Showing 48001 words to 51000 words out of 281271 words

Chapter 17 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1216

Maleek yake, he just wants to take revenge shi dai zuciyarsa suna masa take Maleek yayi masa Zagon Kasa, ya bude motar ya shiga yayi mata key jin kamar yana marmarin gurin da suka saba zama da abokansa ya saka shi nufar wani gurin shakatarwar na dabam, domin baya son ya sake shiga safgarsu tun bayan wulakancin da suka masa na zabar Maleek su barshi.




MALEEK POV.

Babu wanda yace Uffan a cikinsu bayan Abiey ya gama labarta cewar Ameer yace shi be san yarinyar ba be san inda ta fito ba kuma ba shi da alaka da ita.

“Amman karyar yake yi yana son ya kulla mana wani abun ne kawai”

Namra ta fada cikin jin haushi domin ji take kamar ace yana gabanta ta kwada masa mari. Ummi ta kalleta a hankali jin yadda take magana da zafin rai sai dai bata ce komai ba ta mai da kanta kasa tana jin zuciyarta ba dadi. Maleek ya saka hanayensa aljihu

“Wata kila kuma gaskiya ya fada, domin na san waye Ameer baya shakar ya amsa laifi komai girmansa matukar ya aikata zai ce shi yayi, idan har be amsa ba to be aikata din ba ne”

Namra ta girgiza kai.

“To waya aikata? Waye zai yi hakan bayan shi? Ko da ma ace wani ne yayi ai shi ne sila, kai da Ummi kamar kuna son kare Ameer din nan makiyin mu ne fa”

Maleek ya nunata da yatsa.

“Don't you dare raise your voice on me, na ce be aikata ba and i meant it tun da ya amsa cewar ba shi ba ne ba shi din ne ba, beside ai yarinyar tana da baki sai ta fadi wanda ya dauko ta”

“CP yace yarinyar bata jin hausa, kuma bata iya turanci ayi communicate da ita ma ya zama aiki”

Cewar Abiey with curious face. Ummi ta kalli mijinta da fuskarta ta wadanda lafiya bata wadace su ba.

“Yarinyar tana Katsina ne?”

“Eh likitoci sun ce zata samu wata daya zuwa 6 kamin ta warke garau”

“We can stay with her a nan har ta samu sauki kuma ta iya fahimtar yarenmu ko kuma mu mu fahimcin nata, then sai a hadata da yan'uwanta”

Maleek ya karba mata.

“Shi ne akwai yafi daman police sun san da maganar in case of wani abun ya faru suna sane, tun da yarinyar bata da wanda zata zauna a gurin can KT din, maybe ma daga wata kasar aka satota aka samu motar a ajeye aka saka ta a ciki, mude Allah tana raye that's just it”

“Shi ne, tun da mace ce be kamata a barta a can ba, ba zata samu kula yadda ya kamata ba, kuma babu kowa a can tare da ita, ko ba komai mu muke da hakkin kula da ita saboda a motar Nimra aka ganta”

Ummi ta sake fada duk da ta san ba lallai ne Abiey ya yarda ya dauki shawarata a yanzu ba, Nimra kam bata ma falon domin ganin take kamar mahaifinta be bukatar ganinta a yanzu bayan duk abun da ta jefasu ciki, itama kanta tana kunyar hada ido da shi.

“Kar kuma mu aikata abun da zai zama mana na nadama daga baya! Kar ta zama mana cuta”

Abiey ya fada a nasa fahimtar kamar be kamata yarinyar ta zauna a gidan ba, domin mai son abin ka ya fika dabara.

“Ko da ta zo da wata muguwar manufa Allah ba zai barta ba, domin mu mun yi da niyar kwarai ne, kuma Allah yana kallon zuciyar kowa”

Wannan karon da gwarin guiwa Ummi take fadar haka, Mahmood ma be ce komai ba domin shi dai baya goyon bayan kawota a gidan kamar yadda yake a zuciyar Namra.

“Idan ma haka ne, ai shi Mahaifin yaron ya fi cancanta ya rika saboda dansa ya jefar da motar”

“Idan kuma be rikata ba, sai mu rika rayuwa ce be kamata a salwantar da ita saboda jayayya ta son zuciya ba, In Shaa Allah babu wata matsala da zata faru”

Ummi ta amsawa Abiey da yayi maganar with full confidence.






