Showing 3001 words to 6000 words out of 281271 words
yaja ya zauna ya kalli mahaifinsa dake kallonsa da irin duba na mai laifi. Fadada fuskarsa da murmushi shi ne abun da ya fara yi sannan ya dauki plate ya soma zubawa kansa abinci.
“Miyasa ka kori ma'aikatanka?”
Ya dan tsaya daga zuba abincin da yake, ya kalli Daddy.
“I told them kar wanda ya sake shigo min office da kazanta, shi dayan be ji ba na lura rigarsa ta jiya ce ya maimaita kuma be wanke ta ba, dayan kuma karni yake Daddyn kasan yadda nake jin warin mutane, bana son kazanta ko kadan kuma bana son na ji mutum ba kamshi”
Daddy ya girgiza kai cikin damuwa.
“Amman Ameer wannan be kai ace ka sallame su daga aiki ba? Kuma bayan sallamar ka ce ba za a ba su salary su na wannan watan ba, secondly an fada min jiya ka kade wani mutum da mota”
“Shi ma wasa yake da brayuwarsa, overtaking yayi, ya ba ni haushi sosai shiyasa na yi masa haka next time ai zai san muhimmancin rayuwarsa”
“Wannan duk ba hujja ba ce Ameer, rayuwar mutum tana da muhimmanci”
Cewar Momy tana kallon ďa ďaya tilo Namiji kuma farincikin mijinta.
“Zan kiyaye next time, amman dai hakan ba yana nufin wani banza ya taka ni na kyale shi ba, kuna da damuwa da mutanen da be kamata mu damu da su ba”
Ya tsayar da cin abincin da yake ya sake duba mahaifinsa.
“But Daddy I'm sorry”
Da sauri Mr Bashir ya girgiza masa kai domin ko kadan baya son bacin ran ďan nasa Ameer.
“No No No don't, Daddy loves you so much”
Ameer yayi murmushi ya cigaba da cin abincinsa.
“Daman ai kai baka laifi a gurin Daddy da dai mu ne”
Cewar Teema sai duk suka saka dariya har Daddy, Ameer ya kai fork dinsa ya dauko namanta ya cinye sai ta fara kukan shagwaba, dariya yayi ya mike tsaye tare da daukar kofin lemun dake gaban Daddynsa.
“Momy thank you for the lunch yayi dadi sosai”
“Baka ci komai ba ai ka tashi, ina zaka je?”
“Abokaina ke jirana akwai inda zamu je yanzu nan”
“Take care”
Daddy ya fada masa yana kallonsa, domin ya san ba karamin aikinsa ba ne a kira shi a sanar da shi Ameer yayi wani laifin ko kuma yayi fada da wani ko ya karya wata dokar kasa.
“I will Daddy ba zan janyo maka magana ba”
Daddy yayi murmushi, sallama Ameer yayi musu sannan ya fice daga bangaren.
___________________
Ga wani sabon zubi,
Sabuwar shimfida mai zafi
A sabuwar Shekara.
ku daura Belt dinku domin wannan tafiyar ba mai sauki ba ce.
Haka kuma ba free book ba ne, paid book ne a 300.
Few pages ne muke da su na free, sauran duk na kudi ne.
One page ne kullum da yarda Allah, sai dai bana posting Monday da Friday, saboda wani uzurin, haka kuma idan ban samu yi a ranakun posting ba zan sanar kuma zan ranka page din In Shaa Allah.
Yadda na fara lafiya Allah ya amince min na karasa shi cikin aminci da farinciki, Ameen.
Ina fatar zaku karbe shi hannu hudu ba ma biyu ba. 🥰
If you want to Subscribe pay 300 to
2451879008
Hadiza Abubakar
Zenith Bank
And sent the evidence of payment to 08036126660
Yan Nijar zaku biya ta wannan line +22790165991
Za ku iya samun WANI GARI a Arewabooks @KhadeejaCandy domin pages din can za su dara na nan yawa.
Lastly idan kin san zaki biya domin ki fitar dan Girman Allah da ya hallice ki karki siya, idan kuma kika fitar min hakika kin cutar da ni kuma idan ina da hakki Allah zai saka min domin ba zan yafe ba.
