Showing 234001 words to 237000 words out of 281271 words
shi, me yake bukata daga garemu? Idan rakiya yayi toh zai iya komawa mun gode da zuwansa, amman ba zamu zauna da butulu irinki ba, idan muka yi kora ba ma bukatar dawowarta a cikin danginmu, a da mun yanke shawarar kasheki, sai dai Eid ya bauta miki ya jure duk wata kalar azabar mu saboda mu barki ki rayu, ta karkashin kasa mun yi ta aika miki da mutuwa har a daren jiya, abun mamaki kin aje al'adarmu da addininmu saboda kin ga na wadanda suka fi mu karfi. Tabbas yaro baka shigo garin mu ba sai da ka shirya, domin wani be taba gwada karya mana dokoki haka ya kwashe lafiya ba, ba mu tana tsarrafa tsafi irin wanda muka yi a daren jiya ba, amman komai ya kasa samunka a kusa da dakin ma aljannunmu ba su kusanta ba, a tare da kai mun ga aljanna mai irin tsafinka mun saka wadanda suka fita karfi da iko sub rabata da kai a tunaninmu ita take baka kariya, da muka sake aika tsafi sai ya dawo mana, tun farkon shigowar muke ta jefarka amman jifar ta kasa isa a inda kake, madubin tsafinmu ya kasa ganin fuskarka, jama'ar da ake turawa su kiraka kana saka musu fargaba da tsoro, a yanzu ba ma jayya da kai mu dai ba ma shiga gonar kowa kuma ba ma son a shiga gonar mu, Eid ya fada min tun jiya ka dage sai ka ga Sarki zaka tafi, fadi bukatarka Sarki zai sallame ka ka yi tafiyarka”
Sarkin ne da kansa yake fada Eid na fassara masa dan dolensa, mamaki da jindadi da kauna ya hana Nuwaira cewa komai sai kallon Maleek dake cike da burgewa.
“Alhamdulillah, hakika duk wanda ya dogara ga Allah shi kadai Allah ya isar masa, ni bana tsafi van tana tsafi ba, kuma ban taba sanin yadda ake yinsa ba kuma bana fatar yinsa, ni dai na san ina bautar Allah ba tare da shirka ba, sannan ina karanta ayoyi da addu'o'in kariya, a jiya ma na kwana ina karanta suratul Bakara, kuma duk wanda yake karanta iya da ayatul kursiyu Allah ya turo mala'ikunsa su yi gadin Mutum ne, a inda mala'ika yake kuma aljani be isa ya raba gurin ba, muka karanta ta a gidanmu shiyasa kuka aika tsafinku be isa a garemu, domin idan aka karanta sau daya a wata tana tsare gida ta hana duk wani abu mai cutarwa rabar gidan har wani wata, saboda wannan ni ba tsafi nake ba da za ku surfafa bincike da za ku fahimci wannan addini ne ba tsafi ba, kuma ina fatar wata rana za su aje na mu addinin da al'adar ku karbi cigaban da duniya ta zo da shi haka ma ku rumgumi musulunci ku watsar da tsafinku”
Cikin alfaharin da jindadi Maleek yake fada ana fassarawa Sarkin da yarensa, har sai da ya kai karshe sannan Eid ya ce.
“Ba mu bukaci ka tallata mana addininka ko al'adarka ba, ka bar mu da na mu, kai ma ka rike naka, Sarki yana tambayar dalilin ganinsa da kake son yi, kuma ina ganin ka samu abun da kake bukata zaka iya tafiya”
“Aa ban fadi bukatata ba tukuna, dan haka ba zan bar garin ba sai na isar da abun da ya kawo ni”
Eid yaja numfashi da karfi da bakinciki sannan ya fadawa Sarki abun da Maleek ya fada.
“Tuk rid jaur bhakar suuf hutk garfha ifftuk galink galink ket”
Eid ya juya ya fassarawa Maleek.
