Showing 66001 words to 69000 words out of 281271 words

Chapter 23 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1207

fice, warware takardar Waira ta yi ta duba tana ta kallon rubutun kamar ace ta iya karanta ko kuma akwai wanda ya iya a kusa da ita ya fada mata abun da ke cikin takardar. Jin motsin bude dakin ya saka ta yi saurin boye takardar a bayanta, a zarane ta matsa baya ta fashe da kuka, kallon Maleek ta yi ke ma Mahmood domin bata gama tantance fuskar wanda ya mareta a dazun din ba, ita dai ta ji saukar mari a kokarinta na neman ceto kuma wanda ya mareta yayi yanayi da wannan. A take ta fashe da kuka jikinta na rawa sosai hakan ya saka Mahmood be karaso kusa da ita ba ya tsaya daga bakin kofar ya juya ya fadi cewar

“Tsorona take fa, wata kila ta dauka Maleek ne”

Ya juyo yana kallonta yayi mata murmushi, gaba daya sai ta kara rikicewa ta boye fuskarta, har sai da ta ji muryar Ummi sannan ta dago, Ummi na kai hannu ta tabata sai ta mike tsaye da sauri ta rumgume Ummi jikinta na bari sosai.

“Mahmood fita tsoronka take”

Mahmood ya juya ya fita, sai Ummi ta zaunar da ita a kasa ganin ta fi son zaman a nan ita ma ta zauna.

“Da a ce a fito dake falo ki zauna tare da mu ne, baki so?”

Bakin Ummi kawai take kallo tana son fahimtar abun da take fada mata, na kurame Ummi ta yi mata alamar mari ta a fuska ta sake yi mata alamar ba za a sake ba tana mata murmushi sannan ta kwantar da kanta a kafadarta ta dan kauce fuska saboda wari da bakin Waira yake.

“Gobe za a tafi dake asibiti a duba lafiyarki da hannunki, da kuma bakin nan da kika ji ciwo dazun, Allah yasa ki ba mu hadin kai”

Ummi ta fada, sai Waira ta lumshe ido ta ji wani yanayi da bata taba ji ba, domin ita ma bata san dadin uwa ba bata san dadin wani yayi mata haka ba, ita sam bata san dadin wani ya rabi jikinta ba sai Eid shi ma kuma iyakarsa rike hannunta ko daukarta idan ta kama, a rayu a inda take kwana ita kadai a dakin babu uwa ba uba babu yan'uwa sai beraye da zakaru...



NIMRA POV.

Tun da ta yi sallah Magariba bata fita dakinta ba har aka gama Isha'i sannan ta gabatar Sallah Isha'i ta yi shafa'i da wuturi, ta sauya tufafin jikinta zuwa na bachi, sannan ta fita dakin ta sauko downstairs, ta zuba abicin da ta san zata iya cinyewa ta dauki spoon da cup ta bar dinning.

“Daki zaki ci abinci?”

Namra ta tambaya ganin ta fara sabon halin da ba nata ba.

“Eh”

“Wai sai fushi kike da mu sai ka ce mu muka miki wani abu a gidan, ina ce Abiey ne kawai yake fushi da ke a gidan nan amman sai wani kebe kanki kike kamar kin ga makiyinki”

“Dazun saboda ni yarinyar nan da aka kawo ta rumgume Ya Maleek me kike tsammani idan yayi arba da fuskata”

Namra ta tashi zaune fa kyau tana kallon Nimra da matukar mamaki, domin bata nan komai ya wakana a gidan, tana gurin aiki daga gurin aiki kuma ta wuce gurin Gwaggonsu bata dawo ba sai da Isha'i.

“Ta rumgume shi fa kika ce? Kamar ya? Ita yarinyar ta san shi ne”

“No tsoro ta ji, na je ina nemanta ita kuma ta fito da gudu kamar mahaukaciya ta rumgume shi, kin ga marin da yayi mata sai da bakinta ya cika da jini”

“Yana ina shi?”

“Oho kila ya fita daga gidan”

“Yarinyar fa?”

“Tana dakin dake kusa na shi”

“Tab...”

