Showing 45001 words to 48000 words out of 281271 words
Kubrah, itama bafulatana ce, komawa bayan Sa'ade Kubrah tai jikinta yana rawa, juyawa suka yi suna kallon ta. Hawaye na zuba daga idanunta. Dake dukkan su yara ne babu me hankalin da zai iya cewa wani abu ne, Yarima Sadeeq da Abuturab suna hango su, daga can wurin class. "Me ka fahimta?" "Kai dalla kawai dai bata yi appreciate da zuwan su bane" "har yau baka son kome akan masu matsalar nakasa ba, kaga lokacin da suka tawo, da gudu yarinyar ta isa wurin matar, ganin mijin yasa ya fara ja baya. " "Case closed don Allah kayi naka matsalar" Abuturab ya fada, domin baya son magana, idanun shi na kan Sa'ade da take bubuga bayan Kubrah. Takowa mijin matar yayi, ya cire hannun Sa'ade ya fara kokarin janye ta jikin sa, da karfi ta fashe da kuka. Ya juya ga Yayarta yana kallon ta irin kallon shu'umancin nan ya fara magana. "Salmah ba zaki mata magana ba." Jikinta yana kerma ta mata alamar ta daina ihu. "Ki gaya mata bana son ganin yaran nan a tare da ita ko na dauki mugun mataki " ya fada yana shiga gaban motar, sai kallon su ake, haka ta shigar da Kubrah motar, da aka saka mishi tintak. Sauke glass din motar yayi yana bin su da mugun kallo, a mugun tsorace suka juya, kamar zasu kifa. Musamman Sa'ade da ta hango tsanar su a fuskar shi. Hango Yusuf tayi yana nimansu, da gudu ta isa wurin shi dake ya basu baya, ta ja rigar shi. Juyawa yayi ta fada jikin shi tana murna.
18
Hakkin Mallakar
Mai_Dambu
08130269641
16
WAIRA POV.
Yanayin iskar dake shiga da fita hancinta ba irin wanda ta saba shaka ba ne, yanayin hasken dakin da gininsa kadai ya sanar mata ta baro duniyarta. A ina take? Shi ne abun da ya fara zuwa ranta, daki ne yalwatacce irin na marasa lafiya, an saka labule a inda take kwance an mata shinke da wadanda ke gefenta. Yanayiyar da take ji ke sanar da ita cewar ba ita kadai ce a cikin dakin ba, tunanin dalilin zuwanta gurin take tana son ayyana cewar mutuwa ta yi ko kuma a wani gurin take na dabam. Ta dago hannunta da sauri ta kalli inda macijin ya cijeta sai ta ga an nada mata wani farin abu an daure hannun, ga wani karfe a gefen hannunta na hagu da aka rataye wata jakar leda da bata san na minene ba, zabura tayi ta tashi zaune jin kamar akwai abu a hannunta ya saka ta duba hannu sai ta samu an daura mata wani karamin abu an saka wata yar fata an danne. Idonta ta dora a gurinta tana dubawa a iya zurfin tunaninta jininta ne ake sha ko kuma aka sha. Da sauri ta sauko saman gadon na Asibiti jin kamar ta taka ruwa ya saka saurin duba kasa, wani farin abu ne a kasan mai sulbi sai sanyi yake, ta koma saman gadon da sauri ta rumgume kanta tana jin wani sabon hawaye na cika idonta, tsoro ya gama cika zuciyarta ya bayyana a jikinta, domin ko wane bangare na jikinta sai da ya amsa. Hannu ta saka a jikin kayanta sai ta ji aljihunta wayan babu komai, da sauri ta kai hannu ta taba kanta nan ma babu komai, hannun mai lafiya ta saka ta dafe kanta ta kwala wani uban ihu, duk wanda ke Ward din sai da ya tsorata, Nurse din da suke duty da ranar suka iso kanta da gudunsu.
“Lafiya miya same ki?”