©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:48 PM] My S Line: ©KHADEEJA CANDY 17


Tun a jiya da ya gama aikinsa ya bar asibitin be sake shigowa ba sai washe gari, yanayin aikin da ya tarar a office na duba patient ya saka be bi ta kan patient din suke kwance ba, sai abokin aikinsa ne yayi da zimmar shi zai duba su da rana idan zai fice. Misalin karfe daya da yan mintuna ya tashi aikin, sai dai be dauki komai nasa ba ya fita yayi Sallah a Masallacin, sannan ya dawo Office din ya bude akwatinsa ya dauki Stethoscope tare da wasu files ta saka Lab Coat ya fice, ya dade yana magana da wani abokinsa da ya tarar a ward din yana hira da nurse, tattauna suke akan zaben da za a gabatar na Nigeria da kuma wanda suke ganin idan aka zaba zai kawo canjin da sauyi a Nigeria. Safar hannu ya fara sakawa, Nurse din da suke duty suka rufa masa baya su biyu domin gabatar da na su aikin. Daya bayan daya ya rika bi yana duba mutane kamin ya kawo gurin yarinyar da ya duba jiya, gaba daya gadonta a zagaye yake an rufe shi da curtains din da ake rufe gadon marasa lafiya, yana daga curtains din Nurse din dake gefensa ta ce.

“Yarinyar fa ina tunanin kamar bata da hankali, tun jiya bata barin kowa ya taba ta kuma ta koma karkashin Bed din sai kuka take Halima tace min ko bachi bata yi sai ta leko sai ta koma ta boya”

Shiga yayi ya leka karkashin gadon sai ya hangota ta cunkushe guri daya ta rumgume hannunta mai ciwo. Hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayarsa ya kunna flashlight dinsa ya haska ta sai ta yi saurin rufe idonta domin hasken yayi mata yawa, tun da take a rayuwarta bata taba ganin hasken gulub ko na fitilar hannu ba, iyakar su hasken aci balbal ko na wutar itace ko ta kara. Nurse din zata yi magana sai ya daga mata hannu ya kashe fitilar ya mika mata hannunsa.

“Baby girl zo nan”

Kin kallonsa ta yi balle ma ta mika masa hannun, mikewa yayi tsaye ya ciro kudi aljihunsa ya fita daga gurin ya aiki daya daga cikin masu sharar gurin ta siyo masa apple da ruwa.

“Tun jiya bata ci abinci ba, kuma aka rasa wanda zai kula da haka?”

“An kula fa masu jinya sun bata abinci ko dazun, amman ba ta ci ba ruwan kawai ta sha, kuma ta ki fitowa a kasan gadon”

“Police din jiya ba su dawo ba?”

“Bana jin sun dawo, shi ma wanda aka bari nan ba a nan ya kwana ba kuma be dawo ba, da sun dawo da mun samu labari kuma babu wanda ya zo dubata, ni ina ganin kamata yayi ace sun dauki hotonta sun saka a Internet ko Allah zai saka a dace da yan'uwanta”

Dr Shuraim dai be sake cewa komai ba, ya cigaba da duba masara lafiyar da suke gabanta, har sai ya gama sannan ya karbi aikan da yayi ma mai share sharen Asibitin, son ganin yadda zata kaya ya saka suka biyo bayansa har da wace ya aikan. Dukawa yayi ya lekata tana ganin fuskarsa sai ta yi saurin rufe ido. Sabuwar takardar ya karba ya dora mata apple din akai ya tura mata, sannan ya aje ruwa ya dauke kansa. Be yi zaton zata yi saurin aminta ta taba ba, sai gata ta miko hannu ta dauki Apple daya, ta fara ci da sauri, ko tsayawa bata yi ta tauna da shi da kyau take hadewa tsabar yunwar da take ji, ta sake miko hannu ta dauki na biyu ta cinye ta dauki na uku har ta cinye Apple din guda uku sannan ta miko hannu ta dauko gorar ruwan, murda ta yi sai ta ji mabudin da karfi ba kamar na dazun da aka bata ba, hakan ya saka ta turo gorar waje, Dr na ganin haka sai ya dauki gorar ya bude mata ya sake ajewa, sai gashi ta ziro hannu ta dauka ta sha ta turo masa rabi. A nan ya lekata sai ta sako masa ido tana jin sake jiki da shi ba kamar sauran da take ganinsu kamar dodo ba.

“Baby Girl zo nan”

Ya mika mata hannu, kalmar Baby Girl ya zauna a kanta, tun a jiya da ya furta mata ba kalmar kawai ba, har da wasu maganganu da aka yi ta dauki wadanda ake yawan furtawa duk kuwa da kasancewar bata san ma'anarsu ba. Kallon hannunsa dake sanye da safa take kamar mai tunanin zuwa, ganin hakan ya saka ya dawo ta hannu ya cire safa daman ba a san likita da kyama ba, ya sake mika mata hannu, ta dade tana kallon hannun kamin ta yarda ta mika masa nata, tana sai ya riko hannun ya janyota alamar yana son ta fito, tana ganin haka ta yi saurin sakin hannunsa, be gaji ba ya sake mika mata hannun yana furta mata sunan da yake son ta saba da shi, wannan karon buge masa hannun ta yi domin ta sanar da shi cewar ba zata fito ba, murmushi ya sake mika mata hannu a karo na uku.

