Showing 186001 words to 189000 words out of 281271 words
zaune ba shi da kyau kuma akwai mutane da yawa a gidan amman ta tsaya kai da fata ita bata bukatar komai daga gareni, dauren min fuska da take ma abun yana damuna sosai”
“Daman ba zai yiyu ta saurareki cikin kankanen lokaci kuma ya fahimce ki ba, dole na sai kin bata lokaci kuma kin yi hakuri, ki kwantar da hankalinki Zahra ke dai kina aikata hakan ne da zuciya daya, dan haka ki yi hakuri kuma kar hakan ya saka ki fasa kyautata musu, ai ita ma idan zata yi adalci kin yi musu duk yadda ake yi, kuma girma ya kama yanzu, ta san kuma karfi ba daya ba, ba zata iya ja dake ba idan ma ta ce zata yi shari'a ne, kuma silar wannan abun ba gashi Mr Bashir ya dauke mata nauyin komai ba? Wannan ma kawai jindadinta ne, dan Allah karki saka damuwa a ranki kin san dai yadda jikinki yake”
Ummi ta sauke ajiyar zuciya, zata sake maganar Waira ta mike tsaye tana fadin.
“Ummi assignment din ba'ayi min ba, kuma gobe school za su min fada idan ba ayi ba”
Ummi ta rage murya.
“Dauki assignment din ki tafi falo duk wanda kika tarar ki ce yayi miki assignment din”
“Toh”
Ta amsa sannan ta nufi kofar fita ta bar Ummi tana ta wayarta, tana fita dakin Namra ta shigo rike da waya a hannunta, can one seater ta zauna tana kallon Ummi dake waya.
Waira dakinta ta shiga ta dauko jakarta ta bude ta dauko littafin da aka bata assignment din ta dauki pen ta sauko kasa. Maleek ta tarar zaune a kasan carpet, ya rufe ko ina na jikinsa da jacket, kafarsa ma sanye da safa kansa ma na sanye da jar hular sanyi. Tea mai zafi na gabansa da kananan cincin a plate ya maida hankalinsa gurin Plasma dake kunne yana kallon wani documentary da ake a Al Jazeera. Zuwa ta yi ta tsaya kansa sai kuma ta ga kamar hakan be dace ba, a kokarin na yi tarbiyar da Ummi take dorata ta zauna gefensa tana kallon yadda dress din yayi masa kyau.
“Ya Maleek ga assignment da aka bani a school sun ce gobe za a kawo”
Juyowa yayi ya watsa mata wani banza kallo ya dauke kai. Bata damu ba ta fara bude littafin tana nuna masa.
“Ni kika maida kafiri kenan? Idan karatun Allah ne sai dai ki samu Ameer, yanzu kuma da yake na boko sai kika kawo min ga dan iska da duniya ko?”
Salon magana da yayi ya bude mata babi da ta yi masa fahimta ta dabam.
“Ni ban ce kai dan iska ba ne, iska ai ba shi da ďa, duniya ma bata da ďa”
Ya watsa mata harara ya dauke kai.
“Aka ce miki ni jahili ban san komai a addinin ba”
“Baka taba fada min ba, shi ma da farko ba tambayarsa na yi ba, shi yake fada min yanzu kuma da nake jin dadi shiyasa nake tambaya”
Ya kalleta ya dauke ido, ganin kamar ba zai mata ba ya saka ta mike tsaye tare da zomonta da littafin.
“Ummi ce ta ce idan na sauko duk wanda na gani na bashi assignment din yayi min”
Banza yayi mata har sai da ta fara taka stairs sannan ya kira sunanta.
