Showing 42001 words to 45000 words out of 281271 words
kumfa ba, a take yaji ya shige masa a idon, a nan yaji wani sabon amai na taso masa yana ta jin kyankyami a jikinsa, tun da yake a rayuwar be taba wanka tara at the same time ba sai yau, ba wanka iya na sabulu ba har da na tsarki sai da yayi ba kuma dan yayi komai ba, sai dan ganin Waira da yayi da tabata da carpet din yake ji ba kamar ma har da wankan tsarki yana bukata saboda kazantar ta yi jawa wata kila idan be yi wankan tsarki ba zai iya jawa kansa matsala aki karbar sallah shi.
Ya san yadda Hajiya Jamila take sakawa a tsabtace komai na dakinsa amman hakan be kwantar masa da hankali ya taba tawul din dake aje a bathroom din ba, haka ya fito ya nufi gurin da tufafinsa suke aje ya dauko sabbi fil ya saka sannan ya shafama jikinsa mai ya saka turare, talkami ya saka ya sauko fito daga dakinsa zuwa falon Hajiya Jamila tea ta fara tarbonsa da shi sannan ta zuba masa soyayyaen nama domin ya san yadda yake son naman da aka soya suya mai kyau, doya ta sarrafa masa da miyar kabeji wanda ta ji kaza, tun kan ta kawo masa abincin kamshi ya cika hancinsa. Lafiya lafiya ya fara cin abincin kamin ya tuna da kazantar Waira sai gashi ya tashi da sauri ya nufi bathroom din Hajiya Jamila cikin tashin hankali ta bi bayansa tana tambayar ko abincin ne be masa dadi ba ko kuma wani abun ya gani a ciki. Haka ta tsaya a bayansa tana kallonsa har ya gama aman ta kunna fanfo ta tara masa ruwa ya wanke bakinsa.
“Wani abu ka gani a cikin abincin ne?”
“No inda na tafi ne na ga wata kazanta da ban taba gani a rayuwata ba”
“Ina kaje Ameer?”
“Wani daji ne, a KT”
Bedroom suka dawo, ya zauna ya labarta Hajiya Jamila duk abun da ya faru ciki har da motar da Nimra ta bashi and da reason din da yake ganin ya saka ta ba shi motar. A yanayin yadda ya bata labarin ta gama fahimtar bashi da gaskiya domin shi ya fara tsokanar abokin nasa amman tsoron bacin ransa ya saka ta kasa nuna masa sai tausarshi take kar ya aikata abun da zai zame masa matsala.
“Da ka yi hakuri ka kyaleshi Ameer idan ma ya ci amanarka zai gani a nan gaba, zalinci ba shi da kyau idan ka zalinci mutum komai ta dade sai hakkinsa ya fita, ka saka masa ido kana zaune hakkinka zai ita matukar ya zalince ka Allah ba zai bar shi ba”
“Ni ko ba a taba ni ba, kin san zan taba balle kuma an taba ni, bana bari ga Allah”
Ya amsa mata kai tsaye, numfashi ta sauke a hankali ta mike tsaye.
“A dauko maka wani abincin?”
“Na koshi, a sama min flight din da zai tafi Abuja anjima zan kwanta yanzu idan babu kuma zan je da mota”
“Ba zaka kwana a nan ba?”
“No ina son na je na duba jikin Daddy hankalina ba zai kwanta ba sai na ganshi”
Hajiya Jamila ta shafa kansa, sannan ta fice cike da damuwar da ita kadai ta santa. Kwanta yayi saman lafiyayyen gadon abun ka da wanda ya marmarin bachi nan da nan bachin yayi gaba da shi.
