Showing 183001 words to 186000 words out of 281271 words
stupid thing is idonsa sun kasa daukewa daga barin kallon hannun Waira dake cikin na Ameer ko fuskarsu be kalla ba idonsa yana kan hannayensu, Waira kam ta ma manta da wani Maleek baya son tana taba maza hankalinta ya tafi gurin abincin da ta tarar Ummi na zubawa Mahmood. Cikin karfin hali Ummi take murmushin a lokacin da ta sauke idonta akan danta Ameer, tana tsananin sonsa da son farincikinsa burinta kawai ta kyautata masa.
“Ameer ka tashi Waira ta jaka waje ko?”
“No ni na tafi da kaina, ta tarar da ni a can ne, Good Morning”
Sai a lokacin ya saki hannun Waira, sakin hannun da yayi ne yayi hankalo da Ummi ta lura cewar yana rike da hannunta suka shigo kenan! Ummi ta zagaya ta ja masa kujerar da take son ya zauna, sai ya zauna yana mata godiya.
“Thank you”
Sannan ya kalli Maleek da gayya ya ce
“Good Morning Maleek”
Ba dan Ummi tana gurin ba, Maleek ba zai amsawa Ameer ba, ba kuma dan komai ba sai dan ganinsa da yayi tare da Waira wani tukukin bakin ciki ke turnikeshi. Amsawar ma da kai yayi masa sannan ya kalli Waira yana jin kamar ya kamata ya fara dukata har sai hannayen da ta rumgume Ameer da su karye. Mahmoud kam da kansa ya mikawa Ameer gaisuwa sannan ya shiga gaba da cin abincinsa. A take Ummi ta fara zuba masa abun da Hanne ta girka, daman Maleek da Mahmood tuni a kusa gamawa da shi. Da wata fuska mai kamar munafurci Waira ta gaishe da Maleek kai tsaye ya sauke kansa kasa yayi mata banza, Mahmood kuma ya dago ya amsa yana tsokanarta.
“Sai yanzu kika gan mu? Ko idonki be gani dazun ne?”
“Yana gani mana, ai na jira kowa ya gama ne”
Maleek yaja kujerarsa baya ya mike tsaye ya fice daga falon zuwa waje domin baya jin shiga daki, kuma baya son zama a inda idanuwansa za su ga abun takaici da haushi. Waira ta ja kujera zata zauna Ummi ta dakatar da ita.
“Kin yi brush? Kuma shoes din da kike yawo da shi a falo, da shi kika fita? Kuma still kika sake dawowa da shi? Wannan wane kalar kazanta ne Waira? Tashi ki cire shoe's din can waje”
Ta wara ido, ita kam ba ma ta talkamin da Ummi ta yi mata magana take ba, tunawa ta yi da Ameer ya bar sarewarsa da wayarsa a inda suka zauna dazun..
“Ka manta waya da sarewa a can, bari na dauko sai maka”
“Oh haka fa”
“Toh idan kin dauko ki bar talkamin a waje karki shigo da su”
Ummi ta fada sai ta amsa mata da kai sannan ta juya ta wuce daga falon, hankali na gurin abun da take son daukowa dan haka bata lura da Maleek dake gefen entrance din ba ta hauka abun da a dan karamin stairs dake gurin ta nufi Garden, dukawa tai ta dauki wayar Ameer da sarewa sai da ta gwada busa sarewar sannan ta juyo tana murmushi sai jin ta yi ta bugi mutum, tana daga kai ta yi arba da Maleek yana kallonta fuska babu annuri, kamar bakin hadari ta dan yi baya kadan gabanta na faduwa.
“Wato ke saboda kin cika har kin batse, har ke da kanki kike bude hannu ki rumgume Ameer ko?”