“Waira”
Hausawa suka ce mai nema dole a biye yake, haka ta juyo ta dawo ta zauna a gabansa. Sai ya karbi littafin ya bude har ya kai gurin assignment din, ita dai kallonsa kawai take tana yana ta mata solving math, ta saka hannayenta ta rumgume jikinta saboda sanyin da ake a waje ga kuma na Ac da tun da ta zo gidan bata san wata rana da aka taba kashe shi ba, gwara ma daki akan rage ko a kashe amman a falo ba a taba shi komai sanyi komai zafi ko damina. Sai da ya gama solving din sannan ya cire jacket din dake ya rufa mata saman jiki, ya cire hular kansa ya mika mata, sai ta karba sannan ta karasa saka jacket din ta saka hular.
“Ki daina zama haka kina jin sanyi”
Murmushi ya bayyana a fuskarta ta kalli kanta tana fuskarta na kara fadada da annshuwa kallo daya zaka yi mata ka fahimci jindadin dake ranta na karramata da Maleek yayi ya bata rigarsa da hularsa saboda tana jin sanyi. Hannu biyu ta saka ta dauki tea cup din dake gabansa ta rike da hannu ta sha. Ya kalleta duba irin na mai rauni ta tarin damuwa a zuciya, ta sakar masa dara daran idonta tana murmushin ta ya fadar masa da gaba.
“Sanyi nake ji, kadan na sha”
Ta fada sannan ta aje cup din ta dauki cincin daya ta ci.
“Thank you Ya Maleek”
Kallonta kawai yake ya kasa cewa komai har ta mike tsaye ta dauki notebook din ta nufi stairs tana shinshina rigar dake ta kamshin turarenta, yau dai kam Maleek ya faranta mata rai. Dakinta ta shiga ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta sai dariya yake kamar sabuwar mahaukaciya, ranta fes ta farinciki kamar wadda aka yi ma gafara.
AMEER POV.
Ya kai hannu ya shafa fuskarsa yana kallon titin da motocin dake gabansa.
“Ina son idan Hajiya ta koma gida, zan yi magana da Daddy”
“Akan me?”
Humairah dake gefensa tana kallonsa ta tambaya. Ba tare da ya kalleta ba ya amsa mata.
“Waira”
Sai a lokacin ta dauke idonta daga barin kallonsa ta fuskanci gabanta.
“Ummi zata yarda?”
“Me zai haka? Ummi tana son abun da nake so”
“Ita yarinyar fa?”
Ameer yayi murmushi tunawa da ita kadai da yayi abun faranta rai ne a gurinsa.
“Bata da matsala ta saba da ni, ita kanta da za a tambaye ta wa take so zata fadi sunana ne”
Humairah ta hade wani abu da ya tsaya mata a makoshi ta juyar da kanta tana kallon wani gefen.
“Are you okay?”
Ya tambaya jin ta yi shiru tana kallon wani gurin na dabam. Sai ta amsa masa ba tare da ta kalleshi ba muryarta kasa-kasa kamar wadda aka cilastawa magana.
“Ina tunanin yadda Ummi zata tarbe mu ne, bayan duk irin abubuwan da Hajiya take mata”
“Ummi bata da matsala, ba zata miki wulakanci ba, ita da take neman mutane ma, shiyasa na dauki a yanzu ai so nake ku sabu da ita su san juna domin na fahimci kuna da fahimta daya”
Bata sake cewa komai ba, shi ma kuma be yi ta kanta ba tukinsa yake be tsaya ba sai da ya isa gurin wani shopping mall.
“Ina dawowa”
Ya bude motar ya fita, binsa ta yi da kallo har ya shiga Mall din sannan ta sauke ajiyar zuciya. Be jima ba ya fito wani ma'aikacin Mall din yana biye da shi rike da leda biyu, Ameer ya bude back seat aka saka masa ledodin sannan ya rufe ya bude motar ya shiga ya taka motar. Tafiyar ta shiru ce babu wanda ya ce wani uffan har suka isa gidan. Harabar gidan ya faka motarsa ya bude ya fito, sai ta zauna kamar mai jiran ya bude mata ta fito.