Mafarkinsa gaba daya akan yarinyar da tunaninta ke saka shi tashin zuciya da mai ne, ba mafarkin abun da ya faru a dajin yake ba, mafarki yake akan wata yarinyar da aka tsabtace ta sha ido da kwalliya, kamshi ta ko'ina ta ratso taron jama'ar da ake gabatar da Event din da be san na minene ba, ta iso gare shi, sai ya risina kamar mai jiran isowarta ta saddan kansa kasa alamar girmamawa a gareta ita kuma ta cire wani zare a hannunta ta daura masa a wuya ta yi mashi murmushi, sannan ta juya ta fice daga taron a zuwa wani dakin dake da icen tuffa ga kuma wani itacen na dogon yaro (Dalbejiya or Bedi) a tsaye. Can kuma mafarkinsa ya sake daukarsa zuwa gidansu Nimra, kuka ya hango tana yi tana fadar shi yayi kisa ba ita ba, hakan ya sake haddasa fada a tsakaninsa da mahaifinsa har ya sake korarsa a karo na biyu...! Firgigit ya farko daga bachin na rana ya yarfar da hannu ya shafe wuyansa, tsabar kyamar Waira da yake ko a mafarki ya ga ta taba shi kazanta yake ji, Even though ya san mafarki ne amman hakan be hana shi sake yin wani wankan ba, har mamaki yake in wanda haukar mafarki da kwashe kwashe shi miye hadinsa da kazama da har zai kawo masa ita a bachi, ba kawo ta ne kawai matsalar ba daura masa zaren dake hannunta da tayi a wuya shi ne matsalar domin jinsa yake kamar gaske.
Tsaki yaja yana shafa turare a wuyansa, lallai ya yarda mummunan mafarki daga shaidan yake, domin idan ba shaidan ba ta ina za a ga wannan yarinyar kazama ta yi wanka ta yi kyau tsabtsab da ita har su kamshi, a yau kam ya tabbatar da mafarkin rana shirme ne. Sai da ya saka wasu tudafin sannan ya sake komawa bathroom din yayi alwala ya fito ya karbi key din motar Hajiya Jamila ya fice daga gidan, gida biyar ya wuce sannan ya isa inda masallacin unguwar yake, yin Sallah in time kuma cikin jam'i is one of his favorites, sai dai baya jerawa da mutane sai dai ya tsaya a gafe daya, idan kuma ya samu Masallaci ya cika sai yayi sallah a waje, Saboda kar jikinsa ya taba na wani indai ba abokansa ba, sai kuma mahaifinsa da mutanen da yasan suna tsabta a yadda yake so, haka Allah yayi shi akan kyamar mutane da yake har warinsu yake ji wani lokacin.
Bayan an sallame ya fito ya dawo gida, a nan ya samu Hajiya Jamila na hada masa cake, bayan ta gama take fada masa ba za a samu flight zuwa Abuja da yamma nan ba, amman ta masa Booking din Private jet, kuma ya jidadin haka cake din kadan ya ci daman he's not that foodie abu kadan idan ya ci ya ishe shi wani lokacin ma Lemu kawai zai wuni a cikinsa.
Karar tsayawar motar YaYan Hajiya Jamila ya tuna masa da sarewa, da sauri ya saka hannunsa aljihu yana lalabe kamar a ciki ya aje ta.
“Oh...”
Ya furta hakan yana jin wani sabon bakinciki.
“Lafiya?”
“Sarewata na bari a motar yarinyar can Wallahi”
“Mantuwa ka yi?”
“Eh ban tuna ba sai yanzu”
“Sai siyen wata kenan?”
“Ba za a samu mai kyau irinta a yanzu ba, and akwai wanda ya saka min wani abu a sarewar nan wanda idan na busa take tafiya yadda nake so”
Zanjabil da yar'uwarta Hurriyya ne suka shigo falo, suna ganinshi suka yo kansa da gudu suna murna, sai dai bacin rasa sarewarsa ya saka be wani sake musu fuska sosai ba, tunaninsa na yadda zai dawo da barsa hannunsa ne, ya san zai sha fama amman haka zai dawo da ita ko da kuwa yakin duniya na uku ne zai afku.
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
.............
