, har sai da ya gaji da tsayuwa ya fice daga falon, yana maida kofar ya rufe sai ya jingina da kofar ya lumshe ido yana murmushi...
AMEER POV.
Zagaye zagaye Daddy yayi ta masa sannan ya fada masa gaskiyar abun da Abiey ya fada masa na irin amsar da suka samu daga gurin Nuwaira. Ameer yayi murmushin da hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo ya hade wani abu da ya tsaya masa a makoshi.
“Daman na saka ran haka, domin na lura da yadda take mu'alama da ni babu so a ciki”
“Wata kila lokaci take bukatar a bata...”
“Aa Daddy, da ace kudi yana siye rago kyau na san zaka iya siya min, idan har bata son aurena bana son na aureta a dole kuma iyakar son gaskiya da zan nuna mata a yanzu shi ne na barta ta auri wanda take so, ko da kuwa bera ne, indai hakan zai saka ta farinciki ni ba ni da matsala zan jur har na saba, sometimes dole ne mu karbi kaddara, Humairah tana yawan fada min haka, kuma ni ma ya zamin ishara wata ma rai ta rasa saboda ni, ni me yasa ba zan iya hakuri ba? I have to accept this Daddy”
Duk kokarin da yayi na danne zuciyarsa sai da hawayen bakinciki suka zubo a idonsa.
“Haka ne, wani lokacin kana ganin abu sai kuma ya zama ba alheri ba ne a gareka, Allah ya saussauta maka Ameer, zan yi magana da Abiey ya daga maka kafa har ka warke daga wannan ciwon kamin ka samu sukunin son wata a ranka”
“Ba zan taba warkewa ba daddy har a bada, kuma ba zan bari hakan yayi tasiri gurin hana ni cika burin Ummi ba, wannan ne lokacin da zan amsa sunana na cikeken musulmi mai yarda da kaddara”
Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Ameer cike da tausayi.
“Allah zai maka mafita soon Ameer”
“In Shaa Allah”
Ya tashi ya fice daga falon. Dakinsa ya shiga ya kwanta sai ya ji gadon baya masa dadi, ya tashi zaune zaman ma babu dadi, a take ya fara safa da marwa yana son yayi kuka ya kasa domin abun ya fi karfin kuka a gunsa, sai dai mamaki kawai yake da dariya wani gefen kuma yayi murmushi. Da ya ji kamar ba zai iya da zaman gidan ba ne ya saka ya fice daga gidan ya nufin gidan kakarsa, a nan kam ya samu sukunin yin kuka bayan ya budewa Humairah zuciyarsa. Dole ce kawai ta saka ya shiga gidan Abiey da daren ranar domin ya gama shirinsa na tafiya ziyarar Ummi, kuma yana son tafiya yayi ma Abiey Namra Mahmood da Maleek sallama har ma da Nuwaira. Daya bayan daya ya biyu yana sallama da kowa, Abiey ya dade yana masa nasiha kuma ya nuna masa babu hannu ko laifin kowa a ciki, bayan ya gama karanta masa muhimmanci yarda da kaddara, hakan da Abiey yayi masa ya saka shi jin sanyi domin be saka tsammanin Abiey zai zaunar da shi ya masa nasiha mai ratsa zuciya haka ba, bayan duk abun da ya faru a tsakaninsu sai a yanzu yake tsantsar nadama da bakinciki abun da ya aikatawa Nimra, a yanzu ya fi gane yayi kuskure fiye da baya. Bayan ya fito ya shiga dakin Mahmood ya gaisa da shi kuma yayi masa bankwana tafiyar da zai yi ya shiga dakin Namra a nan ne hankalinsa ya tashi a lokacin da yayi arba da Nuwaira abun ka da mai karfin hali kuma sai kallonsa take, sai yayi mata murmushi ya ce.
“Zan tafi gurin Ummi gobe kina da sakon da za a kai mata?”
Ta kalli Namra sai ta kasa cewa komai.
“I'm sorry for loving you Nuwaira, i was afraid of leave you, amman yanzu na fahimci we are not mean for each other, ina miki fatan alheri kuma ina miki addu'ar Allah yasa wanda kike so ya rike ki amana ya so ki fiye da ni, ban cancanki ba Nuwaira a gane hakan a yanzu, kin cancanci auren tsabtatacen mutum wanda kika so saboda samun farincikinki, baki cancani mutum mai son kai da rufe ido ga bukatun wasu ba irina, duk haka kuma zan miki godiya domin zuwanki a rayuwata ya canja rayuwata ya koya min darasi da karatun da ban san da shi ba a baya”
Hawaye ya sauko idonta maganarsa na taba ta, sai dai ita dai ta san har ga Allah bata jin son Ameer da aure, ko da kuwa zata rasa Maleek ne, ba Ameer ba har Eid da yake dan'uwanta bata jin zata iya aurensa, haka ma bata jin tana yi ma Sulem dinta irin wannan son, Maleek kawai wanda yayi nasarar cike wannan ramen a zuciyarta.
“Bana nufin cutarwa dan Allah ka fahimta”
Sai ya mata murmushi ya girgiza mata kai.
“Noo please don't cry idan ban fahimce ba waye zai fahimce ki? I know what you mean”
Ya kalli Namra dake rike da system.
“Zan wuce gurin Ummi gobe ayi mana gafara ban san ta rai ba”
“Ameer dan Allah karka hukunta kanka karka dorawa kanka laifi akan abun da ya faru, dukan mu muna kuskure, please don't feel bad akan abun da ya faru, i wish i could do something”
“You're such a wonderful Sister, thank you sai na dawo”
Ya juya ya