Ganin dukansu sun saka tufafi kala daya ya tsorata, ba zata ce ba mutane ba, domin suna da duk wani abu da take da shi sai dai tufafin jikinsu da yarensu ya banbanta da nata. One after the other ta rika binsu tana kallonsu so take ta ga fuskar wanda ta sani amman ina, babu fuskar da ta sani a cikinsu, gashi ta kasa fahimtar yaren da suke mata. Dayar dake sanye da safar hannu ta kai hannu ta taba hannunta sai ta yi saurin buge mata hannun ta kara matsawa baya.
Kamar kurma haka ta zame musu, bata aikin komai sai hawaye tana kara matse jikinta da ginin dake bayanta, gaba daya ji take duniyar ta juye mata upside down, ta kasa gane a ina take da su wa take? Waya kawo ta a nan duk bata sani ba, idan ma ta sani me zata yi? Komawa a garin nan ta san ba zai yiyu ba, haka zama a inda macijin ya cijeta ma ba zai wadata da komai ba, sai dai abun da bata fahimta ba, wanda ya kawo ta nan me zai mata? Me yake nema a gareta.?
Wani namijin ne na dabam ya zo dubata, sai dai shi baya sanye da kalar tufafin dake jikin mata, nasa tufafin kala dabam ya dora wata farar riga sama. Hannu kawai ya kai ya taba kafarta sai ta ji tsikar jikinta ta tashi, kallonsa take a fuska be mata kama da wanda ta sani ba, sai dai jikinta na bata taba sanin mutumen da bata san waye ne ba, ko kuma ta taba ganinsa ko kasancewar tare da shi sai dai ta kasa tuna a ina balle ta san waye shi. Shi kam be ce mata uffan ba ba kamar sauran matan dake ta damunta da magana ba, su ma da suke masa magana be amsa musu ba, sai hannunsa da ya saka aljihu ya ciro Apply ya mika mata ganin ta ki karba sai ya aje a saman gadon ya kai hannunsa jikin fuskarta ya share mata hawayen da suka zubo mata, nasa idon na cika da kwalla, da sauri ta kai hannunta zata dafa shi sai yayi saurin dauke hannun kamar ya san abun da take nufin aikatawa. Ba tare da yayi magana ba ya fice daga gurin Nurses din dake tsaye sai mamaki suke, ganin be fadi komai ba be kuma dubata yadda ya dace ba yayi tafiyarsa. Ganin ta ki magana sai kuka take ya saka suka tunanin bata iya magana, tunanin bata jin yarensu be zo musu a rai ba, domin wasu ma sun dora mata hauka ganin tufafin dake jikinta ga kuma tarin dattin daya boye ainahin kyaunta.
Tun suna mata magana cikin dadi rai har suka gaji suka tafi suka kyaleta, daman irin Asibitin nan ce ta Gobnati ta marasa galihu da ba a ciki kula da mutum kamar babbar Asibiti ba, ko kuma Private Hospital, bata kallon ko'ina a yanzu sai kasa Tile din dake kasa take son tantance minene a gurin da yake sanyi dazun data taka, komai ya zame mata kamar mafarki, wacan rayuwar ta garinsu take jin tana marmari sai dai babu halin komawa a yanzu. Jin yan hanjinta na kukan sanar mata neman agajiya ya saka ta dauki Apple din da ya aje a gurin ta kai bakinta ta gutsura ta ci, tsoro baya bari ta tauna yadda ya kamata idan ta saka shi a bakinta ta raba shi biyu ko uku sai ta hade, da haka har ta cinye, sauka ta yi a hankali sai ta sake jin irin sanyi dazun hakan ya saka ta komawa saman gadon ba shiri, sai ta takure kanta ta fashe da kuka. Hankalinta be kara tashi ba sai da ta ga shigowar wasu mutanen na dabam ba na dazun ba, ba kuma wadanda ta taba gani ba, wadannan sanye suke da bakin kaya gaba daya jikinsu.