Ta sauke idonta tana mamakin yadda yake damuwa da abun da ba laifi ba ne a gurinta, idan ma addini ya hana ita ai ba addinin take ba, shi kuma Ameer da yake yi be yi complain ba sai shi dan kawai ya tsaneta. Ta yi gefe kamar zata kauce sai ya sha gabanta
“Ina magana kina tafiya? Ina zaki je? Kin raina hankalin mutane ko?”
Yanzu kuma tsoron magana take kar ta karawa kanta laifi a gurinta, dan haka ta yi shiru ta marairaice fuska tana shafa sarewar dake hannunta. Bakinciki fa fushi zuciya na irin wanda ya kasa controlling kansa ya saka shi fisge sarewar ya kefar kusa da pool. Ta bude ido ta saki baki tana mamaki.
“Ta Ameer ce fa?”
“Ameer din miye tsakaninki da shi, ban gargade ki akan tana jikinki da yake ba?”
Cikin bacin rai da ya fi kama da shagwaba ta yi kokarin bashi amsar abun da ya tambaya
“Amman kai ai....ai... Kana taba ni har a nan ma, kuma kana shafawa min jiya ba har kiss ka yi min ba, amman idan Ameer ya taba ni sai ka yi fada saboda mu baka son mu”
Ta juya tana kara bata fuska ta nufi inda sarewar take. With shock ya bita da kallo kamar wani sakare ya san ko rantsuwa yayi ba zai yi kaffaraba Ameer ne ya saka mata ta fadi haka, domin shi dai be san yayi mata haka ba, Allah ma ya kiyaye ya ji me a jikinta? Shi ko so zai yi idan ma Allah ya kaddara masa son a mace zai yi babbar mace mai amsa sunan mace ba ita ba. Shi da rika hannun mace ma aiki ne a gurinsa zata masa kazafin ya taba ta. Takawa yayi ya isa inda take tana goge sarewar a jikin kayan bachinta.
“Indai Ameer ya saka miki fadin haka, to be samu sa'a ba, domin ni kowa ya san ba halina ba ne, ko da halina ne ba zan yi ke ba, Allah na tuba balle kuma ba abun da na saba yi ba ne, babu wanda zaki fadawa haka ya yarda”
Watsa masa wani kallo mai kama da harara.
“Ni ba wanda ya tsara min, ai ka yi ne na gani, har ina bachi ka fara taba ni ka dauka bachi na mai nauyi ne sai gashi na farka kuma yi min kiss a front head ya fita”
Rage ido yayi yana kallonta, this time around ya gane dai mafarki ta yi wata kila rakiyar da yayi mata da dare ta shiga dakinta bayan shiga bachi ya dauketa ta yi mafarki sai ta dauka kamar a zahiri ne hakan ya faru.
“Ko ma dai minene na fada miki karki sake hada jikinki da na Ameer, karki kuskura ki sake because wannan lokacin ba wasa nake ba, kuma sai na fadawa Ummi abun da na ga kin yi”
Yana kaiwa karshe ya saka hannunsa ha hankadata sai ta tafi suuuuu tana kara zuwa cikin Swimming pool, tare da fada da wayar da sarewar tana kokawa da ruwan domin bata taba fadawa a ruwa haka ba, ban da zuwa gidan Ummi ma da ta waye take wanka akai akai, bata san ta ga ruwa ko ruwa ya ga jikinta ba, dan haka bata hada hanya da ruwa ta iya hawan tsaunuka da bishiyoyi amman ban da shiga ruwa saboda rashin son wanka. Ya juya zai yi tafiyarsa sai ya ga tana yin kasa yadda take fisge fisge ma kadai ya isa ya saka shi gane bata iya swim ba, ga muryar da ta bude domin neman ceto idan ta je magana sai ruwan ya wuce mata.
“Fito mana kina wani abu kamar baki iya ruwa ba, I'm not like Ameer balle ki raina min hankali little girl like you...”
Yana fadar haka, kamar ya ce mata kara, sai ruwan ya hadeta gaba daya ta yi kasa. Ba tare da tsayawa tunanin komai ba, without any thinking ya yayi tsalle ya fada ruwan domin cetonta...