“Ya fadi bukatarsa ba ma son zamansa a cikin garinmu”
“Ina neman auren yarku Nuwaira ne, saboda a yanzu irin addini take yi, ta saba da irin al'adata da kuma dangina, ina tunanin bata da bukatar zama a cikin garin nan, domin ba zata canja addini ba ba zata sake komawa addininku ba, kuma ba zata karfi kujerar tsafin da kuke son bata ba, idan har kuka yarda kuka ba ni aurenta zan dauke ta mu bar garin nan da ita yau din nan ba sai gobe ba, kuma ba za su sake ganinmu ba, ina tunani bata da amfani a gareku a yanzu saboda ta karya dokokinku kuma kun yafe ta kamar yadda ka fada”
Eid ya mike tsaye ya bar kujerar da yake zaune ya nufo inda Maleek yake cikin zafin nama, kamin ya karasa Sarkin ya daka masa tsawa.
“Karka kuskura kai kanka ga halaka, kana ganin wannan matashin ka san sai da ya shirya sannan ya shigo garin nan, neman yake a taba shi ya janyo mana fitina, fassara min me yake da bukata”
Sai da Eid yayi da gaske ya yaki zuciyarsa sannan ya iya fadawa Sarki abun da Maleek yake da bukata, daga baya ya jadadda masa da cewar ba za su aminta da haka ba, domin wannan ya zama cin fuska, kuma saboda ta karya dokokinsu har sun yi fushi da ita sun yafe ta ba shi yake nufin a barta ta aure wani bare ba. Sarki ya daga masa hannu.
“Yanke hukunci ba a hannunka yake ba Eid karka zafafa, kuma kar bacin rai ko soyayya ta saka ka manta da ka'idodi da dokikin garin nan, idan muka yafe mutum muna nufin cire hannayenmu daga duk wani lamari nasa, ko da kuwa zai mutu ne, kuma ba zamu tarbe shi ba ko da zai bukaci dawowa a garemu, ba kuma zai aura daga garemu ba.
Kaka ya taba fada min cewar kamin a haife ni, wasu mutane biyu sun taba karya mana doka, ya saka aka koresu daga garin nan, har yanzu babu ruwanmu da iyalansu, ta farko daga cikin gari take, lokacin da dadin tsafi yayi mata yawa sai ta zurfafa ta dauki maita, mu kuma ba mu yarda da maita ba, duk wani tsafi bayan wanda muka gada gurin iyayenmu ba mu yarda da shi ba, sanadin hakan muka kora Iya ta bi duniya, har yau babu ruwanmu da zuri'arta, bayan ita kuma Wasim ɗa daga masarautar nan, soyayya ta dibeshi kamar yadda take son dibarka a yanzu, ya karya mana dokoki ya shigo mana da bare, kuma ya fitar da ita ba tare da izinin kakanmu ba, daga karshe ya zabi addininsu da al'adarsa ya watsar da ta mu, hakan ya saka shi ma muka yafe shi, shi ma babu ruwanmu da shi da zuri'arsa, dan haka karka yi kuskure biyewa son zuciya ta kai ka ta baro”
“Duk wata azabtarwa da wahala da na jurewa sha a gurinku, tsawon lokacin da Waira ta dauka bata kusa, na jure ne saboda ina sonta ban taba fadawa kowa wannan maganar ba amman zan fade ta a cikin fadar nan, na san kowa ya lura da hakan, na raine ta tun tana karama har ta fara wayo, rana daya kuma sai wani ya dauke min ita?”
Wani daga cikin manyan masarauta da suke gurin ya mike tsaye ya isa gurin da Eid yake tsaye ya dafa shi.
