Showing 114001 words to 117000 words out of 281271 words
jikin kofar ya samu shiga sai ya rufe gate din ita kuma ta tsaya kusa da inda ya nuna mata jikinta na rawa gabanta na faduwa. Kamin yau idan wani ya zo yace yana son ganin masu gidan kai tsaye masu gadin suke ba shi damar ya shiga domin haka Ummi tace musu, sai dai Umarnin da Abiey ya bada na cewar kar a sake Nimra ta fita gidan ya aaka suka tsaurara tsoro gudun kar wani abun ya faru a dora laifin a kansu.
[6/18, 7:54 PM] My S Line: *Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
38
MALEEK POV.
Yana shiga dakinsa ya shiga closet dinsa ya aje jakar ya fito ya sauko downstairs ya zauna a dayan side din da kujeru suke, sosai ya maida hankalinsa gurin plasma dake kunne yana kallon film da MBC 2 suke hakawa. Sai da suka tafi talla tukuna hankalinsa ya kai gurin wayarsa dake kan ďayan set din kujerun tana ringing da hanzari ya isa gurin ya dauki wayar tare da amsa kiran da ya biyo bayan miss calls din dake bayyana a saman kiran.
“Maleek kana ina?”
“Ina cikin gida, bana kusa da wayar ne”
“Ka same ni bangarena zamu gaisa da mijin Namra, na kusa karasowa”
“Okay”
“Kuma ban ce ka zo min da kananan kaya ba”
Yayi murmushi kawai ya sauke wayar yana kallon kansa domin kananan kayan ne a jikinsa. Haurawa yayi sama ya canja tufafin jikinsa zuwa shadda ash color ya fesa turare ya saka kular Zanna bukar yar ubansu, ya canja talkamin kafarsa ya saka wandanda za su dace da shaddar jikinsa be damu da duba madubi ba domin ba yin kyau ko akasin haka ne a gabansa ba burinsa yayi shigar mutunci kamar yadda mahaifinsa ya bukata, be fice dakin ba sai da ya murza wani karamin turare a hannunta ya shafe hannunsa zuwa wuyansa, ya dauki wayarsa ya saka aljihu sannan ya sauko stairs din yana wani irin kamshi na tashin hankali kamar shi ne angon. Kofar fita falon ya nufa tana tafiya kamar mai tausayin kasa. Entrance din bangaren Ummi ya tsaya yana kallon gate din gidansu, a hankali ya juyo yana kallon motar Shuraim sai ba motar yake kallo kai tsaye ba, kyakkyawar halittar Allah mai matukar burgewa da daukar hankali yake kallo, Waira ce tsaye jikin motar can side din da ace bata mike tsaye ba ba zai iya sanin tana gurin ba, ita ma bata mike tsaye dan sanin cewar shi ne tsaye a gurin ba, sai dan kamshin turaren da ya kaiwa hancinta hari ta kasa jurewa har ta leko a zatonta zata ga Sulem dinta ne sai ta yi arba da abokin fadanta.
Yayi kyau, kyau da ake kira da kyau irin kyaun dake fitar da asalin kyau da siffar kyau a jikin namijin, da haramun ne ka yi masa kallo daya ka dauke ido. Hular kansa ta zauna das kamar sai da aka sauna kalar zaren da girman aka zaka masa domin shi kadai kawai. Shaddar ta haska fatarsa ta kara masa kwarjini da cikar izza irin ta jinin sarauta, daga ita har shi sun dauki lokaci suna kallo junansu, ko wane na tantance kyaun dayan jinsinsa. Waira ce ta fara sulalewa kasa ta zauna tana rike da zomonta, a lokacin da idonshi suka daina ganin kyakkyawar fuskarta sai hayyacinsa ya dawo jikinsa ya dauke kai ya sake maidawa gurin gate din yana hade yawun bakinsa da suka tsinke...
