Showing 192001 words to 195000 words out of 281271 words
Maleek ba dan shi Maleek din ya fahimci zuciyarsa ba.
“Idan kuma mahaifiyarka da gaske take fa? Ameer ba zai cutar da Waira ba? Kuma idan muka yi bincika muka tabbatar da haka zaka yarda mu aura masa ita?”
Kamar an kashe mutu haka Maleek yayi shiru a wayar ko numfashinsa ba aji Abiey kuma yana testing dinsa ne domin gane ko daidai a ma'aunin da ya dora ďansa Maleek. Rasa yayi me zai ce idan yace ko a haka be be dace da aurenta miye hujjarsa? Saboda ya wulakanta ta could be enough? Idan kuma babu hujja zai iya yiyu ace ya tsani Ameer din ne.
“Abiey yarinyar nan bata dace da aure a yanzu ba, ni da zaka dauki shawara kuma ka amince ka saka Ummi ta amince zan fitar da ita waje ta yi karatu mai kyau kamin ta dawo ta yi hankali ta san kanta then by that time tana da yancin zabar abokin rayuwa, amman a yanzu ko ba Ameer ba ni bana son ganin kowa a tare da ita, ita fa bata san wa take so ba, kalli yadda ta rika waken tana son Shuraim a baya sai ka dauka saurayinta ne, idan wani ya samu irin haka ai sai iya amfani da weakness dinta ya cutar da ita, bayan duk abubuwan da ta yi going through”
“Maleek”
Abiey ya kira sunansa a natse.
“Na'am”
“Umminka ta san ka kira ni?”
“Okay don't tell her, karka ma nuna mata mun yi waya, maganar Ameer da Waira kuma ka barta a hannuna Waira tana karkashin iko na ne a yanzu, that's mean nine jagoranta a yanzu, and na manta ma ban fada maka ba, tun kwana baya na saka a bincika min garinsu ko za a samu danginta”
“Okay”
Maleek ya fada sannan ya sauke wayar yana dan jin sassauci a ransa, dazun kan jin yake kamar ya cire zuciyar daga kirjinsa ya jefar tsabar bakinciki da rudani. Gallary wayarsa ya shiga ya kama hoton Waira da ya dauke ta tana bachi ya sakar mata ido kamar wani maye, can kuma ya kai hannunsa yana shafa screen din.
“Yadda kike da kyau nan kika fada hannun Ameer ai kin shiga uku, yana gama abun da ke kudirinsa zai maida ke karamar bazawara, kara dai idan kika wayo a aura miki mutumen kirki wanda ya san mutumcinki, ba mamaki ma wannan kyau naki ne yake rudarsa”
Magana yake da kansa yana jin cewar Waira da wani mutum mai mutumcin da sanin ya kamata ta dace ba Ameer ba. (Ni kuma na ce Maleek har yanzu baka san ka fada ba? Hmmm muje dai zuwa mahauci ya hau kura)
AMEER POV.
After yayi dropping Humairah ya nufi gurin friends dinsa he spends time with them sai bayan Sallah Isha'i ya nufi gidan Daddy. A al'adar da ya daukarwa kansa a yanzu yana shiga gidan fuska a not like can baya da yake musu yadda yake so. Teema ce amsa nasa sallamat da yayi domin ita kadai ce a falon.. Tsabar farinciki da murnar da yake ciki sai ya isa har inda take zaune ya ja mayafinta.
“You know Daddy na yawan fadar na yi aure ko zaku bi sahu ko? To nidai am already dan haka sai ku fito da na ku”
Ta wara ido with full of surprised ta ce.
“Da gaske? When? Wace lucky girl ce wannan?”
“Za ku ji a gurin Daddy”
“Wow I'm so happy”
Ta mike tsaye cike da murna tana kiran Mummy.
“Mummy sauko ki ji Mummy Mummy”
Ameer yayi saurin rufe mata baki.
