Showing 222001 words to 225000 words out of 281271 words

Chapter 75 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1205

rantse gidan iyayenta ne zata bari a kaita wani gurin dabam.

It takw them 8hours kamin su isa Kt from Abuja, saboda yanayin tafiya da kuma dab tsawar da suka yi. Hotel suka yi kama police din dakinsu dabam separately, Maleek ma dakinsa dabam Nuwaira ma aka kama mata dakin, sai dai ta kasa natsuwa tun da suka iso har sai da Dr Shuraim ya iso gurin, Maleek be yarda ya bar su sun kebe dabam ba, ya kira Nuwaira ta fito reception din ta hadu da Dr Shuraim, ganin Maleek ne kadai ya hana ta rumgumar Dr Shuraim domin ta yi marmarinsa ba kadan ba, and shi ma yayi marmarinta ba kadan ba, kamin ya fara bata labari ita ta fara bashi and all of her story abun da ya faru tsakaninta da Ameer ne, a yanzu da baya kusa da ita take marmarin take missing dinsa and the saddest part is be rakota ba da zata zo.

“Saurayinki ne shi Ameer din?”

Ta yi jimmmm for tunani kaminnta girgiza masa kai da sauri.

“Aa shi ma kamar kai yake”

Can kuma ta dan turo baki.

“Ya dan fika so na kadan”

Dr Shuraim yayi murmushi.

“Waya fada miki? Yanzu dai gidanmu zamu tafi ki kwana a can kamin gobe sai na rakaki mu tafi tare ko?”

Ta dan leki Maleek dake zaune gefe yana ta danna wayarsa, sai dai hankalinsa yana kan su not gurin wayar da yake dannawa kawai yana pretending ne.

“Ba zai bari ba”

Dr Shuraim ya juya ya kalli Maleek ya kalleta.

“Saboda me? Ko da na lura yana azabtar da ke ko? Shiyasa kike son Ameer din da ban sani ba, na lura da hakan”

“Ya daina yanzu, baya min komai”

“Hmmm gashi ya tsare mu a nan, bari na masa magana”

Dr Shuraim ya juya ya kalli Maleek ya zai yi magana Maleek ya dago kai ya mikawa Nuwaira waya.

“Gashi Ameer ya kira za ku gaisa”

Cikin wani irin murna da farinciki marar misaltuwa Nuwaira ta karbi wayar ta mike tsaye ganin video call ne ta fice faga gurin. A nan Maleek ya mike tsaye ya kalli Dr Shuraim ya ce.

“Ba zata bi ka ba, zata zauna a nan ne har zuwa goben da zamu tafi that's the rule zaka iya tafiya idan ka gama”

Yana fadar hakan ya nufi hanyar shiga cikin hotel din ya bar shi a gurin tsaye da mamaki, a yanzu Dr Shuraim ya kara yabawa da rashin kyaun halin Maleek da kuma rashin mutuncinsa. Allah kadai ya saka Dr Shuraim tsayawa a gurin tsayawa a gurin shi ma dan kar Nuwaira ta dawo bata tararda da shi ba ta ji babu dadi, rakiyar da yayi niyar yi musu ma fasawa yayi domin ya fahimci ba jutuwa za su yi da Maleek ba. Harabar Hotel din ta fita gaba daya, tana gaisawa da Ameer a video.

“So ya kike?”

“Ba lafiya kalau ba i miss you me yasa baka zo? Gashi idan na tafi garinmu babu wanda zan sakw gani, kuma babu waya”

“Zan saka Maleek ya baki waya zaki karba?”

“A garin mu ba za a yarda ba, ba au yarda da irin wadannan abubuwan ba”

“Shikenan zamu yi bankwana daga yanzu kenan?”

“Ba zaka kira ni anjima da kuma gobe da safe ba kuma da dare?”

“If Maleek ya yarda”

“Zai yarda zan masa magana, bari na kai wayar gurin Sulem ku gaisa”

Sunan Shuraim kawai da ta ambata sai da ya ji gabansa ya fadi, ba dan kar ranta ya bace ba da ba zai gaisa da shi ba. Sai dai ba zai iya gudun abun da ta bukata ba domin ba zai jure gani bacin ranta ba.