Da dan sassarfa ta isa hostle din su, bata yarda ta shiga cikin hostle din ba, amma tana iya hangota, yadda ta tsuguna a gaban locket ɗin su, dake an gansu tare babu wanda ya kawo wani ta'addin tazo yi, tana kokarin bude locker din kenan Rahilah ta isa kwanar su. A firgice ta mike tana zare idanu. Nade hannu a kirji Rahilah tayi tana mata wani irin mugun kallo daga sama har kasa. Hàdiye yawun tsoro tayi tana faɗa mata ita bata dauki kome ba, rab'a gefenta Rahilah tayi ta kuma rufe locker din, sannan ta juya tana watsa mata kallon banza ta nuna mata hanya. "kar nan kuma ganin ki a cikin mu, ki tsaya iya kanki." Hàdiye yawu tayi ta wuce simi-simi kamar wacce aka watsawa ruwan zafi. Sannan Rahilah ta tafi ya same su.
***
Hajiya Daulah.
Tsura mishi idanu tai, ta rasa abin da zata gaya mishi ko zata mishi ta ji dadin rayuwarta asalima irin mugun b'acin rai take ji. "Abdulhakim meye nufinka? Nace ban isa da kai ba ne?" D'ago kai yayi idanun shi jajjur. "Kiyi hakuri bani da lafiya ne shi yasa ban je ba" tabbas matukar takardun shi suka fito zai gudu ya bar Hajiya ba zai iya da rigimar ta ba, ta hana shi sakat. "Ka sani ina kallon ka ne, duk lokacin da ka cika ni zan bata mata ka rai" ta fada tana bubbaga hannunta a kasa. "Allah ya huci zuciyar ki" ya fada yana barin falon, ita kanta bata son tana mishi fada anyhow, dauke kai tayi tana son ta bincika ta ina ta gaza a kulawar da take mishi? Amma baki daya baya damuwa da ita kamar yadda yake damuwa da mahaifin sa. Tana zaune a wurin Afiyyah ta shigo a gajiye, zama tayi tana kallon Hajiya. "Hajiya naga motar Yaya. Yana sama ne?" "Eh yana can" da gudu ta haura sama tana zaune. "Assalamu alaikum, Ya Abdul Barka da dai. Dama dama" kallonta yayi cikin kulawa sosai. "Kina son wani abu ne?" Ya tambaye ta a sanyayye. "Hmm uhmm, dama akan Sophia ce ta ce na" "get lost" da sauri ta juya, "mtsew" ya kawar da kan sa. Da gudu ta isa falon. "Hajiya" kura mata idanu tayi domin bata son magana. "Sophia ce ta ce min" "wuce ki bani wuri bana son magana don Allah" daga haka ta wuce mai da hankalinta tv, wurin karfe shiga Taufiq ya dawo. A kofar shigowa suka hadu. "Ya Abdul ya kake?" "Lafiya muje sallah" "tab na gaji idan na farka cikin dare zan yi sallah amma yanzu wallahi na gaji, idan bayi yau ba zan yi gobe in sha Allah" ya fada yana shiga da goyon jaka a bayan sa. "Allah ya kyauta" ya fada yana dauke ajiyar zuciya, ya nufi hanyar masjid da yake jikin gidan su, bai da so gidan ba, sai da aka bayan isha. Tunda ya shigo ya hango su a wurin cikin abinci masu aiki sai kaiwa da komowa suke. Bai ce musu cikanku ba ya wuce abin sa. "Abdul" Hajiya Daulah ta kira shi. "Na'am" ya amsa yana juyowa baki daya. "Zoka zauna ka ci abinci" ta fada a tausashe, domin bata son yayi ta yawo babu abin arzikn a cikin sa. "Na koshi" ya fada can kasar makoshinsa. "Zo nan Babana " ta fada a raunane, domin baki daya yadda yake bata son abin da zai iya lalata mata shirinta na son yayi aure ba. Takowa yayi har inda ta nuna mishi ya zauna yana kallon abinciin. "Ci" ta ce masa. Babu musu ya fara ci. "Hajiya kin mai da Yaya