Showing 225001 words to 228000 words out of 281271 words

Chapter 76 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1208

ta dauko ta mika masa.

“Ameer ya tsaya min har safiya”

Be ce mata komai ba ya fice. Sai ten na safe suka gama duk wani shiri na su, a nan hankalin Nuwaira ya kara tashi sanin ta kusa rabuwa da su Ameer da Maleek ko da yake Ameer yayi mata bankwana tun a shekaranjiya jiya kuma ta yi bankwana da Shuraim. Ba ma kamar lokacin da wanda ya san hanyar garin ya iso tare da karin wasu police biyu da za su raka su garin, suka kama hanya suna cikin motar da suka shigo ita da Ameer police din biyu dake cikin shiga ta farin kaya suna a motar Maleek biyun da za su kara musu rakiya suna sanye da uniform su kuma suna a cikin wata motar ta dabam tare da wani dan kusa da garin wanda zai nuna musu garin amman ba zai shiga ciki ba.
Hanyar kawai Nuwaira take kallo bata gane komai ba har sai da suka isa bakin kofar garin sannan ta gane garinsu, domin bata taba fita garin ba, ko a lokacin da ta gudu ba ta hanyar gari ta fita ba. Sai dai abun da ya bata mamakin ganin Eid tare da wata tawaga ta mutanen da ta sani da kuma wadanda bata sani ba tsaye a bakin kofar garin suna jiran isowarta. Dukannin mutanen suna sanye da tufafin garinsu, mazan na sanye da walki matan kuma na sanye da rigar saki wasu kuma suna sanye da warkin skirt da rifar ganye kamar yadda suke yi, wasu kuma riga da skirt din suka na fatu ne. Idonta ya cika da hawaye now she know what she missed ta fita motar zata tafi gurinsu Maleek ya dakatar da ita.

“Ya aka yi suka san zaki zo?”

“Suna da tsafin da za su iya kirana na zo, kamar yadda suka yi yanzu, kuma suna da kalar tsafin da za su iya sanin halin da nake ciki”

Ta amsa masa.

“Littafin da Ameer ya ce a baki, akwai addu'o'in safe da maraice a ciki, idan kina yi tsafinsu ba zai yi tasiri akanki ba, kuma ba Ameer ya ce kar mu barki ki tafi ke kadai zamu shiga cikin garin mu bawa Sarkin hakuri sannan mu fito”

Tana kokarin bude baki ta fada ma Maleek abu ne da ba zai taba yiyuwa ba, Eid ya nufo inda suke yana mata magana da yarensu yana nuna Maleek har wani cika yake kamar zaki, Maleek ya tsorata da ganin Eid not because of be yi addu'a ba no sai dai tsoro wani abu ne da Allah yake sakawa a zuciyar bayinsa, and yayi arba da abun da be saba gani ba, wato ganin mutane a cikin shigar da ba irin tasa ba, ga kuma wanda ya nufo inda suke yana magana da yaren da ba zai iya jin komai ba.

“Ki fada masa shi ko tawagar da suke tare da ita, ba zai taba shiga cikin garinmu ba, rikon da suka yi miki mun gode za su iya komawa daga nan, addini da al'adar da suka ara miki kika zo mana da ita, ki ba abar su su koma da ita, tufafi da duk wani abub da kika san ba na garin nan ba ne karki shiga da shi”

“Zan fada mata, daman tun can na fada masa ba za su iya shiga cikin garin ba, amman addini da tufafi wani abu ne na dabam da ya shafi rayuwata babu ruwanka da wannan”

Ta bashi amsa da yaren. Ya kara takowa ya kai hannu ya taba fuskarta yana mata magana a hankali da yarensu.

“Ikke tek tek far der tik Waira”
_aki watsar da komai waira_

“Ban da addinin nan, karka takura sai a aje Eid ba zan iya ba, na gamsu da wani abun da baka taba ji ba da na tabbatar da a yanzu kai ma ka aje wannan addinin ka dauki wanda na zo da shi”

Ya kama hannayenta ya rike.