Happy reading 🫶🏻
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
_Na Khadeeja Candy_
2️⃣
Sai da ta gama rawar sannan ta shiga cikin gidansu ta zarce bandakin da aka hada manyan itace gurin ginashi, ta saka tokar murhu ta goge jikinta tare da bakin gawayi, sai da ta tabbatar jikinta ya yi tass sannan ta dauki ruwan dake cikin kaskon kasa ta zuba tun daga saman gashin kanta har zuwa kafarta, ta saka talkamin danko ta fito bandaki tana daure da gayen ayaba ta shiga dakinta. Wata brown gown ta dauko doguwar rigar da zata tsaya iya guiwar kafafuwanta ta bayyana farare kuma tsala tsala cinyoyinta. A hankali ta yaryarda gashin kanta ya kwanta bayanta, sannan ta fito waje ta nufi wani itacen fulawa ta tsinke fulawar ta laka a kanta.
Daga gurin ta fara ajujuwa tana dariya har ta isa gurin da ruwan saman da aka yi mai kama da bakin kwarya ya kwanta sai ta leka kanta tana kallon kyakkyawar fuskarta, da yadda furen fulawar ya kawata jikaken gashin kanta. Babu madubin duba fuska a kaf fadin garin, idan mace ko namiji suka yi kwalliya ko suka zo ganin fuskokinsu suna zuwa ne a gurin da ruwa ya wanta irin wanda yake aje a guri daya baya motsi su kalli kansu, wasu kuma suna zuba ruwan ne a wani muhalli na dabam su bar shi a ciki a matsayin madubinsu sai kuma ma su amfani da tsafi su ga fuskarsu. Ta cikin ruwan ta yi arba da Eid yana kallonta fuskarsa da murmushi, a take ta juyowa tana murmushi ta kalli saitin inda yake tsaye, babu shi a zahiri domin ya bata a idonta da duk idon dan'adam mai gani, sai dai tana iya ganinsa a cikin ruwan yana kallonta, kyalkyalewa ta yi da dariya mai matukar dadin sauraro da burgewa ta tsallaka ruwan ta mike hanya tana tafiya sai ya mika hannunsa ya kama nata ya tsayar da ita daga tafiyar da yake, wannan karon ta ganshi ido da ido domin ya so ta ganshi din ne, ba a yau ya saba yi mata haka ba, ya boye mata kansa ta yadda sai ya ga dama zata ganshi, ita ma tana daf ta iya duk wani abu da ake da tsafi da zarar ta cika shekara 20, an bata kambun sarautar da aka aje mata tun gabanin haihuwarta.
“Eid”
“Waira... Kin yi kyau... Irin kyau da ya gagarin duk wata yarinya sa'arki, kyau yana zumudi kamin ya ganshi a fuskarka, kina yi ma kyau kyau Waira ke sarauniya ce ta kyakkyawan matan duniya”
Kwayar idonta yake kallo yana karanto mata baitukan da ke kama da waken da zuciyarsa take rubutawa. Fararen idonta masu tsananin farin da ya haddasa sauyawar kwayar bakin idon zuwa blue na zube a cikin nasa, murmushi ta yi irin murmushin dake kirgita duk wani saurayi mai jini a jika, ta cire hannayenta daga nashi ta yi gaba da fara tafiya tana masa magana da yarensu.
“Idan ban yi wanka ba, kana cewa ina da kyau, idan na yi wanka ma kana cewa ina da kyau, ta ya zan yadda?”
Yayi murmushi yana gyara walkin dake kugunsa.
“Saboda idan ba ki yi wanka ba, kina yi da kyau, idan kuma jikinki ya hadu da wanka yana yi ma wankan kyau”
Ta tsaya cak har sai da ya tararda ita suka jera a tare sannan ta kalleshi.
“Ka koyo karatu?”
“An haramtawa duk wani ďan garin Garuk koyon karatun wasu da ba na kasar ba”
“Kai ba gwani ba ne gurin sarrafa halshe”
“Na koyo ne saboda ke, kin taba fada min kina son sabon abu da ba kowa ya iya ba kin tuna?”
