Showing 198001 words to 201000 words out of 281271 words
tsakaninsu ba, kuma na san hakan zai haifar da matsala da karin rashin fahimta ne a tsakaninsu, a maimakon a samu mafita sai abun ya kara lalacewa”
“Ina ganin kamata yayi ki fito fili ki fadawa Ameer gaskiya nima zan sanar da Maleek”
“Ba lallai ne ya fahimta ba, Ameer yana da wuyar sha'ani, yar alakar dake tsakaninmu zata yi tsami, da ma ace zan iya tankura Maleek wata kila shi zai iya hakura, domin Ameer yana son Waira sosai fiye da tunaninka, yadda kike ganin kamar cutar da ita zai yi ba zai yi haka ba, na ga kaunarta idonsa”
“Amman kuma kika kasa ganin hakan a idon Maleek karki zama selfish mana Zahra, ni ma ina son farinciki ďana fiye da yadda kike son Ameer, ina bin komai a hankalin ne saboda Matsalar da kike ciki... Dan haka ina ganin abun da ya dace kawai a fitar da yarinyar nan waje ta yi karatu kamin mu ga abun da Allah zai yi”
Ummi bata da karfin cewa komai a yanzu, ta san Abiey ba zai fahimce ta, haka ma Ameer ba fahimtar da zai yi ba.
“Allah ya zaba mana abun da ya fi zama alheri, bari na shiga kitchen”
Ta wuce ta nufi kitchen, yana ganin haka ya san akwai abu a kasan zuciyarta daman shi ma juyawa yayi ya fice daga falon ya koma bangarensa. Sai da ya wuce sannan Waira ta sauko daman tun dazun tana labe a saman ba dan tana ji abun da suke tattaunawa ba kuma ba dan tana son ta ji din ba, sai dan bata son Abiey ya ganta, domin zuciyarta na yawan raya mata Abiey baya sonta. Ta sauko ta shiga Kitchen sai ta Ummi ta rike fridge sai kuka take a hankali, ta saba ganin Ummi a kitchen da asubar fari irin haka, amman sai idan akwai dalili kamar tana son shirya abun karyawa da wuri saboda wani ko ita, amman a ka'ida Ummi bata shiga kitchen sai 6:30am ko 7 ma.
“Ummi...”
Ummi ta juyo ta kalli Waira da ta kira sunanta, sai ta ji kamar ace tana da wani iko da zata cewa Waira ki cire sonki a cikin zuciyar kowa.
“Are you okay, ko Abiey ya miki fada ne na ganshi ya zo”
Ummi ta share hawayenta.
“Labe kike mana?”
“Aa na zo zan shiga dakinki na dauko abun sallah ne sai na hango kin fito na zo saukowa sai na ganshi shiyasa na koma na boya na san ai baya so na”
“Abiey be tsane ki ba Waira ki daina saka wannan a zuciyarki”
Ta daga mata kai son sanin damuwar Ummi da abun da ya saka ta kuka ya saka Waira tambayar Ummi.
“Ummi can I hug you?”
Ummi ta daga mata kai, sai ta rumgume Ummi ya rufe ido, babu abun da bata gani ba, tun daga kan maganar da Ameer ya fadawa Ummi har zuwa wanda Abiey ya fadawa Ummi akan Maleek da kuma na yau da Abiey yayi magana da ita. A cikin duk abubuwan bata ga na damuwa ba, da zai saka Ummi kuka ba, domin duk cewa suke suna sonta ita kuma a gurinta haka abun ne mai kyau sai dai kalmar aure da ta yi ji a ciki shi ne abun da ya fi daga mata hankali. Ta dago daga jikin Ummi ta kalleta sai Ummi ta sakar mata murmushi.
“Mun yi magana da Abiey ne akan yana son ya fitar dake wata kasar ki yi karatu”
“A nan fa?”
“Ba wai na aminta ba ne, zan yi shawara na ga idan hakan ya dace kuma idan kina ra'ayi”
“Bana so, bana son wani gurin da ba nan karatun da nake a nan ma ya isa ai, ba kullum ina zuwa school ba, Mai Lesson ne ya daina zuwa ai amman ni ban fasa yin darasi ba”
Tana fadar haka ta saki Ummi ta fice daga kitchen tana shirin yin kuka.