TEAM MALEEK.
TEAM AMEER
ko da yake Maleek ya ce me zai yi da ita. Amman dai ni dai ina hango wani abu a zuciyar Maleek Allah yasa ku ma kuna hangowa 🤣
[7/22, 10:47 PM] My S Line: 60
Da sauri ya fito da ita daga cikin ruwan a aje abakin gabar yana kallonta. Kamar wanda dabara ta bacewa haka gurfana a gurin yana kallonta not knowing what to do, halin da ya ganta a ciki ya mugun rikita shi yadda take ta tari tana bude baki ya saka masa tausayinta, idonta har rine da ja alamar ruwa ya shiga cikin idon. Gashin kanta ya jike shakaf. Cikin karfi hali ta mike tsaye tana ta tarin sai yayi saurin mikewa tsaye shi ma yana kallonta, a lokacin ne kuka ya zo mata, domin a yanzu ta tabbatar Maleek makiyinya ne nakarshe da baya bukatar ganin rayuwarta ko da wasa.
“I'm sorry ban san cewa baki iya ruwa ba... Da ba zan miki haka ba”
Ta kalleshi idonta na rawa ta raba gefensa zata wuce.
“Karki shiga falon a haka mana, bari na sama miki wani abu”
Ya fada yana dauke idonsa daga barin kallon jikinta, domin ruwan da ta shiga ya saka kayan bachi kama jikinta abun ka da silk material, bata saurareshi ba ta cira kafa ta fara takawa tana fadin.
“Idan baka son ganina a gidanku zan iya tafiya wani gurin amman ba sai ka kashe ni ba”
“Ban yi domin na kashe ki ba, kawai dai raina ya bace ne”
Ya biyo bayanta sai dai yayi iya kokarin da zai yi ya hana idonsa kallon abun da ba halalinsa ba, har suka fito daga Garden din, sai da ta kusa isa kofar falon sannan gabansa ya koma faduwa saboda abun da Ummi zata ce bayan ta ja masa kunne akan dauke idonsa daga ganin alakar Waira da Ameer.
“Waira can you please tell Ummi ruwa kika fada na je dauko ki?”
Yana kokarin cire rigarsa ya fadi haka, sai ta juyo ta kalleshi a kokarin na mamakin yadda yake son boye abun da yayi ashe ya san ba abu ne mai kyau ba kenan kokarin kasheta. Sai dai ta manta da duk wani tunani da take a lokacin da ta yi arba da kirjinsa dake dauke da tarin kwarzantaka da kirar cikaken namiji matashi mai jini a jiki kamar shi.
“She already warned me akan ki, zata ce ban ji maganar ba kenan”
Magana yake da baki, amman idonta na gurin hallitar da Allah yayi masa mai daukar hankali da duk wata natsuwa ta ya mace. Slowly ya sauke kansa ya kalli kirjinsa sannan ya kalleta.
“What?”
Kamar an mata shokin haka ta dawo hayyacin har wani fisgar numfashi take, kamar wanda aka jefowa shi daga sama. Ta juya jiki babu karfi ta cigaba da tafiyarta, bata san wani abu sha'awar namiji ba, bata san soyayya ba, bata san cikaken da rago ko mai rangwame a maza ba, sai dai ta san kirjin Maleek da ta gani a yau yana daga wani bangare da ya burgeta na shi. Ta dora hannunta ta tura kofar falon ta shiga, Maleek ya bi bayanta bayan ya sarkafa rigarsa a kafada. Ameer dake rike da Spoon ya dago ya kalleta, kamin idonsa su sauka a gurin Maleek dake tsaye a gefenta babu riga a jikinsa shi ma kuma jike yake kamar ita, wani irin kishi ne ya fisge shi.
“Wanka kuka yi?”
