Showing 180001 words to 183000 words out of 281271 words

Chapter 61 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1202

taba kafarta mai lafiya, ya daga zanenta zuwa guiwarta ya shafa kafar ya kalli fuskarta mamaki da rashin yadda da karyar da suke kokarin mayar mata a matsayin gaskiya ya saka ta sakin baki da ido tana kallonsu, can kuma ta kalli Humairah ta ce.

“Humaira ke kin gane abun da kike nufi”

Hunairah da tun da ta fahimci abun da yake nan take kuka, ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana kara rushewa da wani sabon kukan.

“Dan Allah ku min bayani, kaina ya kasa dauka na kasa fahimta abun da kuke nufi”

Ummi ta koma ta zauna a kujerarta, yayinda Ameer ya kwantar da kansa a kafarta mai lafiyar hawaye dake fita a idonta suna zuba a kafar, ba tare da damuwa da tsabtar Hajiya ko kazantar ba, yau ya manta cewar kafar almajira mai yin bara a titi, mai zama a gidan da yake jin kyama da kazanta take rayuwa, shaukin son sanin mahaifinsa da kuma ganin kakarsa ya mantar da shi komai. Be taba tunanin haka ake ji idan aka hadu da uba ko dangi uba na kusa ba sai yau, lallai yau ya yarda shi ba ďan Mr Bashir ba ne, domin be taba jin shaukin da sarkewar zuciya dan gani ko tarayya da wani a cikin family Mr Bashir ma, amman gashi a yau yana yi, zuciyarsa har wani fisga take how he wish ace Mahaifinsa ma yana raye.

“Hajiya, ban yi zaton abun zai bayyana ta haka ba, ban yi zaton ta haka abun zai zo ba, ban san ta ina zan fara miki bayani ki fahimta ba, Ameer ji...ka... Kan...ki... Ne.... Ne.... Dan.... Da.... Na.... Na... Na... Na... Na....”

Sai numfashinta ya sarke da halshenta ta kasa karasa sentences din dake gaba.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un..... Ta ya? Ba yar ta mutu ba? Wa muka binne kenan?”

“Wadda kuka binne ba jikarku ba ce, ba ni na haifeta ba, ni ďa na haifa ba mace ba”

“Yanzu kuma kin kara rikita ni, toh da kika haife shi ina kika boye shi? A ina kika aje shi har ya girma? Idan ma gaskiya ne me zai saka ki aikata hakan?”

“Gaskiya ne Hajiya, Wallahi wannan yaron ďan Deen ne, jininsa ne ďan da na haifa ne”

Hajiya ta kalli Ameer tana bata fuska irin na tsofin dake kokarin ganin sun ci karfin kuka, amman ina sai da ta yi sai dai bata bari sautin kukan ya fito ba.

“Me yasa kika boye shi? Kamaninshi sak na Zaharardeen tun ranar da na fara ganinsa na ga kama yake da Deen, amman zuciyata bata raya min cewar shi jinina ba ne, me yasa kika boye shi? Me zaki yi tabbatar min da yaron nan jika ne? Ta ina zam gamsu?”

Ta inda Ummi ta ji zata iya, ta fara fede mata biri da wutsiya, ita kuka Humairah kuka Hajiya kuka Ameer hawaye.

Hajiya tayi kuri da ido sai hawaye take bayan gama kukan. Ummi ta share majina ta kalli Hajiya da yanayin da take ciki ta ce.

“Hajiya ki ce wani abu mana”

Hajiya ta kalleta ta kalli Ameer sai ta sauke dauke idonta.

“Dan Allah Hajiya ki yi magana ko da tsunuwa zaki furta min na cancanta, kuma na shirya tarbonta da Ameen, amman ni ban aikata hakan a nufin na cutawa kowa a cikinku ba, ban aikata haka ba saboda na son zuciya ba”

“Toh me zan ce Zahra?”

“Ki fadi duk abun da kike son fada Hajiya, na cancanta, na shirya neman afuwarki sai dai ban yo zaton abun zai zo mana ta wannan sigar ba, tunanina da zatona kuna kano har yanzu, ina ta kokarin shirya zuwa kano na kai Ameer a gurinki na nuna masa ku da sauran dangi kuma na roki yafiyarku”