AMEER POV.
“Abun is na ma rasa me zan ce”
Ameer ya hade yawu yana marairaice fuska kamar gaske.
“I know shiyasa tun farko ban fada ba, amman yanzu ina kokarin ganin na gyara abubuwan da na bata ne, dan Allah karka min mummunar fahimta ne”
“Nonono ka yi tunani mai kyau, amman aure ba abu ne da za ayi wasa da shi ba, kuma a yanzu da kake kokarin gyara abubuwa hakan yana da kyau, sai dai dole ne ka nemi afuwar yarinyar”
“Zan yi haka Daddy, na gode sosai da fahimta, me kake son mu tattauna?”
“No karka damu wata rana zamu yi magana akai ci abincinka”
Daddy ya fada da murmushi a fuskarsa, Ameer ya fara cin abincin yana jin wani iri, domin be tsaya ya saurari shakuwar Daddy ba, kuma be kamata yace masa no a duk wani abu da zai gabatar masa ba, shi dai be masa wannan karyar dan kawai ya hana shi fadar abun da zai fada ba, sai dan ya samu mafitar gabatar masa da Waira kamin shi ya gabatar masa da wata a matsayin matar aure.
“Daddy ba zan jidadi ba idan baka fada min abun da kake son mu tattauna ba, please ka fada min ko gankali zai kwanta”
“Zan fada maka amman ba yanzu”
Cewar yana murmushi sai dai zuciyarsa ta kasa yarda abun da Ameer ya fada masa a yanzu, kuma ya kasa natsuwa wata kila saboda ya ji abun ne wani irin kamar ba abun da kai zai kama ba. Ameer yayi bachi a daren mai dadi da saka nishadi, saboda tunanin Waira. Washe gari da 6:30am ya fita daga gidan zuwa gidan Ummi saboda ya samu kai Waira School da wuri, domin ya daukarwa kansa nauyin kaita makaranta kullum kuma ya daukota. Bakwai da yan mintuna ya iso gidan ya shigo falon yana ta zuba kamshi. Sai dai yana shigowa ya tararda Mahmood da Maleek da Namra a dinning sai ya saka jin babu dadi, kara ma Mahmood suna dan good time da shi, amman Maleek da Namra makiyansa ne kamar yadda shi ma suke kallonsa a makiyansu, Sai dai ganin Ummi da yayi ya dan saka shi jin sanyi, ya karasa gurin cikin gadara ya dafa kujera ya gaishe ta.
“Ummi ina kwana”
Ta dago ta kalleshi yanayi fuskarta da idonta sun fada masa ba lafiya ba.
“Lafiya Kalau how was your night?”
“Alhamdulillah”
“Ga breakfast din nan”
“Let me drop Waira makaranta first”
Yana fadar haka ya juya ya nufi upstairs, Maleek ya ji kamar ya juya ya ce masa wani abu, sai kuma wata zuciyar ta hana shi sai dai be jindadin yadda yake kai Waira makaranta a kullum.
“Ya iso nan baku gaisa ba? Anya rayuwa zata yiyu a haka? Kuna abu kamar ba yan'uwa juna ba, sai k”
“No Wallahi mantawa na yi mun saba gaisawa da shi ai”
Mahmood ya fada yana wanke kansa Namra da Maleek ne dai ba su ce komai ba. Hakan kuma be yi ma Ummi dadi ba. Ameer ya haura sama ya tura kofar dakin Waira ya shiga, sai ya same ta zaune saman gadon tana ta kuka shabe shabe har muryata ta shake. Da sauri ya karasa kusa da ita ya risina gabanta ya kai hannunsa ya dago fuskarta tashin hankali ganin hawayen sahibarsa karara a fuskarsa.
“Lafiya waya taba ki?”
