Showing 240001 words to 243000 words out of 281271 words
ma be san tana fita haka ba, and ya manta when last ma yayi dariya mai sauti da saka zuciyarsa nishadi irin yau since yana tare da abokansa tun suna in group, sai kuma a lokacin da yake kebewa da Abiey da Mahmood suna hira, a nan idan abun dariya ya tashi yana yin dariya idan babu mata ko Ummi ko kuma kannensa a kusa.
“I guess ina yi, gashi dai yanzu kin gani”
“Amman baka taba yi a gidanku ba”
“Gashi ina yi a garinsu Nuwaira ai”
Magana yake kamar ba shi ba, every sentence every word da nishadi da annashuwa suke fita a bakinsa. Tana kallonsa sai kawai suka fashe da dariya at the same time kamar wasu mahaukata.
“What are we laughing?”
Ya tambaya yana kokarin maida dariyarsa murmushi, sai kallon Nuwaira yake da har lokacin dariya take har da hawaye.
“You're so beautiful”
Ya fada a ransa, a zahiri kuma kallonta kawai yake yana murmushi har ta gama dariyar. Wani abun da Nuwaira bata yi tsammanin za a barsu, su aikata ba shi ne shigowa da wasu abubuwan da ta yi guzurinsu tun a garin Abuja, Maleek ya dauko jakarta kayansa ita kuma ta dauko wasu daga cikin abubuwan da zata iya, suka dauko wasu abubuwan ci da Ummi ta bata domin samun abun kaiwa a bakin salati. Duk wani motsi na su yana kan idon jama'ar garin suna kallonsu kamar sun samu tv, musamman ma wadanda ba su taba gwada barin garin ba suna ganin komai na su bakon lamari, wadanda suka saba bawa idanuwansu abinci kam hakan ba bakon abu ba ne a gurinsu.
One of those laces da aka bata ta bude ta shimfida a kasa, Maleek ya leka bandakinta ya fito yana jin kamar zai yi amai domin be saba shiga irin wannan bandakin ba, kuma be jin zai iya shiga nata ma.
“Babu wani guri da zan iya yin wanka?”
“Zaka iya yi a cikin korama?”
Ta tambaye shi bayan dogon nazari da tunanin inda zai yi daidai da rayuwarsa.
“Maybe bana son canja wasu tufafin ban yi wanka ba na yi datti da yawa”
“Muje na nuna maka”
Shi ya fara fitowa daga cikin dakin sannan ta biyo bayansa sai da suka tafiya ta tsaya ta dube shi.
“Ya Maleek ko dai ka hakura da wanka har ka koma gida?”
“Why? Don't tell me zaki koma ma rayuwarki ta baya”
“No ina jin tsoron kar Eid ko sarki su yi maka wani abu na cutarwa”
“Zan yi addu'a kamin na shiga, kuma na yi addu'a kamin na fito babu abun da zai same ni”
“Amman...”
“No amman baki ga yadda nake rayuwa ba? Ha hankalina kwance?”
Ta daga masa kai cikin damuwa.
“Muje”
Ta cigaba da tafiyar ba dan ranta ya so ba, shi kam kalle kalle kawai yake har suka isa gurin wasu abubuwan suna burge shi, domin an kawata su sosai ga itatuwa ko'ina suka bi, uwa uba ma da suka isa koramar yadda ruwa ke saukowa daga kan duwatsu suna zuba gwanin burgewa.
“Cire dankwalinki”
“Ba kuna cewa ba kyau mace ta bayyana gashin kanta da jikinta ba?”
“Kamawa ta yi ai cire wani abu zan nuna miki”
Ta cire dankwalin hakan ya bawa yalwatacce gashin kanta da ya sha gyara damar saukowa bayanta.
“Juya”
Bata iya yi Maleek musu tun asali hakan ya saka ta juya bayanta. Sai ya saka dankwalinta ya daure mata ido gam yadda ba zata iya ganin komai ba.
“Ya Maleek minene?”
