Showing 270001 words to 273000 words out of 281271 words

Chapter 91 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1184

shirya ka kuma ya nuna mana yasa ina da rabon gani”

“Zaki gani Ummi In Shaa Allah”

Ta dade tana hira da danta sannan ta tashi ta fita cikin mutane. Kusan babu gidan tv da be haska dauren auren da aka yi a babban Masallaci Jumma'a dake Abuja ba, domin daurin aure ne da ya samu halartar manyan mutane lungu da sako na nigeria har ma da waje kasar. Daga bangaren Daddy da Abiey sai kuma bangaren Shuraim da kuma surukan Daddy da suka kasancewa manyan mutane. An yi ma Abiey kara haka ma Daddy an masa kara domin daurin aure ne na farko da kowa wannen ya fara yi, kuma sun halarci na wasu dole su na ayi musu a nasu ko dan Naira... Bayan saukowa daga Sallah Jumma'a aka daura auren Maleek da Nuwaira, Ameer da Humaira, Namra da Shuram, Ramla da Yunus, Afrah da Aliyu, Bilqis da Mu'azzam ƴaƴan Mr Bashir.

Baya daurin auren aka yi liyafar cin abinci babbar hotel din Fancy Home dake Abuja, babbar hotel ce da ko titin ta baka isa ka hau ba sai kana wani shege ko dan wani shegen wato rich people. After dinner ko wane ango ya nufi inda Amaryarsa take domin yin hoto da kuma gaisawa da danginta. Ameer ya nufi gidansu Humarah Shuraim kuma ya nufo gidansu Namra Maleek ma haka gida ya dawo domin tasa amaryar yar gida ce.

Wannan ne second time da Humairah ta ji tana jin nauyin daga ido ta kalli mutumen da a yanzu zata iya kiransa da mijinta, yau ne ranar da duk wani buri da take da shi ya cika, a yau hawayenta na farinciki ne Allah ya mallaka mata abun da take da neman zabin Allah akansa, a yau duk wani Ciwon So ya warke zuciya ta samu muradinta hankali kuma ya kwanta. Hannu ya saka ya rika fuskarta ya dago kanta sai ta kasa kallonsa har lokacin hawaye farinciki take, kasancewar babu kowa a falon ya bashi damar kai bakinsa saitin inda hawayenta ke zuba ya sumbance su, sai ta rufe idonta gently ya sumbanci saman fatar idon.

“Yanzu idan na rungume ki babu wanda zai ce akan me, ke ma kuma baki isa ki hana ni ba”

Da wani irin shauki da annurin zuciya yake fadar haka yana kallonta, ta yi irin kyaun da be tana ganin ta yi ba sai yau da take rana ce mai muhimmanci a gareshi. Murmushi ta yi ta rumgume abunta ba tare da ta kalleshi ba, kamshinsa da ba rabo da jikinsa ya rufe ta har sai da ta lumshe ido. Dariya yayi mai sauti ya dagota daga jikinsa sai ya ga idonta a rufe, iskar bakinsa ya busa mata saman idon ya kai bakinsa ya sumbancin hancinta tun tana counting har lissafi ya bace nata, kamin ta ji bakinta cikin nasa sun dade suna musayar yawu sannan ya cire bakinsa ya rumgumeta yana jin kaunarta har cikin ransa. Sun dauki lokaci a haka kamin ya dagota ya sumbance a karo na biyu ya rika hannunta suka fito daga dakin ana ganinsu aka fara dariya ana daukarsu a waya. A falon suka zauna Photographer yana fada musu yadda za su yi, yana daukarsu hoto cikin kunya Humaira take yarda ayi, shi kan gogan daman can ko a lokacin da ba daura ba yayi balle a yanzu da yake jin ko komai yayi mata babu mai ce masa dan me, Ameer irin angwayen nan da ba su da kunya kuma ba sa gudun magana, gashi ya samu shy shy bride.




MALEEK POV.