“Baki san iya lokacin da ya dauke ni ina bauta ina azabtuwa saboda neman Sarki ya yafe miki ba Waira, ba na kisan da ake zargin kin yi ba na guduwar da kika yi, wannan kisan ni na aikata kuma na fadawa Sarki haka, amman dauko wani addini ki shigo da shi wannan abu ne da ni kaina ba zan yarda da shi ba balle kuma sarki da jama'ar gari, bayan kuma kin sa abun da yake jiranki, shiyasa na yi ta nanata miki cewar karki jefar da addininki karki dauki addinin wasu”

“Ta yaya yaushe”

Ya kai hannunsa ya bugi goshinta da karfi har sai da Police din suka matso da zimmar rike su Maleek kuma ya kai hannu da sauri ya buge hannunta. Sai ga jini yana fita ta hancinta kamar rufe ido a bude haka ta tuna a wacan ranar da Ummi ta fada mata Malaminta yana son ganinta duk wani abun da ya faru a ranar a take a gurin ta tuna shi. Eid ya fisge hanunsa ya yarfar yana watsawa Maleek wani mugun kallo ya kalli Police din dake cikin uniform da kuma masu sanye da kayan gida, shi dai wanda yayi jagorancin zuwa garin yana can labe gurin mota yaki ma fitowa dan kar a ganshi.

“Kar wanda ya taba ni a cikinku, rakiya kuka yi kun kawo ta mun gode zaku iya tafiyarku”

Da mugun mamaki suke kallonsa jin yayi musu magana da hausa, bayan kuma tun zuwansu gurin da yare yake magana da Nuwaira.

“Ina malamin da yake koya min karatu Eid?”

“Ni nake koya miki karatu ba shi ba, tun a ranar da aka daukeshi yake na fanshe shi, zomon da kika baro a can ni ne na baki ba shi ba, shiyasa ban taba bari kin taba ni ba, domin na san zaki iya ganewa, babu wani Malami Waira sai ni na yi siffar wannan mutumen ne saboda na samu shiga, ina bibiyarki da duk wani hali da kike ciki zan iya yin komai shiyasa na kashe tun ranar farko da aka kawo shi na yi siffarsa, a duk tsawon lokacin babu kalar azabar da ba gani ba Waira saboda ke”

Ya juya mata bayansa ta yi arba da tambunan dake bayan farar fatarsa, sai ta dauke ido hawaye na sauko mata ta kalli Maleek da yaren hausa ta ce.

“Ya Maleek za ku iya tafiya ni kun kawo ni gida na gode”

“Me yake fada? Ba zamu tafi mu barki a nan ba, gashi tun yanzu ya fara tsorata ya fitar miki da jini a hanci, dole mu shiga ciki mu yi magana da Sarkin”

“Zancen shiga cikin garin ba zai taba tabbatuwa ba, saboda haka mu yi hakuri mu yi bankwana a nan”

“Idan ba za su yarda mu shiga duka ba, to ni zan shiga, ba zan barki ki tafi ke kadai ba, Ameer ma ya roki na yi masa haka ni kaina hankali ba zai kwanta ba sai na tabbatar kina cikin koshin lafiya”

“Babu abun da zai same ta, a can inda ta tafi wani abun be same ta ba balle a garinsu? Ina tare da ita babu wani damuwa zaku iya tafiya, shiga a cikin garin nan kamar kiran mutuwa ne idan kuma kin shirya sai ku shiga mu gani”

Eid ya fada musu da yaren da za su fi fahimta, wato yaren Hausa. Police din suka fara kallon juna, Maleek ya mika hannunsa for the first time ya rike hannun Nuwaira.

