Showing 54001 words to 57000 words out of 281271 words

Chapter 19 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1264

za'ayi da ita ya fi komai tsaya mata a rai, Maimoon ta kawo kayan sai Hajiya ta rikata ta yi mata irin na babba da yaro ta saka kanta a tsakankanin kafafuwanta Maimoon na zuba shampoo tana murza mata gashin dake a damke ana wankewa sau daya ta yi amfani da shampoo amman duk yawansa sai daya kare akan Waira, saboda dattin da kanta yake dauke da shi da kuma yawansa domin ya sauko har yama taba tile, duk yadda ta so ta kwaci kanta kasawa ta yi har sai da Hajiya Hajara ta wanke mata kan tass. Bata tsaya jiran komai ba ta kama rigar dake jikimta ta cire a nan suka tsaya kallon tufafin fatar dake a matsayin skirt dinta da kuma wanda ta yi riga da shi wacce ta tsaya mata iya kirji, da taimakon Hajiya Hajara Maimoon ta yi mata wanka wanka bana wasa ba, ba kuma daya ko biyu ba sau hudu suna murza mata jikinta soson yayin baki jikinta kuma yayi fari tass, hannunta mao ciwo ne kawai ba a wanke ba, shi ma iya bakin inda aka daure mata, kafafuwanta kuma Hajiya Hajara ce da kanta ta rike kafafuwan ta wankesu, ta saka abun gogewa ta goge mata dan abun da ba za'a rasa ba saboda rashin saka talkamin da take. Maimoon ta dauko tawul ta daura mata sannan ta janyo hannunta ta fito da ita, idonta yayi ja sosai saboda kukan da ci, ta yi ihu har ta gaji ta yi shiru dan kanta. Maimoon ta zaunar da ita saman gadonta a hankali sannan ta dauko baby oil din da take shafawa ta fara shafa mata a kafufuwa, babu yadda ta iya bayan mika wuya haka ta zauna kamar gumki Maimoon ta shafe mata jikinta ko'ina, sannan ta dauko hand dryer ta jona ta kunna, Waira na jin rurun abun sai ta zabura ta fashe da kuka.

“Ke ba jimi ciwo za'ayi ba”

Ina fa sai ta ki ta tsaya busar mata da kan yadda ya dace ganin haka ya saka ya mike tsaye ta bude akwatinta ta dauko mata doguwar riga ta karen miski ta saka mata sai ga Waira ta mike tsaye Maimoon ta ja mata rigar har kasa. Hannu ta saka tana tabawa, ta san karen misk domin suna saka irin wannan kayan a garinsu sai dai ba kowa ke sakawa ba sai mai wani mukami a garin. Girgiza kai ta yi bata damu da babu komai a jikinta ta cire rigar ta jefar ta dauki tawul din ta kare jikinta.

“Aiko akwai aiki, kina nufin saboda ya miki yawa ba zaki saka ba”

A zaton Maimoon saboda size dinsu ba daya ba ne ya saka ta guji rigar. Haka dai ta daure ta dauko mata wata rigar buba ta mika mata, sai ta karba ta rike tana kallon atamfar dake jikon Maimoon ta sauko har kasa, ita kan bata taba saka kaya har kasa ba, iyakar doguwar rigarta guiwa ne. Maimoon ta karbi rigar ta dauko mata riga da skirt sai ta karba ta rike rigar atamfar tana ta kallo musamman zip din dake jiki har da saka yatsanta ta taba ta ji yadda yake, Maimoon ta karba ta saka mata rigar, irin dinkin nan ne da ake kawo riga har gurin guiwa sannan ayi mata straight skirt, ta bude mata skirt din ta daga kafarta ta saka mata sai ta fisge kafar ta lake kafada.

“Ba zaki saka ba? To kina son wando?”