“Kwantar da hankalinka Jarumi na, akwai mata da yawa a cikin garinmu da suke sonka, akwai matan da suka fi Waira kyau da komai ciki da wajen masarautar nan, ka rufe idonka daga ganin Waira ka bude idonka a garesu cikin kankanen lokaci za a gama da su, karka yarda zuciya ta deba ka gujewa umarnin masarautar nan, domin wannan matashin ba zai yarda ya barka maka Waira ba, ko da kuwa ka yarda ka koma cikin kalar tsafinsa ne, idan kuma muka hana masa ita zai iya gwada jayayya da mu”
“Toh a bar mu mu kara mana, sai a gane waye jarumi”
Ya fada da kakkausar murya yana tabe baki kamar zai yagashi.
“Ba mu taba gwada yaki ba, kuma ba zamu gwada saboda wata korariya a garinmu ba, ban yi tunanin karfin tsafi zai yi tasiri a gareshi ba, ko da ya ce ba zai aureta ba, ba samu yarda ta aura daga garemu ba wannan shine magana ta karshe”
Eid da duk sauran mutanen da suke fadar suka risnar da kai domin nuna biyayya ga Umarnin Sarkin da ba a musawa. Eid ya dago yana kallon Maleek fuska kamar an aiko masa da mutuwa, zuciya kamar bakin maciji dake cike da dafi, ya fice daga fadar yana hararar Maleek yana huci kamar zai fitar da hayaki. Duk wani abun da ake fada Maleek be ji ba, domin da yarensu suke maganar, Waira kuma jinta da ganinta tunaninta mamakinta zuciyarta da ruhinta gaba daya sun tafi gurin mutumen da take kira da yayanta wato Ya Maleek. Furucinsa na cewa yana son aurenta da jarumtar da ya nuna akanta sadaukarwa neman kareta sassauta ra'ayinsa da nema mata farinciki da yanci wani abu da ya kai ta rubuta a dutsen da ba goge zane da alkalamin zinari. Hawaye take irin hawayen da ba zata iya fadar na minene ba a yanzu, na farincikin abun da Maleek yayi mata ne ko kuma na samun yancinta ko kuma na komawa da zata yi gurin matar da ta zame mata uwa? Ko kuma dai na fasa kasheta da aka yi ne? Wata kila kuma na tsafin da suka ce sun yi ta aikawa Maleek ne be same shi ba.
“Nuwaira...”
Kamar wadda aka jefowa numfashi daga sama haka ta zabura ta dawo hayyacinta, sai ta lumshe ido tana jin ba a taba kiran sunanta da dadi kamar yadda Maleek ya kirata a yau ba. Rufe idon da ta yi sai ya saka shi tunanin ko bata ra'ayi ne musamman ma da yayi arba da hawayen dake zuba a idonta gashi tun da ya furta maganar take kallonsa ta kasa cewa komai kuma ta kasa dauke idonta daga gareshi.
“Ko baki so ne? Karki damu, na yi hakan ne saboda na sama miki hanyar fita daga garin nan, idan sun amince sun ba ni aurenki da zarar mun fita ba aurenki zan yi ba, za a miki aure ne best on zabinki”
Rashin Eid a fadar da zai iya fassara musu abun da Maleek yake fada, ya saka Sarkin amfanin da nasa baiwar ta tsafi ya yi communicating da aljannunsa suka fassara masa abun da Maleek ya fada, hakan kuma ba karamin dadi yayi masa, domin ya fahimci Maleek ba gaske yake son Waira ba, hakan na nufin zai fara mata yi mata butulci da zarar sun bar garin kenan, kuma hakan ya nuna Waira bata son shi, a kokarin Sarki na bakanta musu ya kalli na hannun damansa ya ce.
“A fadawa Dardu ya tada busa ya hura wuta, mata su fara nika ganyen za a daura aurensu a yanzu”
Nuwaira ta bude ido da sauri ta kalli Sarki domin daga ita sai jama'ar garin suka iya jin abun da Sarki yake fada ban da Maleek. Sarki ya kalleta yana tana tauna hakora ya ce.