“Zaharadeen be miki komai ba sai alheri Zahra, talaka ne, amman tufafinki baya bari ki wanke, sai dai ya wanke miki ya goge, ko da ya aureki baki iya girki ba, amman haka yake zaune da ke, sai dai ya siyo muku abinci ko ya girka, kamin ki fadi kina son wani abu ya aikata miki, kowa yace be zon Zahra Deen be son shi, saboda ke babu halin da be shiga ba, akan me zaki saka masa da wannan? Me ya miki? Cewar dole ce ta saka kika aikata saboda kina tsoron rasa rayuwarsa shin kin kai ni ni uwarsa ne? Ba gashi kin yi aure kin cigaba da rayuwa ba? Ni ko fa? Ba ni da mai maye min gurbinsa, duk na tuna cewar Deen ya tafi be bar min jika ba sai na yi kamar na yi hauka, zuciyarki bata raya miki ina bukatar ba ki kawo min shi ko sau daya na gani? Malam ya har ya bar duniya be san yana da jika ba, ya zaki yi da hakkinsa? Wace Wahala ce taki Malam be sha ba, amman sai ki saka masa da wannan? Saboda muna talakawa ne ko kuma saboda kina ganin ba mu da hakki ne? Shim kaunar Deen ne baki yi har yanzu ko kuma son zuciya ne kawai irin an ďan adam?”

Gefen mayafi Ummi ta saka ta share hawayenta tana jin wani gwarin guiwar magana yana tunkarota.

“Hajiya zaki iya tuna, wani lokaci da Deen ya tirsasa Dr Zainab yayar Abiey yin karya ta yi min kazafi cewar ina dauke da cutar HIV? Saboda kawai a fasa aurena da Abiey? Kuma yayi nasara Ammy da yan'uwanta suka ce ba zai aureni ba? Mutumen da na fara so aka saka mana ranar aure? Kuma ba a fadi haka ba sai a ranar da za a daura min aure? Bayan tara mutane da shela? Zaki iya tunawa?”

“Ramuwa kika yi kenan? Amman shi Deen ai ya aikata miki haka ne saboda yana kaunarki, tun da kuka taso yaron nan yake kaunar, kawai saboda ya san ba za'a yarda ya aureki ba ne ya saka shi aikata haka, kuma a cikin wasiyar da ya bar miki ai ya fada komai”

Ummi ta daga kai

“Kwarai ya fada min saboda yana sona ne, saboda yana tsoron rasa ni ne? Saboda yana son rayuwa da ni ne? Saboda idan babu ni a rayuwarsa zai iya shiga wani hali, komai yana cikin kaina ban manta ba”

Ta mike tsaye.

“Toh ni ma na aikata kwatankwacin abunda Deen ya aikata, tunani be bani zai mutu ba, hankalina be kai gurin da zan fahimci kuskure ba, saboda idanuwana a rufe a wacan lokacin, fatana kawai na samu kudin aikin Deen, bayan aikatawa kuma sai tsoron abun da zaku jefe ni da shi ya saka dole na barwa Mr Bashir yaron, kamar dai yadda Deen ya kasa fada min cewar shi ya shirya a yi min gwajin karya ace ina da hiv, saboda Abiey ya fasa aurena, bayan aure kuma na yi gwaji yafi a karga ba a ga cutar ba, wannan sai ya saka na zargi Abiey da butulce min yaki aurena saboda ina talaka shi kuma dan sarauta dan masu arziki, ashe abun ba haka yake ba.... Kuma Deen ya kasa fada min saboda yana tunanin idan ya fada min gaskiya ba zan yarda na zauna a gidansa ba, ba zan yarda na so shi ba, yana tsoron kada kallon da nake masa a matsayin Jarumin da ya taimaki rayuwata ta ceto ni daga kunyar duniya a ranar daurin aurena ya tashi zuwa wani monster, ban san gaskiyar komai ba sai bayan ransa, sai da ya mutu Hajiya, amman a haka kike nemawa danki uzuri saboda yana naki, ni kuma kike son shiga tsakanina da ďana, kin san shekara nawa na yi wannan cutar tana cina? Kin san wutar da na kunnawa kaina take cin zuciyata da jikina? Kin san yaushe ne Ameer ya fara saurarena yana kallona a wata mace mai mutunci? Cikin watan nan ne? Amman a yanzu kokarin lalata alakar kike, ni ma rayuwata ba mai tsayi ba ce, kamar dai ďanki, abubuwa da yawa da ke kika samu gani a matsayinki na uwa kuma kaka ni ba zan samu ganinsu ba”

Tana magana hawaye bin wasu hawaye. Ta mikawa Ameer hannu.

“Ba ni makulli zan tafi gida”

Ameer ya dago ya kalleta sai kuma tausayinta ya kama shi, wasu abubuwan da ya ji ta fada da be san da wanzuwarsu rayuwarsa ba sun saka ya fahimci ita ma dai ta sha gwagwarmaya kamin ta samu salama.
[7/20, 10:36 PM] My S Line: 59

Humairah ta kara taku uku dake tsakaninta da Ummi ta duka har kasa ta ce.

