Showing 102001 words to 105000 words out of 281271 words

Chapter 35 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1214

dalilinta na kin son auren Nimra da wanda take so, domin ta ga komai a madafar iliminta sai dai illar ce ta kasa gani har yanzu.

“Waira?”

Ta kalleshi da idanuwanta masu kamar na mage.

“Lafiya kike yau?”

Ta girgiza kai domin ya saba fahimtarta tun kamin ta fada masa komai, ita kuma bata boye masa damuwarta a duk zuwan da yake gidan, wannan ya saka take jindadin zuwansa fiye da zuwa makaranta da ake takura mata. Ya bar jikin allon ya dawo kusa da ita ta tsaya.

“Fada min meya faru yau kuma?”

“Ummi tana son Mijin Nimra, kuma Ummi tana da ciwo, kuma ciwon zai kasheta ta mutu kamar Waira, amman ba ta fada ba, Ya Maleek ya daki Nimra kuma Nimra tana son... ”

Ta kasa karawa domin bata rike sunansa ba saboda haka bata san yadda ta kwatanta shi ko ta kira shi ba, Dattijon yayi murmushi ya dauko kujerar ya dawo kusa da ita ta zauna.

“Ki daina damuwa da matsalar wasu, ke ma kina cikin taki matsalar ai, ki daina kuka haka nan kukanki yana saka ni jin babu dadi”

“Toh”

Ta amsa tana kallonsa idonta na sake cika da wasu hawayen. Ya saka hannunsa aljihu ya dauko apple ya mika mata sai ta karba ta rike, a can idan suna darasi take cin apple kullum idan ya bata yau kuma da take cikin kuka da bacin rai sai ta kasa ci ta rike Apple din kawai a hannu, mikewa yayi tsaye ya nufi jakarsa ya bude ya dauko farin zomo ya nufota da shi ya dora mata saman jiki sai ta saki apple din da sauri ta rike zomon.

“Neman wannan zomon ya saka ban zo jiya gurin darasinki ba, ina fatar kina son shi”

“Sosai sosai”

Ta rumgume shi a jikinta tana jin kamar beranta ne na baya data rasa.

“Thank You”

Murmushi da farincikin da ya gani a fuskarta wanda ya kawarda bakinciki da bacin ran da take ciki ne yafi komai faranta masa rai kuma daman abun da yake son gani kenan. Ta mike tsaye ta aje zomon zata rumgume shi sai yaja baya da sauri.

“Aa aa aa, dauki jakarki ki shiga ciki darasi ya kare sai gobe idan na dawo”

Ta juya ta dauki zomon da ya fara neman gurin boya tana dariya fararen hakoranta a waje kamar ba ita ba, ta dauki jakarta da dayan hannunta ta fito daga gurin ta nufi part din Ummi da gudunta, tsaye yayi yana kallonta da murmushi a fuskarsa har sai da ta fice sannan ya nufi jakarsa ya dauka ya fice daga gurin, har ya isa gate be daina waigen part din kamar ya san zata dawo ta daga masa hannu, sai gata ta fito daga part din tana masa waving hakoranta a waje. Daga inda yake ya daga mata hannu sannan ya fice yana tafiya kamar mai ciwon kafa.
[6/17, 10:49 PM] My S Line: 34

Bayan ya wuce ta dawo cikin falon ta fara neman zomonta da ya bata daga inda ta aje shi.

“Uteee Teee Uteeee”

Kiransa take da yarenta kamar an fada mata yana jin abun da take fada, abun da bata taba yi a gidan ba wato magana da yarenta shiyasa har yanzu babu wanda ya san kalar yaren da take a gidan.

“Ukur tek fi, utee utee kat...”

Fada masa take idan ya fito zata ba shi abinci mai kyau mai dadi. Ta fara leken kasan kujerun dake falon sai ta hango inda yake boye jikin wata kafar kujera, rarrafe ta yi ta isa gurin ta kama shi ta fito tana dariya ranta fal da farincikin da ta manta when last ta yi murna na samuwar wani abu.

