Showing 33001 words to 36000 words out of 281271 words

Chapter 12 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1197

zai samu kebewa ya huce haushin abun da ta aikata, ta san yayi haka ne saboda kar matsalar ta su ta yi yawa, kuma yayi mata hakan ne saboda ya ladaftar da ita da abun da ta yi masa. A hankali Ummi ta aje numfashi tana jin abun nan da ya saba tsaya mata a zuciya ya tsaya kyam ya tokare mata zuciya.

“Tashi muje ki kwanta”

Ba musu ta mike tsaye Ummi ma ta yi tsaye tana rike da hannunta kamar wata karamar yarinya suka nufi upstairs, sai da Ummi ta tura kofar dakinta ta bude sannan Nimra ta shiga ta kwanta Ummi ta kashe mata wutar tana tunatar da ita cewar ta yi addu'ar kwanciya, sannan ta ja mata kofar dakin ta rufe. Ummi na fita Nimra ta mike tsaye ta rumtse ido tana jin wata sabuwar damuwa na kwankwaso mata kofa, a nan ma bachi yace ba da shi ba, fir idonta suka ki kusantar inda bachi yake har asuba gashi shaidan yayi galaba a kanta ta kasa raya daren da ko da Nafila biyu ne ko karatun Qur'ane. Gaba daya tunaninta ya tafi akan abun da zata aikata Ameer ya yarda da ita, wace hanya zata bi ta gamsar da shi cewar ba da hadin bakinta aka yi ma abun sa yake zarginta da shi ba, ta damu sosai ita kanta neman dalilin damuwar take ta rasa.
Misalin tara ta fito dakinta Namra da mai aikinsu Ramatu suna zaune falo suna kallon maimaicin wani shiri da Zee word suke, kallo daya yar'uwarta ta yi mata ka gama fahimtar akwai damuwa a tare da ita, domin idonta ya nuna bata samu bachi ba kamar yadda idon Mahaifiyarsu ma ya nuna dazun da ta shiga ta gaisheta. Sai dai bata ce mata komai ba domin ta lura Nimra bata son kallonta abun da ke nuna mata son magana akan hakan kenan. Har zuwa lokacin da ta zauna a falon trying number wayarta da ta bawa Ameer take amman bata zuwa.


Bachi ya dauke shi sosai be san lokacin sallah azuba yayi ba har sai da rana ta fito ta haska fuskarsa, sannan ya tashi zaune sai da ya karewa kereren dajin kallon sannan ya ja tsaki ya mike tsaye one of the best thing dake bata masa rai akwai missing Sallah, ya tsani lokacin Sallah ya fita be yi Sallah ba, mika yayi sannan ya fara leka sannan ya juya da zimmar ya juyawa ba dan ransa ya so ba ya koma gurin motar Nimra ya dauki ruwan da ya siya yayi alwala, sai kuma ya juyo ya duka ya dauke carpet din da ya kwanta a kai, sannan ya nufi wani gurin kai kama da hanya, to his surprise sai ya hango manyan duwatsu da korama a gafensu, hakan ya faranta masa rai daman dan dole ne kawai zai tafi dauko ruwan da suke cikin motar natar da yake yi mata kallon makiyiyarsa a yanzu.