“Okay bari na ga mutumen da ya sace zuciyar Waira”

“I'm Nuwaira now no more Waira”

Ta gyara masa

“Yeah that's right Nuwaira nice name i like it”

Ta yi dariya, sannan ta isa ta mikawa Shuraim wayar.

“Sulem gashi zaka ga Ameer din gashi nan zaku ce ina wuni wa juna”

Shuraim ya karba yana murmushi.

“Hello I'm Dr Shuraim i guess you didn't know me amman Maleek ya san ni, because Namra ta yi introducing dina gurinsu”

“As her boyfriend?”

“Yeah as her fiance i think”

Sai duk suka yi dariya Ameer ya dan ji sanyi a dansa jin cewar Shuraim yana da wadda yake so.

“Nuwaira tana yawan ba ni labarinka, I'm the first person da na tsinke mata zoben daka bata abun da tunani ya bani kai saurayinta ne so I'm little bit jealous”

Shuraim yayi dariya.

“I'm her besty ina tunanin, domin nine mutumen farko da ta fara haduwa da shi bahaushe kuma ta jidadin haduwar da shi, you don't have to be jealous bana cikin game dinki, and ta min complain cewar baka rakota ba why?”

Ameer ya dan yi shiru.

“Bana son ban kwana ne that's i hate good bye, and tace ta tsane ne”

Ta yi saurin amsawa cike da shagwabar da bata san tana yi ba.

“Aa ban ce na tsane ka ba i didn't say that”

Ameer yayi murmushi ya ce

“Ki kaiwa Maleek wayar zan yi magana da shi”

Sannan yayi sallama da su ya sauka. Shuraim ya kalleta yana reading mind da face dinta

“Me yasa kika tsane ne?”

“Ban ce haka ba fa, kawai dai bana son halinshi ne sometimes kuma yana batawa Ya Maleek ni kuma bana son a bata masa”

“Saboda shi kike so?”

Ta yi kamar bata ji ba.

“So you love Maleek yaron da bashi da kirki yanzu nan ya gama fada min maganar banza ya tafi, bayan kuma ya san yar'uwarsa nake so at least na cancanci mutuntatawa a gurinsa ko yaya ne, kuma saboda shi ba zan rake ki garinku ba gobe kuma ba zai bari ki tafi gidan mu ba, daman na fada mikin wannan yaron takura miki yake baki yarda ba”

A take ta ji ranta ya bace, akan me wani zai batawa Shuraim dinta rai, bacin ran ma kuma akanta. Ya mike tsaye ya dauko ledar dake gefensa ya aje mata a gabanta.

“Ga tsarabata nan, zan tafi. Wata rana zaki gan ni a garinku idan sun yarda ko da yake ban san ya zan fara neman baki ba.”

A nan wani sabon hira ya kaure a tsakaninsu, ta fara fada masa rules and regulations na garinsu da kuma matsalolin da take tunanin zata fuskanta idan ta koma har sai da ta bawa Shuraim tausayi.

“Me zai saka ba zaki zauna a nan ba?”

“Kirana suke yi dole sai na tafi”

“No wannan abu ne da zaki saka rayuwarki a hatsari baki bukatar yin haka”

“Garinmu ne dole na tafi ”

Ya kai hannunsa ya shafa kanta.

“I Wish zan iya yin wani abu, Allah ya sauya tunaninsu kuma tsareki”

“Ameen”

Ta sauke kanta kasa hawaye na mata zuba sannan ta dauki ledodin da wayar Maleek ta yi tsaye tana kallon Dr Shuraim har ya fice.
[8/6, 10:37 PM] 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲: 73

AMEER POV.

Peach Suite ne jikinsa sai farin gilashin da ya kara masa kyau da gwarjini. Gilashin ya cire bayan ya gama waya da Nuwaira ya aje wayar ya fisge kansa ya kwanta jikin kujerar dake juyawa ya cika bakinsa da iska ya busar.

“So this is me..”