“A ina ka koyo?”
Ta tambaya cike da son sani, sai ya dafa kafadarta suka cigaba da tafiya kai kace masoya ne ba yan'uwa ba.
“Duniya tana da fadi Waira, mutane ko cikinta kuma suna da yawa, kowa yana dauke da baiwa da basira, idan kika yi nisa da garin Garuk zaki hadu da wasu jama'a masu saka tufafi ba irin na mu ba, suna kwalliya da kwana a muhallin da baki taba ganin irinsa ba, suna hawan motoci wasu kuma babura...”
Ta dago kai tana kallonta.
“Outa.. Outar... Ooter”
Haka ta yi ta maimaita kalmar mota amman ta kasa hada harufan a daidai balle ta furta kalmar ta fito yadda a yadda ake fadar ta, saboda ba yarenta ba ne, hasali ma bata taba jin kalmar ba. Dariya ce ta subuce masa ganin ta dage sai ta furta sunan Mota kuma ta kasa.
“Mota...”
“Minene haka?”
“Wani karfe ne da suke hawa, mai tsananin gudu fiye da dabobinmu, kala kalar karfe ne wasu sun fi wasu tsada wasu kuma a sake suke wasu kanana ne wasu suna da kafa hudu wasu kuma uku wasu biyu, suna cin abincin da ba irin na ku ba, ko kadan rayuwar bata kama da ta mu”
“Ta ina ka sansu?”
“Saboda ni ina tsallakawa na bar garin Garuk na iya yarensu na ci irin abincinsu, na saka kalar tufafinsu na kwanta a irin muhallinsu na shiga abun hawansu, sai dai ke duk baki san wannan ba saboda baki taba leka wani garin ba, amman jama'ar garin nan da yawa sun san da wadannan abubuwan saboda suna fita, wasu kuma suna shigowa a garin neman sa'a ko nasara akan wasu abubuwan, akwai yan garin nan da aka kora suka koma can, akwai kuma wadanda suka tsalle garin nan suka auri mutanen can suna maida rayuwarsu a can”
“Hmmmm uhmm a can ka koyo iya magana kenan?”
“Na koyo abubuwa da yawa daga garin, kuma na koyar da wadanda na aminta da su”
Ta rausayar da kai tana kallon wani katon tsauni mai tsananin tsawo, a take ta dauke hannunsa daga kafadarta ta nufi tsaunin da gudunta, daga inda yake tsaye ya daga muryarsa yana fadin.
“Suna da gidaje masu tsawo kamar tsaunin nan, wasu kuma ba su kai haka ba, wasu kuma sun dara, sai dai su ba a hawansu kamar yadda kike hawa”
“Ba su more rayuwa ba, wanda baya hawan tsaunuka yadda nake hawa be more rayuwa ba, wanda baya hawan itace be more rayuwa ba, ka fada musu duniyarsu bata kai ta mu dadi ba”
Tsayawa yayi yana kallonta cike da burgewa fuskarsa da murmushi, yadda take falfala gudu sai na rantse da Allah wani ya biyo ta ko yake kokarin kamata, sai dai ba ko daya tsananin kiriniya da iya hawan tsaunuka da tsananin gudu ya saka ta kware sosai, irin kwararwar da ace gasa ake ita ce zata zo ta daya, kamar ribi haka ta haye tsaunin har can sama ta mike tsaye tana kallon dajin da ba bakonta ba ne dajin dake cike da albarkar itatuwa da ciyayi ga kuma ruwa ta ko'ina, babu abun da take dai dariya ba tare da aman mata komai ba haka take a duk lokacin da take cikin nishadi.
AMEER POV.