“Idan ka ga na saki hannunta, to na yi magana da Sarkinku ne kuma na tabbatar zata rayu cikin aminci ne”

Eid ya nuna Maleek da tsaya kamar zai tsokane masa ido.
[8/9, 8:10 PM] My S Line: 74

“Ki fada masa ya cire kansa daga lamarinki in ba haka ba zai yi nadama”

Maleek yake nunawa amman da Nuwaira yake magana da yaren garinsu.

“Ba zaka cutar da shi ba Eid kai dan'uwa ne a gurina, mai matukar son abun da nake kauna, mai son abun da nake so, mai gudun bacin raina da kukana? Meya same ka ka canja? Kalamanka da kamanin da nake gani a fuskarka ba su ne na Eid da na tafi na bari ba, wannan mutumen shi da iyayensa tarbe ni, sun saka hannu biyu sun rumgume ni, ba dan sun san daga inda na fito ba sai dan karamci da sanin ya kamata irin na su, sun nuna min kauna, a gurinsu na san abun da ake kira da tsabta da kauna da soyayya, a gurinsu na san me iyali yake nufi, a lokacin da zuwa gida ya kama ni, suka sako ni a mota suka rokoni har kofar garinmu akan me kake tunanin idan ka nuna masa tsaya zan ji dadi? A wane hali zan bari ka cutar da shi? Da wace Hujja zaka zabe ni ka bar shi?”

Eid ya dauke hannunsa yana kallon Nuwaira dake magana taba zubar da hawaye. Ta sauke kanta kasa ta kalli hannun Maleek dake rike da nata, sannan ta kalleshi.

“A nan garinmu ne Ya Maleek zan rayu cikin aminci da yardar Ubangijin Kaaba”

“Hakan ba zai gamsar da ni ba Nuwaira, sai na ga halin da zaki kasance kuma sai na yi magana da Sarkinku”

Cikin wata kalar murya mai kamar ta zaki Eid ya zabuwa Maleek har jijiyoyin dake jikinsa suna bayyana.

“Waye kai da zaka ce zaka ga sarki? Mutanen dake cikin fadar sarkin mu ba baka isa ka gani ba balle Sarkin da kansa, duk wani abun da ka yi ma Nuwaira kai da iyalinka mun gode zaka iya tafiya”

Eid ya hade hannun biyu yayi masa godiya har da sirinawa sannan ya nuna masa hanyar da suka fito.

“Ban taba tirjiya ko musayar yawu da kafewa akan abu daya ba sai yau, idan da tsafi kuke taka ni ina takama da wanda yake da ikon akan komai da kowa, and mark my words sai na yi magana da Sarkinku zan tafi sai na tabbatar Nuwaira tana cikin aminci, idan har zan iya barin wani abu ya same ni to zan iya barin Nuwaira ta cutu kenan”

Sai a lokacin yan rakisarsa suka saka baki domin sun lura a yanzu ya wuce gona da iri, su dai rakiya suka zo kuma sun kawo yarinyar a gidansu akan wace hujja zai nace dole sai ya shiga cikin garin.

“Am Malam Maleek ko? Akwai maganar da nake son yi da kai dan Allah dan zo ka ji”

Maleek baya son disga mutumen a cikin mutane hakan ya saka binsa gefe yana janye da hannun Nuwaira. A lokacin da suka koma gefen sai mutumen ya kasa cewa komai saboda ganin yana rike da hannun Nuwaira.

“Da ka dan sake ta sai mu yi magana”

Maleek ya kalleta ji yake kamar idan ya sake ta Eid ko wani daga cikin mutanen da suke tsaye bakin kofar garin zai iya yin tsafi ko kuma su ja Nuwaira da karfi su tafi da ita su bar shi a gurin.

“Zaka iya fadin maganarka”

Mutumen ta sake kallon Nuwaira sannan ya kalli Maleek.