“Ummi, dan Allah kar fushin zuciya ya jaki ki fita a wannan halin, ki zauna zuciyarki ta sauka, sai Ameer ya kaiki gida, mu bar abun da ya wuce ya zama tarihi, mu fuskanci gaba”

Ta fadi haka nan ne saboda Hajiya da mahaifiyarta Bahijja sun sha bata labarin abun da Deen ya aikata a baya, bata san Ummi ce macen da aka aikatawa haka ba, sai a yanzu hakan ya ninka tausayin da take mata a sanin da ta yi mata na sabuwar mahaifiyar Ameer. Ummi ta zauna a hankali domin ita ma tana bukatar zaman, Ameer ya dago daga kafar Hajiya ya kalli mahaifiyarsa dake kokarin tsai da hawayenta.

“We're not equal, kowa yana da good and bad side, I'm sorry for what I said earlier mu tafi na kaiki gida”

Ummi ta ki kallonsa wani kullin hawaye da ta kebe na zubo mata.

“Ka bani key kawai ni zan iya zuwa, idan ba zaka iya zama da ni ba, zaka iya tafiya gurin Mr Bashir ko wani guri inda ka zaba, ba zan cilasta kowa sai ya zauna da ni ba, ba dole ne kowa sai ya soka ba. Na gaji haka nan yanzu kuma, duk wanda ba zai fahimce ne, zai iya fassara ni da yaren da yafi fahimta da ganewa, zan hakura da komai nima na gwada rayuwa, kalubalen kuma ya isa haka, a yanzu ba ni da karfin dauka”

Mikewa yayi tsaye ya taka bayanta ya tsaya, ta yi tunanin ko wata maganar zai fada mata ko ya nuna mata wani abun sai dai ga mamakinta sai ta ji ya rumgumeta.

“Ina son a haka Ummi, yanzu na fara enjoying iyayena na gaskiya, no matter how you're, ko da kuwa ace kun fi kowa talauci duk yadda nake kyamar talauci zan zauna da ku, Humairah ta taba fada min na yi hankali da rayuwa, amman ban fahimce me take magana akai ba sai yanzu, i regret everything na sha wulakanta yarinyar nan, at the end gashi ta zama ashe yar'uwata ce ta jini, ni ma ban aikata abu mai kyau ba so you're not the only one”

Ummi ta rufe ido ta kai hannunta ta dafa hannun Ameee tana kuka. Hajiya kam har Ummi ta bar dakin bata sake furta komai ba sai hawaye take tana bin Ameer da kallo, duk wani reason da Ummi ta bata na abun da ya saka ta aikata abun da ta aikata da kuma neman a fahimce har ta kwatanta mata da ďanta Hajiya bata ji ta gamsu da shi a matsayin Hujja ba, zuciyarta da idonta na kallo Ummi da wata manufa da bakinciki marar misaltuwa. Ko sallama da Ummi ta yi ma Hajiya bata amsa ba sai Humairah ce ta amsa mata suka fita tare da Ameer yana gefenta suna tafiya har suka isa gurin motar, jiri ke dibanta sai dai bata yarda ta nunawa Ameer ba sai ta jingina da motar dake kusa da inda Ameer har sai da Ameer ya bude motarsa sannan ta yi hanzarin shiga ta zauna.


The following day is weekend amman Ameer yayi saurin farkawa bachi, domin tun kamin sallah asuba ya farka yayi jiran ayi sallah, after sallah be sake komawa bachi ba, and because of Ummi bata jin dadin jikinta tun jiya da suka dawo daga duba Hajiya ya saka ta koma bachi bayan gama azkar din safiya. Wayarsa ya dauka ya saka aljihu sannan ya dauki sarewarsa ya fito daga dakin ya nufo kasa. Tun kamin ya karasa saukowa Namra dake zaunw ta mike tsaye ta nufi hanyar da zata sadata da bangaren mahaifinta, ita dai a rayuwarta ta tsani Ameer a rayuwarta, a zatonta zama zai yi a falon dan haka ta tashi ta fice.
Ameer ya mata kallo daya ya dauke kai ya nufi kofar fita daga falon gaba daya. It's morning but he want some fresh air, yar damuwar jiya nan yake son ta fice masa a rai a gaba daya, domin bayan dawowarsu gida ya kira best friend dinsa wato Daddy ya fada masa abun da ya faru, and Daddy be kwana ba har sai da yaje asbitin duba ta for the very first day yayi magana da ita ya fahimta da ita abubuwan da yake son ta fahimta kuma ta fuskanta. Compound din gidan ya fara tsayawa yana duba inda zai fi masa dadin zama ya busa sarewarsa kamin ya takawa ya isa Garden din gida that is different da na gidansu, domin na gidansu Daddy ya kawata masa shi da irin ado da yanayi da yake son Garden da Pool event though ba ko yaushe yake zama a gurin ba. Kamin ya karasa a inda zuciyarsa ta raya masa zama wayarsa tayi kara, ya saka hannunsa ya ciro wayar ya duba ‘Dawood’ Ne rubuce a screen din wayar, mai da wayar yayi aljihu har sai da aka sake kira sannan ya yi picking ya kara wayar a kunnesa amman yayi shiru yana jiran sai Dawood ya fara magana.