“Daga yau sunanka Zill”

Ta fada da yarenta sannan ta mike tsaye ta nufi hanyar Kitchen. Tana bada baya Maleek ya saukowa daga stairs din da yake tsaye ya nemi guri ya zauna da mamakin yaren da ya ji a bakin Waira.

Ita kan tana leka Kitchen din ta ga Hanne da Ummi a ciki sai ta ja ta tsaya ba tace komai ba.

“Me kike so Waira?”

“Barta ta dauki abun da take so, it's high time ace komai sai an yi mata, ita ma ya kamata ta fara mu'amalantarmu kar mar yan'uwanta”

Ummi ta fada tana juyowa ta kalleta, sai Waira ta lake kafada tana son yi kukan shagwaba.

“Waya baki zomo?”

Ummi na tambaya sai dariya ta biyo bayan kukan da Waira take son yi.

“Teacher....”

Ta amsa tana shafa shi.

“Ke kika ce masa kina so?”

Ta girgiza kai.

“No amman tana so”

“Ina so”

Ummi ta gyara mata.

“Ina so”

Ta sake fada.

“Ummin za ci abinci”

“To zo ki daukar masa”

Ta shiga cikin kitchen din ta nufi gurin da ake aje kayan marmari ta dauki kwatankwacin abin da ta san tana ci ta saka a plate. Hanne ta kalleta tana gyara tumatur ta ce.

“Zomo ya fi son giďa da salat ko karasss”

Waira ta kalli Ummi.

“Ummin zaki siya Karass, gida salak”

“Muna da karas a fridge ai sai dai a nemo giďa da salat, Hanne duba mana Fridge akwai karass ki dauko mata”

Hanne ta nufi inda Ummi ta fada ta bude ta dauko ledar karass biyu, domin Ummi tana sakawa a kullashi a leda kamar na siyarwa aje idan an antashi amfani sai dai a dauko kawai. Waira ta karba ta dora sannan ta fito falon hannunta rike da plate daya dayan kuma rike da zomo, wayo idonta ya fara yi tana kallon inda zata aje zomon be gudu ba, duk abun da take Maleek be kalli inda take ba. Takowa ta yi a hankali sautinsa ganin shi kadai ne a falon, kusan lokaci daya aka cire masa tsoronsa daman ta rage tsoronsa domin ya dan canja ba kamar da ba, dazun ma saboda ta ganshi da bulala ne ya saka ta tsorata.
Ta nufe shi ta aje plate din kasa ta kama zomon da hannu biyu ta dora masa saman jiki ba tare da tambayarsa zai rike mata ko akasin haka ba, da sauri ya dago yana kallonta irin lafiya kike?

“Kar ya gudu rike sosai da kyau”

Ganin zomon zai sauka jikinsa ya saka yayi saurin rikewa kamar yadda ta bukata.

“Good”

Ta masa thumb up, bata san baya son mace ta taba jikinsa ko ta rabe shi ba, domin bata taba rumgumarsa ko taba shi ta ga abun da yake damunsa ba, a iya tunaninta bashi da halin kirki ne a farkon zuwanta gidan, daga baya kuma ta ya sauko har yakan zauna ayi hira da shi sai ta fahimci ya jefar da wacan halin nasa ne marar kyau, yanzu ya shirya mu'amala da kowa.
Bata tare da tunanin komai ba ta juya ta koma kitchen ta dauko wuka da wani babban tray ta dawo inda yake zaune rike da zomon ta zauna a kasa ta fara yanka karass din tana yanka apple, shi dai kallonta kawai yake, he's feel something different about her, lokuta da dama tana masa abun da baya iya musa mata ko yi mata magana, not like other girls da zai iya kashewa ma idan suka masa haka, tun bayan marin da ya taba mata a karon farko da taba jikinsa be sake sha'awar kai hannunsa a jikinta da sunan duka ko hukuncin ba, a wacan karon ma da ta rika shi ya ji wani yanayi na dabam ba zai iya bayyana yadda yake ba, ba jindadi ba ne kuma ba na rashin dadin ba, wani abu ne da be taba jin irinsa ba a rayuwarsa yana ďaya daga cikin dalilin da ya haddasa masa daukewar numfashi na wucin gadi, wata kila saboda mace bata taba rumgumarsa ba ne, balle ya san ya dumin jikin mace yake idan ya gwaraya da na namiji duk da kasancewar a fusace ta hau stairs din a wacan lokacin bacin ran da be san na minene ba.