“Bana son ki kalleni ne”
Ya cire rigar vest din dake jikinsa ya daure hannayenta ta baya.
“Ki tsaya a nan sai na fito”
Ba tsirara yayi ba rashin riga a jikinsa da kuma short din ya bari a jikinsa be baya son Nuwaira ta kalleshi a haka. Sai da yayi addu'a sannan ya shiga gefen koramar ya tsaya yana wanke jikinsa. Tana tsaye a gurin da ya barta gabanta na faduwa ganin take kamarba zai gama wankan lafiya ba, zuciyarta na ta raya mata Eid zai iya masa wani abu.
“Ya Maleek baka gama ba?”
“Na gama...”
Ya rada mata daidai saitin kunneta, kamin ya kwance mata hannunta ya bude mata ido har ta matsu.
“Oh”
Ta dafe zuciyarta tana kallonsa sama da kasa, ya wanka jikinsa fes ya canja tufafi a yanzu jean ne a jikinsa da T-shirt.
“Muje”
A tare suka jera suna tafiya, ita kam sai hakura ta yi da wanka domin ita ma ta ji ba zata iya shiga bandakin ba, kuma bata son ta yi nisa da Maleek jikinta kawai ta wanke ta fita daga dakin har sai da ta canja tufafi sannan ya dawo. Idan za su yi Sallah sai da ya duba agogo ya gane lokacin yin Sallah yayi domin babu masallaci a kusa da garin ma balle kuma garin, a cikin kayan kwalan da makulashen da Ummi ta yi mata guzuri suka ci, dan ruwan gorar da yayi musu saura ya sha rabi ya bata rabin ta shanye. After sun gabatar da Sallah Isha'i ya dauko wayarsa yana ta dubawa rashin shigar kira ya fara damunsa domin ya san hankalin iyayensa zai tashi.
“Ya kamata ka tafi gobe”
“Ba tafiyar ce damuwata ba, rashin samun network ne damuwata, ba zan tafi na barki ba ba tare da na yi magana da sarkinku ba, kuma Nuwaira ko da na yi magana da shi i just feeling like ba zan iya barinki a irin wannan rayuwar ba”
“Ban san abun da suke ma shiri ba, amman wani be taba karya dokokin garin nan kuma aka kai wannan lokacin Sarki be saka an kama shi ba, ko kuma a hukunta shi, amman ni har yanzu be aiko min ba, kuma Eid be dawo ba, ina ta jin tsoro Ya Maleek kar su cutar da kai”
Ya jingine wayarsa domin ta haska dakin da babu komai a cikinsa sai duhu, without saying anything, ya yarda addu'a zata yi masa aiki kuma yana tare da kariyar Ubangiji but deep down inside him ya san yana jin tsoron shairinsu sai dai baya nunawa a fuska saboda kar su gani kuma kar ya daga ma Nuwaira hankali. Ita ma bata sake cewa komai ba sai tunani take kala kala, ganin hakan ya saka shi daukar wayarsa ya koma can bakin kofar dakin ya shimfida rigar da ya cire dazun ya zauna tare da bude qur'an application dake ciki wayarsa ya fara karatun al'qurane. A take ya ji duk wani tsoro da ke tare da shi ya kau aminci da natsuwa suka lullube shi, Nuwaira ma dake can gefe tana kallonsa sai bachi ya dauke ta saboda dadin karatun dake ratsata.
*** *** ***
“Me yasa kika dage sai kin raba ni da shi? Me na yi miki? Akan wane dalili zaki kawo shi inda za a raba mu?”
Nuwaira ta daga kai ta kalli matar dake ta masifa tana kuka.
“Wace ce ke?”
“Matarsa ce ni, idan kika raba ni da shi yaransa ki yi yaya da su?”
Ta nuna mata yaran biyu dake tsaye gefe daya dayan kuma yana hannunta.