“Keee sirri ne wannan daga ni sai ke, bana son kowa ya ji, idan ma wani zai ji to zai fito daga bakin Daddy ne”
Ta daka tsalle tana murna.
“Okay shikenan ba zan fada ba”
Murmushi yayi ya nufi upstairs hakoransa basa rufuwa saboda farincikin da yake ciki, gaba daya a yau ji yake kamar an masa kyautar Waira. Ya shiga wanka yana murza sabulu a jikinsa yana rausayawa yadda zai rayu da Waira yake tunani, one day ace tare za su yi wanka, gata ta iya zuba shagwaba yadda zata narke masa a jiki tana kuka yake da raya a zuciyarsa. Ya fito wanka ya fada saman gado kamar wani karamin yaro ya saka tawul ya goge kansa. Ya gama shiryawa ya tsaya gaban madubi yana kallon kasan ya dauki wayarsa yana yi ma kansa selfie, a yanzu kam ya yarda son Waira ba kadan ya kama shi ba, domin soyayyarta na kokarin maida shi wani karamin yaro, shi da yake ganin ya fi karfin karamar yarinyar yar under 20yrs. A yanzu ya yarda soyayyar gaskiya bata bukatar ado, kuma babu ruwanta da kyau ko muni, haka ma babu ruwanta da talauci ko arziki matsayi ko asali, kamin son Waira ya kama shi babu irin dokokin da be gindayawa soyayyarsa ba amman a yanzu ya mantasu gaba daya babu ko sharadi daya da ya gindayawa kansa.
Ya shiga bangaren Daddy yana ta zuba kamshi kamar kullum, fuskarsa har annuri take saboda farinciki da yake ciki. Daddy ma kallo ďaya yayi masa ya fahimci haka, sai kuma ya jidadin daman baya son yin maganar da shi a cikin wani yanayi na bacin rai.
“Fuskarka sake kamar ka san Mummy ta maka favorite dinka”
“Kai kace ta yi min? Ko kuma ita ta yi da kanta”
Daddy ya daga hannunsa a kokarinsa na gyara hannun Egyptian Jallabiyar dake jikinsa saboda ya ji dadin cin abincin na dare da kyau.
“Ni na ce ta girka maka, saboda ina da special abu da zan fada maka kuma zan roka ka min, and i hope ba zaka ce min aa, na yanke shawara ne ba tare da saninka ba, sai dai ban yi hakan dan na bata maka ba, sai dan ina ganin zai taimaki rayuwarka, domin abu ne da na dade ina jira, kuma na ga kai kamar baya gabanka dan haka zan matukar farinciki idan ka amsa min, sai dai ban ce ka amsa a dole ba, domin ka san na fi kowa son abun da kake so, ina son farincikinka fiye da komai”
Ameer yaja kujera ya zauna gabansa ya soma faduwa zuciyarsa na raya masa kamar Daddy zai gabatar masa da wanda be zata ba ne a matsayin wanda zai aura, ba dan ya san wacece ba, sai dan ya fahimci kamar hakan din ne duba da kalaman da ke fitowa a bakin Daddy. A take yaji kamar an datse masa rabin jindadin da ya shigo da shi gidan, a kokarin na ganin ya kawar da tunani ko bukatar Daddy yayi yunkurin yin wani abu.
“Ina tunanin babu wani abun da zaka bukata ko ka gabatar min na ce maka aa ko da kuwa zai cutar da ni, balle kuma na san ba zaka so abun da zai cutar da ni ba, zan baka dama ka fara saboda ka gabatar da cewar kana son magana da ni tun a jiya da safe, amman nima ina da maganar da nake son na fada maka mai muhimmanci”
Daddy yayi masa alama da hannu.
“Go ahead you first..”
“No Daddy ai ka riga ni”
“No ina saurarenka ai kai ka fara”
“Amman ni ne babba dan haka na baka umarni ka fara fada min”
Ameer yayi murmushi, sannan ya dauki plate ya bude abincin ya fara zubawa.