“Common fito mana tun da ba ke ce Waira ba, balle ki yi jira na bude miki”
Ta fada da kamar zolaya da wasa, sai da ya yaki zuciyarta sannan ta samu nasarar murmushi ta sake kai hannu ta bude motar ta fito tana karewa gidan kallo. Shi kuma ya rufe gefensa ya bude back seat ya dauko ledodin ya nufi ciki ta ruwa masa baya tana mamakin yadda masu arziki basa jin zafin zuba kudinsa a kasa su gyara muhalli kamar ba za a mutu ba.
[7/24, 5:13 PM] My S Line: 61
Maleek na zaune falon rike da cup din tea sa da Waira ta sha ta aje, Ameer ya shigo falon tare da Humairah. Ko inda suke be kalla ba har Ameer ya nunawa Humaira inda zata zauna, ita kuma ta zauna tana mikawa Ameer gaisuwa. Ya kalleta a tsanake sannan ya amsa mata da kai ta mike tsaye ya fice daga falon. Ameer ya nufi upstairs domin sanar da Ummi zuwansu.
Ummi ta aje numfashi bayan gama sauraren Namra sannan ta ce.
“Mahaifinki ba shi da matsala, tun a kwana baya da na yi masa magana yace zai yi bincike, kuma na tabbatar a yanzu yayi binciken ko kuma yana kan yi, zan sake tuntubarsa na ji”
Namra ta shafa wayarta tana fadin.
“Shuraim din yana ganin kamar Abiey ba zai yarda ya aure ni ba ne, saboda abubuwan da suka faru, yace mahaifinsa ya fada masa komai bayan yayi masa bayanin zuwan da yayi irin tarbar da ya samu da kuma crisis din da suka faru”
Ummi ta kai hannu ya taba kafadarta.
“We're all learners or experts in one way or the other, we're not perfect kowa yana making mistakes kamar yadda ni ma na yi, idan kuma har irin wannan ta kasance be kamata mu dora laifin akan wani ko wata ba, kamar yadda be dace mu bar wasu su cutu ko abun ta shafe su ba, ni dai a ganin da nayi ma yaron nan ina ganin kamar zai yi mutumci da rikon amana, domin akwai natsuwa sosai a tare da shi, after all abun da ya faru still yana bibiyarki yana son a ba shi dama, hakan ya nuna da gaske yake sonki kuma idan kika aureshi zaki jidadi”
“I hope so, nima ina son na yi aure just to make you happy, Ummi you are always telling us burinki a yanzu ki ga aurenmu, Nimra is no more yanzu ni ce kadai hope dinki”
Tana maganar hawaye na sauko mata, Ummi ma kokari ta yi ta hana kanta hawayen amman zuciyarta is melting, babu dare ko ranar da bata tunawa soft hearted lady Nimra, even though mutuwarta ya saka Namra zubar da duk wani ji da kai da ganin ta fi kowa ko banbanta da wasu, daman she's quiet bata son hayani ba kamar Nimra ba dake saurin sabawa da mutane. Hakan kuma ya saka ta kara zama very quiet she talk only when it's necessary.
“Haka Allah ya tsara, dole mu hakura mu karbi kaddara, addu'a ce abar da take bukata a gurinmu yanzu, and i happy for the decision you made, Allah ya hada kanku ya sa mijinki ne har aljanna”
“Ameen”
Ta amsa tare da saka hannu ta goge hawayen idonta. Shigowar Ameer ce ta saka ta mikewa tsaye rike da wayarta ta fice daga dakin ba tare da ce masa komai ba. Ummi ta bita da ido ganin ba su gama tattaunawa ba ta fice saboda shigowar mutumen da take ma kallon makiyinta. Ameer ya kalleta ya dauke kai ya tsaya daga jikin kofar dakin ya kalli Ummi.
“Ummi kina da bakuwa a falo”
Ummi ta dan bude ido try to mai da hawayen idonta cikin idon dan kar ya zubo, ta ari murmushi ya yafa a fuskarta.
“Bakuwa?”