Bata da sabon panta hakan ya sakata dauko short na mata daga kafarta ta saka mata, shi kan wando ta saba shi domin suna saka na saki, hannu daya ta saka ta kama wando taja shi har saman mazaunan, Maimoon ta dauko turare ta saka mata sannan ta dauko mataji ta fara taje mata kan a nan fa aka fara sabon fada saboda zafi take ji sai ta ki yarda Maimoon ta taje mata kan da kyau, a dole ta bar mata shi haka ta saka mata mai a kan ta dauko ribbon dinta ta hade mata gashin guri daya ta yi mata parking sannan ta saka ribon din. Gashin ya sauko har rabin bayanta.

“Ji yadda kike da kyau dan Allah, amman kowa yayi miki wannan chabon kazanta a jiki ya ci amanarki, daman saboda ya boye kyauki yayi haka, ji ido har wani ruwan bula ya kwanta a ciki ga hanci gashi kamar na yar aljana, kai gaskiya Allah ya iya halitta”

Ita kam Waira bakin Maimoon kawai take kallon yarenta na sauka a kwakwalwarta idonta kuma na son tantance abun da bakinta yake furtawa. Kamin su dago kai a tare su kalli kofar dakin da aka bude, Waira na ganin fuskar da ta sani sai ta yi saurin ta nufi gurinshi tana wani kuka kamar na shagwana domin babu hawaye a idon sai dai ya kumbura saboda kukan da tayi, rike shi ta yi da dayan hannunta ta juyo ta kalli Maimoon tana jin wani irin tsanarta a ranta domin idan akwai abun da tana a rayuwarta bayan mutuwa to wanka ne, yau kuma anyi mata shi akan dole. Juyowa Dr Shuraim yayi ya kalleta sai ya ganta kamar ba ita ba, domin an wanke ta tass datti nan duk ya fita ga gashinta a mata farkin gwanin sha'awa.

“Bata son skirt amman an saka mata wando, Yaya ta yi kyau ko?”

Ya daga ma Maimoon kai, sai Waira ta girgiza masa kai, a tunaninta wani abun Maimoon take nufin ayi mata ya amsa mata da kai, kamin ta riko hannunsa tana nuna masa bathroom din.

“Miye?”

Ya wuce gaba ta bi bayansa suka shiga bathroom din sai ta duka ta saka hannu ta dauko tufafinta, wannan ta dauko rigarsa ta mika masa, sai ya karba ya aje yana murmushi nata tufafin kuma ta rumgume abunta. Dayan hannunsa ya saka ya dafa kafadarta ya matsar da ita gurin madubin dake bathroom din ya duka ya dan daga ta kalli kanta a madubi, da sauri ta rufe idonta, domin basa amfani da madubi a garinsu, da ruwa suke amfani su ga fuskarsu, ko kuma yi tsafi su ga fuskarsu, ba yau ne karo na farko da ta taba wanka ba, tana wanka amman sau daya a shekara kuma a duk lokacin da ta yi wanka taba duba kanta a ruwa ko kuma Eid yayi mata tsafi ta ga fuskarta, sai dai a yau yadda ta ganta kyar a jikin madubin ta san an mata wanka da ya amsa sunan wanka ta wanku iya wankuwa, jikinta har yanzu ciwo yake na murzar fatar jikinta da Hajiya Hajara ta yi da soso. Ya sauke ta kasa sannan ya fito bathroom din tare da ita suka fice daga dakin gaba ďaya. Yadda aka shigo da ita tana kallon ko'ina haka take kallo a lokacin da ya fito da ita falon kamar zata zubar da ido. Kujera ya nuna mata ta zauna sai ta ki zaman har sai da ya nuna mata kayan marmarin dake a plate gabanta, sai ta sake shi ta aje kayanta a gefe daya ta saka hannu ta dauka, abun ka da mai jin yunwa sai ta fara ci da sauri ita kanta bata tantance kalar yunwar da take ji ba har sai da suka fara sauka a cikin hanjinta. Zaunawa yayi a saman kujera yana kallon yadda take daukar fruits din tana ci, bata ko tsayawa ta tauna da kyau sai ta hade.