“Daddy idan baka manta ba, last year da aka yi rigima da Maleek da kuma kanwarsa Nimra akan wata yarinya da aka gani bayan motarsa har na ce ban santa ba ka tuna?”
“Ai ban manta ba go ahead”
“A zahirin gaskiya, na boye maka ne kawai kamar yadda na fada maka a baya, na san yarinyar lokacin da fushin zuciya ya dauke ni na tafi Katsina na shiga wani kauye da ban san kowa ba, kuma a al'adar mutanen garin idan bako ya zo suna aurar masa yar garin kamin su ba shi damar zama a cikin garinsu, to nima haka ne ya faru da ni, suka aura min yarinyar nan Waira sannan suka ba ni damar zama a garin, sai dai ko kamin safiya ta waye na fahimci al'adunsu da addininsu ya sha banban da nawa, kuma ba zasu yarda su bar ni na yi kalar addininsu ba, dan haka na gudu da yarinyar na baro garin ba tare da saninsu ba, da na zo da ita sai na barta a dajin ta nan maciji ya cijeta, kuma at that time na yi zaton ta mutu dan haka na nadeta na sakata a bayan motar na barta a nan ya dawo gida, saboda a wacan lokacin ban san yadda zan gabatar da ita a matsayin matata ba, kuma ni ban ma dauki wacan auren a matsayin aure ba, sannan ina ganin sigarta da tawa ma ba kala daya ba, but Now Daddy want to correct my mistakes ina son duk wanda na batawa na faranta masa kuma na roki yafiyarsa, now am already na karbi Waira a matsayin mata, kuma zan sakata a gaba muje har garin iyayenta saboda sanin asalinta, na san wannan magana ce babba amman na boye maka ne saboda zuciya tana raya min bad things a wacan lokacin amman yanzu Alhamdulillah komai ya canja and i loved her”
Kusan ya kwashe kafafuwan Daddy na cewa ya aureta tun a can, wani irin mamaki da ban al'ajabi ne ya bayyana a fuska Daddy ya sarkafe hannunsa da juna yatsunsa suka shiga cikin juna ya rasa ta ina zai kama zaren zancen.
[7/26, 9:39 PM] My S Line: 63
Abiey ya aje cin abincin dare da yake ci, ya kalli Ummi fuskarsa da shauki irin na wanda ke dauke da labari mai dadi. Ita ma dubansa take zaman jiran ya gama cin abinci take ta gabatar masa da kudin Ameer.
“Ina da labari mai dadi da zan fada miki, amman ba zan fada ba sai kin ba ni goro”
With surprise din da ya bayyana yanzu a fuskarta take sake duba Abiey.
“It seems like, we both have a good news to share, nima ina da labari mai faranta zuciya da zan baka”
Abiey ya girgaza kai yana fadada murmushin dake fuskarsa ya ce.
“Nawa ya fi naki dadin sauraro da kuma saka farincikinki, domin wani abu ne wanda ni da ke da duk wani makusanci yake jira, ba ma kamar ke da kika tashi hankalinki akansa”
Ta zurfafa a tunani wai ko zata hango albishir din da Abiey yake mata, amman ta kasa ganin komai, ta san bata gabatar masa sa zancen Namra ba na neman a bawa Shuraim dama ya turo magabanta sa, balle tace Abiey zai amince ne ba tare da jan wani dogon zance ba, haka ma ba shi da good understanding da Ameer balle ta ce Ameer ya fara sanar masa ne kamin ita.
“Na gane, Mr Bashir ya fada maka abun da Ameer ya fada min yau”
Abiey ya dauki spoon din ya cigaba da cin abincinsa wannan karon dariya yake.
“Baki canka daidai ba, Mr Bashir tun a lokacin da kike kokarin ganin Ameer ya san gaskiya rabon da na yi waya ko magana da shi, kuma wannan albishir din ba abu ne da ya shafi ďanki Ameer ba, wannan na ďana ne Maleek”
Cike da son sani Ummi ta kara matsawa kusa da mijinta ta rike spoon din da yake cin abincin ta saka cikin plate ta maida plate din gefe.