“Bana so Ummi tace Abiey zai kai ni wata kasa karatu, ni kuma bana so”
Cikin tsananin kuka take fada masa iyakar gaskiyarta bata son barin gidan nan, domin ta sha wahala kamin ta sabu da su, taya za a kaita wani gurin kuma inda bata san kowa ba? Kukan da take na kiyayyar tafiyar ne Ummi bata ma san tana kukan ba, gaba daya tunaninsu tana ciki tana shiryawa.
“Abiey baya so na na sani shiyasa zai min haka”
Ta sake fada cikin muryar kuka. Ameer ta mike tsaye rai a bace ya fice daga dakin tun kamin ya sauko kasa ya fara aiko da tambaya rai a bace yana nuna upstairs.
“It's because of na ce ina son Waira shi ne Abiey zai dauke ta ya kaita waje karatun?”
Gaba dayansu suka dago suna kallonsa, Mahmood da Waira da ba su san abun da yake faruwa ba suka ji abun kamar daga sama. Ummi ta nufeshi da sauri tana girgiza kai.
“Aa daman akwai wannan maganar tun da dadewa kuma ba wai an yanke hukunci ba ne za a duba aga idan abun da zai a iya ne”
Ummi ta kai hannu ta dafa kirjinsa domin ta lura da yadda ya dauki zafi gaba daya yanayinsa ya sauya. Maleek ya mike tsaye ya nufo inda Ameer yake tsaye yana fadin.
“No ba Saboda haka ba ne, saboda ya isa da ita ne, saboda yana jin shi ya riketa ya yi mata komai a lokacin da ka gudu ka barta kuma ka ce baka santa ba, a yanzu Abiey ne gatanta yana da ikon yayi yadda yake so da ita, a ciki har da yiyuwar duba baka aurenta ko akasin haka, cancantarka ta kai a baka innocent girl like Waira ko kuma aa, so kai ma a karkashin ikonsa kake a yanzu dan haka ka taka a hankali, nan gidansa ne karka manta”
Ameer yayi murmushi ya nunawa Ummi Maleek da hannu.
“You see i told you ai, ba takamarka gida ni da Waira zamu bar muku gidan, sai ka yi yadda kake so, karka manta nine silar zuwanta a nan gidan, idan kuma kudi ne damuwarku then tell me the price i will pay”
Namra ta mike tsaye ta nufo inda yake tana daka masa tsawa.
“Daga baya kenan? Wai Ameer me yake damunka? Taya zaka tsaya a gaban idonmu kana fadar magana son ranka kamar kai kake mulkarmu? Baka da wannan yanci ya kamata kasan da wannan, kuma price din da Abiey ya kashe gurin gina rayuwar Waira ba zaka iya biya ba, domin baka da komai kuma baka yi gadon komai ba sai tsiya, kai ba dan babban attajirin da kake kallo a matsayin uba ba ne a yanzu, kai dan talaka ne jikanta talaka jikar tsohuwar dake bara a titi, kuma dan uban da aka rasa kudin aikin mahaifinsa har sai da aka siyar da cikinsa you're nothing Ameer but pieces of trash...”
Tana kai aya Ummi ta kai hannu ta juyo da ita ta wanke mata fuska da mari hudu masu kyau, sannan ta nuna ta da yatsa jikinta na rawa ta ce.
“Ban yafe ba, idan kika sake fadawa Ameer wata mummunar kalma makamanciyar wannan Allah ya isa tsakanina da ke...!”
Maleek da ke tsaye gafen Ummi tana kallonta da mamaki ya ce.
“Ummi akan Ameer din?”
Tasaaaass kake ji Ummi ta bashi na sa kason na mari.....
[7/27, 5:45 PM] My S Line: 65
“Ummi you slap him...?”
Mahmood ya fada with shock yana kallon Ummi.
“Duk abun da kuke yi, ba Ameer kuke yi ma ba, ni kuke yi ma, saboda ni komai ya faru, idan zaku ci mutumcin Ameer ku fuskance ni kai tsaye ku ci mutumcina amman ba Ameer ba, idan baku kaunaci junanku a yanzu da nake raye ba when zaku so junanku? Bayan na mutu? When when when?”