There is something special about her, her unique skin colar da gashinta da ya banbanta na kannensa, the way she talk idan ta kama dole iya zaman da ta yi a gidan na shekara daya ua fahimci tana da kiyaye doka, domin duk wani abun da ta san za a mata fada idan ta aikata tana kokarin kiyayewa musamman a abun da ya shafe shi, bata cika magana ba hakan na matukar burgeshi da ita domin baya son yawan surutu tana da natsuwar da idan ba a kusa da Ummi ta zauna ba zata nemi bayan kujera ta boya. Yana fara kallon kyakkyawar hallitar da Allah yayi a fuskarta na dagon hanci da blue eyes ga karamin pink lips sai zuciyarsa ta buga da mugun karfi kamar zata fisgo ta fado kasa. This is first time da yake kallonta da wani irin kallo da be taba yi ma ya mace ba, kowane motsin da hannunta yake da na abun da take yankawa har zuwa zaman da ta yi da kuma daukar abun da ta yanka ta ci, even taunawar da take kallon yadda bakinta yake motsi yake.

“Waira...”

Ummi wanda ta fito daga kitchen ta yi tsaye cak tana kallon ikon Allah. Maleek da Waira suka kalli inda take, Maleek mamakin tsayuwarta a gurin yake ya manta da abun da yayi a yau sabon abu ne da be taba yi ba, Waira kuma jiran take ta ji abun da Ummi zata fada bayan kiran sunanta da ta yi. Ummi ta karaso gurin ta nuna zomon dake hannun Maleek, sai Maleek ya kalli zomon.

“Oh ta ba ni rikonsa ne waya taba zomo?”

“Kuma ka rika?”

Ta kalli Waira ya kalli zomon ya daga kafadunsa he can't tell why ya rike mata zomon.

“Ummin ai baya ciwo”

So take tace cizo. Ummi ta yi murmushi dake tare da hawaye daman kukanta a kusa yake.

“Wow...”

Mikewa yayi tsaye ya taku daya ya kara matasawa inda Waira take zaune tana facing dinsa, ya dora mata zomon saman jiki ya kabe jikinsa ya nufi hnayar fita falon. Ummi ta duka a gurin tana kallon Waira.

“You're so special Waira, zuwanki gidan nan ya taimaka min sosai kin canja rayuwar ďana, sanadinki na fahimci abun da ban fahimta ba akan Maleek, komai yana da sanadi, ke ce sanadin canjawa Maleek”

Bata kula da zancen da Ummi take ba saboda hankalinta yana kan sabon abokinta.

“Ummin ki rike Zilll zan yanka abinci”

“Ki bashi wanda kika yanka idan na dawo sai na rike miki, zan duba bangaren Abiey ne”

“Tohm okay”

Ta amsa har sau biyu sannan ta shiga bashi abincin. Ummi ta ja kumatunta tana kara jin kaunarta ta mike tsaye tana murmushi ta nufi hanyar da zata sadata da bangaren Abiey. Tana tafe tana tunanin abubuwa biyu da suka zo mata a lokaci daya, wato ganin Ameer da kuma abun da Maleek yayi a yau, da ane ko taba zomon ba zai yi ba saboda Waira ta taba shi, amman a yau wai shi ne ya rikewa Waira zomo ta zauna a kusa da shi tana kusantarshi tana yanka abu, kuma idonsa na kanta.