“Fada min wani abu ne mai faranta zuciya da ya shafi Maleek? Kuma ka ce abun da na dade ina jira ne”
“Kwarai kuwa”
Ya furta sannan ya dauki ruwa ya sha yana murmushin dake bayyana farincikin dake zuciyarsa ya ce.
“Madam sai fa kin ba ni goro”
“Shikenan zan girka maka abinci mai dadi gobe”
“Abinci kin fi kowa sanin be dame ni ba, kawai ki ce zaki min tukuicin zama ba tare da kin yi wani aikin ko da daukar cup ne ba har na tsawon wata daya”
Ummi ta san abu ne mai wahala ta iya haka, domin tana son taba aiki musamman ta tasan mijinta baya son cin abincin a waje sai dole, ta fi kowa sanin bukatarsa na son ta daina yin komai saboda ta samu hutu yadda ya dace. Sai dai ƙaguwa da ta yi na son jin albishir din ya saka ta amince.
“Na yarda”
Abiey ya mika mata hannu.
“Deal... ”
Sai ta yi dariya ta girgiza kai.
“Kai dai ba zaka taba girma ba”
“Girma saboda me? Dama ace akwai yara sai na san na girma amman daga ni sai ke a daki ki dauko min zancen girma, ai ni yadda kika san yaro dan shekara goma sha bakwai haka nake jin kaina ke kuma yar sha ďaya”
Ummi ta fashe da dariya sosai kamar ba ita ba.
“See har na manta when last ki min irin dariyar nan, shikenan kin maida ni tsoron karfi da yaji, alhalin zan iya auro yar Shida ko bakwai sa'ar Waira”
“Ko dai Wairar kake so? Daman ku maza komai kankantar mace ko tsufanta burgeku take, to an riga ka dai sai hakuri”
“Aa ni ido be taba kaiwa can ba, amman idon ďana Maleek ya kai gurinta, shi dai ya ga ruwan dake masa wanka, daman kuma na dade da fahimtar haka, kawai dai na saka masa ido ne na ga iya gudun ruwansa, na dade da fahimtarsa, ke baki ga haka ba? Yadda ya sauko ya canja rayuwa tun daga zuwanta gidan nan har zuwa yau?”
Kamar hoto haka Ummi ta tsaya kallon Abiey, gaba daya sai ta ji kamar an cire mata lakka jikinta babu karfi har na numfashi, duk wani farinciki da hanzari da take da shi na son fadawa Abiey abun da Ameer ya gabatar mata sai ya kau, rudani da tunani ya cika kwakwalwarta. Daman Maleek ya fada masa yana son Waira tun da dadewa ko kuma yanzu ne ya fada masa saboda ta fada masa Ameer ya ce yana sonta.
“Are you not happy?”
Abiey ya tambaya yana kallon yanayinta, shi kansa ya san ya karya mata guiwa, ya yanke zaren duk wata magana da take dauke da ita, cikin wani yanayi mai kama da rudani ta dube shi ta ce.
“Yaushe Maleek ya fada maka haka?”
“Gaskiya, an kwana biyu amman dai jiya ya nuna min yana son ki sani, shiyasa na fada miki”
“Meyasa baka fada min tun a jiya ba sai yau?”
“Ban samu zama ba, kuma kin ga yau na ga kina cikin farinciki kamar zaki fi jindadi”
Ta mike tsaye tana fara takawa, farincikin da Abiey yake tsammanin gani a fuskarta ya gagara bayyana, damuwa da firgici suka cika mata ruhi, da ace ba mace daya suke so ba, tabbas zata fi kowa farinciki, domin abun da take nema ne ya samu, musamman ma a gurin Maleek da bata taba ganin haka daga gareshi ba. Ta juyo ta dawo ta zauna tana ta kallon wani bangare na dakin.