Gurin wani karamin dutse ya aje carpet din sannan ya nufi gurin ruwan, a hankali ya rika sauka har ya isa bakin gabar da ruwa sai da ya mika hannu zai saka a cikin ruwa sai kuma ya tuna, ya kwanta a gurin da be san mi ua taba shi a gurin ba, secondly ya taba carpet be wanke hannunsa ba, to taya zai yi amfani da hannu ya taba ruwan da zai kai bakinsa ya kuskure. Wani dogon tsaki yaja ya juya a dolensa ya koma gurin motar ya bude ya dauko sabulu da ruwan ciki ya wanke hannunsa sannan ya dauki box din sarewarsa da wasu abubuwan da zai iya ci ya sake dawowa gurin koramar, can gefen duwatsun ya nufa yayi fitsari, ya dawo carpet din ya fara shimfidawa ya aje komai a gafe sannan ya sake wanke hannunsa ya shigar da hannayen ya fara alwala sai da ya gama da yanayin fitowar rana yayi amfani ya gane gabas a dajin, cikin natsuwa ya gabatar da Sallah asuba dinsa sannan ya gyara zama yana karanta ayatul kur'asiyu bayan ya gama ya daga hannunsa sama yayi mahaifiyar addu'a, bayan yi ma uwarsa da Daddy ya fada masa cewar ta rasu addu'a, baya kara wata addu'a ko wace iri ce ba halinsa ba ne weather ta neman tsari ce ko ta neman wani abun duniya, sai dai be taba fashin yi ma mahaifiyarsa addu'a ba, domin yana jin marmarinta duk da kasancewar be taba ganinta ko da a hoto kamar yadda be san kowa nata ba, domin Daddy be hada shi da kowa a matsayin dan'uwa ko yar'uwar mahaifiyarsa shi kuma be damu da hakan ba, sai dai a yau yana jin marmarin mahaifiyarsa fiye da ko yaushe, ya tabbatar da ace yau mahaifiyarsa tana raye da ba zata bari mahaifinsa yayi masa wannan korar ta wulakanci ba.
Jikinsa ne ya bashi cewar ana kallonsa sai ya juya da sauri ya kalli tsakankanin manyan duwatsun da suke gefensa, sai dai be ga kowa ba, ido ya kurawa gurin sosai yana kallo ko wani abu zai fito ko kuma a sake lekowa amman be ga komai ba. Gyara zamansa yayi ya bude box din sarewarsa ya daukota ya rike yana shafawa. Tunawa yayi da lokacin da yake busar da Nimra ta ji har wata yar karamar alaka ta shiga tsakaninsu, duk wasu kalamai da ta furta masa a lokacin sai da suka dawo masa, a take ya kara jin ransa ya kara hauhau wa ya jagula, busar da iskar bakinsa yayi ya kai tsarewar bakinsa ya rumtse ido, busar sarewa na daga abun da ke kawar masa da bacin rai ko damuwa idan ya samu kansa a daya daga ciki. Busawar ya fara yi cikin kwarewa da gwaninta kamar yadda ya saba, a take gurin ya dauka.