“Eh Humairah ce na kawo miki ku gaisa, zata tafi school na ce bari na zo da ita ku gaisa sai na yi dropping dinta a school din”
“Maa Shaa Allah, aiko ka yi tunani mai kyau kamar ka san kullum burina da tunanina yadda zan kara kusance da alaka a tsakani na da su, ko da yake na lura kakarka bata son kulla wata alaka da ni, wata kila bata shirya yafe min a yanzu ba”
Ameer ya bar jikin kofar ya nufi inda take ya zauna kusa da ita.
“Sometime bama fahimtar abu cikin sauki, ko kuma a kankanen lokaci, wani abun ma sai an mana matashiya an lurar da mu suke gane alfanu ko kuskuren dake cikin abun, dan haka mu bata time ita ma a sannu zata sauko har ku samu fahimta juna. Ai tun da Waira ta yi nasarar tankwara ni na sauko na fahimce ki, na san kowa zai fahimce ke a duniyar nan Ummi, domin na san ni ni a kadan kaina ina da wuyar sha'ani, amman within period of time yarinyar nan ta bude brain dina na fahimci komai, that's why I like her”
Ummi ta kallonsa kawai take da shauki tana jindadin yadda yake nuna son kasancewa da Waira.
“Ina fatar zaka zama haka da sauran yan'uwanka ma, kamar Namra ita ce kadai kanwarku mace a yanzu, amman na lura bakinka da nata be taba haduwa ba tun da ta zo gidan nan”
Ya karkato ya kalleta.
“Ita ya kamata ace tana gaisheni, ko dan ta gan ni zata dauke kai, bayan kuma ni yayanta ne”
“Zan mata magana zata gyara, amman ba daga girma ba ne Allah be ce karami ko babba zai yi zumunci ba, zumunci na kowa ne, idan kuka ce zaki tafi a haka bayan rayuwata ba zaku yi zumunci ba, kuma abun zai fi cutar da Namra a yanzu domin ita ta rasa yar'uwa bata da abokin shawara a yanzu”
“Ya kamata ta girmamani then”
“Zan yi magana da ita, amman kai ma ya kamata ka girmama na gaba da kai, misali Abiey ko da ace ka girme shi ya kamata ace ka girmamashi saboda yana aurena, amman da rana daya baka taba zuwa ka gaishe shi ba, na ga ko ba komai ya girmeka ai kuma ya haifi kamar ka, sannan yana aurena”
Ameer ya hade yawu.
“Shi ma be taba kwatanta zuwa ya dubani ba a bangarenki, tun da na zo gidan nan ban taba ganinsa a bangaren nan ba, be shigo ya tambaye ya nake ba, idan Maleek ne ko Mahmood zai masa haka? Hajiya ta fada min komai akan Abiey irin kiyayyar da ya nunawa mahaifina, hakan ma sai ya saka na kara yi miki uzuri wata kila yana daga cikin mutanen da suke cilasta miki rabuwa da ni, Hajiya ta fada min Abiey baya son mahaifina ko kadan, wata kila kiyayyar mahaifina ce ta shafe ni nima ya tsane ni”
Ummi ta masa duba irin na mai rauni ta girgiza kai tare da kai hannu ta shafa fuskarsa.
“Ba zan ce Hajiya ta maka karya ba, amman iya sanina tsabani da rashin fahimtar dake tsakanin Abiey da mahaifinka irin wadda aka saba samu ce gurin samarin dake takarar neman aure, babu abun da zai saka Abiey ya tsane ka, idan har Mr Bashir zai kaunace ka alhalin be hada komai da kai ba, to ko Abiey ya fi dacewa yayi maka wannan kaunar saboda yana auren mahaifiyarka”
Ameer ya mike tsaye.