Furtawa yayi yana murmushi da mamakin kansa yadda ya zama wani iri saboda soyayya, har yake jin kamar ba zai iya kyale Nuwaira ba ko bayan tafiyarta, yana jin zai saci kafa ya bita ne ko da kuwa kowa be sani ba, domin ya fi jin kaunarta a yanzu fiye da lokacin da take kusa da shi. Mikewa yayi tsaye ya saka hannunsa daya aljihu dayan kuma yana rike da wayarsa ya nufi kofar fita office din yana dialing number Maleek. Wannan karon voice call ba kamar dazun da yayi video ba, shi ma saboda ya ganshi online ne kuma soyayya ta hana shi girman kai ta hana shi danne zuciyarsa daga duk wani abun da yake ji akan Maleek har ya kada kansa ya kira shi, sai dai be bari Maleek yace komai ba ya fada masa zai gaisa da Nuwaira ne. Tsaye yayi a ta inda yake iya hango kasan ma'aikatan dake ya hada hada a kamfanin yana sauraren wayar dake ringing, ta yi ringing ta katse Maleek be dauka ba ya sake kira be daga ba, hakan ya saka yanke shawarar aika masa sako.

‘Pick the call’

‘Bata kusa’

Maleek ya maido masa da reply, sai ya sake aika masa sako.

‘Da kai nake son magana’

Yana aika sakon ya sake kira, Maleek yayi picking aka rasa wanda zai fara magana a cikinsu, har sai da Maleek ya gaji ya ce.

“Zan aje wayar”

“i just call na yi magana da kai akan Nuwaira, i know baka ra'ayina but please karka duba wannan, ita ma kanta ba zaka son ganinta a cikin damuwa ba, kuma ba zaka so ganin ta shiga wani yanayi bayan baka nan ba”

“Ban fahimce ka ba”

“Ban sani ba ko ta fada mana, ni dai ta fada min cewar idan ta koma kasheta za'ayi saboda abubuwan da ake ganin ta aikata, a yanzu kuma ka ga ta samu kari, kamar sanja shiga daga wadda ta saba zuwa ya mu, ga kuma addini uwa uba, wannan kadai ya isa ya saka su cutar da ita, kuma ina tunanin zata zubar da duk wani abu da ya danganci tsafi a yanzu saboda ta karbi addinin musulumci, wata kila saboda wannan ma kawai ba za su kyale ta ba, tana fada garinsu ba a karba bako amman please karka barta ta shiga garin ita kadai ya kamata ku shiga tare da ita domin tabbatar da lafiyarta, kuma ka yi magana da su ka nema mata yafiyarsu, ka musu bayanin yadda za su gansu su barta ta yi addininta, na manta ban siya mata littafin addu'ar ba please ka siya mata kamin ku tafi, na san bata iya karatun arabic ba zai fi kyau ka siya mata wanda zata karanta da tarjamal hausa ko turanci, make sure she's safe please”

Maleek be ce komai ba ya aje wayar bayan Ameer ya gama rattaba masa abubuwan da zai yi Ameer ya roki ne kawai saboda yana ganin wannan ce kadai mafitar da yake da ita, ko da Maleek ba zai yi ba ya dai fada masa idan kuma yana da niya ya tunatar da shi a yanzu. Gabansa na bugawa da karfi ya sauke wayar Nuwaira ce kawai a mind dinsa a yanzu da take kusantar garinsu ne yake tuna abubuwan da ta fada masa, ya san ko da garinsu ba haka yake ba zata samu kalubale idan ta koma musu da sabon addinin balle kuma wani gari irin garinsu zai yi wahala su iya fahimtarta har su daga mata kafa, sai a yanzu yake jin me yasa ma ya barta ta tafi? Me yasa be dange ya hana tafiyar ba? And babu wanda yayi tunani irin nasa? Ko dai yace Maleek ya dawo da ita? Anya zai yarda ma ya dawo da ita din idan ya fada? Ko dai ya kira Ummi ya fada mata? Be kama yanke shawara ba wata zuciyarta ta ce

“Ameer relax ko da ta zauna dole wata rana zata tafi, kuma babu fa'idar zaman a nan bayan kuma zaka yi ta cutuwa da kaunarta ba, idan kana kaunarta ka bi bayanta bayan tafiyarta sai ka dawo da ita da Hujja a nan ne zaka nuna tsantsar kaunar da kake mata kuma ta san kaunar gaskiya ce”

Ya amince da shawarar da zuciyarsa ta bashi, da haka ya samu sa'ida har ya koma office din ya hada abubuwan da zai hada ya fita.