“Tun da kika shigo rayuwarsa kika sauya komai, da na shaka masa liyi da mata, amman kina zuwa kika fara kawo min matsala yanzu kuma kika kokarin raba ni da shi, bayan kin nisanta ni da bana samun lokacinsa kamar da, ni ma musulma ce be kamata ki yi min haka ba, ba ki san tsawon lokaci da na dauka a tare da shi ba, duk yadda zan yi na rabaku na yi amman kin zama karfen kafa, ni ce nake miki siffarsa ina taba ki, amman haka be yi tasiri akanki ba, na fito miki a fili ba sau daya ba amman ba ki kyale min mijina ba”
“Ni ban miki komai ba...”
A take matar ta jefar da ďanta ta yi cikin Nuwaira ta shake wuyanta da karfi.
“Ki yi min, ki yi min, ki yi min”
Shi ne abun da take fada ya shake Nuwaira da dukannin karfinta, Nuwaira sai fisge-fisge take tana neman ceto numfashinta na kokarin daukewa. Daker ta iya fisgo kanta ta farka daga bachin sai ta tashi zaune da sauri tana hakki ta rike wuyanta. Maleek da har lokacin karatu yake ya haska fuskarta.
“Lafiya?”
“Wata mata na gani a mafarki ta makure ni sai fada take da ni, wai na kawo ta inda za a raba ku, matar da nake gani dakinka ce kuma ta ce ita matarka ce”
And now he's smile ya bar inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna.
“Matata kuma? How are you okay”
Nuwaira na shafa wuyanta ta ce.
“Baka mafarkin wata mata? Ni na fada maka ina ganin mace a dakinka da har da yayanta ma, ita ce ta fara sumar da ni a lokacin da na fara ganinta a dakinka har ka mareni lokacin da na tsorata na rike ka”
“Shiyasa kike tambayar ina da mata? Ba ni da mata ni ban taba cewa ina son kowa ba, balle kuma aure”
“Ni ma na yi mamakin da bata fitowa ta zauna a tare da mu, amman ban gane aljana ce ba sai yanzu, saboda ta fada min har kuna da yaya baka mafarkinta ko ganinta kai?”
“Sometimes amman ina daukar duk mafarki ne ba gaske ba, kuma da can nake yi daga baya na daina”
“Ta makoreni sosai”
Tana maganar tana kuka, da fitilar wayarsa yayi amfani ya haska wuyanta, sai ga shakin yatsu gurin ya mata ja alamar jini ya kwanta.
“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Subhanallahi”
Fada cike da mamaki, ayatul kursiyu ya karanta ya tofa mata a wuyan tare kula'uzai.
“Nuwaira dole ki dage da addu'a, kuma ki yi kokarin raba kanki da tsafin da yake cikin jikinki saboda, so that ki samu full kariya daga Allah, wata kila idan kika rabu da tsafin ba za su taba iya sarrafa ki ba, saboda karfin addu'a, and we have to leave this place by tomorrow hankali be kwanta ba, na kasa samu bachi...”
Ta gyada kai tana jin zafin wuyan nata har lokacin, sai dai kuma bata jin zata iya barin garin.
[8/10, 6:44 PM] 🦋-🦋: 76
AMEER POV.
Ta tunani da kuma fargaba ya fito bayan ya faka motarsa a harabar gidan Abiey. Yadda ya ga Abiey yana safa da marwa waya a kunnesa ya dan daga hankalinsa domin yanayin Abiey yana nuna ba lafiya ba, kuma shi be taba ganinsa a harabar gidan ba tun da ya saka kafarsa a gidan ma sai yau. Ameer yayi kamar ya wuce bangaren Ummi sai kuma ya ji be natsu da hakan ba, dole ya nufi gurin da Abiey yake tsaye ya saka hannayensa biyu aljihu ya soke kai kasa da fari ya yi zaton ko ciwon Ummi ne ya zafafa ya saka Abiey a wannan halin, sai dai sauraren wayar da Abiey yake abubuwan da ya ji yana furta ya nuna ba akan Ummi ba ne, a take gabansa ya soma faduwa. Tsayawa yayi a gurin har sai da Abiey ya gama wayar sannan ya matsa kusa da shi.