“Ummi kar mu bar Humairah tana ta jira”
Ummi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike tsaye suka fice daga dakin, ita ta sauko kasa shi kuma ya nufi dakin Waira, domin tun da ya shigo be ji motsinta ba kuma ya san ba time din zuwa makaranta ba ne balle yace ta tafi school haka ma idan ba ta school bata zuwa ko'ina. Slowly ya murda kofar ya tura, tana zaune akan stool tana kallon kanta a madubi ta juyo ta kalli kofar ganin Ameer ne ya saka ta murmushi. Shi ma murmushin yake yana takawa a hankali har ya isa inda take ya jingina da madubin.
“Fuskarki bata bukatar kwalliya Waira, Allah yayi miki hallitar da zata wadace ki ta gamsar da duk wani namiji mai kallonki”
Ta kai hannu tana gyara gashin kanta dake cushe cikin jar hular sanyi da Maleek ya bata.
“Rigar nan nake dubawa da hula ta min kyau ko?”
Ya kalli rigar jacket din ta mata kyau sosai even though ta mata yawa, balle kuma hular da ke yi duk wani farin mutum kyau.
“Sun miki kyau, Ummi ta siya miki?”
Ta rika rigar ta kai masa a hanci.
“Kamshin waye yake yi?”
Perfume din yayi masa kama da wanda ya taba ji, but ba zai iya fadar wake kamshin irin perfume din kai tsaye ba.
“Ya Maleek mana, shi ya ba ni rigar da saka min hula saboda na ji sanyi, Ummi tace naje na kaiwa duk wanda na gani a falo yayi min assignment sai na kai masa shi ne ya ba ni”
Cikin zumudi da jindadi marar misaltuwa take fadawa Ameer haka, ita dai yau kam Maleek ya burge ta kuma ya biyata duk wani kallo na mugunta da take masa yau ya kau a idonta saboda ya bata riga ta saka, ara mata yayi ko kuma bata yayi duk bata da tabbacin ko daya, sai dai tana jin cewar ya nuna mata kulawa hakan kuma ya saka ta farinciki. Kamar an yi ruwa an dauke haka murmushi yayi batan dabo a fuskar Ameer.
“I'm just joking rigar bata miki kyau ba, wannan ma kayan maza ne ba na mata ba, kuma sun miki yawa be kamata ki saka ba, sannan kuma bana son ganin komai a jikinki ko a maganar matukar ya shafi wani namijin ba ni ba”
Yana maganar yana kicin-kicin cire mata rigar, ita dai hular tuni ya cireta ya jefar. Sai ta kamashi da kokawa tana son hana shi cire nata jacket din.
“Ni ina son abuna haka karka cire min Haba Ameer yana min kyau na gani, ina son kayan mazan haka, ya nuna min kulawa ne kawai fa, duk wani abun kyautatawa da Ya Maleek zai min ina so i like it”
Cak Ameer ya tsaya daga kokarin rabata da rigar da yake ya dauke hannayensa, ba dan kukan da take kawai ba har saboda furucin da ta yi masa a yanzu. Ita kuma bata fada da wata manufa ba sai dan abun da ta fahimta kuma ta dade tana jira, wato ranar da Maleek zai daina hantararta da yi mata fada.
‘Ba laifinki ba ne, na gane idan na yi wasa daga like it sai like him then love him, ina shuka wani zai girbe okay...’
Ya fada a ransa sannan ya juya ba tare da ya ce mata komai ba ya fice daga dakin, ita kuma ta tashi tana kuka ta nufi inda ya jefar da hular ta dauka tuna lokacin da ya cire nata zoben da Shuraim ya bata, shi kawai baya son ya ga an bata kyau. Yanayin yadda ya fito daga dakinta ya sauko kasa ya zauna a kusa da Humairah is something else, domin babu annuri a fuskarsa, ya hade rai kamar wanda aka yi ma bushara da bakin labari, zuciyarsa sai sake-sake take masa idan ta kwance masa wacan ta saka masa wannan. Duk wata hira da Ummi take da Humairah hankalinsa baya gurin, shi ya matsu