***   ***    ***
Misalin karfe tara na dare Maleek yayi knocking din kofar dakin Nuwaira yana dauke hannunsa tana bude masa, carpet dinta sallah ta ya gani a bakin kofar sai dakin hawaye shakab a fuskarta.

“Shigowa zaka yi?”

Be ce mata komai ba ya saka hannu ya dauke carpet din ya shigo dakin ya karasa gurin wata kujera daya dake cikin dakin ya zauna.

“Zo na nuna miki wani abu”

Ta isa inda ta risina kasa sai ya bude littafin addu'ar ta turanci ya mika mata.

“Karanta nan na ji”

Ta kalleshi sannan ta karanta bakin abun da zata iya ta kalleshi domin bata fahimta.

“Addu'a ne tsare yinsu a kullum”

Ya tsaye sai ita ma ta mike tsaye.

“Ya Maleek ba zan iya kwana a nan ni kadai ba ai, kuma dazun na fita ban gane dakinka ba na dawo”

Ya juyo ya kalleta.

“Toh me zaki yi a dakina”

“Kwana mana ina jin tsoro a nan”

“No ba haramun ne kwana daki daya dake musulunci ya hana”

“Amman ai ina jin tsoro”

“Haka zaki yi hakuri, kuma nan akwai tsaro babu wanda zai tana ki”

Ganin zai fita ya barta ya saka ta ce.

“Zaka kira min Ameer? Please irin yadda ka kira shi dazun?”

“Dazun ma shi ya kira ba ni na kira shi ba, kuma yanzu yayi bachi”

Kawai ta bare masa baki ta fashe da kuka kamar karamar yarinya, da mamaki ya juyo ya kalleta ya rasa me zai ce mata, shi ma tashi damuwar ta isheshi zata kara masa da wata.

“Me aka yi?”

“Ba zaka kira min Ameer ba, daman Sulem ya ce baka min kirki shi ma ka masa rashin kirki, raina ya bace da ka yi fada da shi”

“Munafurci yayi min kenan? Ya ce wani abu na yi miki? So yake ki tsane ni kenan?”

“I already did...”

Ta fara fashewa da kuka, dauke kai yayi ya fice daga dakin sai ya biyo shi ta fito tana kuka, yana yi yana juyowa ya kalleta ganin da gaske kukan take kuma binsa take ya saka shi tsayawa.

“Me kike so wai? Karki tara min mutane nan fa”

“Ba zan iya kwana ni kadai ba, idan na tafi dakinka ba sai ka kwanta saman gado na kwanta kasa ba?”

“Ba zan yi hakan ba, ki koma dakinki”

Ya fada mata cikin tsawa har sai da ta sha jinin jikinta, ya juya ya fara tafiya kenan Ameer ya kira shi sai ya juyo ya aje mata wayar a kasa.

“Gashi nan ya kiraki”

Ta karasa da sauri ta dauki wayar sai dai bata ganin komai sai fuskarta.

“Ni ce ai babu wanda ya kira”

“Ki taba maballi green”

Yana fada yana tafiya, sai ta taba maballin sai ga fuskar Ameer ta fito yana ganin Nuwaira ce sai ya saki fuska yayi murmushi.

“How are you? Me kike yi ma kuka?”

“Na fadawa Ya Maleek ba zan iya kwana ni kadai ba, yace shi ba zai kwana da ni dakinsa ba, na ce ya kira min kai be yi ba kuma ina jin tsoro”

“Babu abun da zai same ki just ki yi addu'a, tafi ki kwanta yanzu”

“Ni kadai?”