Me kike yi a nan wa kike jira, duk baya bukatar amsarsu, yadda aka yi ta fito daga cikin falon ta zauna a gurin ne abun tambaya a gurinsa, jira ko me take yi a gurin ya san amsarsu, ko da ya tambaye ba zai wuce tace masa tana jiran Sulem ba, domin a gurin motarsu ta tsaya. Yana kokarin zuba hannayensa aljihu ta sake lekowa irin leken da be yi kama da gulma take ba, ta gefen ido yake kallonta rabin idonsa na kan gate din da aka buden ragowar kuma suna kan Waira dake kallonsa, tana ganin motar Abiey ta kunno kai cikin gidan sai ta mike tsaye gaba daya ta bar jikin motar ta nufo hanyar shiga falon inda Maleek yake tsaye. Tana doso inda yake tsaye gabansa ya tsanata faduwa na rashin dalili kuma ya kasa kallonta har ta iso gurin ta ratsa gefensa ta wuce. Sai da ya sauke numfashi mai nauyi sannan ya samu sukuni a zuciyarsa, tun da yake a rayuwarsa be tana jin abun da yaji a yau ba. After Abiey ya faka a compound din gidan ya sauko ya isa gurin motar yana masa sannu da zuwa.
“Maa Shaa Allah, haba ko kai fa yanzu da ban maka magana ba da kananan kayan zaka saka ka fito a matsayinka na yayan Namra”
Murmushi yayi as respond ya karbi jakar dake hannun driver mahaifinsa suka jera a tafe kamar ba uba da ďa ba, kamin su karasa apartment din Abiey yayi masa tambaya uku ya kasa bashi amsar ko daya.
“Ai tun kamin ya zo a matsayinka na dan'uwanta kuma namiji, wanda nake sa ran ko bana raye ko kuma nan gaba kadan zaka iya gudanar da komai ya kamata ace ka mata tambayoyi akansa”
“Abiey ka san ba wani sakewa nake da su sosai ba, so ban cika son shiga rayuwarsu ba”
“Amman ai na ga alakarka da su yanzu ba kamar da ba, ka samu lafiya inji Umminku kasan ita ce kullum take ganin baka da lafiya”
Abiey ya fada yana dariya. Maleek kuma ya kai hannu ya bude babbar kofar falon Abiey ya fara shiga sannan Maleek ya biyo baya. Falon farko babu kowa a ciki hakan ya bawa Abiey da ďansa Maleek damar shiga kofar dake cikin falon wacce zata sada su da corridor dakin Abiey ba sai sun bi ta cikin karamin falon da Namra ta sauki surikinsu ba. Abiey ya fara shiga dakinsa kai tsaye ya zauna tare da Maleek yana fadin.
“Kira Namra ka fada mata ta sanar da bakonta zamu shigo mu gaisa da shi yanzu nan”
“Abiey ba zaka huta ba?”
“Hutun me? Aiki na bari na zo nan fa kuma muna gama gaisawa zan koma”
Maleek ya ciro wayarsa dake aljihu a maimakon ya kira sai ya aika mata da sako. Abiey kuma ya kira Ummi Dr Zainab ta amsa wayar.
“Ka dawo”
“Eh ina dakina tare da Maleek”
“Toh bari idan kun gaisa da shi sai mu fito muma mu gaisa da shi”
“alright”
Ya aje wayar, after like 20 minutes Namra ta shigo dakin ta zube kasa ta gaishe da Abiey kanta a kasa tana mai jin kunyarsa abun da bata saba ba.
“Abiey na fada masa”
Mahaifinta yayi dariyar farinciki yana zolayarta daman ya saba wasa da yayansa ba maza ba matan ba balle kuma Ummi da take matarsa.
“Toh Gimbiya Namra bari mu tafi mu gaisa da Yarima”
Ta rufe ido tana dariya. Shi ma dariyar yake Maleek kam kallonsu kawai yake kamin ya mike tsaye tare da mahaifinsa suka fice daga ďakin. Shuraim na jin an taba kofar falon sai suka kara daidaita natsuwarsu domin Namra ta sanar musu mahaifinta zai shigo ya gaisa da su, kusan a tare Shuraim da abokinsa suka mika tsaye suna amsa sallamar Abiey. Maleek ne ya riga karasa inda suke ya mika musu hannu suka gaisa sannan ya zauna a kusa da inda suka zauna. Shuraim ya mikawa Abiey hannu biyu ya gaisa da shi as well as abokinsa.