Sai da ya shiga dakinsa ya dauko dollars ya saka aljihunsa sannan ya dauki wayarsa da makullin mota ya fice. Babu abun da ke tashi a motar sai kidan disco ya kure volume kamar yadda ya kure gudu kai ka rantse da Allah shi kadai ne a titin Abuja, haka yake daman can be damu da rayuwar kowa ba sai tashi, gashi yana wasa da kudi kamar shi kadai ne dan mai nera a Abujar, ga uban girman kai gaisuwar tsiya ma bata hada shi da mutane balle ta arziki. Kai tsaye Q-town ya nufi wata mahada ce ta samari da yan mata, sai dai shi da abokansa ta su mahadar a VIP take wanda suke biyan kudin da ko shekara suka yi ba su zo gurin ba ma'aikatan gurin da mamallakinta be isa ya bawa wasu inzinin zama a gurin ba, yana faka motarsa sai da kowa dake gurin ya kalli motar domin ta banbanta da sauran motocin da suke guri, ba dan mahaifinsu ko kuma su ya fisu kudi ba, sai dan shi din ya fi su girman kai da ba zai iya hawan motar da suke hawa ba, haka kuma duk wata sabuwar mutane da ta shigo a garin Abuja yana cikin mayan matasan da suke fara hawanta, irin motocin da yake hawa daidaikun yayan manya zaka gani da ita a Abuja.
Sai da ya fito sannan ya rufe motar ya shiga cikin gurin, mutane dake harabar gurin hashakatawa sai kallonsa suke, wasu na masa kallon burgewa wasu kuma na masa kallon haushi saboda girman kansa da yadda yake jin isa, wasu yan mata kuma na kyasawa duk da kasancewar suna tare da samarinsu domin Ameer namiji ne cikakken namiji.
VIP ya shiga turare na masa escorting, daman shi da kamshi da tsabta kamar dan jumma da ďan jummai ne they're 5&6 duk inda yake tsabta da kamshi na gurin, haka ma duk inda tsabta da kamshi yake yana gurin. Zaratan samari uku ne suka dago kai suka kalleshi ban da Maleek da ya maida hankalinsa gurin wayar dake hannunsa kamar be san da shigowar Ameer ba, zamansu a tare ya zama kamar na dole tun ana karatun kasar waje har suka dawo a naija suka hada team dinsu na 5 buddies Ameer da Maleek basa ga maciji da juna, Sabida ra'ayinsu da tafiyar rayuwarsu da ta banbanta da ta juna, ko kadan Maleek baya son wani abun da ya shafi mata, sannan mutum ne da babu ruwansa da girman ko son wulakanta wani, tsabanin Ameer da wani lokacin yana kan taba mu'amala da mata, ga almubazzaranci da duniyar da aka sama masa ita tun kamin girmansa, sai dai ba sa iya rabuwa da shi shi ma kuma baya iya barinsu zama da junansu ya zama kamar dole, sauran samarin kam suna shiri da kowa kuma babu munafurci a tare da zamansu, sai dai ko wanne yana ji da kansa domin iyayensu suna da arzikin da za su dama su sha su watsar a yadda suke so a garin Abuja kuma a aka musu ido. Sai da ya zauna sannan shi ma ya kalli gurin da Maleek yake.
“Marry ta zo nan?”
Ta gangan ya kira sunan abokiyar sheki ayarsa saboda Maleek na gurin kuma ya san yadda Maleek ya tsani haka.
“Ba ta zo ba, saboda babu wanda yake irin sana'arka a nan”
Maleek ya fada ba tare da ya kalli abokin nasa ba, sai dai zuciyarsa tafasa take saboda ya ambato masa abun da ya fi tsana a duniya. Wani shu'umin Murmushi Ameer yayi yayi relaxing akan kujerar.
“Yeah saboda na fi ku lafiya ne”
“Ka fi mu samun zunubi dai, domin baka tsaya ga bahaushiya sai ga Kirista”
“An zo gurin, bana son bahaushiya ne saboda hausawa suna barin gashin kai, ni kuma kyama ta tana da yawan da bana son ganin gashin kai a mace, saboda haka bana iya rabar mai barin gashin kai, sai wanda zata aske ko zaka samun bahaushiyar da bata barin gashin kai? I can pay”
Ya karasa yana murmushin shakiyanci. Sai a lokacin Maleek ya dago ya kalleshi yana kokarin danne bacin ransa dan kar ya bayyana a fuskarsa.