A hamkali ta shigo falon tana sanye da farin lace ta yafa farin mayafi hannayenta da karfa duka jan lallen ne mai masifar kyau, tana doso inda yake zaune sai ya mike tsaye da farar shadda ce jikinsa an nada masa rawani yana sanye da tsadaddar Alkibbar sarauta dakin sai kamshi kamshin turarensa yake zuwan Nuwaira kuma sai kamshin ya gauraya ya bada wani kalar kamshin na dabam murmushi take tana kallonsa har ta iso inda tsaye yana jiran isowarta.

“Subhanallahi Alhamdulillah”

Ya furta sannan ya duka kasa ya kai goshinsa yayi sujudar godiyar a cikin yayi addu'a, sannan ya dago ya daga farin lace din dake jikinta ya sumbanci saman kafarta da ya sha red henna, ya kalli kwayar idonta dake yawo cikin idonsa.

“Na dade ina jiran wannan ranar, ranar da zaki zama halal dina, ranar da zaki min murmushi ki samu lada kuma ranar da zan taba ki na samu lada, ranar da zaki zama halalina ni kadai, yanzu ke tawa ce ni kadai Nuwaira...”

Ya kai hannun zai taba fuskarta.

“Bismillahir Rahamanin Rahim”

Ya fada sannan ya taba tsokar kumatunta, ya shafa ya matsar da bakinsa ya sumbanci gurin, ya sumbanci gaban goshinta ya sumbanci kumatunta na hagu, ya sumbanci saman hancinta ya sumbanci gefen bakinta ya sumbanci dayan gefen sannan ya sumbanci saman lisp din da suke matukar daga masa hankali. Ya bude alkibbarsa ta fado kirjinsa ya rufe ta da alkibbar ya rumgume yana sauke sanyayyiyar ajiyar zuciya. Ita kuma ta yi lamo tana jinta wani sabo yanayi da bata taba ji ba, kamin ya bude alkibbar ya dago kanta ya saka yatsansa yana laba lebenta.

“I love you”

Murmushi ta yi sai ya dora fuskarsa saman nata, hancinsa da nata suka yi tarayya, numfashinsu ya fara gauraya, idonta da nashi suna blinking a take, ya rika kunkurunta da dayan hannunsa dayan kuma ya kama hannunta ya saka yatsunsa cikin nata ya jimke. Bata hankara ba ta ji sanyi yana sauka a lips dinta na yawunsa da suka jika lebensa numfashi yayi da karfi sai ta rufe idonta shi ma ya lumshe na shi ya kama lips dinta na kasa a hankali ya fara tsosawa...
[8/21, 5:35 PM] 🦋-🦋: 85

Two Weeks later...


Ta bude murfin pot din kamshin stew ya fara tashi, sai ta juyo ta kalleshi tana yar siriyar dariya.

“Ka ji ko? Kamshi yake yi”

Maleek ya aje wayar dake hannunsa ya karaso kusa da matarsa ya rika kunkurunta yana shafa cikinta dake cikin rigar material, a madadin ya kai hancinsa saitin inda zai ji kamshin abinci sai ya kai hancinsa a wuyanta ya fara goga mata zirin hancinsa yana lasa wuyanta a hankali.

“Miyar fa na ce ka ji kamshinta”

“Uhmmm”

Shi ne abun da ya fita daga cikin gurnaninsa sai yayi kamar be ji ba ya lumshe idonsa, ya kai hannunsa yana bin layin hallitar wuyanta da yatsansa, yana maida gashin da Allah ya wadata ta da shi dayan gefen.

“I Love you”