“Wannan ce bakuwar ta mu”

Cewar wani Magidancin mutum dake zaune akan wheelchair fuskarsa sak ta Dr Shuraim.

“Ita ce Doctor”

Hajiya Hajara ta amsa masa tana bayansa tana turo keken, da sauri Waira ta cire hannu a fruit din ta rike kafarsa tana yi ma mahaifin Dr Shuraim kallon tsoro da mamakin yadda kamarsu ta bace kamar an tsaga kara.




©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:48 PM] My S Line: *W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*

Wadanda ba su account za su iya turo mtn card ta 08036126660

19

Bata jin kalma ɗaya daga cikin maganar da suke, sai ta san akanta ake maganar domin yanayin kallon da suke mata ya nuna haka, ita duk abun da ake bata yarda ta saki hannun Dr Shuraim ba, bata yarda da kowa ba sai shi bata jin sakewa da kowa sai shi kadai, domin shi ya fahimci kalar abun da take iya ci gashi baya cutar da ita, idan ma yayi mata allura to tana a sume ne bata sani ba, ba kamar mutanen da take ganin sun rike ta da karfi sun mata allura ba, ga kuma wadanda suka mata wanka.
Duk yadda suka yi kokarin sakata ta yi alwala sai ta ki daman can bata son taba ruwa balle kuma bata saba yi ba, bata taba sanin idan za'ayi ibada tsabtace jiki ba, musulunci ba addininta ba ne, saboda haka bata san komai akan addinin ba, sai ma ya zame mata wani bakon lamari ganin suna alwala sannan suka shimfida carpet suna abun da ba zata iya kiransa da ibada ba, domin bata ganin abun da suke bautawa, ba kamar su da abun bautarsu suke ganinshi ido da ido ba, ko suna amfani da aljannun ne, shi ne abun da ya fara zuwa mata a rai, domin ta san yadda aljannu suke iya sarrafa komai ciki har da sakawa ayi musu kalar bautar da suke so, ba abun da ya bata mamaki kamar yadda suka saka manyan tufafi suka rufe jikinsu, Dr Shuraim da mahaifinsa suna a gaba, Hajiya Hajira da yarta Maimoon kuma suna baya.
  Dr Shuraim ne yaja sallah suna sallame yayi addu'ar sallah sannan ya juyo ya kalli inda take ya sakar mata murmushi har ta yi kamar zata mayar masa sai dai ganin Maimoon na kallonta ya saka ta rufe idon nata gaba daya ta daina kallon kowa. Jin motsin mutun ya saka ta bude idonta daman so take ta ga idan ya gana ibadar, da sauri ta nufeshi ta kama hannunsa ta rike tana nuna masa dayan hannunta dake mata zogi.

“Akwai allurar da ya kamata ayi miki da yamman nan amman babu ta anan, dole sai naje pharmacy na siyo”

“Daman an taba barin mutum babu magani a irin wannan ciwon haka? Kamata yayi kamin ka ba su takardar transfer ka haɗa musu da ta magani ai”

Cewar Mahafinsa.

“Hankalina ya tashi ne shiyasa ban tsaya na yi abun da ya dace ba, domin har yanzu gani nake kamar cutar da yarinyar nan za su yi”

Yana maganar Waira na kallonsa bata ko kibta ido gaba daya hankalinta ya tafi gareshi kamar tana jin abun da yake fada, wani irin sakewa da natsuwa take ji idan tana kusa da shi, kamar sun fito ciki daya haka take jinsa. Ya nuna mata gurin zama.

“Zauna a nan can zan je na dauko magani”

Ta girgiza masa kai ko bata jin yarensa ai tana fahimtar zama yake son ta yi, ita kuma bata jin zata iya haka ita kadai har sai idan tare za su zauna. Babu juyin duniyar nan da be yi ba akan ta zauna ya tafi ya siyo mata magani amman ta ki, da ya zaunar da ita sai ta tashi tana riƙe masa hannu.