Abdul kamar wani yaro" inji Taufiq yana dariyar shakiyanci, murmushi tayi tana kallon Abdul din da yake cin abincin kamar bai da hakora a bakin sa. "Nayi magana da hajiya Nazirah akan Sophia ko zaka fara zuwa ne?" "Kwat" ya hàdiye abinciin bakin sa, yana kallon ta. "Baka fahimci me nace ba ne?" "Na fahimta " bata bar shi ya sake wani magana ba, domin ta lura da magana a bakin sa ta mike tana cewa"Allah ya taimaka ya daidaita kanku" "Amin" ya fada muryan shi yana rawa. Dauke kai tai tana haurawa sama, tana halkance da shi, yadda yake kallonta. Amma bata jin zata iya kyale shi. Tana barin wurin ya mike shima ya nufi waje, yana shan iska baki daya kome ya tsaya mishi cak, bai da wani kuzarin da zai fadi abin da yake damun sa, tare da fadar likita yace saboda ciwon shi ba zai iya zama da mace ba, tunda shi ciwon haihuwar shi aka yi da ita ba daga sama ya same ta ba, domin da daga sama ne tabbas da yanzu yana da mata da yara kamar kowa, kuma abin da yake kara dagula lissafin sa, shi ne har yau bai da wacce zai nuna a matsayin yana so asalima har yanzu bai da cikakken lokacin da zai kalli mace domin kansa. Sai dai ya musu kallon tsoro ya wuce. Shigowar motar Dr Sharif wato mahaifin su. Mikewa yayi ya nufi wurin sa, ya jira sai da yayi parking sannan ya kashe motar ya fito, amsar jakar hannun mahaifin su yayi yana faɗin. "Barka da zuwa." "Yawwa Abdul Hakim ya na same ku?" "Alhamdulillahi" ya fada suna jerawa, "Ya Aunty Faridah?" "Tana lafiya sun ce na gaishe ka" ya fada yana kallon sa. "Kana da damuwa ne ?" "Na'am" sai kuma yayi yar murmushi, sannan ya sosa kansa. "Ba kome" ya fada yana tafiya ciki da sassarfa. "Abdul Hakim meke damunka?" "A'a babu kome" ajiyar zuciya Dr Sharif ya sauke tare da bin bayan sa. Dakin Abban su ya kai mishi kayansa, sannan ya wuce dakin su, a duk lokacin da Mahaifin su yake gidan yana jin wani irin kwarin gwiwa da ita yake kwana, sai da Dr Sharif ya huta sannan ya wuce dinning table ya ci abinciin sa. Sannan ya wuce dakin Hajiya Daulah. Hankalinta yana kan wasu takardu ya shiga ya ja kujeran mirror ɗinta. Ya zauna yana kallon ta, "Ranki shi dade zaki bani aron lokacin ki?" "Emmm!" Ta fada hankalinta yana kan takardun, "ina son ki ajiye kayan gabanki muyi magana akan rayuwar Abdul Hakim" sai lokacin ta ajiye takardun ya zuba masa idanu. "Ina jinka" tattaro nutsuwar sa yayi ya kalle ta sannan ya ce mata. "Abdul Hakim ba zai iya zama da mace ba, duk yadda kike son yayi aure na fiki kaunar haka, domin har auren yar Sultan an bashi, ba na gaya miki haka ne domin ki d'aga min hankali ba, na gaya miki ne domin ki san matsalar d'anki, ba zai iya zama da macen da kike ra'ayi ba, likitan shi ya tabbatar da matukar shi yaga mace yana so tow zai iya zama da ita kuma idan tana son shi zata zauna da shi, ba auren dole ba." "Kana nufin zan matsa mishi yayi aure ne? Ko kana son cewa na takura mishi da zancen aure?'" "hmm" yayi murmushi me sauti yana kallon ta, kafin ya ce mata." Ko daya ina son ki tuna da cewa shi din amana ne Allah ya bamu tsakanin mu da shi akwai hisabi kar ki yi abin da zai tsaya a gaban Ubangiji