“Zamu aura miki shi, kuma zamu cire duk wani tsafi da kariya ta mu da take jikinki yanzu nan, kuma duk wani abun da zai faru ko ya biyo baya karki neme mu, babu mu babu ke da zuri'arki”
Kasa cewa komai ta yi sai har lokacin hawayen ba su daina sauko mata ba. [8/9, 8:09 PM] 🦋-🦋: 74
“Ki fada masa ya cire kansa daga lamarinki in ba haka ba zai yi nadama”
Maleek yake nunawa amman da Nuwaira yake magana da yaren garinsu.
“Ba zaka cutar da shi ba Eid kai dan'uwa ne a gurina, mai matukar son abun da nake kauna, mai son abun da nake so, mai gudun bacin raina da kukana? Meya same ka ka canja? Kalamanka da kamanin da nake gani a fuskarka ba su ne na Eid da na tafi na bari ba, wannan mutumen shi da iyayensa tarbe ni, sun saka hannu biyu sun rumgume ni, ba dan sun san daga inda na fito ba sai dan karamci da sanin ya kamata irin na su, sun nuna min kauna, a gurinsu na san abun da ake kira da tsabta da kauna da soyayya, a gurinsu na san me iyali yake nufi, a lokacin da zuwa gida ya kama ni, suka sako ni a mota suka rokoni har kofar garinmu akan me kake tunanin idan ka nuna masa tsaya zan ji dadi? A wane hali zan bari ka cutar da shi? Da wace Hujja zaka zabe ni ka bar shi?”
Eid ya dauke hannunsa yana kallon Nuwaira dake magana taba zubar da hawaye. Ta sauke kanta kasa ta kalli hannun Maleek dake rike da nata, sannan ta kalleshi.
“A nan garinmu ne Ya Maleek zan rayu cikin aminci da yardar Ubangijin Kaaba”
“Hakan ba zai gamsar da ni ba Nuwaira, sai na ga halin da zaki kasance kuma sai na yi magana da Sarkinku”
Cikin wata kalar murya mai kamar ta zaki Eid ya zabuwa Maleek har jijiyoyin dake jikinsa suna bayyana.
“Waye kai da zaka ce zaka ga sarki? Mutanen dake cikin fadar sarkin mu ba baka isa ka gani ba balle Sarkin da kansa, duk wani abun da ka yi ma Nuwaira kai da iyalinka mun gode zaka iya tafiya”
Eid ya hade hannun biyu yayi masa godiya har da sirinawa sannan ya nuna masa hanyar da suka fito.
“Ban taba tirjiya ko musayar yawu da kafewa akan abu daya ba sai yau, idan da tsafi kuke taka ni ina takama da wanda yake da ikon akan komai da kowa, and mark my words sai na yi magana da Sarkinku zan tafi sai na tabbatar Nuwaira tana cikin aminci, idan har zan iya barin wani abu ya same ni to zan iya barin Nuwaira ta cutu kenan”
Sai a lokacin yan rakisarsa suka saka baki domin sun lura a yanzu ya wuce gona da iri, su dai rakiya suka zo kuma sun kawo yarinyar a gidansu akan wace hujja zai nace dole sai ya shiga cikin garin.
“Am Malam Maleek ko? Akwai maganar da nake son yi da kai dan Allah dan zo ka ji”
Maleek baya son disga mutumen a cikin mutane hakan ya saka binsa gefe yana janye da hannun Nuwaira. A lokacin da suka koma gefen sai mutumen ya kasa cewa komai saboda ganin yana rike da hannun Nuwaira.
“Da ka dan sake ta sai mu yi magana”
Maleek ya kalleta ji yake kamar idan ya sake ta Eid ko wani daga cikin mutanen da suke tsaye bakin kofar garin zai iya yin tsafi ko kuma su ja Nuwaira da karfi su tafi da ita su bar shi a gurin.
“Zaka iya fadin maganarka”
Mutumen ta sake kallon Nuwaira sannan ya kalli Maleek.