Nimra ta haye sama da abincin ta shige daki ta rufe ta aje tuwon akan carpet tare da ruwa, sannan ta zauna ta fara ci, ta dan ci da yawa domin rabon da ta ci abinci mai yawa haka tun da aka fara tashin hankalin nan ita ma ta shiga a damuwa abincin ma ba ya mata dadi sai abu mai ruwa. Brush ta yi bayan ta gama ta dauke plate din ta dora akan karamin tebur din dake dakin, ta hau gado ta kunna data.
Misalin Sha daya na dare sakon Ameer ya shiga mata ta Instagram a take ta tashi zaune jiki na rawa ta fara amsa masa, a cikin kalaman da take aika masa har da wadanda take ganin be kamata ta tsaya tana masa magiya haka ba, amman ta kasa ganin illar hakan har sai bayan da ta riga da tura, tashi ta y zaune tana tunanin yadda zata yi ta bincike abun da yake cikin motar har ta sani idan akwai sarewar Ameer a ciki. Fitowa ta yi dakin ta nufo downstairs kamar zata sauko sai kuma ta fasa ganin Namra na zaune a falon a har lokacin sai ta nufi dakin Ummi, knocked ta fara yi sannan ta tura ta shiga babu kowa dakin, juyowa ta yi ta dawo ta nufi dakin Waira domin ta fi kyautata zaton Ummi tana can tare da ita, a nan ma sai da ta kwankwasa sannan ta tura ta shiga.

“Ummi kina nan har yanzu?”
.
Ta tambaya da mamaki, Ummi ta kalleta.

“Yarinyar nan bata son na daga da zarar na motsa sai ta tashi ta rike min hannu, wata kila tsoro take ji har yanzu ko kuma tana kewar mahaifiyarta ne”

“Ummi sai ki biye mata, ki zauna tare da ita har tsawon wannan lokacin”

Ta sakw fada yayin da ta karasa kusa da ita ta duka. Sai Ummi ta kai hannu ta shafa fuskar Nimra.

“Zan tashi, nima na jidadin zaman ne, ina ta jin kewarku kuma lokacin da kuke da kurciya kamar ita haka kuke yawan rabar jikina”

“Har yanzu ma ai ba mu daina ba, kuma ba za mu taba girma da hakan ba”

Ummi ta yi murmushi sannan ta cire hannun Waira a hankali ta aje kasa ta mike tsaye, da sanda suka fice daga dakin ita da Nimra saboda kar ta farka. A bakin kofar dakin Nimra ta fara yi Ummi tambayoyi.

“Ummi an bincike motar kuwa?”

“Ina tunanin police din sun yi bincike ai, ba su koma ba ma sai gobe za su kama hanya tun da sassafe”

“Kuma ba su ga komai a motar ba?”

“Da sun gani da sun fada ai, mi yasa kika tambaya?”

Ta dan hade yawu tana tunanin irin amsar da zata bawa Ummi.

“Akwai a motar wanda na siya few days before abun ya faru kuma akwai ATM dina da waya a motar ina tunanin ko Ameer ya bar su a ciki”

“Sarewa kuma? Ki yi me da sarewa ke ba namiji ba? Zan tambaya Abieyun ku na ji idan akwai a motar”

“Idan kuma babu Ummi ki karba min key din na duba da kaina”

“Okay”

Ya juya ta nufi hanyar dakinta, Ummi ta bita da ido tana karantarta, domin ta ninka a kiriniya lokacin da take da kurciya, tunanin Ummi dole sai dara nata saboda ita uwa ce kuma ta bata shekaru masu yawa, a take zuciyarta ta raya mata sarewar ba ta ta ba ce, sai dai bata nuna mata hakan ba kuma bata ce mata komai ba har ta shige dakinta. Ajiyar zuciya ta sauke ta taka zuwa kofar dakin Maleek ta tura ta shiga, hango shi kwance saman gado ya daga mata hankali cikin kulawa ta shiga dakin ta karasa har gurin gadonsa ta kai hannu ta bude blanket din da ya rufa da shi ta taba jikinsa ta jishi da zafi sosai kamar an kara a wuta.

“Subhanallahi”

Ya bude ido da sauri ya kalleta, sai yayi hanzarin tashi zaune yana kallon agogon bangon dake dakin, tun da ya kwanta bayan gama Sallah Magariba be sake farkawa sai a yanzu da hannu Ummi ta taba jikinsa.

“Baka da lafiya ne?”

Ummi ta tambaya, sai ya kai hannu ya taba jikinsa.

“Ba sosai ba”

Ya mike tsaye ya nufi bathroom, Ummi na zaune har yayi alwala ya fito ya nufi inda carpet yake shimfide ya tada ikama ya fara Sallah.



HUMAIRA POV.

Sai da ta taso daga makaranta sannan ta wuce gurin aikinta, daman ta kan yi hakan shiyasa ta fi kaunar duty dare, idan kuma har tana da duty rana kuma ga karatu wani lokacin suka yin canjen aiki ita da abokan aikinta, wani yayi amfani da lokacinta ita kuma idan ta dawo sai ta dauki lokacinsa, a haka dai take ta kai da kawo na ganin sun yi survive ita da iyayenta, ba abu ne mai sauki a gareta ta hada abu biyu a lokaci daya ba, kamar aikin Restaurant da kuma karatu da yake bukatar lokaci sosai, sai dai rashi da neman abun dogaro da kai ya saka a dole ta sabawa kanta da wannan wahalar har ya kan zama idan bata je aikin ba bata jindadi, kuma bata isa ta jefar da karatun da makomarta da na iyayenta yake ciki ba. Washe garin data dawo kowa sai tambayar ya fuskarta yake, wadanda suka samu labarin abun da ya faru daga baya kuma suka jajanta mata, ba sosai suke ake baki suna zaginsa ba, saboda akwai Security Camera tsoron suke kar su zure da yawa a duba Camera a gani su ja kansu matsala. Ita kanta da fargaba ta yi aikin na yau tana ta tsammanin ganin takardar kora daga mai gurin ko kuma ďansa dan gadara bata ga ko daya ba har ta gama duty ta direban gurin ya kaita gida.