Kai ta daga sama tana kallo kamar a saman ne ake busar, cikin karfi hali ta dago ta mike tsaye zuciyarta na bugawa da mugun karfi ta taka kafar tana dingishi ta sake lekoshi a karo na uku. A take zuciyarta ta raya mata cewar Eid ne, sai dai kammanin da tsayin ba iri daya da Eid ba, kamar yadda tufafin jikinsa ma suka banbanta da na garinsu, sai dai ta yi imanin Eid ne kadai ya iya irin wannan busar sarewar, komai kwarewar mutum ba zai iya yinta ba, kuma babu wanda ya san tana a gurin balle ya zo sai Eid da zai iya ganinta ko Sarki a cikin tukunyar tsafinsu. Ta sani idan Eid ne ba zai cutar da ita ba, sai idan wani ne zai yi yanayi da shi din amman ta iya zai iya busar kamar shi? Idan kuma Eid ne me zai saka ya saka wasu tufafin da bata taba ganin kowa da su ba. Ko dai an yi hakan saboda ta fito a kama ta ne? Ko kuma Eid din ne da gaske. Takowa ta fara yi tana dingishi har ta fito jikin duwatsun tana kallonsa. Jikinsa ya sake bashi cewar ana kallonsa a take ya daina busar ya juyo ya kalli saitin inda take tsaye. Tun asali can Ameer ba irin masu tsoron nan ba ne hakan ya saka shi tsayawa yana kallonta da mamaki. Rigar fata ce a jikinta wacce ta tsaya iya kirjinta ta bar cikinta a sake, tana sanye da walki irin wanda mata suke sakawa kafarta babu talkami sai jini da ya bushe a kafar, kana kallonta ka sa fara ce sol sai dai tarin dauďa da dattin dake jikinta sai suka mata kamar an shafa mata laka, gashin kanta a yamutse yake kamar anyi yaki, sai dai ya sauko har bayanta, tana da manyan idanuwa farare ga dogon hanci da karamin baki, gefen bakinta ma jini ne ya bushe mata, babu komai a cikin fararen idanuwan sai tsoro da fargaba da kuma yunwa, domin har saman rigarta yana kallon yadda zuciyarta ke bugawa saboda motsin da gurin yake. Kamar wanda aka ci garinsu da yaki haka take tsaye komai nata a birkice yake, a rayuwarsa be taba ganin mace a yanayin da ya ganta ba, ba tsiraicinta ne abun kallo a gurinsa ba, domin ya saba ganin mata in bikini kuma ya sha ganin tsiraicin wanda yake mu'amala da ita, to him ganin tsiraicin mace is not a big deal, yanayin tufafin jikinta ne a abun kallo a gurinsa da kuma tarin daudar da ya tabbatar da shi ne a haka da yanzu ya mutu.
Mikewa yayi tsaye sai ta yi baya baya cikin dingishi tana masa kallon tsoro ganin fuskar da bata taba gani ba kuma bata sani ba, sai ta koma kallon Sarewar dake hannunsa, wata kalar sarewa ce da bata taba ganin irinta ba, gaba daya ma bata yi kama da sarewa ba, tana ganin hakan ta san ba Eid ne ba, beran dake hannunta ta dora a saman kanta domin shiryawa gudun da ta san ba lallai ne ta iya ba. Sai a lokacin ya lura da bera a hannu kuma ta saka shi a kanta, kamin ya karasa zaro ido amai ya cika masa baki a tsaye yayi ta fesa aman kaman ya duka yana jin kamar ya amayar da hanjin cikinsa, domin be taba ganin kazanta irin wannan ba a rayuwarsa, a yanzu kam ya gasgasta ba mutum ba ce aljana ce domin mutum ba zai zauna a irin wannan yanayin ba da wannan dress da kuma kazanta har yana rikon bera, wani abu ya rika ji kamar ana kwantarsa, jiki na rawa ya dauki gel din dake gurin ya nufin bakin ruwan ya cire tufafin jikinsa. Waira na ganin haka ta juya da sauri ta koma inda take boya ta boye tana kuka, ba kukan tsoro kawai take ba har na yunwar da take ji.
Sai da ya shafe jikinsa ko'ina na sabulun bayan ya cire tufafin jikinsa sannan ya saka ruwan ya wanke jikinsa, baya cire kaya ya sake sakawa sai dai wannan ya zame masa dole domin ba shi da wasu tufafin da zai canja.

“Allah ya tsine maka albarka Maleek”

Ta fada yana kara jin tsanar abokin masa, domin saboda shi komai ya faru, juyowar da zai yi sai ya sake ganinta a gurin shimfidarsa tana ganin ya ganta sai ta yi saurin dauke biscuits din da ya aje a gurin ta fara gudu da dingishi har ta shige gurin ya boya, ko motasi bata yarda ta yi ba gudun kar ya biyo sawunta, sai da aka dade bata ga alamar shigowarsa ba sannan ta kai ledar biscuits din a bakinta ta fara taunawa, bata san ana budewa ba balle ta yi kokarin yin haka, ko da ace guba ce a ciki ci zata yi domin yunwa take ji sosai jikinta har rawa yake, taunawa take amman bata jin komai sai sul6i da ledar take da shi, jefar da ledar ta yi ta dauki dayar ta kai baki ta tauna ita ma dai kamar ta farkon ce hakan ya saka sake jefarwa hawaye na sauko mata. Kwantawa ta yi a gurin ta rufe ido, sai ta sake jiyo busar sarewar da Eid ke yi kamar yadda ta ji a dazun, wannan karon ba ta yi yunkurin tashi ba sai kawai ta fashe da kuka tana tuna yadda take rawa idan yana mata busar, gashi ta kasa gane waye wannan Eid din ne ko wane? Shirya mata hakan aka yi saboda a kamata?
A karo na biyar ta sake tashi zaune ta mike tsaye ta sake lekawa, sai ta same shi tsaye yana busar yana kallon inda take, da alama so yake ta fito, domin tana fitowa sai ya daina busar ya tsaya yana kallonta, hawaye sharaf a fuskarta. Ya juya yana kara karewa dajin kallo sannan ya sake kallonta.