“Baby girl”

Ta miko masa hannun ta kama hannunsa ya janyota sai ta somawa fitowa a hankali, tana lekowa ta ga ba shi kadai ba ta yi saurin komawa. Juyawa yayi ya kallesu

“Kun tsoratata”

Fita suka yi daga gurin suka ja mata curtains din suka labe suna lekonta.

“Baby girl...”

Ya fada bayan ya mika mata hannu, sai ta buge masa hannu a karo na biyu. Lekawa yayi ya ga irin zaman da tayi sannan ya daga kansa ya saka hannunsa yana tafiya da yatsunsa kamar tafiyar mutun kamin ya kai inda take sai ta buge masa hannu. Lekawa yayi mata fuska sannan ya mika hannunsa ya rama bugun da tayi masa a hankali, sannan ya janye hannun da sauri, kamin ya sake mikawa ta sake bugewa, haka suka yi har sau biyar sannan ta yarda ta rike hannunsa ta leko kamar wata bera ta kalli gurin ganin babu kowa ba kamar dazun ba ya saka ta fito gaba daya taba kallonsa da idonta kamar za su masa magana. Saurin kawarda idonta yayi daga barin kallon rabin kirjinta da ke waje, zagen dake kan gadon na asibiti ya dauka zai nada mata a jikinsa sai ta buge zanen, ganin hakan ya saka ba tare da kyamar komai ba ya cire lab coat din dake jikinsa ya saka mata sannan ya fara kokarin mikewa da ita tsaye a nan wata sabuwar rigimar ta bullo ita san ba zata mike tsayewa, ganin take kamar wani abun zai mata, har sai da ya kama rigar ya fara saka mata button din da karfi, sannan ta kalli rigar da take jikinta ba wannan karo na farko data saka rigar data rufe jikinta har guiwarta ba domin tana saka gown da take a cikin tufafin kala uku da suke duniya, abun da bata taba ba shi ne saka tufafin da engine ya saka har aka saka wani anini a jiki. Kallon rigar take sosai kamin ta kalleshi idonta sun yi zurun zurun irin na wandanda yunwa ta samu sa'arsu ta yi musu kamun kazar kuku, ga dan karen tsoron dake fuskarta kamar yayi magana. Murmushi ya saka mata a kokarinsa an kwantar mata da hankali da kuma sakawa ta aminta da shi.

“Ya akai tufafinta sika yage?”

Ya tambaya domin ya san suna bayan curtains din a boye suna lekenta.

“Dazun da Doctor Mu'azu yace a fito da ita ayi mata allura saboda ko an bata maganin ba zata sha ba, shi ne ta yi ta kokawa da mutane har ta barka kayan”

Kamar ance mata kamata za su yi sai ta juya da sauri zata koma kasan gadon hanzarin riketa Dr Shuraim yayi sai ta juyo ta rumgume kam tana kuka jikinta ko'ina rawa yake, ba a taba mata daukar karfe aka soka mata a jiki ba sai wannan karon da ta samu kanta a duniyar da bata san kowa ba kuma kowa be santa ba, yadda ta kamkame shi ko kwakkwaran motsi kasa yi yayi. Hankalinta be kara tashi ba sai da Police din da aka bari ya tsareta ya leko dakin da uniform dinsa wannan karon bakin wando ne da riga sky blue a jikinsa, a nan ta kwala wani irin kara da siririyar muryarta irin karar nan dake shiga cikin kunne ta hana kwakwalwa kwanciyar hankali da sukuni, har sai da Dr Shuraim ya rufe kunnensa.

“Fita fita fita”

Dan sanda ya fita waje, sannan ta yi shiru ta kara kankameshi, tana wani numfashi kamar zata shide, jikinta rawa yake ta ko'ina tana daga kai sama kamar ta ga abun tsoro. Dr Shuraim be yarda yayi motsi ba har sai da ta samu natsuwa sannan ya dagota jikinsa ya kama hannunta mai ciwo a hankali ya duba, sai ta yi saurin fisge hannun ta boye bayanta, sai dai bata yarda ta sake rigarsa da dayan hannunta da yake lafiya ba, gaba daya a firgice take wata rayuwa take gani da bata mafarkin yi ba, ga wasu mutane da bata san inda suka fito ba, komai ganinsa take kamar mafarki. Tausayinta sai ya kama shi sosai domin yadda hawaye ke mata zuba abun tausayi ne sosai ga wanda ya san zafin hawaye. Zaunawa yayi saman gadon sai ta zauna daf da shi kamar zata shige a jikinsa ta saki rigarsa ta kama hannunsa ta rike, shi kadai ne mutumen da take jin zata iya aminta dashi, ko ba komai shi ya bata irin abun da take iya ci kuma yayi kokarin fahimtarta har ta sake jiki da shi.