©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: *W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*

23

Washe gari bayan gama Sallah Asuba Ummi ta shiga dakin Waira ta same ta zaune ta kasa ta takure guri daya.

“Kin farka? Ni ban san sunanki ba, ban kuma taba jin maganar ki ba, balle na fahimci yarenki ma”

Waira dai kallonta kawai har ta karaso kusa da ita ta zauna saman gado ta kama hannunta a hankali ta duba. Sannan ta rika ta ta mikar tsaye tana mata alama da ta tashi su shiga bandaki, bata yi musu ba, domin ita ma kanta fitsari ya cika mata mara kuma bata son shiga bandakin da take masa kallon ya fi dakinta ma ta yi fitsari, yadda kofar za ta yi kara idan aka tura ko rufe take tunani, Ummi ce ta bude mata ta shiga kamin Ummi ta yi mata alamar komai ta risina kasa ta juya baya ta saki fitsari a nan, ganin hakan ya saka Ummi ta yi saurin juyawa ta fice daga bandakin. Ba ta saba yin tsarki bayan fitsari ba hakan ya saka bata yi tsarki ba ta mike tsaye taja wandonta sama ta juyo ta fito. Duk yadda Ummi ta yi juyim duniya ta nuna mata yadda zata wanke baki sai ta ki idan ta mika mata brush ai ta yi irin yadda ta yi a gidansu Shuraim wato ta lashe man ta aje brush din, sai da Ummi ta kama fuskarta ta wanke a fanfo ta nuna mata ta yi alwala a nan kam ta girgiza kai domin ta fahimci ibada ce suke wacce ba irin tata ba, ta ga hakan tun a gurin Ameer da kuma Dr Shuraim.
  Ummi bata cilasta ta yin alwala ba, daman tana kallonta ta san ba addininsu daya ba, sai ta janyo hannunta ta fito da ita, bata tsaya da ita a dakin ba, ta fito da ita har waje saboda ta sha iska kuma ta dan sake jiki da su. Sakin baki ta yi ta daga kai tana kallon sama dakin tun da take a rayuwarta bata taba ganin gidan da ana gina aka kawata ginin da kyalen kyalen duniya ba irin wannan, bin Ummi kawai take a baya suna saukowa idonta na akan falon, ba ma kamar da idon nan nata ya sauka akan plasma dake kashe, bata san me ake da ashi ba, amman zata iya tuna ta ga irinsa a gidansu Dr Shuraim sai dai na su be kai wannan girma ba, gurin saka plasma da aka yi har wata wuta ke fita a gurin ga an dora kananan fulawoyi an masa decoration. Saman cushion Ummi ta zauna da ita sai ta ji kamar ta zauna a saman ruwa saboda sanyin ac da ya sauka akan kujerun ga laushin da suke da shi kamar kaďa, da sauri ta sauka ta zauna kasa.

“Zan je na shirya abun karyawa”

Ummi ta fada tana mata nuni da kitchen da kuma alamar abinci, ita dai bata ce komai ba sai kallon bakin Ummi dake motsi take, kamin ta bita da kallo har ta isa gurin tv ta kunna mata saboda ta dan sage kewa. Wani irin tsoro ne ya kama Waira jikinta ya fara rawa ganin mutane a ciki manya kamar za su fado suna magana, kusan a rayuwarta wannan ne karo na farko da ta ga mutane a guri mai girma haka, ita dai fuskarta kawai zata iya shaidar ta gani a cikin ruwa ko kuma tsafin da Eid yake mata ta kalli kanta idan ta yi kwalliya. Numfashi ta fara yi ta karfi tana fisga kamin ta saka hannunta ta rike kanta ta bude murya iya karfinta ta kwala wani uban kara, sai da Ummi ta duke a gurin dafe da kunne, Mahmood da Maleek suka fito daga dakunansu da sauri Namra ma ta fito da sauri, domin asuba ce komai tsit yake gidan kuma irin mai daukar magana ne, ita ma kuma ba daga baya ba gurin iya fasa kunne da tsuwa. Mahmood ya sauko da sauri ya isa gurin Plasma ya kashe domin ya fahimci shi take yi ma ihu, a maimakon ihunta ya ragu sai ya karu sakamakon ganin Maleek da ta yi tsaye bakin stairs yana kallonta, domin a yanzu ta gane shi ne ya mareta ganin fuskarsa babu annuri yana mata wani kallo mai kama da harara, sai ta nufi kofar kitchen domin ita kadai ce a bude a lokacin ita dai gurin tsira kawai take nema. A nan ma Mahmood be yi kasa a guiwa ba ya nufeta da sauri ya rikota ya juyo da ita, tsoron kar yayi mata irin abun da Maleek yayi mata tana ganin Mahmood ma namiji ne. Ummi ta karaso ya rumgume ta lokaci daya ta yi shiru kamar ba ita ce ke ihu ba.