Ta tambayi Ameer ta tambayi Maleek ta tambayi Namra dake dafe da kunci tana hawaye.
“Kwana nawa ya rage min? Kullum kokarin gada kanku nake amman sai kara bandarewa kuke yi? Ni haka zan gama rayuwa cikin bakincikin yaya? Why? Kuma ace duk saboda mace kuke wannan abun? Ni kadai ce uwa? Ba ku san abun da yake damuna ba, a kullum kara min bakinciki kuke”
Maleek ya sauke ajiyar zuciya a hankali.
“I'm sorry Ummi ban yi saboda na bata ranki, abun da Ameer yayi ne ya wuce hankali, please forgive me amman zan tabbatar masa da cewar be isa ya dauke Waira daga gidan nan ba, ko da kuwa hakan na nufin yaki”
Fita yayi daga falon bayan gama fadar hakan, Namra kuma ta haye sama tana kuka sosai. Mahmood ya watsawa Ameer wani banzan kallo ya fice a fusace. Sai aka bar Ameer a tsaye jiki babu karfi kamar wanda aka sarewa gaɓoɓi ya kasa motsawa daga inda yake saboda gorin da Namra da Maleek suka masa ta ce. Ummi ta kalleshi a hankali tana hawaye.
“Are you happy now? Dan farinciki da kowa ya tashi da safen nan ka wargaza shi, ga breakfast dinka can ka ci kafin ka fita”
Ta zagaye shi ta haye sama, tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta kira Ya Maryam domin take kallo a matsayin uwa a yanzu kuma ita ce abokiyar shawararta. Ya Maryam ta numfasa bayan ta gama sauraren Ummi ta soma bata shawarar abun da take ganin zai fi zame mata mafita.
“Ba zaki iya zabe wa zai aureta a cikin yayanki ba, kuma irin wannan rashin jituwar dake tsakaninsu zai iya haifar da gaba da kiyayya da zata shafi yayansu kuma ta cigaba da bibiyarsu har bayan rayuwarki, ni dai a nawa ganin karki bari kowa ya aureta a cikinsu”
“Ni ma na yi wannan tunanin, kuma abun da ya faru a yau ina yi ma Ameer uzuri, a yadda na fahimta yana da saurin fushin zuciya, kuma a yadda Waira ta fada masa kai tsaye za a kaita waje karatu dole yayi zaton saboda shi ne, na san be kamata yayi magana a tsaye ba, amman....”
Ta yi shiru. Ya Maryam ta ce
“Zahra kina son Ameer da yawa ko ba haka ba?”
“Ko wane ďa da irin yadda Allah yake dorawa uwa soyayyarsa a zuciyarta, Ya Maryam ina jin kamar na cutar da yaron nan, ina jin kamar rashin kasancewarsa a kusa da ni ne ya haifar duk wani hali da yake ciki, wata kila da yana tare da ni da haka be faru ba, kuma idan ban so Ameer ba waye zai so shi? Mahaifinsa be raye a yanzu, Abiey baya son Ameer ko kadan na lura da haka, a dan lokacin da ya rage min ina son na kyautata masa, ko da shi zai munana min idan bana raye zai yi nadama kuma zai gane na nuna masa soyayya”
“Haka ne, maza da yawa basa son ƴaƴan matansu, kalilan ne suke so, balle kuma Abiey da yake da riko da kasa manta abubuwa, sai hakuri”
“Amman su mata suna son yayan mazanjensu ko? Na rike nasa yayan kamar nawa, hakan be isa ya saka shi son Ameer ba?”