Ya rada mata a kunne muryar can kasa kamar mai tsoron wani ya ji, bakinsa ya bude gaba daya ya hade kunnenta yana tsosa, tana jin haka ya san kokarin wuce gona da iri yake, domin ta fara fahimtar Maleek tun a daren ranar da aka kawota, bata wani abu tsoron daren farko ba, bata da kawayen da za su tsorata ta da haka a rayuwa irin ta garinsu kuma bata taba cin karo da wani abu makamancin daren farko ba. A iya tsawon rayuwarta bata san wata alaka na shiga tsakanin mata da miji ba, a tunaninta idan an yi aure an yi kenan shi kenan kin zama matar mutum shi am ya zama mijinki, ta san kiss da rikon hannun ko rumguma, bayan wannan tana taba sanin ana wuce gona da iri ba gurin taba wasu bangarorin na jikin mace. Har yanzu kuma ta kasa sabawa da irin abubuwan da Maleek yake mata tun da ya taba gwada son yin mu'alama da ita ta ji zafi bata sake yarda ko hannunsa ya kai a gurin ba, a ranar ma sai ta kasa bachi sai kallonsa take domin bata taba ganin namiji babu tufafi kamar yadda ta ga Maleek ba, hankali be tana kaiwa ta lura da wani abu a jikin wanda ba jinsinta ba sai a lokacin. Jin halshensa na yawo a cikin kunnenta har cikin kusuwar kunnenta ya saka ta yi saurin juyowa ta fuskance shi, zare kunenta da ta yi a lokacin da be yi tsamani ya saka yawun bakinsa zubowa a lips dinsa sai ya saka halshensa ya lashe kamar wani maye, ya bude idanuwansa da suka canja launi ya kalleta kamin ya saka hannayensa ya zagaye, ita kuwa sai kallonsa take tana ganin kamar an dauke Ya Maleek dinta ne ya kawo mata wani dabam.

“Ummi tana can tana jiranmu”

Ya daga mata kai, sannan ya saka karfinsa ya dagata sama har sai da ta fishi tsayi, ya riketa da dayan hannunsa ita kuma ta dora hannayenta akan kafadarsa ta kwanto da fuskarta a saman fuskarsa tana dariya.

“Idan mun dawo za yarda ko?”

Yana maganar yana kissing bakinta.

“Da me?”

Ya kai hannunsa ya shafa bayanta zuwa inda zata fahimci yarensa.

“Kin ga ai gobe zan tafi ba ki sani ba ko ba zan dawo ba Please Princess”

Ta girgiza kai tsaye alamar ba zata yarda ba, sai ya sauke cike da damuwa.

“Haba Nulik, yanzu ya kike son na yi? Haka zamu yi ta zama? To miye auren Fisabilillahi?”

“Idan anyi aure za ayi girki ayi zama tare a yi kwama shikenan sai kuma a haihuwa”

“Toh haka nan ake haihuwa daga sama ake jefon yayan? Kullum sai na fada miki amman kin kasa fahimta, waye zai yi aure da lafiyarsa ya aje Amarya har sati biyu be mata komai ba”

“Mu a garinmu ba ayi, ku dai kuke yi”

Tana fada tana turo baki gaba. Ya kai hannunsa ya biyu ya dora a kirjinta.

“A addinin kowa ana yi, Matsalar da aka samu gurin koya miki addinin ba a fada miki yadda zaki kula da miji da bashi hakkinsa ba, sai aka maida hankali gurin koya miki ibada kawai, Mama Maryam bata koya miki komai ba wai?”

Ta buge masa hannu ta dan juyar da fuska.

“To ita ita ita... Bata san haka ba, wannan ai duk haramun ne, ni ba zan yarda ba ni gaskiya ba zan yarda da wannan abun ba sai dai a fasa auren... ”

Be san lokacin da ya fashe da dariya ba.

“Kin auro yarinyar, ni da ke mutu ka raba talkamin kaza, kuma babu abun da za a fasa idan ma zaki daina wahalar da ni ki daina, tausayinki nake shiyasa kawai nake daga miki kafa, amman jiyan nan kika gama cika min baki akan kina son ki haifi yara da yawa”

“Na fasa haihuwar bana so”

Ta bata fuska sosai ita dai a bakin gaskiyar ba zata yarda da wasu dabi'u da hallaye da Maleek ya tsira mata ba tun bayan da aka daura aurensu abubuwan da kwakwalwarta suka kasa dauka.

“Ni da na san haka zaka zama ba zan yarda da auren ba, wannan abun Ummi ma idan ta ji sai ta yi masifa ai”

A take dariyar dake fuskarsa ta bace, ya hade mata fuska kamar be taba murmushi ba.