“Ashe kuwa idan zs a tafi da ita akwai aiki”

Amsawa Hajiya Hajara.

“Nima shi nake gani, saboda bata yarda da kowa sai ni, na ji suna zancen ayi mata allurar bachi, amman na faɗa musu cewar zai iya cutar da ita saboda ba ciwo take ba, balle ace tana kwana ba bachi”

Sai tausayinta ya kara kamasu, musamman ma Mahaifinsa, sai da yayi da gaske sannan ya ɓanɓare hannunta daga rikon da ta yi masa ya mikewa Maimoon ta rike masa ita da karfi, ya fita da sauri domin kokarin kwace kanta take a hannun Maimoon tana kallonsa alamar so take ta bishi. Tana ganin ya fice sai kwala uban ihu da ya saka a dole Maimoon ta sake ta ba shiri sai ta koma gefen kujera ta rakube tana ta kuka, tun tana kukan da ruwan hawaye sai ga jini na fito mata a idon amaimakon hawaye, babu wanda ya kula a cikinsu, saboda Hajiya Hajara ta ja mijinta gefe ta inda zai kalli TV da kyau, Maimoon kuma tana kitchen tana mulka tuwon shimkafa da tun kamin magariba ta gama miyarsa. Hannu biyu Waira ta saka ta taba jinin dake zubo mata ta kalla, take hankalinta yayi mugun tashi domin bata hawayen jini Eid ne yake hawayen jini idan yayi kuka, kukansa kuma yana nufi abubuwa da yawa abu ne mawuyaci yayi kuka idan kuma yayi to ta ɓace masa ne. Tsafi aka jefata da shi ko kuma Eid ne a cikin wata matsalar wata kila kuma Eid din ne a kusa, ta leka falon tana kallon ko'ina kamin ta dawo ta sake boyewa daga nan kukanta ya tsaya. Tana ta sauren abun da zai sameta.

“Ina take?”

Shi ne abun da Dr Shuraim ya fara tambaya a lokacin da ya shigo falon, Mahaifiyarsa ta fada masa inda take boye. Gurin ya nufa ya lekata har ta zabura sai ta tuna tafiya yayi ya barta sai ta koma ta zauna ta hade fuska ta juya masa baya, shi kam ba ta fushin da take yake ba jinin da ya gani a fuskarta da hannunta ne ya daga masa hankali. Ya aje ledar maganin dake hannunsa da sauri ya kama hannunta yana dubawa.

“Ina kika samu jini?”

Ta kalli hannayen nata, sai ya juya da sauri ya kalli iyayensa.

“Ta jima kanta ciwo ne?”

“Miy faru?”

“Jini ne a fuskarta da hannu”

“Subhanallahi jini”

Hajiya ta karaso tana dubawa.

“Tun da ka fita bata fito daga gurin nan ba, in da ba ta jiwa kanta ciwo ba, to babu wanda ya taba ta, sai dai ko idan ciwon dake hannunta ne”

“No duba da kyau ki gani, babu jini a hannunta ko kadan”

Ya nuna mata hannun, kamin ya shiga yi ma Waira na kurame, yana nuna jinin yana tambayarta da hannu a ina jinin ya fito. Sai ta nuna masa idonta a nan ya maida hankali gurin idon sai ya lura har yanzu akwai sauran jini a ciki dubawa yake sosai ko zai ga inda ta ji ciwo a idon har jini yake fito mata.

“Yarinyar nan abar tsoroce Shuraim ka yi saurin hannata musu ita kar ta mutu a hannunmu, tun da nake a rayuwata ban taba jin mai kukan jini ba amman yau Allah ya nuna min, anya mutum ce kuwa? Idan kuma mutum ce to sun riga sun bada jininta mutuwa zata yi”

Cikin yanayi dake nuna be jidadin maganar Hajiyarsa ba ya juyo ya kalleta.