“Lafiya kuwa na ji kana fada”
“Ba dole na yi fada ba, imagine saboda a sama musu tsaro na saka police suka raka su tun daga nan, kuma bayan sun isa can aka kara musu wasu biyu, wai yanzu dayan yake fada min su sun juyo suna cikin Katsina Maleek kuma yana can garin ya dage sai ya shiga ciki su kuma ba za su iya shiga ba saboda haka suka dawo, ji min wata maganar banza ba za su iya shiga ba suka bar min yaro ya shiga shi? Kuma saboda ya raina min hankali sai fada min yake wai garin da mutanen garin suna da hatsari ba sa son baki, na fada masa idan wani abu ya sami ďana sai na yi shari'a da su, kuma su koma su taho min da ďana, shiyasa tun jiya ina ta kiran wayarsa bata shiga, Ummi ma tace ta kira shi ya fi a kirga wayar be shiga ba”
Ameer be san lokacin da kai hannu ya dafe kirjinsa ba, saboda bugun zuciyarsa da karu daman tun da ya farka yake jin ba lafiya ba, gashi kuma yanzu Abiey ya fada masa abun da zai hana shi bachi.
“Allah yasa ba wani abu ya same Waira ba”
“Waira ko Maleek?”
Abiey ya tambaya yana mamakin jin yadda ya bar dan'uwansa yake fargabar kar wani abu ya same wata.
“Dukansu Allah yasa suna cikin aminci”
“Ameen, karka fadawa Ummi wannan maganar domin kasan bata da lafiya be kamata ta ji wannan abun tashin hankalin a yanzu ba, karka kuskura nuna mata komai”
Da kai kawai Ameer ya iya amsawa Abiey ya juya ya nufi hanyar shiga part din Ummi, Abiey kuma ya nufi bangarensa yana kara kiran wata number. Sai da Ameer ya isa kofar falon Ummi ya kai hannunsa ya taba kofar sai ya kasa murdawa ya tura ya shiga, saboda jikinsa a mace yake, damuwar dake zuciyarsa kuma ta nuna a fuskarsa, Ummi zata iya tambayarsa be san yadda zai kare kansa ba. Fasa shiga falon yayi ya juya ya nufi motarsa kamin ya isa ya ciro wayarsa ya gwada kiran number Maleek amman bata shiga sai yankewa kiran yake. Kamar wanda ke shirin rasa rai haka ya bude motar ya shiga gabansa na tsananta faduwa zazzabi na neman rufe shi.
Daker da sudin goshi ya samu kuzarin murza key motar yayi reverse ya fita daga gidan, be yi nisa ba ya ji kamar ba zai iya tukin ba sai ya faka gefen titi ya kifa kansa a sitiyarin motar kalaman da Nuwaira ta fada masa kawai yake tunawa, yawan nanata cewar idan suka koma a garin kasheta za ayi ya tsaya masa a rai. Sai a yanzu yake jin ina ma shi ya raka ta ba Maleek ba? Me yasa da Abiey ya ce ya rakata ya musa masa be amsa ba..? Shigowar kiran Humairah ne ya saka shi dagowa da sauri ya kalli wayar with hoping Maleek ne ya kira ganin sunan Humairah ya saka shi rufe ido ya sauke ajiyar zuciya ya busar da iskar bakinsa.
MALEEK POV.
Sai da rana ta fara haskowa sannan Maleek ya kwanata a inda Nuwaira ta tashi ita kuma ta fito waje ta zauna tana shan ranar tana taba wuyanta har lokacin ciwo yake mata, tun kamin aje ko'ina ta fara missing din gidan Ummi.
Juyawa ta yi a hankali ta kalli Maleek dake bachi sai tausayinsa da kaunarsa suka kama ta wanu be taba gwada kare lafiyarta kamar shi ba, gwadawar da zai jefa rayuwarsa a cikin hatsari saboda ita, be damu da rashin kyau dakin va ya kwana a haka, kuma ta taya ta gyara dakin be nuna mata kyama ba, wani abun da yake burgeta da shi be taba gwada taba jikinta ba sai a lokcin da ya ceto a ruwan swimming pool sai kuma ajiya a kokarinsa na kareta daga danginta. Taba ta da ake da dare ma tana zaton shi ne a yanzu ta gane ba shi ne ba, sakamakon mafarkin da ta yi jiya.