“Dr Tafiya za'ayi da ita”

Dayan police din da ya iso ya fada yana leko gurin.

“Yanzu?”

“Eh daga can office aka ce mu taho da ita za a wuce da ita Abuja ne?”

“Gurin me? Yarinyar da bata da lafiya?”

“Sun ce za a kula da ita a ne a can za su sama mata wani Asibitin, kamin a gano inda yan'uwanta suke, baban yarinyar da aka tsince ta a motar ne zai rika kamin a gano danginta”

Shiru yayi be ce komai ba, domin shi ma ya san yadda kasar take cikin domin yana cikinta, baya son ya shiga hurumin sa ba nashi ba, ba dan haka ba zai tambaya ya ji ko an hukunta wanda aka kama motar tata. But a yanzu ba shi ne babbar damuwarsa ba, damuwarsa ina za a kai wannan yarinyar? Da gaske rika ta din za'ayi ko kuma so ake a yi mata wani abu a rufe case din? Idan ma da gaske ne abu ne mai wahala ta yarda da bisu idan ta bisu kamin ta saba abu ne mai wahala domin ya lura da yanayinta tana da wuyar sabo. A take ya ji tausayinta ya cika masa zuciya sai dai babu yadda zai yi ya hana faruwar hakan domin ba huruminsa ba ne.

“Okay zamu shiryar takardar transfer, wace asibitin za a kaita a Abuja?”

“Ba mu da masaniya akan wannan”

“Ya kamata ku sani, saboda kar a cutar da yarinyar nan, ina ganin huruminku ne”

“Eh zamu sani ai dole, for now dai ba mu sani ba saboda case din a hannun manyan mu yake, su za su kula da komai”

Daga haka be sake cewa komai ba, har aka dauko masa tarkadun da komai suka miko masa yayi rubutu a kai sannan ya mikawa police din file dinta ya mike tsaye, tana ganin haka sai ta mike tsaye, a karon farko ta lura da fankar dake lake a sama tana bada iska, tun da take a rayuwarta bata taba sanin wani abu makamancin wannan ba sai yau, kallon fankar take sosai tana mamakin minene a gurin. Bata ankaro ba ta ji an taba hannunta dubawar da zata yi sai ta yi arba da masu bakaken kayan nan na jiya suna kokarin bata da mutumen da take jin kamar ta dade tare da shi. Wani irin kara ta saka tana fisgar hannunta tana son ta kubuce daga rikon da suka yi mata amman ina karfi ba daya ba, ko a babba balle ita da take matashiya, da karfin tsiya suka rabata da Dr da zuciyarsa ke masa ba dadi shi ma jin yake kamar ya dade tare da ita, musamman da be san inda za a kaita ba, Allah kadai ya san abun da za'ayi mata wata kila cutar da ita za ayi be sani ba. Fashewa ta yi da wani irin kuka ta fara fisge fisge police din ya dauke ta sama sai ta miko hannu tana son riko Dr Shuraim daya fito waje ward din yana kallonta zuciyarsa na masa ba dadi, hannu kawai take miko masa alamar ya rikota tana girgiza kai tana kuka sosai kamin ta kai bakinta ta gantsawa Police din cizo ba shiri ya sake ta sai ta rugo a guje ta gurin Dr Shuraim ta rumgumeshi da karfi tana kuka, dayan police din ne ya zo zai rikata sai Dr ya dakatar da shi.

“Kyaleta”

Hannu ta kai ta bugu Dr Shuraim da mugun karfi da kafa bakinta a kirjinsa ta cijeshi tana dukan kirjin nasa, so take ta ce miyasa zai bari a tafi da ita amman bata da bakin fadin haka domin bata jin yaren da suke fahimta kamar yadda su ma basa iya fahimtar yarenta. Sai dai kwarewa irin ta masu basira da hikima sai ya fahimcin haushinsa take ji, hannu ya saka yana rarrashinta.

“Yi hakuri ya isa”

Shiru ta yi kamar ba ita ce ta bude baki tana ihu ba, sai ta yi tsit ta kwantar da kanta a jikinsa kamar mage ta rufe ido gam, mutane suka yi cincirodo sai kallon ikon Allah suke, daga ma'aikan Asibitin har wandan ake jinya da masu jinyar, wadanda ba sun da zamanta ba a gurin ba ma sai da suka sani, har yan wani Ward din sai da suka zo kallonta.

“Dr ka samu mata”

Wani likitan ya fada yana zolayarsa, Dr yayi murmushi be ce komai ba, ya kalli police din ya ce

“Bari na dauko kayana sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login