“Allah yasa idan muka je ki fada mata, ki ga yadda zan fasa bakinki ki jure stew din ki fito mu tafi”

Ya fice daga kitchen din, bacin ran da ta gani a fuskarsa ya saka ta ji babu dadi, har da yan hawayenta. Haka ta juye stew ta hade s7 guri daya a basket din ta dauko ta fito falo, sai ta same shi zaune yana rike da key. Mikewa yayi tsaye ya dauki basket din.

“Idan kin saka hijab dinki ki same ni a mota”

Ta bishi da kallo har ya fice, sai kawai ta ji bata bukatar yin komai sai kuka, ai ko fita zai yi janta yake har gurin motar yana rumgume da ita yana kissing dinta haka ma idan ya dawo, amman yau saboda ta ce ba zata yarda da wannan rashin imanin da yake son aikata mata ba sai yayi fushi. Kamar wata karamar yarinya haka ta shiga dakinta da komai na cikinsa fari ne tun daga kan Turkish furniture din har curtains, ta dauko hijabinta ta saka ta fito tana tafiya tana shura kafafuwanta har ta fito waje. Yana ganinta ta fito daga motar ya bude mata bangarenta, sannan ya iso garenta ya rumgumeta yana murmushi.

“Wannan fushin na minene?”

Sai ta fara kukan shagwaba kamar wata yar baby.

“Ba kai ne ba, daga kawai na ce ba zan yarda ka aikata min wannan rashin musuluncin ba sai ka yi fushi saboda ka san ina sonka sosai”

“Toh zaki yarda?”

Ta ki ce eh ko aa zuba masa kukan shagwaba take, irin shagwabar dake rikirkita namiji musamman wayaye wanda ya san me duniya take ciki. Kunnesa ya kai ya rada mata wata magana mai girma a kunneta a take ta daina kukan ta dago daga kirjinsa tana kallonsa sakaka, be yarda sun hada ido ba ya ja hannunta yana murmushi ya nufi motar da ita ya sakata a front seat ya rufe, ya zagaya dayan side din ya shiga ya murza key sai ta juyo tana kallonsa. Hannu ya mika ya kama hannunta ya kwanto da ita jikinsa ya fara tukin da hannu daya, sabon mai gadin na su ya bude masa gate yana daga masa hannu, Maleek yayi masa horn ya fice daga gidan. Sai da suka fara nisa sannan ya saki hannunta bude gurin da ya koyawa kansa aje sweet tun bayan aurensu ya dauko daya ya bude ya saka mata a baki, ya dauki daya ya sha.

“Laa ashe nan kake aje sweet din da kake shigowa da shi kullum?”

Ta san kullum idan zai dawo gida zai shigo yana shan sweet ne, idan ya kwatanta lokacin dawowarsa gida ko ya kama hanyar gidan sai ya bude ya saka a baki, bakinsa yayinta kamshi, wani sa'in shi da kansa zai bata ragowar idan yaje kissing dinta wani lokacin kuma da kanta take saka hannu a bakinsa ya ciro shi ta saka a bakinta, ranar da ya so su yi kurciya kuma sai ya hana mata har sai ta yi ta kokawa da shi har ta samu nasara ya karbe. Hannunsa ya kai yana taba bakinta kamin ya tura mata yatsana a baki ta cigaba da tsosa tare da sweet din dake cikin bakinta, cikin dabara ya zare minti tare da yatsansa yayi saurin jefawa bakinsa yana dariya.

“Ka shanye naka ne?”

Ta turo halshensa ya nuna mata duka mintin biyu da na shi da nata da ya karbe.

“Kin san gida fin karfi kike min ko? Sai ki danne ni ki karbe ko kuma idan muna kiss ki karbe min ko da ban yi niyar baki ba”

Ta mika masa bakinta.

“Toh ayi kiss din”

Ita a wayonta idan ya zo kissing dinta sai ta kwashe har nasa, sai da ya kalli titi da kyau sannan ya mika bakinsa ya mata kiss saman lips dinta be yarda ya shigar da bakinsa ba. Ya saka hannunsa ya lakaci hancinta.