“Malam Maleek kai fa take yi ma ihu can you please go back to your room?”

Ba tare da yace komai ba ya juya ya haye sama, Namra kuma ta karasa sauko tana fadin.

“Gaskiya ba zamu zauna da yarinyar a gidan nan ba, jin yadda take ihu tana mana hauka a gida tun da asuba”

“Bata saba ba ne shiyasa”

Mahmood ya amsa mata yana kallon Waira.

“Wane irin kauyenci ne wannan? Bata taba ganin plasma ba ko kuma iskancin ne kawai Nimra ta ja mana masifa”

“Ba fa bachi kike ba ihunta kuma ta yi ne saboda ta ga abun da bata saba da shi ba, ya kamata ki mata uzuri ba mu san duniyar data fito ba, so ki daina daga murya kina mata fada karki firgitata lafiya ma bata wadace ba, marin da Maleek yayi mata ma ban manta ba”

Da fada Ummi ta karashe maganar tana Namra dake kokarin sakewa domin har son ta yi ta kai hannu ta riko Waira. Ba dan ta ga bacin rai a fuskar Ummi ba da ba zata juya ta koma kai tsaye ba har sai ta yi ma Waira gargadin da ta yi niya. Ba dan ta so ba ta juya ta haye sama, aka bar Mahmood sai Ummi a falon. Daker Ummi ta dago kam Waira daga jikinta sai dai tana kallon Mahmood sai ta maida kan jikin Ummi ta boye fuskarta.

“Ya sunanta?”

“Ban sani ba, bata taba magana ba”

Mahmood ya mika hannunsa ya kama hannunta ta raba da jikin Ummi da karfi, sannan ya zaunar da ita akan kujera sai ta rufe ido ta sauka daga kan kujera, idonta a rufe.

“Don't hurt her please”

“Oh no Ummi sai ka ce baki san ni ba”

Ummi ta nufi kitchen so take ta shirya ma mijinta abincin safe kamin ya farka. Mahmood kuma ya nufi sama ya shiga dakinsa, sai a lokacin Waira ta samu damar bude idon sai ta nemi bayan kujera ta boya. Wannan karon ya sauko kadarsa da safa da kuma talkami hannunaa rike da littafi da biro, kitchen ya fara lekawa nemanta sannan ya fito ya fara bin bayan kujerun kamar ya san zata boya a nan, hangota da yayi ya saka shi komawa kitchen din ya dauko fruit a tray ya dawo gefen kujerar da take ya aje, plate din ya zauna yana fuskarta kofar fita falon, hannun kuma yana ta zane a jikin littafin daya fito da shi. Kamshin kayan marmari da ta ji ne ya saka ta rarrafa ta leko tana ganin da mutum a kujera sai ta koma baya ta boya, tana sauraren abun da zai biyo baya, jin shiru ya saka ta sake lekowa ta kalli Mahmood da gangan ya ki kallon gefenta har ya gama lekonsa ta koma, can kuma ta sake lekowa sai dai wannan karon da ta leko sai ta mika hannu ta dauko ayaba dake kan plate din ta koma da sauri ta boye a bayanta gabanta na faduwa tana sauraren abun da za'ayi mata, sai da ta sake lokowa ta ga be kula da abun da take ba sai ta sake dauke daya, ta sake boyewa tana saurare kamar dai dazun. Jin babu motsin kowa ya saka ta bude ayabar ta fara ci, duka biyun ta cinye sannan ta sake lekawa ta dauko pear ta boya ta cinye, ta sake komawa ta dauko kankana dayan bayan daya ta rika daukar abun da ke plate din har sai da ta dauke komai, Mahmood na kallonta sai dai be nuna mata ya gani din ba, har aat da ta gama daukewa sannan yayi murmushi ya aje mata takardar da ya zana tare da biron. Lekowa ta yi ta ganin farin abu sai ta yi saurin boya, har na tsawon lokaci sannan ta sake lekowa ta dauki takardar ta sake boyewa. Zane ne a jikin takardar na mutane biyu mace da namiji, an yi musu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login