“Bismillah”
Abiey ya fada yana nuna masa kujera, tsantsar ladabi da girmama na gaba ya hana Shuraim zama a saman kujera saboda Abiey ya zauna saman kujera yana ganin be dace shi ma ace yana kan kujera ba.
“Sannunku da zuwa”
Sai suka amsa da yauwa suka zauna a kasan Shuraim kansa na kasa kamar wani mace, Abiey kam kamar ya samu tv haka ya rika kallon saurayin mai shirin zama surukinsa.
“Namra ta fada mana zaka zo, saboda mun bata damar zabar wanda take so, mun yi maganganu da ita, sai dai ina tunanin yana da kyau mu kai ma ka gabatar mana da kanka, kuma ka yi hakuri da tambayoyin da zan maka”
“Ba komai Abbah, daman shiyasa na zo ai, saboda mu san juna kuma na yi bayanin kaina, idan na koma sai na sanar da iyayena su same ku da maganar ko a yanzu ma sun san da maganar sun dade da sanin Namra sai dai a yanzu ne magana mai karfi zata shigo”
Abiey ya tsuke ido yana kallon Shuraim tare da murza tsayansa daya da hannunsa kamar mai kokarin tuna wani abu.
“Sunana Muhammad Shuraim, ni likita ne ina aiki a General hospital Katsina, kuma ina dan taba aiki Peach Hospital Katsina sai dai ita Private Hospital ce, mahaifina ma likita ne sunansa Dr Hamid Muhammad iyayena yan asalin garin Kano ne, sai dai zama ya dawo da su a Katsina, na yi karatuna a jami'ar BUK na yi master a ABU zaria, kuma ina shirye shiyen fita waje domin cigaba da karatuna In Shaa Allah, ni na na farko a gidanmu ina kanwa wacce ta yi aure tana Kano akwai kuma dayar tana nan tare da mu ita ma tana kusa da yin auren In Shaa Allah, mahaifiyata tsohuwar malamar makaranta ce, yanzu kuma da ta yi ritaya tana kasuwanci na tufafi da kayan shafe shafe na mata”
“Kai ďan wajen Dr Hamid ne?”
Abiey ya tambaya yana nunashi daman zuciyarsa ta raya masa haka tun shigowarsu ta farko a falon da yayi arba da fuskarsa.
“Eh ni dansa ne”
Maleek ya kalli Mahaifinsa.
“Kama san mahaifinsa kenan Abiey?”
“Ni kuwa na san Dr Hamid farin sani, daman ina ganin fuskarka na san cewa kai dansa ne”
Cikin yanayi na rashin jindadi Abiey yayi maganar yana kebe baki ya girgiza kai. Sannan ya kalli Maleek ya ce.
“Kira mahaifiyarku tare da Dr ta zo su ganshi”
Maleek ya tashi ya fice, Shuraim kuma ya dan dago ya kalli Abiey da ya tsare shi da ido irin kallon da ke nuna ba a maraba da kai, suka hada ido da abokinsa ya sauke kansa kasa yana jin wani iri, domin dai be san shi ko mahaifinsa da wani abun da za a nuna shi ba, ba kuma mamakin jin cewar Abiey ya san shi yake ba domin mahaifinsa kwararen likita kamin jinya ta ci karfinsa wata kila shi ma ya san mahaifinsa ne da hanyar aikin da mahaifinsa yake. Kusan gaba daya suka shigo falon ban da Jabir da baya gidan sai kuma Umar dake can dakin Mahmood yana safgar gabansa, Dr Zainab da Mahmood sai Ummi da Waira ke bayanta ita kuma tana covering din face dinta saboda kukan da ta yi, Yesmin da Juwairiyyya suka shigo daga karshe Maleek na bayansu. Waira na hango Shuraim ta bar gurin Ummi ta nufi inda yake ta zauna jikinta na gogar nasa, ta saka hannunta ta kama hanshi hannun ta danka mishi takardar daya rubuta mata kuma ta lakame hannu. Kunya da ganin kamar hakan be dace ba ya saka ya matsa ya cire hannunsa cikin nata sai ta kara matsowa daman can a a'adarsu zama a kusa da wanda ba muharraminsu ba ko taba shi ba wani abun zunubi ko laifi ba ne a gurinsu. Idonta ya rufe bata ganin kowa a falon sai Sulem dinta yadda take washe hakora ma kadai ya isa ya fahimtar da mutun cewar akwai kyakkyawar alaka tsakaninsu, yana matsawa sai itama ta matsa ta kama hannunsa zata rike sai ya fisge. Dukawa ta yi zata leke fuskarsa Maleek ya daka mata tsawar da sai da yawun bakinta suka tsarke ta fara tari babu shiri.