“Ba gani ba? Zan jira sai kin yi bachi kamin kin kwanta zan koya miki addu'ar tsari”

“Ya Maleek ya kawo min wani littafi ma na addu'a wai”

“Yayi kyau, kin ga zaki iya kenan”

Haka yayi ta janta ta hira har ta koma dakin, ya tambayeta an kawo mata abinci ta ce an kawo mata na rana da yamma ma an kawo mata haka after Magariba ma an kawo mata. Wayar ya saka ta aje gurin kan gadonta ta rufe dakin yana hira da ita ta shiga bandaki ta yi fitsari ta fito ta hau saman gadon ta kwanta sai ya saka ta dauko littafi ta bude tana nuna masa ya saka ta karanta inda ya ji ta yi ba daidai ba sai ya gyara mata yana karantawa tana binsa har ta karanta addu'ar kwanciya bachi ta kwana tana kallonsa gaba daya ya gama burgeta domin jin take kamar yana kusa da ita ne.

“Karka kashe wayar Ameer ko da na yi bachi”

“Okay zan yi ta kallonki har ki farka hakan yayi miki?”

Ta daga masa kai.

“Ameer i didn't hate you”

Yayi mata murmushi daman ya san bata tsane shi ba, kawai dai bata mishi irin son da yake mata ne.

“I know, ki yi ta addu'ar da na koya miki har bachi ya dauke ki”

“Okay idan na koma can gobe zan yi missing dinku all”

“Ina fatar dai wani abun da zai same ki ba, kuma ba zaki jefar da addininki ba”

Kamin ta bashi amsa har bachi yayi gaba da ita, daman ga gajiyar mota ga kuma na kukan da ta yi ta rusa dazun. Kallonta yake yana murmushi bachi take amman hakan be rage komai daga kyauta ba. Ya fada mata zai yi gadinta kuma yayi sau biyu tana farkawa cikin dare sai ta ganshi idonsa biyu yana kallonta.

“Ba zaka yi bachi ba”

“Indai zan yi gadinki ki yi naki bachin cikin natsuwa da kwanciyar hankali shi ne farinciki ne, zan yi nawa da rana koma ki kwanta yanzu sallah nafila zan yi”

“Minene Sallah nafila kuma?”

Dare amman hakan be hana shi bude mata wani sashe na karatun Nafila da fa'idarta ba, sannan ya tashi ya shiga bandaki yayi alwala a lokacin duk tana kallonsa har ya fara sallah sannan bachi ya sake yin gaba da ita. Can cikin bachi tana ji yana kiran sunanta a hankali sai ta amsa ba tare da ta tashi ba.

“Tashi asuba ta yi”

“Ina jin bachi ai”

“Haka zaki daure ai, haka muke yi muma tashi ki yi sallah zan tafi masallaci yanzu”


Ta tashi zaune tana murza idon, kamin ta kalli wayar shi kuma yana kallonta a system dinsa ganin yake kamar tana kusa da shi ta cika masa System din kuma wannan ne karon farko da ya raya dare yana kallonta har garin Allah ya waye.

“Thank you Ameer”

“You're welcome ki yi addu'ar farkawa bachi mana”

Ta yi saurin janyo littafin ta bude tana dubawa yana karanta mata har ta biya.

“Good Morning”

“How was your night?”

“Fine”

“You can say Alhamdulillah instead of Fine”

“Okay”

“Good zan tafi masallaci”

Yayi mata sallama sannan ya sauka. Shi kansa bachi yana gadinta a yau ya masa rana domin yayi addu'ar kwanciya bachi a kokarinsa na koya mata, daman ya iya kawai dai ba yayi ne saboda shi dan iskan kansa ne duk wani abu na addini ne dame shi ba a baya, ba kamar yanzu ba da yake ta saituwa a hanya.

Time da aka shigo mata da abun karyawa Maleek ya shigo dakinta, a tunaninsa zai same ta cikin damuwa ko kuka ne sai ya same ta wasai not happy not sad.

“Good Morning”

“How was your night”

“Fine no Alhamdulillah”

Ta fada duk da kasancewar bata gama gwarewa a furta kalmomin larabci ba. Ya mika mata hannusa.

“My phone”

Ta nufi inda wayar take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login