Ya furta kai tsaye, furucin da ya bawa Maleek haushi taya zai yi wanka da karamar yarinyar kamar Waira, ko ba ita ba shi sam ba zai iya rayuwar karya ko ta aure da mata ba, ya san zai iya zama a inuwa daya da su a yanzu da rayuwarsa ta sauya amman ba a irin inuwar aure ko ta zina ba. Ummi ta kalli Ameer da mamaki Mahmood ma haka kana kallonsa ka san da gayya yayi maganar fuskarsa ta munana alamar ganinsu haka be masa dadi ba.
“Ruwa na fada sai Ya Maleek ya cire ni”
Maleek ya kalleta da sauri never thought zata rufa masa asiri kamar yadda ya roka, wannan ne karo na farko da ta burgeshi, wani abu ya karu a zuciyarsa bayan tausayinta da yake. Ameer ya aje spoon din hannunsa ya mike tsaye yayi kanta, Maleek kuma ya kama hanyar stairs be ko kula da Ameer din ba.
“Taya zaki fada ruwa? Gurin da na aje wayata da da sarewata akwai tazara mai yawa a tsakani fada min yadda aka yi kika kai gurin ruwan?”
Ta yi shiru tana kallonsa a yanzu kuma bata san kalar karyar da zata yi tace shi ya kai ta gurin har ta fada ba. Ameer ya tsaya kanta.
“Idan ma ruwa kika fada ba zaki iya fitowa ba ne sai an dauko ki?”
“Ni ban taba shiga ruwa ba”
Ta fada a shagwabe tana son yin kuka.
“Ina wayar take? Ina sarewar?”
Sai a lokacin ta tuna da wata waya da sarewa da ta saki a lokacin da ta ji ta a gabar mutuwa.
“Suna ruwa”
Kallonta yake so yake yayi mata fada kuma baya son ta yi fushi da shi, sai dai sam yanayin da ya ganta tufafin bachinta sun kama jikinta, ga kuma Maleek da yake ganin ya ganta ya bakanta masa rai matuka, wani irin kishi yake ji kuma wannan ne karon farko da yake jin haka, domin ya zauna da Nimra be taba jin wani abu na kishi akanta ba ko sau daya, haka ma yayi zama da Angel ita ma baya jin kishin komai akanta, kawai dai baya son ta hada tarayyarsa da wasu mazan ne saboda yana kyamarsu, kuma yana jin ya fi kowa, but Waira is different from them, komai da yake jin a kanta ya banbanta da yadda ya saba jinsa komai about ita is real da gaske son ta yake kuma baya son ganin kowa ya rabe ta.
“Waira shiga ciki ki canja ki sauko ki ci abinci, maybe bata iya ruwan ba ne, kuma kasan Maleek ba zai ga tana kokarin mutuwa ba ya kyaleta”
Ya juyo ya kalli Ummi cikin damuwardata kasa boyuwa fuskarsa.
“Ummi ta ya za'a ce bata iya ruwa ba? Ruwan ba mai yawa ba kamar na gidan nan? Kuma idan har taimaka mata zai yi ai hannu ya kamata ya mika mata ta riko ya fito da ita ba wai su shiga ruwan ba?”
Ummi ta mike tsaye ta nufo inda suke tsaye.
“Ameer Waira ba a gidan ta tashi ba, ba lallai ne ace ta iya kalar rayuwar da kuka ba, zuwanta gidan nan ma if i can remember ko ruwa bata son ya taba jikinta, maybe shi ya saka bata iya ruwa ba”
“I hope so”
Ya fada sannan ya dauke kansa ya nufi stairs sai kuma ya juyo ya kalli Waira dake takowa a hankali.
“I'm sorry, let me go get my phone”
Kallonsa kawai ta yi ta sauke idonta kasa shi ya nufi kofar fita Waira kuma ta nufi stairs...