“Ke.... Waira... Me yasa baki da hankali wai? Tashi daga nan ko na takaki get out”
Ta mike tsaye da sauri hawaye na zuba tari na zo mata kamar wacce ta taba taji, a take Shuraim ya ji ba dadi ya dago ya kalli Maleek da fuskarsa ke daure yana watsawa Waira harara. Rikice ta nufi gurin Ummi Maleek ya sake daka mata tsawa data saka ta fashewa da kuka mai karfi.
“Get out na ce, na rantse da Allah sai kin fita”
Ta kalli Shuraim ta fice da sauri jikinta na rawa. Ummi bata cikin yanayin mai dadi hakan ya saka bata ce komai ba, ita ma kuma ta san abun da Waira take yi be dace ba.
“Ai ba laifinta ba ne, tun da ba a koya mata addini ba, yarinyar da bata san halak da haram ba? Bata san Allah da ma'aikinsa ba, Kai ta san ka ne?”
“Eh ni ne likitan da ya karbe ta a lokacin da aka kawo ta asibiti maciji ya cijeta, dan sabu da nine a lokacin”
Shuraim ya amsa cikin muryar dake nuna be jidadin abun da aka yi ma Waira ba, kuma yana son sanin abubuwa da yawa a game da zamanta a gidan da kuma alakarsu. Abiey ya kalli Ummi yana nuna Shuraim.
“Ga ďan Dr Hamid yarki ta kawo mana a matsayin wanda zata aura, kamar dai Nimra”
Ummi ta yi gyaran murya ta ce.
“Maa Shaa Allah, muna maraba da hakan ga dukan alamu yaro ne mai hankali da tarbiya, kuma muna fatan abun da muka gani a fuska mu jishi a zahiri idan mun bincika, idan akwai alheri aurenka da Namra, Allah ya saukar da natsuwa da kwanciyar hankali da fahimtar juna a tsakaninmu da kuma kai da ita, idan kuma babu alheri Allah shi ne mafi sanin daidai ina fatar rabuwa ta zo cikin mutunci da aminci ba tare da an cutar da juna ba”
Yanayi maganar farko ta Abiey da kuma amsar da Ummi ta biyo baya da ita ya karantar da shi cewar akwai wani abu da be sani ba kuma suke kallonsa da shi. Kowa ya amsa da Ameen a falon har shi sannan ya dago ya kalli Dr Zainab dake tambayarsa mahaifinsa.
“Tana nan, ya bar aiki yanzu saboda shekaru sun ja kuma yana fama da ciwon sashe ba komai yake iya yi ma kansa da kuma spinal cord injury”
“Dole...”
Abiey ya fada sai duk suka kalleshi har Ummi dake kokarin nuna masa abun da yake ba daidai ba ne da ido, balle kuma Maleek da Mahmood da ba su fahimci komai ba, Shuraim ma kallon Abiey yayi da karshen zancensa ya biyo tare da kora da hali.
“Mun gode sosai da gabatar da kai Shuraim sai ka ji daga garemu”
Abiey ya mike tsaye ya fice daga falon, Ummi ta bi bayansa. Abiey na shiga dakin ta rufe shi da fada.