A nan ta gane kowa ya banbanta, sai dai bata iya gane akida ko al'adar kowa balle ta iya fahimtar ko tufafin jikinsu suna walkiltarsu ne, wadanda suka zo yanzu kuma saka ta suka yi gaba da tambayoyi kala kala, suna rike da abun abun rubutunsu, kamin Likitoci uku su sake ziyarta ciki har da wanda ya zo dazun be mata magana ba, sai gashi shi ma yana mata tambayoyin da bata fahimcin yaren ba balle ta bada amsa. Ruwa a gorar dayan dan sanda dake sanye da bakin tufafi ya mika mata tare da abincin a takeway, ta sani tana bukatar ruwa sai dai tsoronsu da rashin sanin waye su mutanen ya saka ta kasa mika hannu ta karba, Apple din da likitan ya aje mata dazun ma bata taba ba, cikinsu kuma babu wanda ya damu ya tambaya waya bata apple din. A kokarinsa na burgeta ya bude abincin dake cikin robar takeaway, dafadukar shimkafa ce da cinyar kaza. Sam bata gane cewa shimkafa ce ba domin am sarrafa ta ba a babin da ta sani ko ta taba gani ba. Hawaye ke mata zuba kamar an bude karamin fonfo tsoron take gashi ta rasa gane yaren da suke magana da ita, ga mutanen sun kashi har kashi kashi kowa tufafinsa dabam, wani abun da ya bata tsoro kuma yadda suka tsareta wasu na kallonta wasu na damunta da magana wasu na rubutu, hankalinta be kara tashi ba sai da dayan likitan ya miko hannnunsa ya riko hannunta.
“Ahir hir Ahir verrr yat tour tour tor”
Ta fada da karfi ta fisge hannunta daga rikon da yayi mata, likitan nan ne dai na dazun da ya bata Apple, duk kirko kirko suka yi suna kallonta ba da farko kallon kurma suke mata ganin taki magana, a yanzu kuma da ta yi magana ta ba su mamaki, domin wani sabon yare suke ji a tare da ita.
“Kamar Fulatanci take Dr Shuraim”
Wanda aka kira da Dr ya juyo ya kalli dan'uwansa da mamaki.
“Ba fulatanci ne ba, fulatanci yarena ne da shi take yi da na ji”
“Kasan ance fulatancin ko wane gari ya banbanta da sauran”
“Yes, kalmomin suka banbanta amman muna gane yaren juna wannan ba fulatancin ba ne, wani yaren ne na dabam”
Ya sake juyawa ya kalleta da manyan idonsa masu matukar daukar hankali, cikin kwayar idonta yake kallo.
“Anene fulfulde?”
Ta rumgume kanta tana kara matsawa baya. Be sake ce mata komai ba sai ya dauki abincin ya matsar mata da shi hannu ta saka ta buge abincin ya zube kasa ta dauki Apple din kadai ta rike.
“Waya bata Apple”
Ya tambaya yana kallon Nurses din dake bayansa, suma kallon mamaki suke masa domin sun san shi ya bata apple din da kansa.
“Dazun kai ka bata da kanka”
With confused ya kalli wacce tayi maganar, baya son musu surutu ma bangarensa ba ne balle kuma musu, hakan ya saka be damu ya musa musu ba, all what he thought is wani likitan ne ya bata suka yi zaton shi ne. Matsawa yayi kusa da ita sai ta matsa baya kamar zata shige jikin ginin tana masa kallon tsoro, hannunsa ya kai ya rika kanta yana kokarin duba idonta dake kama da nashi tsabar farin idon, sai dai nata gwaiduwar ciki blue ce tsabanin tashi da take baka wulik, kallo daya zaka mata ka fahimcin kyaunta ya banbanta da na sauran mata sa'aninta duk kuwa da kasancewar dattin dake jikinta. Tana da masifar kyau ga kirjinta a cike daidai har ya fi na sa'arta domin rigar saƙin dake jikinta ta fata tana fito da ainahin zatin kyaunta ne. Be ankaro ba ta dantsara masa cizo a hannu da mugun karfi, abun ka da wanda ya dade be ci nama ba hausawa suka ce masa maye wai idan yayi cizo ba a warkewa da wuri, idan kuma yayi magana sai ta kama Mutun lol, tana dota hakoranta a hannunsa kamar reza haka hakoran suka yaga rigar hannunsa suka shiga har cikin naman hannunsa sai wani zafi yaji kamar an yanke shi da wuka a take jini ya fito sai dai ba mai yawa ba, cikin zafin nama ya fisge hannunsa yana zaro ido
“Easy Girl...”