“Rayuwar namiji dabam take da ta mace, haka ma zuciya kuma hakan ba yana nufin baya sonki ba, na fi kowa sanin Abiey na kaunarki”
“Maso uwa ya so ďandanta Ya Maryam, idan bana raye alaka zata yanke tsakanin yayan Abiey da Ameer”
“Dole ki jajirce ki ga komai ya daidaita tsakaninsu, saboda gaba, kuma ina son na ja hankalinki karki sake yi ma dayansu irin wannan hukuncin na duka a gaban Ameer, idan ma zaki yi to ki kebe kowa dabam Kuma ki saka addu'a a gaba kina rokon Allah ya hada kan yayanki nima zan taya ki, ina nan zuwa satin sama In Shaa Allah”
“Toh Ya Maryam Na gode Allah kawo ki lafiya”
Daga haka suka yi sallama. Ummi ta aje wayar ta mike tsaye ta shiga bedroom ta wanke fuskarta ta fito gyara daurin dankwalinta sannan ta fice daga dakinta zuwa dakin Waira har lokacin kuka take idonta ya kumbura sosai har wani numfashin take sama_sama saboda kukan da take. Ummi ta karasa cikin dakin ta zauna bakin gadon Waira a yayinda Waira take zaune kasa, this is the first time da ta ji bata son zaman Waira a gidan ba dan ta gundira da ita ba sai dan matsalar da zamanta a gidan zai haifar ga ƴaƴan da take neman hadin kansu.
“Me yasa kika fadawa Ameer za a kaiki wani gurin karatu? Idan ina bukatar ya sani ni zan fada masa ba ke ba”
Waira dake zaune kasa ta dago ta kalli Ummi tana jan numfashi kamar zata shide.
“Shi ya tambaya me yasa nake kuka? Ummi bana son na bar gidan nan please”
“Ya zama dole kuma, domin Ameer da Maleek fada suke a kanki, ni kuma hadin kan yayana nake bukata ba watsewarsu ba, saboda ke yau Maleek yayi ma Ameer gori, saboda ke Ameer ya fadi maganar da bata dace ba akan Abiey, saboda ke Waira hadin kan yaya zai tarwatse, fada suke akanki”
“Saboda me?”
Ummi ta kasa bata amsa sai ma mikewa da ta yi tsaye ta nufi gurin da take aje uniform ta dauko mata.
“Tashi ki saka uniform kin yi wanka?”
“Eh na yi wanka”
“Okay ki saka uniform dinki lunch box dinki yana dinning zan yi ma driver magana ya kai”
“Ameer fa?”
“Ya fita daga rayuwarki daga yanzu, ki manta da shafin rayuwarsa, ki goge shi a zuciyarki”
Waira kallon rashin fahimta kawai take yi ma Ummi har ta fice daga dakin. Da tunanin Waira ta saka uniform din bata damu da yadda fuskarta take da jurwayen hawaye ba ta sauko ta dauki lunch box dinta.
“Waira zaki iya gane garinku?”
Ta juyo da sauri ta kalli Ummi dake saukowa.
“Aa ba zan iya ganewa ba, a ka'ida sarki yace idan na gudu ba zan iya gane hanyar gida?”
Ummi ta zauna a one of dinning chairs tana kallonta.
“Me yasa kika gudu?”
Waira ta sauke kanta kasa wasu hawayen na cika ramen idonta, bata tunanin ta taba fada musu dalilinta na guduwa idan na ta fadawa wani a cikinsu Ameer ko Jabir da ta sakewa da yawa.
“Wani aka kashe aka ce ni na kasheshi kuma ban aikata ba, kuma idan na kai wasu shekaru za a bani sarautar tsafin garin ni kuma bana so saboda zasu kashe ni ne idan na mutu”
Ta aje lunch box din ta bude hannun uniform dinta ta nunawa Ummi wani tabo dake hannunta.
“Gadon mu ne, idan an haihu ake mutuwa, a cikin wannan tabon ina ganin abun da ya faru da mutum a baya, ina iya kashe wani idan ina so, ta ciki na iya gane ciwonki da damuwar da kike boyewa ta Ameer, tun kamin ki fada, ta ciki dazun na ga abun da Abiey yayi magana da ke, da zarar na rumgume mutum zan iya ganin komai ko na san komai”
Ummi ta mike tsaye tana kallon Waira da mugun mamaki.
“Kina tsafi kenan? Ban taba yi ba, sun ce sai na girma zan iya saffara komai yadda nake so, a garin mu kowa matsafi ne sai dai wani ya fi wani karfin tsafi, wanda ba dan garin ba baya shiga, rayuwarmu da