“Abun da ka aikata be kamata, yaron nan be san abun da mahaifinsa ya aikata ba, kuma be kamata laifin mahaifinsa ya shafe shi ba”
“Toh me kike tunani? Na bada yata aure ga zuri'ar Dr Hamid? Ko kin manta waye shi?”
“Kai da kake kokarin ganin sirrin nan be fita ba, kuma kai zaka ce ba zaka aurawa yarka wanda take so ba, saboda laifin da bana jin yaron nan ya san mahaifinsa ya aikata”
“Kika san wane kalar hali da shi? Ana son idan zaka yi aure ka zabawa yarka miji na gari”
“To me ye aibun Shuraim? Karka rusa farincikin Namra saboda wani selfish interest na ka, Nimra ta yi kuskure kuma addini ya haramta aurenta da Ameer amman Namra fa? To kake duk yaran su taro suna mana kallon azzalumai? Ka fi kowa sanin meye so karka saka yarka a damuwa saboda abun da wani ya aikata, Namra tana son yaron nan kuma idan har bincike ya tabbatar da ba shi da matsala za mu aura mata shi”
Tana kaiwa nan bata tsaya jiran abun da Abiey zai fada ba ta fice zuwa part dinta. Bayan fitar Abiey da Ummi Shuraim ya mike tsaye yayi musu sallama ya fice falon tare da abokinsa. A waje suka samu Waira tsaye gurin motarsa ta ci kuka har ta gaji ta barwa Allah, tana ganinsa ta mike tsaye da sauri tana kallonsa, ya karaso kusa da ita yana kallonta da damuwa a fuskarsa.
“I'm sorry...”
Sai kawai ta fashe da kuka ta rumgumeshi.
“Ai ga irin ta nan yanzu idan suka leko suka ganka fa? Ko fitowar da muka yi hakan be kamata ba ko sallama baka yi ma Namra ba, kuma kamata yayi ka bari sai kowa ya fice tukuna”
Abokin ya fada cikin rada yana waige waige kamar marar gaskiya.
“Ba damuwata ba ce kai baka ga abun da suka mana ba? Ai ba ni nace ta rumgume ni ba, daga ni bata jindadinsu”
Ya dago kanta ya saka hannu ya share mata hawayenta.
“Waya kawo ki nan?”
“Mutanen nan masu bakin kaya”
Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa jin yadda ya tambaye ta ta amsa masa da saura.
“Yanzu kin iya hausa kenan?”
“Na iya rubutawa wani ina karantawa ina ji duka amman bana iya fadar duka, ko turanci ana koya mana a makaranta”
Cikin kuka take fada masa tana kara komawa jikinsa ta rumgumeshi.
“Su waye mutanen da aka kawo kin gurinsu? Miye alakarki da su?”
“Suna nan, Ummi kadai take so na da Nimra, amman Namra bata so na da Ya Maleek tsawa ma yake min amman Mahmood na so na Abiey ma baya so na”
“Me aka kawo ki yi gurinsu?”
“Dan girman Allah da darajar iyayenka ka shiga motar nan mu tafi, ba mutunci ba ne a tararda kai da yarinyar nan ina ruwanka da alakarta da mutanen gidan? Kai dai abun da ya kawo ka dabam, kar ma ja a fara yi mata fada ko duka”
Rokon da abokinsa yayi masa ne ya saka shi dagota daga jikinsa.
“Zamu tafi Baby Girl amm...”
Bata iya jira ya karasa naganar da zai yi ba ta fashe da kuka tana girgiza masa kai.
“aa aa aa nooo karki tafi, ka zauna a nan ina so, Shuraim ina sonka, ina sonka so much”
Sonshi take da gaske amman ba irin na soyayya ba, irin son nan dai da take yi ma Mahmood da Ummi, sai dai hakan ba hana jin wani iri ba, gaba daya sai ji kamar kar ya tafi ya barta duk kuwa da kasancewar ba tafiya ce ta barin garin Abuja gaba daya ba, tafiya ce kawai ta barin gidan for now.
“Zan dawo ba tafiya zan yi gaba daya ba”
Ta girgiza kai alamar