“Ke aljanna ce?”

Bata san me ya fada ba, hasalima bata taba jin yaren ba bakon yare ne a gurinta, kamar yadda fuskarsa take bakuwa a gurinta, baya baya ta yi ta lafe a jikin dutsen tana kallonsa. He thought bata jin hausa domin yanayinta ya nuna haka.

“Who are you?”

A karo na farko ta ji yaruka kala biyu da ba irin nata ba, kamar yadda tufafinsa ma suka banbanta da nata, yanzu kam ta tabbatar ba Eid ba ne, sai dai kuma bata da tabbacin ba turoshi aka yi a gurinta ba, idan kuma turo shi aka yi to me yake jira da ita be kamata ba?

“Some time I'm such a fool wanda be ji Hausa ba ta ina zai ji turanci?”

Ya fada yana jin zuciyarsa na tashi da alama wani aman yana kusa domin yawun bakinsa sai tsinkewa suke suna cika masa baki. Dauke ido yayi daga barin kallonta ya dauki Box din sarewarsa ya saka sarewar ya fara tafiya yana yamutsa fuska ya kasa daina ganin beran nan na dazu da dattin dake jikinta.

“Daman hakan aljanu suke da kazanta?”

Ya tambayi kanshi kamin ya duka ya fara kwara amai kamar marar lafiya, sai da ya gama ya nufi motar Nimra ya bude ya dauko ruwa ya wanke bakinsa da fuskarsa sannan zauna a bayan motar yana sauke ajiyar zuciya.

*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*


_©Khadeeja Candy_


Na yi mistake din page, na saka 12 Instead of 11 so wannan shi ne na 12 wacan kuma 11.

1️⃣2️⃣

Can kuma ya dago kanshi ya fito daga cikin motar,  ya nufi wasu itacen ya tsaya a gurin yana tunanin makomarsa, gida zai koma ya duba jikin mahaifinsa? Ko kuma a nan zai zauna inda be san kowa ba kuma ba shi da komai, and the most annoying part is duk wani abu da yayi amfani da shi na Nimra ne kanwar makiyinsa, tunanin mafita ya saka shi fara tafiya ya koma yar karamar hanyar nan da ya fito, ashe kaddara ke kiransa domin yana tsaka da leke hallitar nan ta da a bayan ya bar gurin ta fito tana dingishi ta nufi gurin shimfidarsa, wani biscuits din ta dauka ta taba ganin irin na dazun ne, kala ce kawai ta banbanta yasa ta jefar ta nufi inda ya aje Gel din da yayi wanka da shi ta dauka tana ta kallon gorar a rayuwarta bayan gorar zuba ruwa irin wanda ake da ice sai kuma ta kwarya bata san wata gorar ruwa ba, hakan ya saka ta daga ta sama tana kallo kamin ta sauke ta fara kwankwasawa can kuma ta kara kunne ta tana saurare, hakan be gamsar da ita ba sai da ta saka dayan hannunta tana shafa gorar, gurin da ta ga an yi hanyar da gel din zai fito ta kai bakinta tana tsotsowa abu ne da saba gani ba, hakan ya saka bata san dannawa ake sabulun ya fito ba, sai kufan da ya rage kawai ta samu a bakinta, abun ka da mutumen daji sai ta hade tana sauraren yadda dandanonsa yake. Jin babu dadi sai wani makaki da kumfa ya saka ta jefar ta nufi gurin ruwan da yayi wanka ta saka hannayenta biyu ta fara debar ruwan tana sha, a take cikinta ya kulle yan hanjin cikin suka murde ya fara mata ciwo. Tun da take a rayuwarta bata taba jin azabar yunwa irin wannan karon ba, a take ta fashe da kuka ta fadi a gurin ta dafe cikinta. Yana daga kafarsa ya kara matsawa gurin da take domin ita bata san ma yana kallonta sai ya ji abu ya dan taba masa kafa dauke kafar da yayi yana dubawa sai ga maciji, wani tsalle ya kara dakawa ya yi baya da sauri.