“Anki ayi din ke sarkin wayo ko?”

Ta kyalkyale da dariya, shi ma dariyar yayi ya riko hannunta ya saka yatsunsa cikin nata ya cigaba da tukin da dayan hannunsa har suka isa gidan. Be fita motar ba sai da ya taune minti gaba daya ya hade domin be son ya shiga falon Ummi yana shan minti. Back seat ya bude ya dauko basket din abincin da Nuwaira ta girkawa Ummi for the first time in history, tana gaba yana bayanta suka shiga falo, a tsakar falon ta wulgar da talkaminta ta nufi stairs din da gudu tana marmarin ganin Ummi daman kullum sai ta yi masa maganar ya kawo ta amman ya ki sai dai ya kira mata ita a waya su gaisa, da gudu ta baki kofar dakin ta shiga Ummi dake kwance da Mahmood dake zaune yana matsa mata kafafuwanta suka kalli kofar ganin Nuwaira ce ya saka Ummi murmushi, Mahmood kuma ya ce.

“Sai ba ke ma”

Nuwaira na ganin yadda ciwo da rama suka samu muhalli a jikin Ummi sai ta fada jikinta ta fashe da kuka.

“Ya isa ya isa ba gani kin gani ba? Miye na kuka?”

“Ummi i miss you”

“I miss you too Baby Nuwaira, ya sabon gidanki”

“Babu dadi saboda babu ke a ciki Ummi”

“Zaki saba da sannu, mussamman idan kika gina naki iyalin”

A hankali Ummi take magana irin na masu ciwo yana shafa fuskar Nuwaira. Maleek ne ya shigo dakin ya aje basket din daga gefen gado Ummi ya zauna a kusa da matarsa yana kallon mahaifiyarsa zuciyarsa babu dadi.

“Maleek ya kake?”

“Lafiya kalau Ummi ya jikinki?”

“Alhamdulillah ina ta ibada”

“Allah ya baki lafiya”

“Ameen”

“Ga abinci nan Nuwaira ta girka miki”

Ummi ta dan daga kai ya kalli basket din tana murmushi irin na masu karfin hali.

“Tare kuka girka?”

Kamin ya bata amsa Nuwaira ta ce

“Ni kadai na girka Ummi saboda ke na yi, dan Allah ki ci”

“Zan ci mana dole na, Nuwaira ce yau ta girka abinci ta kawo min? Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani ikon ganin wannan ranar, Mahmood dauko plate da spoon na ci abincin yata”

Mahmood ya tashi ya fita tana murmushi, sai Ummi ta kama hannun Nuwaira ta kama na Maleek ta saka na Nuwaira ciki.

“Maleek ga Nuwaira na san an baka amanarta tun a ranar da aka daura muku aure, amman yau ina son na kara jadada maka Nuwaira bata da kowa a duniya sai ni da mahaifinka sai kuma kai da yan'uwanka, ita din amana ce a gurinmu, dan Allah karka cutar da ita, ka rike ta amana ka nuna mata soyayya da kauna kamar yadda ta nuna maka har burinka ya cika, karka yarda ta zubar da hawaye akan ka karka surfa mata bakinciki namiji, karka saka ta yi nadamar kasancewarta a cikin addinin nan karka saka ta ji kewata idan bana nan saboda wani mugun abu da zaka yi mata, ka je har garinsu ka ga gidansu da irin rayuwar da ta taso a cikin, yarinya ce da bata san gata ba, dan Allah Maleek ka zame mata gata rashin uwa da uba, karka yarda wani abu ya rabu sai mutuwa”

Maleek ya jinke hannun Nuwaira hawaye na sauko masa.

“Na miki alkawari matukar ina raye Nuwaira ba zata taba rashin wani abu ba, kuma ba zan taba cin amanarta ba, sannan na miki alkawari zan maye mata gurbin uwa da uba zan bata duk wani gata da ta rasa”

Ummi ta yi murmushi hawaye na sauka a idonta. Sannan ta dubi Nuwaira da tun da ta fara maganar take kuka.

“Nuwaira ki rike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login