“Wato ni abun da nake gani zai fi zame mana masalaha shi ne ka kyale yarinyar nan ta tafi gurin danginta, bukata dai a kawota gurinsu kuma gashi an yi, karka daukarka kanka abun da ba zaka iya ba, ni a yadda na fahimta shi wannan dan'uwanta ne ko kuma da dukan alamu ba shi da kyau hali”

“Haka ne office zaku iya tafiyarku daga nan, daman an dauko ku ne saboda ku rakomu ku tabbatar mun isa lafiya, ina ganin aikinku ya kare daga nan za su iya tafiya”

Office ya tsaya kallon Maleek baki sake da mamaki.

“Ranka ya dade ka taba jin labarin mutanen nan kuwa? Wallahi ba su ragawa kowa kuma dokokinsu ne a haka ya kamata mu tsaya bakin iyakarmu kar mu wuce gona da iri, wannan abun da kake kokarin yi zaka jefa kanka a matsala ne, ba film muke ba, ko a film indiawa suke wannan wautar ba hausawa ba”

“Office karka bata min rai, dan Allah ka dauki mutanenka ku tafi, ba wani abu nake kokarin nunawa na jarumta ba, na fada cewar ba zan tafi ba sai na yi magana da sarkinsu kuma sai na tabbatar Nuwaira zata rayu cikin aminci that's it”

Cikin kakkausan lafazi Maleek yake fadar hakan still yana rike da hannun Nuwaira. Ganin da gaske Maleek yake ya saka office nufar yan'uwansa ya ja su gefe domin tattaunawa. Nuwaira ta kalli Maleek dake rike da hannunta gam da dukanin karfinsa ta ce.

“Ya Maleek zan zauna lafiya na maka alkawari babu abun da zai same ni, please ka bi abun da suka fada maka ka tafi gida, idan Ummi ko Abiey suka ji abun da kake kokarin yi ba za su jidadi ba”

“Babu ruwanki a nan karki sake magana”

Ya fisgi hannunta har tana lilo ya nufi gurin motarsa ya bude ya sakata ciki ya rufe motar. Ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya yi dialing number Abiey a take kiran ya yanke yana muna masa no network, su ma police din kokarin kira suke network dinsu ya yanke, hakan kuma ba karamin daga musu hankali yayi ba gashi wanda yayi jagorancin zuwa gurin ya nuna musu hanya ya kara fada musu yadda garin da jama'ar garin suke. Gashi kuma bakin shiga garin ma kadai babu network ina ga ciki kuma? A haka kuma Maleek yake son su yi risking rayuwarsu saboda rai daya, ran da za su iya kashe su ita ba su kasheta ba, waya sani ma ko plan ne. Dukansu zuciyarsu bata natsu da biyewa Maleek su shiga cikin garin ba, saboda haka suka yanke shawarar juyawa su koma tare da Maleek din da Nuwaira har sai an sake shawara, domin ba za su bar Maleek ya shiga garin ba, ba kuma zai yiyu su tafi su bar shi ba, kamar yadda ba za su yarda su shiga cikin garin ba.

“Ranka ya dade, ina tunanin abun da ya fi, mu tattara gaba dayanmu mu koma gida, albashi idan aka yanke shawarar yadda ya kamata ayi sai a aiwatar daga baya, idan ma su za su zo su dauke ko kuma mu sake kawota ka ga dai sai mu san irin shirin da zamu yi”

Maleek ya dan yi jimmm alamar tunani sannan ya juya ya kalli Nuwaira dake cikin motar tana kallonsa.

“Hakan yayi bari na yi magana da ita”

Ya zagaya ya bude motar ya shiga sai ya bar kofar a bude.

“Mun yanke shawarar zamu koma tare da ke, daga baya sai mu yi tunanin abun da ya dace mu yi”

“Ba zan iya komawa ba Ya Maleek kuma idan ka ce zaka tafi da ni Eid ba zai bari ba, zai iya cutar da kai dan Allah ka tafi”

“Ki daina jin tsoro babu abun da zai iya min, ina da addu'a akwai tsari a tare da ni ke ma ba zai iya cutar da ke ba balle kuma ni, ki cire komai a ranki”

“Ba zan iya komawa ba, ina jin wani abu a cikin jikina ba zan iya komawa ba”

“Zai daina da zarar mun bar nan na miki alkawari kin ji?”