“Kamar yadda Zahra ta wanke shawara na yanke shawarar zan aurar da su duka a watan da zai kama, idan basa da wadanda suke so, akwai yayan yan'uwa da abokai za a hada su”

Shi ne abun da Ummi ta ji daga bakin Abiey kamin ta tura kofar falonsa ta shiga, Dr Zainab ta dago tana kallon Ummi da tausayi a fuskarta har tana zubar da hawaye.

“Zahra kin ga da inda yayi ikonsa? Ashe haka abu ya kasance, wani hukunci sai Ubangiji”

Ummi ta nemi guri ta zauna tana kallon Abiey.

“Ina ganin zamu daga musu kafa zuwa wani lokacin da Nimra zata samu natsuwa, ba mu sani ba ko Namra ma bata da wanda take so kamin lokacin na san ta samu idan kuma akwai sai ya fito, ita kuma Nimra zata samu sakewar zuciya da natsuwa kamin lokaci, domin ba abu ne mai sauki ka rabaka da wani kuma a aura maka wanda baka so ba”

“Ba zan daga musu kafa ba, daman ai sun kai munzalin aure, duk su fito da mazaje ayi musu aure”

“Amman dole a fahimtar da ita dalilin da ya saka ba za a barta ta auri Ameer ba?”

“Ta ina kenan? Shiyasa nake na ce da laifinki a lamarin nan, idan ba haka ba ta ina za a ce Nimra ta kulla alakar soyayya da wani har ta kai ga haka baki sani ba?”

“Saboda ba ni kadai Allah ya bawa ikon kula da ita ba, ni da ita duk a karkashin kiwonka muke Abiey”

Ummi ta amsa masa a gautsine.

“Abun da kike kokarin ki aikata na fahimtar da Nimra ba ni kadai zai shafa ba, ke da Ameer din za ku fi kowa cutuwa saboda rayuwarsa ce zaki rusa, ki haddasa masa bakinciki da ke kanki kuma ki butulcewa wanda yake dawainiya da shi tun yana karami har ya girma”

“Ban ce dole sai ta hanyar fada mata ina da alaka da Ameer ne kadai za a fahimtarda ita ba, amman kai me kake tsoro ne Abiey? Ban ce ka dauki dawainiyarsa ba ban bukaci komai daga gareka ba ni dai kawai ina son ďana a kusa da ni....!”

“That's it, daman na sani ai, amman babu yadda ban yi da ke ba a wacan lokacin akan ki aje yaron nan a hannunki kika ki, sai yanzu yaro ya girma yana rayuwarsa dabam zaki ce ki rusa rayuwarsa kuma ki rusa rayuwar mutanen da suke rike shi a matsayin ďa? Damuwata ba akan Ameer ne kawai ba har da matsalar da zaki jefa kanki a ciki ina jin tausayinki Zahra da abun da zai biyo baya”

Dr Zainab ta kalli Abiey ta kalli Zahra ta dafe kanta.

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, yau Abiey da Zahra ne suke sa'insa? Abun da ban taba gani ba? Subhanallahi wannan abun yayi muni, Zahra ki yi shiru dan Allah karki sake magana”

“Har zuwa yaushe zan yi ta yin shiru Aunty Zainab? Shekara nawa a tare da Abiey? Ina da mafarkai da buri amman na rufe su saboda na samu zaman lafiya da mijina, shim ba ku taba tunanin kewa da kaunar uwa ga ďanta ba? Kai da ya aikatawa yarka haka ka ji zafi balle ni da ya kwanta a cikina wata tara da kwanaki na rike ka shi a hannuna na shayar da shi? Ko ka so Ameer ko karka so shi idan aka tsaga jinin Ameer sai an ga nawa a ciki”

Abiey ya girgiza kai yana murmushi takaici.