“Ka samu wata daga cikin familynku mana, ka bata kudin da kake takama da su, zata aske kai ta baka abun da kake bukata”
Yana fadar haka ya mike tsaye ya dauki makullinsa ya nufi hanyar fita daga gurin. Yana da daf da ficewa Abokinsa Dawood ya ce
“Haba Maleek be kamata ka yi fushi ka tafi saboda wannan yar maganar nan ba”
Juyo yayi cikin fushi yana nuna Ameer da shi ma ransa yake bace saboda maganar da Maleek ya soka masa.
“Then ku gargadi abokinsu ya daina yi mana zancen riba da faduwar kasuwancinsa a nan, domin babu mai hannun jari a irin kamfanin da yake kwasar zunubi”
Ameer ya mike tsaye a fusace ya nufi gurin da Maleek yake tsaye.
“Da kudinka na ke biyan Marry ne? Ko kuma jikinka ne?”
Maleek ya matso kusa da shi.
“Allah ya tsare jikina da rabarar macen da take halalina ma balle haram kuit”
Ya karasa tare da watsa masa yawu a fuska, har sai da Ameer ya rumtse ido, Maleek ya saka kafarsar ya fice daga gurin. Wannan karon ba Dawood ba har Tarig da Babu Abdul sai da suka mike tsaye, Abdul yayi saurin karasowa kusa da Ameer ya dafa shi, domin duk fadan da suke da Maleek be taba tofa masa miyau a fuska ba sai yau.
“Wannan abun na ku ya fara yawa”
Ameer ya bude idonsa da suka kade da ja saboda tsananin bacin rai.
“Sai na kashe yaron nan Abdul ni zai watsawa yawu a fuska? Ni ni Wow”
“No Ameer ka san Maleek baya son zancen mata, amman ko da yaushe kai kake takalarsa, i know abun da yayi maka a yanzu be kyauta ba, amman idan zaka zauna a gurin baka yi abun da zai taba shi ba, Maleek ba zai taba ce maka komai ba”
Cewar Tarig da duk abun da ake be yi magana ba sai yanzu. A fusace Ameer yake kallon Tarig yana fadin.
“You take his side”
“No this is not the right time to take anyone side kawai ina fada maka gaskiya ne”
“Sai na koya masa darasi Wallahi, ni zai watsawa yawu a fuska? Ya san nawa fuskata take? Ya san yadda na tsani kazanta? Sai yayi nadamar wannan abun mark my words”
Ya fisge kansa daga rikon da Abdul yayi masa ya fice kamar zai tashi sama.
MALEEK POV.
Ummi na zaune Balcony tare da yan matanta Maleek ya faka motarsa ya fito a fusace ya nufo kofar falon da suke zaune, tun daga fitowarshi motar zuwa tafiyar da yake take karantar halin da ďanta yake ciki har ya karaso yayi mata sannu ya shige ciki, a take yanayin fuskarta ya canja annashuwa da far'ar dake tare da ita suka gushe, tana tsananin son Maleek irin son da take karantar damuwar ďanta a take, yana cikin farinciki ko akasin haka ko kuka yayi sai ta gane, idan damuwarsa mai yawa ce ko kadan duk tana iya karantar hakan a fuskarsa da cikin idonta. Da sauri ta sauke magen dake jikinta ta mike tsaye ta isa gurin kofar falon ta tura, da kamar fargaba ta kwankwasa kofar dakinsa bayan ta tura kofar ta ji ta a rufe. Sanin kansa ne mahaifinsa ne kadai zai kwankwasa masa kofa idan ya rufe sai kuma kanensa wanda ya tabbatar a yanzu bayan gidan, idan ba dayansu ba ne to mahaifiyarsa ce, ba zai iya barinta ta yi ta tsayuwa a jikin kofar dakin tana jiransa ba, haka kuma ba zai iya ce mata ta tafi ta kyale shi ba, kamar yadda ba zai iya hana ta shigowa ba, a dole ya sauko da kafafuwansa daga kan gadon ya taka ya