*** *** ***
Tun daga Ranar sai Ameer ya daukarwa kansa wani duty, kullum shi zai kai Waira School ya dawo da ita, hw use that opportunity yayi ta fada mata abubuwan da bata sani ba akan addinin musulumci, idan sun dawo kuma yayi ta dora mata da abubuwan da ya sani kasancewar mai yi mata lesson ya daina zuwa a yanzu, sai ya zamana da yamma bata aikin komai sai sauraren Ameer dake karantar da ita yana mata searching din wasu abubuwa, sannu sannu har ta kai Waira zata dauki remote da kanta ta kama peace tv ta zauna tana kallon program din da ake, idan kuma ta dauki wayar Ummi ko Ameer ta shiga ta tana kallon abubuwa, wani zubin kuma game take da wayar. A dan zaman da Ameer yayi a gidan na wata biyu da kwana goma sha uku shakuwa da kyakkyawar alaka mai karfi ta kara shiga tsakaninsa da Waira, idan bata cikin gidan har bata jindadi, ta kan dauke masa kai ne kawai idan Maleek yana zaune a inda suke zaune, kamar falo ko dinning, shi kan shi ya lura bata sakewa idan Maleek na gurin duk yadda yake mata magana ko ya tsokane ta iyakacinta murmushi. Duk tsawon lokacin nan babu daren da Maleek baya shigo dakinta Either ya rumgume ta ko kuma ta taba jikinta, tun abun na damuwarta har ta soma sabawa, some times zata jira ma har sai ya shigo ya fita sannan ta kwanta, domin bata jin ta jindadin sai ta yi bachi ya tasheta, a tsawon lokacin da yake shigo dakinta be taba ce mata komai ba, sai dai kamin ta saba ta gwada buge masa hannu da fada masa bata so, sai dai ganin ba zai daina ba ya saka dole ta hakura. A tsawon lokacin ta kame baki bata fadawa kowa ba, no matter how ta yi unkurin fadar sai ta kasa, some times tana tunanin Maleek yana mata haka ne saboda ya hurar da ita saboda biyewa Ameer da take shi kuma baya son haka domin kullum cikin yi mata gargadi yake, ta hanyar fada mata da baki ko kuma da ido.
Today is Sunday Waira na zaune gefen Ummi rumgume da baby Rabbit dinta sai shafa shi take tana wasa da kunnensa, Ummi kuma hankalinta yana gurin wayar da take da yar'uwarta Maryam.
“Ni dai ina tunanin kamar bata hakuri ba ne, shiyasa ta ce bata bukatar komai, ko abinci aka kai mata na lura indai daga gurina aka tafi da shi haka za a dawo da shi bata taba ba, idan kuma naje dubata da zarar mun gaisa na yi mata ya jiki ta amsa ba zata sake cewa komai ba, amsawar ma kamar an mata dole haka zata ta yi, sannan duk lokacin da Ameer ya dawo indai ya fara zuwa gidanta sannan ya dawo gidan nan ina ganin canji a fuskarsa”
“Zahra kin fi kowa san wacece Hajiya, tun kamin ki auri Deen har kika aure bayan rasuwar da auren da kika yi babu abun da baki gani ba na halinta. Dan haka ki saka mata ido a yanzu ki bita a yadda take son tafiya”
Ummi ta mike tsaye tana sauke ajiyar zuciya.
“Ina burin kyautatawa kowa Ya Maryam, ina son na kyautata mata, na san shi Baba ba zan iya samun yafiyarsa ba, amman ita ai tana raye yafiyarta nake son na nema a yanzu, ba zan iya da hakkin mutane da yawa ba”
“Idan kina son neman yafiyarta sai ki bi ta hanyar ďanki Ameer mana, tun da shi kun samu kyakkyawar fahimta da shi”
“Bana son na saka shi cikin matsala ta ne, burina kawai na kyautata mata irin kyautatawar da zata mantar da ita abun da na yi mata har ta furta cewar ta yafe min, amman ta ki ba ni wannan damar, yanzu kin ga sallamarta za ayi a asibiti na ce zan ba su gurin da za su zauna mai kyau, saboda Ameer ya fada min inda suke