“Kai....”

Ya furta da mugun karfi wanda hakan yayi sanadiyar zaburar Waira da sauri ta tashi zaune tana kallon inda yake tsaye, babu abun da ya zo a zuciyarsa sai ita, a tunaninsa ita ta turo masa macijin har wani bangare na zuciyarsa na raya masa ita ma din macijiya ce. Da sauri Waira ta fito daga gurin idonta kamar za su fado tsabar kallon tsoron da take masa, ganin yayi baya sosai ya saka ta tsaya tana kallon abun da yake yi ma gudu, maciji ne ba wani babba sosai ba sai dai baki ne dake neman shigewa cikin ciyayin dake gurin, tsoron kwari irin maciji ko bera da wasu kananan abubuwan daji ba ba nata ba ne, domin duk wanda ya saba hawa itacen fruits baya tsoron maciji, musamnan icen ayaba, mango da kuma guava. Da dingishi ta nufi inda macijin ya bi tana lekonsa, ganin be yi nisa ba ya saka ta yi hanzarin bin bayansa, Ameer ya zaro ido yana takowa ya leketa. Dukawa ta yi ta saka hannunta ta cafki macijin da yake kokarin tashi tsaye sai ta rikoshi da hannunta ta mike tsaye.


“Bura'uba, yau na ga bala'i ganin ido”

Furucin da yayi ya saka ta juyo da sauri ta kalli inda yake tsaye, a take zuciyarta ta hau bugawa da sauri kamar zata fado, ta fi tsoronsa fiye da macijin dake hannunta, kamar gwalanniya haka take jin yarensa, a tsorace ta sake macijin da take da zimmar sakawa dutse ta kashe, be sauka a hannunta ba sai da ya cijeta.

“Ashashashash.... Atak Atak gil rièèk bisk...”

Bata san lokacin da ta yi furucin ba, tana yarfar da hannu tana ihu, fuskar mamaki Ameer yayi na jin yaren dake fita bakinta domin shi be taba jin yaren ba.

“Zaki yi kyau da gadi, yadda kike da rashin tsoron nan”

Ya fada sannan ya yayi baya baya yana kallon yadda ta fadi a gurin tana ihu gumi na karyo mata kamar wance aka watsawa ruwa, hannayensa ya daga masa.

“No offense...”

Ya furta tare da juyawa yayi tafiyarsa domin be ga mahadinshi da ita ba balle yace zai taimaka mata, ta ina ma zai iya taimakon wanda be sani ba? Ko mutuwa zai aka ce sai ya taba ta zai rayu be jin zai iya taba sai dai ya mutu din, balle ita ce zai ceto.

“Ahhhhhhh Ashhhh”

Ya dan tsaya yana jin karar da take, zuciyarsa na raya masa maybe ma hadin kai ne so ake ya taba ba, idan ba haka ba miyasa ta je ta taba macijin bayan bata da magani, a dayan bangaren zuciyarsa kuma na raya masa be kamata ya tafi ya barta a gurin a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login