ya nima mishi hakkin sa, don Allah kar ki tsannanta mishi, mu kyautata mishi gani nake kamar duk halin da yake ciki mune sanadin haka, don Allah ki yi haquri." Kamar ta rufe Dr Sharif da duka, amma haka ta rufe idanunta ta, na tsawon minti goma sha biyar, kafin ta bude fuskar ta yayi jajjur Idanunta sun kankance domin takai matukar bacin rai, jan drower gadon tayi ta zuba takardun ta cigaba da kallon Dr Sharif, a hankali tayi murmushin karfin hali, ta ce mishi. "Zaka iya tafiya kaina yana ciwo" gyada mata kai yayi domin har ga Allah baya son tashin hankali su ya shafi Yaran su, shi yasa yake mata biyayya kamar ita ke auren shi ba shi ke auren ta ba. Haka ya fito jikin shi a mace ya wuce dakin sa, itama kuma kashe wutar dakin tayi tare da ƙwanciyar ta, amma ba barci tayi ba, sai dai tana saka abubuwa masu yawan gaske akan danta da mijinta, tana son Abdul yayi aure tana son ganin jinin sa a duniya. Ba haka kawai take takurawa ba, Yes tana son ganin sa cikin farin ciki da walwala.
***
Few weeks ago.
Saturday visiting.
Tun safe suke shiri sosai, kai ka rantse da Allah sun shekara basu ga iyayen su ba, idan ka cire Rahilah da take kwance. Sa'ade anyi wanka Umma metro ɗin su, ta musu guga, sai sheki check dinsu yake, ita da Husnah, Kubrah tana rabe a gefe, duk da basu san me yasa take kin zama a cikin su ba, amma haka suke janta cikin su, inda tayi kokarin hana kanta daukar kome nasu, sai na sauran yan room ɗin, idan ana sururun anyi sata, kallo daya Rahilah ke mata ta shiga kame-kame. Dukar pillow da Rahilah take kai Sa'ade tayi, ta bude idanunta da suka yi jajjur. "tashi mu tafi kin ji" ta mata magana, saka hannu tayi a wuyarta ta ce mata. "Bani da lafiya ne" kallon kuru tayi mata, tana son hango iyakar gaskiyar Rahilah, "shi kenan" ta fada suka fita suna mata fatan Allah ya ba ta lafiya, har sun yi tafiya me nisa, sa'ade ta kalle su musu alamar su tafi tana zuwa. Ta juya abin ta, kallon ta suka yi. Kafin kamar hadin baki suma suka biyo ta, ana ta fita a room ɗin ba kowa, sai Rahilah da take zaune tsakiyar gadon tana ta rusa kuka, wani irin maraici da kewar Iyayenta take ji, bata da d'an uwa ita ɗaya suka haifa suka rasu baki daya, yan uwan Baban ta, ba zuwa suke ba, sai dai Aunty ta aiko mata garin kwaki da sugar. Yadda ta cusa kanta a tsakanin cinyarta tana kuka sai yq taba zuciyar duk wanda ya iso in da take, zagaye ta sukayi suna kallonta. Kafin Sa'ade ta dafata, a tsorace ta d'ago kai. Ganin Sa'ade ne, fadawa jikinta tayi tana kuka. Itama kuka take, abu daya ya tsara da kukan su. Shigowar Umma ta saka salati tasan ba wani ji suke can can ba, sai da ta matsa kusa da su, ta musu dakuwa tare da musu al'amar su tafi ana niman Husnah Jafar Kurmi, amsawa Husnah tayi, ta mikawa Rahilah kayanta, suna tsaye har ta shirya, a hanyar tafiya suka gamu da wasu senior sun zo niman Kubrah, Iyayenta sun zo, sai da suka fara zuwa wurin iyayen Husnah, suka gaishe su sannan suka wuce wurin iyayen Kubrah, kallon Kubrah suka yi domin basu ga a lamar Maman ta ba, sai dai da alamar matar da mijinta da dan su daya, matar tana kama sosai da