“Ba zaki gane ba ne Zahra, yaron da kike ta kokarin ki dawo da shi kusa da ke, ba shi da kirki ba ta inda zai girmamamu ko ya tsaya ya fahimce, ina gudun kar bakincikin ya zama mana biyu, domin ba ke kadai zai shafa ba har da ni, duk abun da ya same ki a tare za mu raba either na dadi ne ko akasin haka, sannan yanzu ba abun kunya ba ne ki zaunar da shi ki fada masa yadda aka yi kika rabu da shi? Bayan kin katse masa jindadin da yake a can?”

Ummi ta mike tsaye.

“Ba abun kunya ba ne, kuskuren da na aikata nake kokarin na gyara, amman kai abun kunya ne a gareka yanyanka su ji cewar ka ki ka taimaka min a lokacin da naje neman taimakonka, da ban aikata abun da zan kwanta a gado ya hana ni bachi ba...!”

Abiey ya hade fuska kamar be taba dariya ba, Dr Zainab ta yi saurin runtse ido tana girgiza kai.




WAIRA POV.

A cikin abubuwan da ta yanka ta bawa zomon karas ne kawai ya ci, sauran idan ta ba shi baya karba tana ganin haka ta mike tsaye tana shafa shi, can kuma ta dorashi saman kanta jin sonsa take kamar ranta, kawo mata zomon da malamin yayi ya tuna da yawa daga rayuwarta na baya, hannu ta saka ta cire ribon din dake kanta ta birjita gashin kanta ta dora zoman a saman kanta tana dariya, sai ta fara zagaya falon tana tafiya, har ta isa gurin kofa ta bude ta fito Maleek dake tsaye jingine da kofar ya juyo ya kalli zomon dake saman kanta yana mamakin yadda take rikonsa ko tsoro bata ji.

“Waira zata tafi daji”

Kallonta yake without asking ina ne dajin? Fita zata yi a gidan gaba daya or me take nufi? Bata damu da saka talkami ba ta nufi entrance din ta fara sauka, idonsa ya koma gurin kafafuwanta karamin guddugenta da take takawa tana sauka gurin gwanin sha'awar kafafuwanta ma sun fito sala sala kamar tsokar kaza, kallonta kawai yake har ta sauka ta nufi Garden a nan ya gane Garden take nufi da daji, samun kansa yayi ta saka wayar aljihu ya sauka gurin a hankali ya bi bayanta. Ko da ya shiga gurin har ta kusan raye icen kwakwa dake gurin, kansa ya daga yana mamakin yadda take iya hawan ice ba tare da taka komai ba, sai kafafuwanta da take tsalle da su da hannayenta da ta saka tana rike icen. Abun da ya fara zuwa masa a rai is saboda icen be gama girma ba ne saboda haka ne ba mata wuyar hawa ba, be gama raba dayan biyu ba ta haye sama riko dayan dake kusa da shi ta dira akai, can kuma ta samu sa'ar mika hannu ta riko icen mangoro ta koma kansa, yana tsaye a gurin kusan sai da ta hau duk wani icen dake kusa da kusa da juna. Masu yayan itatuwa ta tsinko ta jefo kasa sannan ta biyo ta sauko ta saka hannu ta dauka ta fara ci, sai da yayi kamar ya ce mata ta wanka kamin ta ci sai kuma wata zuciyar tace ina ruwanka? Cikinka ko nata? Yana kallonta har ta gama ci sannan ta nufi fanfon dake gurin ta kunan ta wanke hannunta ta tara hannayenta ta sha ruwan sai da ta koshi, kana ta nufi gurin da ta rufe zomon ta dauko tana masa magana da yarenta, gaba daya hankalinta be kai kan Maleek dake tsaye can gurin kofar Garden din yana kallonta ba domin ba a gurinsa hankalin nata yake ba. Ta tako ta fito cikin itatuwan ta nufo kofar fita a nanta tsaya tana kallon Maleek da tunanin ko ya ganta lokacin da ta hau itatuwan, dan tsoro da fargabar kar yayi mata fada ko ya fadawa Ummi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login