“Haba Hajiya, yanzu da ace tana ji ai sai ki saka ta shiga tashin hankali, ba a saurin yake hukuci ga abun da baka sani ba”

“To sannu Malam, ga zahiri kana gani zaka ce kar a yanke hukunci ku ji min wani ikon Allah, Doctor ka ga wani abu? Kukan jini yarinyar nan take”

Mahaifin Shuraim ya turo wheelchair dinsa da kansa irin ya karaso gurin da mamakinsa yana kallonta ganin ido yayi mata yawa ya saka ta boye fuskarta.

“Bata son kallo, bari na mata allurar sai na kaita dakin Maimoon ta kwanta”

“Ba dai Maimoon ba kam Shuraim ta cinye min ƴa ana kwana, ko kuma ta mutu ace ita ta kasheta? Aa lalala ni ai lamarinta a yanzu ya ba ni tsoro, bana jin zata kwana a gidan nan ma ka maida ita inda ka daukota can gurin police din su sai su sama mata inda zata kwanta”

Bude baki yayi zai yi magana sai mahaifinsa ya goyawa Hajiya baya.

“Gaskiya, karka aikata irin kuskuren dana aikata wanda nake nadama har yanzu, garin taimako ka jefa kanka da mu a matsala, ko kuma ita yarinyar ma gaba daya”

“Bata yarda da kowa yanzu Abba kai ma ka gani kuma idan nace zan maidata fitina ce”

“Bata yarda da kowa idan za a kaita abujar kai zaka kaita ne? Ji min wata maganar banza? Karka janyo mana masifa Shuraim dan Allah ka maida yarinyar nan gurin tun ranka be bace ba”

Waira ta dago ta kalli Shuraim tana iya fahimtar fada ake masa, wata kila kuma duk saboda ita ne.

“Hajiya mun riga mun yi magana da su, sun ce da safe za su zo su dauke ta sai kuma yanzu na maida musu ita? Idan na kaita a can wani abun ya sameta still ba mu fita daga zargi ba”

“Kara ta mutu a hannunsu, duk abun da zai sameta ya sameta a can, ba nan ba, ka tashi ka kai yarinyar nan na ce maka Shuraim”

Ta daka mashi tsawar data saka shi sa hannu biyu ya dafe kansa da hannu biyu. Waira ta sakarwa Hajiya Hajara ido daman tun da suka dannenta suka mata wanka take tsoronsu balle kuma yanzu da take yi ma Shuraim fada har ya rike kansa.

“Shikenan zan mai da ita”

“Yanzu kuma ba sai anjima ba, daman can ban da karanbani dauko ta ba, haka kawai daga yarinya tana kuka sai ka ce sai ka zo mana da ita”

Tausayinsa sai ya kama Waira ta san duk saboda ita ake masa fada, ba zata fadi abun da suke cewa ba, amman ta san akanta ne suke masa fadan, shi ma tausayinta yaji hakam ya hana shi yi mata allurar da ya siyo sai ya bude maganin kawai ya balla ya saka mata a baki, sai ta bude bakin a hankali saboda yarda da ta yi da shi ba zai cutar da ita ba ya saka mata maganin ta fara sotsawa jin yana da daci ba a yadda ta yi tsammani ba ya saka ta yi yunkurin zubarwa sai ya girgiza mata kai.

“Maimoon kawo ruwa”

Ya kwalawa kanwarsa kira, sai gata da kofin ruwan data debo a tap ta mika masa ya karba ya kai mata a baki, abun ka da wanda be saba ba da zo hade maganin sai ya tsaya mata a makoshi ta kasa hadewa ta dawo da shi a hannunta, sai ya karba ya balla wani ya bata ta kora mata da ruwa a dole ta hade da sauri haka yayi ta mata har ta anye sannan ya rika hannunta suka mike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login