Da sauri Police din da suka zo daukar report dinta suka jo kanta da gudu suka riketa dayan ya juyarda hannunta da karfi zan lankwasa sai Likitan yayi saurin dakatar da shi ganin yana kokarin yi mata illa kamar ya samu katon namiji.
“Nonono she's just a girl karka ji mata mana”
“Ai kara ayi mata haka, what is akwai dafi a bakinta fa? Ba mu san waye ita ba”
Ya fada yana kara matseta.
“Saketa dan Allah ta tsorata ne tana zaton zan mata wani abun ne”
Ya saketa kamar yadda Dr Shuraim ya bukata, sai ta rumgume hannayen nata m har da mai ciwon.
Dr Shuraim ya fice gurin rike da hannunsa har lokacin ciwo yake ji a iz sosai, kamin ya karasa Office dinsu na Likito ya cire safar hannun ya jafa a gurin da aka tana da domin zuba shara, bathroom 2(8 ya fara shiga ya wanke hannunsa sannan ya fito ya dauki audiga ya saka a gurin ya goge, sannan ya cire labcoat din dake jikinsa ya aje ya ciro wayarsa dake ringing ganin mai kiran ya saka shi murmushi.
“Hey Baby Girl”
“Ruhul Kal ya kake ya aiki?”
“Ina lafiya fatar ke ma haka kike?”
“Nima haka, ya Katsina”
“Katsina na nan sai zafin kamar za a kama da wuta”
“Mu kuwa ruwa ake mana yanzu, wani guri na samu na fake ma”
“Daman ku yan Abuja kun fi kowa zama yan gayu, fatar dai ruwan be taba min ke ba”
“Ya jika ni kadan”
“Da ace zan ga ruwan an kuwa da na masa duka”
Ta kyalkyale da dariya, shi kuma yayi murmushin da ya bayyana fararen hakoransa da suka haska bakar fatar jikinsa mai kyau da sheki.
“Take care of yourself zan kiraki idan na bar gurin aiki”
“Toh I love you”
“I love more and more and more Baby girl”
Ya sauke wayar, sannan ya fice daga gurin, dakin da ake aje majiyanta ya sake komawa sai ya samu har lokacin suna nan tsaye akan yarinyar yanzu ma har an samu karin wasu mutane dake kallonta a cikin masu jinya.
“Wannan ai zaku tsoratata ne, please kowa ya koma gurinsa”
Kowa ya wuce ban da police din da suke zon tirsasa ta tayi magana.
“Ba zata iya magana a yanzu ba, a yadda na fahimta ko tayi magana ba zai amfanar ku komai ba, domin ba ta jin yarenku inda ba ta yi hakan da gangan ba, kai kana duba jikinta da yanayin tufafinta kasan ba ta jin yarenmu”
“Amman Doctor zai dauke ta lokaci kamin ta warke?”
“Eh ya danganta da kalar majicin daya cije ta, zata iya sati ko sama da haka a ka'ida dai ana son ta samu kulawa mai kyau na wata daya idan abun yana da karfi wata shida shi ne zata warke gaba daya”
“Okay mun gode, dan sandanmu daya zai tsaya tare da ita saboda bada tsaro da kuma kula da ita, ni kuma zan je na sanar da halin da take ciki”
Da kai ya amsa masa, sannan ya mika masa hannun suka gaisa su biyu suka fice dayan ma da aka bari domin bata tsaro fita yayi saboda ganin Likitan ya zauna a saman gadon da take zaune. Kallonta Dr Shuraim yake yana son fahimtar wasu abubuwa a tattare da ita.