Wa za'a bawa barwa? Wa za'a hanawa? Dukansu yayanta ne kuma dukansu tana bukatar farincikinsu, ba ma kamar Maleek ashe wata rana zai ji yana son wata a ransa har ya fada? A yanzu ta gane dalilinsa na sakin agogon da yayi a dazun da ta fada masa, sai a yanzu ta gane dan shirin da Maleek yake da Waira na soyayya ne, tabbas zuwan Waira ya canja rayuwar Maleek completely, kuma a yanzu ta tabbatar ya riga Ameer fara son Waira. Samun kanta ta yi da murmushi da kuma hawaye a lokaci daya, tausayinta da kaunarsa suka cika mata zuciya.
“Allah sarki Maleek”
Abiey yayi murmushi.
“Ni na dade da fahimtar haka, kawai dai na barshi ne saboda na san idan ta yi wari zamu ji”
“Amman....”
Sai kuma ta yi shiru ta mike tsaye.
“Ameer ya zo min da makamanciyar wannan maganar”
Mikewa tsaye Abiey yayi ya rike matarsa ganin kamar kafafuwanta ba za su dauketa ba.
“Me ya fada miki?”
“Shi ma makamancin abun da Maleek ya fada maka ne, amman abun da ban gane ba me yasa da Maleek ya ji be fada min komai ba? Kuma be taba nuna min ba? Sai ma takurawa Waira da yake ta wani babin?”
“Amman ke baki alamun yana sonta ba? Ni da nake namiji ma na lura da haka balle ke da kike tare da shi kullum? Ko irin yadda yake kokarin taka mata burgi idan tana hulda da wani ba ki lura da hakan ba? Kishi na cikin kauna, ke ma kuma kin san haka sai dai idan kin manta, kuma rayuwarsa ta sauya a yanzu”
Ummi ta kalli Abiey maganar da yayi mata a yanzu tana kara shiga cikin kanta, ta fahimtar da ita abubuwan da ta manta, da kuma wadanda ta gani bata fahimta ba. Ta san rayuwarsa ta canja zuwan Waira ita kanta ta fadi haka, zuwan Waira ya saka danta ya samu lafiya, a sanadiyar Waira ta fahimci danta na da samuwa har aka masa rokon Allah aka masa saukar qur'ane kuma aka yi masa dawafi a makka duk sa saboda ya samu sauki kuma ya samu.
“Maleek ya dade yana son Waira, sai dai shi ma be san sonta yake a lokacin ba, sai daga bayan nan, wannan dalilin ya saka na zurfafa a binciken danginta, ”
“Amman me yasa be fada min ba sai a yanzu da Ameer ya fada a fili? Bayan kuma ta dade a gidan nan?”
“Ban sani ba, wata kila sun fada a lokaci daya ne, amman suna hankali da natsuwa irin ta Maleek mai tunani bana ganin zai yi hakan a yanzu da Ameer ya nuna yana son Waira, kuma ai Maleek ya fi shakuwa da ita, abun ya zama wani ace suna son mace daya”
Ummi ta kwanta jikin Abiey hawaye na sauko mata, farinciki ya jure mata ya zama bakinciki, domin ba zata raba Waira biyu ta ba wa kowa rabi ba, haka kuma ba zata iya bawa Ameer ta hanawa Maleek da be taba jin soyayyar kowa a zuciyarsa ba sai wannan karon. Ba kuma zata bawa Maleek ta hanawa ďanta Ameer da take ji da shi a yanzu ba, take tsananin kaunarsa bayan ta gama bayyana masa farincikinta da jindadin fada mata yana son Waira har ma ta fada masa zata shige masa gaba a komai, kuma shiri take bukata da shi a yanzu, so take ta bashi farincikin da bata samu damar tsayawa ta bashi a lokacin da yake karami.
“Maleek yana yawan cewa Ameer lalata Waira, saboda