Ta yi shiru sai wani abu take kamar wadda bata cikin hayyacinta.

“Nuwaira kalleni”

Ta tsayar kanta a saitin fuskarsa kwayar idonta ta sauka cikin ta shi, wani irin natsuwa da kwarjinin kasa yi masa musu suka cika idonta ta samu kanta da yarda da kalamansa ta kasa sake musu masa.

“Mu tafi?”

Ta daga masa kai.

“Good”

Ya juya ya fita yayi magana da jami'an tsaron ya fada musu ta aminta. Sai duk suka shiga motocinsu ba tare da sun ce komai ba Maleek ya shiga motar da suka zo ya saka key a gurin tashi motar tace ku tuka ni ku gani, ko wace mota ta tashi ban da ta Maleek su kansu sai da mamaki ya kamasu, kuma suka kara tsorata da musamman da suka hango Eid yana kara doso inda suke, biyu daga cikin police din suka fita suna nuna Eid da pistol dinsu.

“Karka matso nan”

“Ba ku san taba ba, bani da matsala da ku Waira zan dauka”

Be fasa nufar inda Maleek yake ba, su kuma suka kasa harbinsa domin ba su da hujjar haka, Maleek kuma sai buga mota yake taki tashi Nuwaira na ganin hakan ta bude motar ta fito, ganin hakan ya saka Maleek bude motar shi ma ya fito gabansa faduwa yake amman ya dake saboda ba ya son Nuwaira ta cuto.

“Kin dawo gida, idan zai saka ki a mota dubu ba zata tashi ba, Sarki ne yake kira dole ne kuma amsa kiran, kai na idan ka shiryawa mutuwa ka taho mu tafi”

“Idan har zan tafi ba tare da ita ba, ba zan taba samun kaina cikin aminci ba, zan yi tunanin wane hali take ciki, kariyar da muka mata alkawari ba mu cika ba, saboda haka ba zan iya tafiya ya bar yarinyar nan ba”

Eid ya juya baya ya nuna ma Maleek kofar. Office yayi saurin karasowa kusa da inda suke

“Maleek karka yarda ka shiga baka san manufar ba”

“Ku dai ku tafi babu mai cutar da wani sai Allah zan fito lafiya na muku alkawari”

“Maleek...”

Dayan office ya dakatar mai kokarin hana Maleek.

“Ranka ya dade ra'ayinsa ya bi, mun dai mun yi iya namu idan ya ji zai iya shiga ciki sai masa addu'ar fitowa lafiya”

Duk yadda suka so su yi convince din Maleek kar ya bi Nuwaira be sauraresu ba, not just because of Nuwairar kanta, har dan yana son na nunawa Eid ba zai iya masa komai ba sai abun da Allah ya hukunta masa. Su dai kam ba za su iya kasada ba dan haka suka shiga motar su suka masa sallama suka tafi aka bar shi a gurin daga shi sai Nuwaira da Eid da kuma mutanen da ke bakin kofar garin suna jiran isowar Nuwaira.

“Yanzu zamu iya shiga da motar?”

Eid ya watsa ma Maleek wani mugun kallo ya kai hannunsa ya rika hannun Nuwaira sai ta fisge hannunta.

“Karka sake taba ni, ni a yanzu musulma ce haramun wanda ba dan'uwana ko uba ko mijina ya rike ni, na canja addini a yanzu ba addinina daya da kai ba, kamar yadda ba zuciyarmu ta banbanta”

Daga Maleek har Eid din kallonta suke babu wanda ya ce mat uffan. Eid ya juya ya fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login