“Baby Girl...”
Ya kirata da irin sunan da yake kiran Babensa, domin be san sunanta balle ya kirata da shi.
Ya leka kasan fuskarta sai ta boye kanta.
“Akwai bukatar ki tsabtace jikinki ki ci abinci a baki magani”
Kamar wacce ta san abun da yake fada sai ta lake kafada daga boyen da take ta fashe da kuka. Da kamar mamaki ya ke kallonta.
“Kina jin yarena?”
Nan ma ta lake kafadar.
“Wane yare kike ji?”
Nan ma ta sake yin abun da ta yi dazu, sai ya fahimci bata son yayi mata magana ne.
“Okay Baby Girl zan barki ki huta”
Ya mike tsaye sai ta dago kanta ta kai apple din hannunta a baki ta fara ci, still tana kuka kamar wata shagwababbiya. Shi dai be sake ce mata komai ba ya fice.
AMEER POV.
Fitar Ameer da kamar minti biyar da fitar Ameer Daddy ya kira Momy sai a lokacin yake fada mata abun da ya faru, da kuma response din Ameer akan cewar shi be san da labarin yarinyar ba.
“Wata kila da gaske ne, kasan Ameer baya tsoron amsa laifi idan ya aikata kamar yadda ya amsa maka cewar ya karbi motar”
Ajiyar zuciya ya sauke mai dauke da damuwa.
“Ina fatar haka, sai dai ina jin kamar ba yarda da shi ba, kwana biyun nan abun da Ameer yake ya fi karfin na baya”
“Jarabawa ce, dole hakuri zamu yi muna masa addu'a har Allah ya shiryar da shi, kuma ni ina ganin kamar ayi masa aure a zai saka ya natsu”
“Tun da nake da Ameer be taba min zancen soyayyar ba, gaba daya mata basa gabansa shiyasa na sha mamaki lokacin da yake fadar akwai wata yarinyar shi har suka samu matsala da abokinsa”
“Kai mahaifine ai, zaka iya zaunar da shi ka nuna masa inda kuskurensa yake, idan ya manta karatun sai ka tusa masa, yaran yanzu sai da haka, kuma duk wata lalace da kake ganin Ameer yayi laifinka ne, sam baka yarda ayi masa magana idan yayi kuskure”
“Akwai yara da yawa da suka tashi a cikin gatan irin na Ameer, amman basa yin abun da yake yi, zai fi kyau mu dora abun a babin kaddara Allah ya hukunta kawai”
“Toh Allah ya shirya mana, amman gaskiya a maida hankali gurin yi masa aure kasan aure yana natsar da Mutum kuma idan an tashi kar a nema masa yar Babban Mutun domin ba ko wace mace ce zata iya zama da shi ba, sai dai a nema masa mai hakuri wanda zata iya bin halinsa”
“Idan kuma yana da wanda yake so fa?”
“Shikenan ta kwana gidan sauki, sai a aura masa daman ai ya kai munzalin auren kuma Allah ya hore komai”
“Nima kuma shekaru suna ja, ina da burin ganin haka kamin ta Allah ta kasance”
Furucin da Daddy yayi sam be yi mata dadi ba, hakan ya saka bata sake cewa komai ababin maganar ba.
“Zan aje waya, saboda ina shirya abincin rana”
Yayi murmushi ya sauke wayar, sannan ya sake kiran CP, duk wani abun da za ayi a kashe maganar Daddy yayi domin baya son damuwa a yanzu kamar yadda likitansa ya tabbatar masa.
Jikin Motar Momy ya jingina thinking of din yarinyar ta mutu yadda zai bata ma Maleek da kanwarsa suna, a yanzu din ma tunanin yadda zai yi amfani da wannan damar ya taba martabar gidansu