“Wato ni abun da nake gani zai fi zame mana masalaha shi ne ka kyale yarinyar nan ta tafi gurin danginta, bukata dai a kawota gurinsu kuma gashi an yi, karka daukarka kanka abun da ba zaka iya ba, ni a yadda na fahimta shi wannan dan'uwanta ne ko kuma da dukan alamu ba shi da kyau hali”
“Haka ne office zaku iya tafiyarku daga nan, daman an dauko ku ne saboda ku rakomu ku tabbatar mun isa lafiya, ina ganin aikinku ya kare daga nan za su iya tafiya”
Office ya tsaya kallon Maleek baki sake da mamaki.
“Ranka ya dade ka taba jin labarin mutanen nan kuwa? Wallahi ba su ragawa kowa kuma dokokinsu ne a haka ya kamata mu tsaya bakin iyakarmu kar mu wuce gona da iri, wannan abun da kake kokarin yi zaka jefa kanka a matsala ne, ba film muke ba, ko a film indiawa suke wannan wautar ba hausawa ba”
“Office karka bata min rai, dan Allah ka dauki mutanenka ku tafi, ba wani abu nake kokarin nunawa na jarumta ba, na fada cewar ba zan tafi ba sai na yi magana da sarkinsu kuma sai na tabbatar Nuwaira zata rayu cikin aminci that's it”
Cikin kakkausan lafazi Maleek yake fadar hakan still yana rike da hannun Nuwaira. Ganin da gaske Maleek yake ya saka office nufar yan'uwansa ya ja su gefe domin tattaunawa. Nuwaira ta kalli Maleek dake rike da hannunta gam da dukanin karfinsa ta ce.
“Ya Maleek zan zauna lafiya na maka alkawari babu abun da zai same ni, please ka bi abun da suka fada maka ka tafi gida, idan Ummi ko Abiey suka ji abun da kake kokarin yi ba za su jidadi ba”
“Babu ruwanki a nan karki sake magana”
Ya fisgi hannunta har tana lilo ya nufi gurin motarsa ya bude ya sakata ciki ya rufe motar. Ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya yi dialing number Abiey a take kiran ya yanke yana muna masa no network, su ma police din kokarin kira suke network dinsu ya yanke, hakan kuma ba karamin daga musu hankali yayi ba gashi wanda yayi jagorancin zuwa gurin ya nuna musu hanya ya kara fada musu yadda garin da jama'ar garin suke. Gashi kuma bakin shiga garin ma kadai babu network ina ga ciki kuma? A haka kuma Maleek yake son su yi risking rayuwarsu saboda rai daya, ran da za su iya kashe su ita ba su kasheta ba, waya sani ma ko plan ne. Dukansu zuciyarsu bata natsu da biyewa Maleek su shiga cikin garin ba, saboda haka suka yanke shawarar juyawa su koma tare da Maleek din da Nuwaira har sai an sake shawara, domin ba za su bar Maleek ya shiga garin ba, ba kuma zai yiyu su tafi su bar shi ba, kamar yadda ba za su yarda su shiga cikin garin ba.
“Ranka ya dade, ina tunanin abun da ya fi, mu tattara gaba dayanmu mu koma gida, albashi idan aka yanke shawarar yadda ya kamata ayi sai a aiwatar daga baya, idan ma su za su zo su dauke ko kuma mu sake kawota ka ga dai sai mu san irin shirin da zamu yi”
Maleek ya dan yi jimmm alamar tunani sannan ya juya ya kalli Nuwaira dake cikin motar tana kallonsa.
“Hakan yayi bari na yi magana da ita”
Ya zagaya ya bude motar ya shiga sai ya bar kofar a bude.
“Mun yanke shawarar zamu koma tare da ke, daga baya sai mu yi tunanin abun da ya dace mu yi”
“Ba zan iya komawa ba Ya Maleek kuma idan ka ce zaka tafi da ni Eid ba zai bari ba, zai iya cutar da kai dan Allah ka tafi”
“Ki daina jin tsoro babu abun da zai iya min, ina da addu'a akwai tsari a tare da ni