Murmushi ne yayi ma kansa muhalli a fuskarta a yayinda idanuwanta suka kallon fuskar Maleek da be san tana yi ba domin bachi yake yi mai nauyi na ranko bachin da be samu yi ba da dare. Jin alamar takun tafiyar mutane ya saka ta dawi da dubanta gurin hanyar shigowa sashenta, tawaga ce daya ta sarki tare da wasu manyan mutanen da ta san su a fadar sarkin.
Da sauri ta mike tsaye gabanta na faduwa wata zuciyar na raya mata taje ta tashi Maleek ta dayan bangaren kuma tana jin tsoron ko Maleek din suka zo cutarwa. Kamin su karaso gurin Maleek ya farka da sauri kamar wanda aka sanarna a mafarki ya fito waje da sauri ya tsaya kusa da Nuwaira.
“Su waye?”
“Daga fadar Sarki suke, ban sani ba ko wani abun za su yi maka”
“Ko kuma ke ba, kar su ce za su dauke ki ko su cutar da ke”
“Idan ni ce abun da sauki, kai ne da ba zan so su cutar ba”
Mutanen ba su yarda sun karaso kusa da inda suke tsaye ba suka ja daga suka tsaya, daya daga cikin zaratan jaruman fadar masu hidima wa Sarkin Garin ya matsa gaba kadan ya fara magana da Nuwaira da yarensu.
“Sarki ne ya aiko tawaga ya ce a taho tare da ke da bakonki yana son ganinku a fada”
Nuwaira ta juya kadan ta kalli Maleek dake gefenta.
“Sarki yana son ganinmu”
“Fada masa zamu tafi bari na dauko wayata”
“Ya Maleek idan kuma cutar da kai zasu yi fa?”
“Babu abun da za su yi min, duk abun da kika ga ya same ni to daman can an rubuta zai same ni ne, amman babu wanda ya isa yayi min wani abu sai da amincewar Ubangijina, ni kuma na yarda da shi ba zai taba bari a cutar da ni ba, ki amsa musu kawai zamu zo”
Yana maganar tana hawaye ganin take ya kasa fahimtar manufar, bayan kuma ta san waye Sarkinsu kuma ta san su waye jama'ar garin, ko da ka kyautata musu idan kai ba dan garin ba ne za su iya cuta maka balle kuma ace ka munana musu ka karya dokokinsu.
“Idan ina ganin hawaye a idonki kina karya min guiwa ne kawai, ba zan ma dauki wayar ba mu tafi”
“Ya Maleek”
Ya aika mata da wani irin sihirtaccen kallo cikin kwayar idonta da ya hana ta karasa kiran sunansa ma balle kuma ta dora da abun da take da kudurin fada. Shi ya fara takawa ganin haka ya saka dole ta cira kafa suka fara nufar mutanen a tare, tawaga jama'ar Sarkin suka yi musu wasu a gabansu wasu baya wasu dama wasu hagu, jama'ar garin da suka fara hada hadar safiya suka fito sai kallonsu suke, wasu kuma daga cikin gida suke fitowa suna kallonsu, ita dai gabanta sai faduwa yake, Maleek kuma ya dagewa zuciyarsa duk wani tsoro ko fargaba ya bar shi a cikin zuciyarsa bakinsa na ta karanta addu'ah har suka isa fadar.
A zahiri ya san Sarautar domin shi ma jikan Sarki ne, hakan ya saka shi yin ladabi ya cire talkaminsa tun kamin su shiga fadar, sannan yayi bismillah ya nasa kafarsa cikin katuwar fadar da aka kawata da fatar farar daminsa, kujerar kuma aka yi da fatar zaki aka dora kan Zakin saman kan kujerar dama da hagu na kujerar kuma kanun manyan