“Ranka ya dade idan an amsa wayar sai magana ma ta gagara? Ana rayuwa aka? Shekara ana tare amman kai da Maleek duk kun guje mu? Kun bata tsakaninku kuma kun guje mana”

Ya zauna sannan ya dan yamutsa fuska a zatonsa Dawood ya kira shi ne saboda yayi masa maganar dawowa da yayi da zama a gidansu Maleek.

“Ka yi waya da Maleek?”

“Aa Wallahi yanzu dai nake son idan na gama da kai na kira shi, ya kake?”

Ya daga kai yana kallon itatuwan gurin kamar su za su sama masa amsar da zai bawa Dawood.

“Lafiya kalau, idan na fito zan kira ka sai mu hadu”

“Okay”

Dawood ya amsa ya kashe wayar, domin ya fahimci abokinsa be cikin mood din yin wayar a yanzu, daman Maleek ne sai yace halinsa na son dogon zance a waya, amman Ameer ba haka yake ba. Ya aje wayar gefe ya bude box dinsa ya ciro sarewar ya kafa a bakinsa ya fara busar yana rufe ido ya bude saboda dadin busar da yake ji da kuma daukewar masa damuwa da kewa. Ba shi kadai ba kusan duk wanda ya ji busar dole ne ta dauki hankalinsa, hakan ya saka Mahmood kara gyara kwanciyarsa sakancewar yau babu aiki, busar sai ta masa kamar kara gyara masa bachin ake. Maleek kuma da windows dinsa suke bude ya aje karatun qu'anen da yake ya nufi window ya tsaya yana kallon abokinsa na baya kuma dan'uwansa a yanzu.

Can cikin bachi Waira ta ji busar sai ta bude ido, zumbur ta tashi zaune, ta sauko da kafafuwanta ta saka talkaminta na teddy ta nufi window ta daga curtains din ta leka Garden din dake kasan windows din ko wane daki na gidan, ta kara matsawa ta bude window gaba daya jin busar da ta yi da kyau ya saka yin murmushi, sai ta juyo da gudu ta nufi kofar dakin ta bude ta sauka sauka tana gudu har ta isa gurin kofar falon ta bude ta fita bata tsaya jira talkamin falon ta canja a na fita harabar gidan ba ta nufi Garden tana gudu da hakki har wani murmushin nishadi take. Ameer na ganinta sai ya sauke sarewar yana kallonta can kuma ya tuna da ni abun da yafi zama masa wajibi idan yana tare da ita wato murmushi ya fadada fuskarsa da shi. Sai dai hakan be hanata fahimtar damuwarsa ba, daman tun jiya ta lura da canji da ta gani a tattare da shi wunin ranar. Bata ganshi ba lokacin da ta tafi makaranta sai dai ta dawo ta tararda yanayinsa a haka ta yi tambayarsa ya ce mata ba komai, shi kuma yayi hakan ne saboda baya son tattaunawa akan matsalar. Yau kuma ta ga haka a tattare da shi, sai dai ta fi dora abun a mazaunin ko baya son zaman gidan ne ko kuma gidan ne baya masa dadi.


“Ameer tashi tsaye”

Ba zai iya musa mata ba duk da kasancewarta karama akan shi, dan haka ya mike tsaye.

“Aje abun busar a can”

Ta nuna masa inda box din yake, sai ya aje sarewar. Takawa ta yi ta matsa inda yake ta ware hannayenta ta rumgume shi, so take ta san abun da yake damunsa, shi kuma sai ya ji kamar ya samu shoulder to cry dan haka yayi mata maraba a kirjinsa ya rumgume kamkam a kirjinsa ya rufe ido, her skin is so soft and smooth. Sun yi minti biyar a haka sannan ta sake shi ta daga kai ta kalleshi.

“Ummi ta yi magana da Grandma dinka ko ba haka ba?”

Yayi murmushi tare da ja saboda hancinta.

“Sannu aljana na manta kina duba”

“Minene duba?”

“Wani abu ne da Allah ya hana saboda ba shi da kyau, amman ke kika yi”

“Saboda me aka hana?”

Ya rika hannunta ya zaunar da ita ya fara karanta mata dalilin hanin da kuma illar aikatawa da tarin zunubi da ake samu idan an yi. Haka suka kwashe rabin safiyar a gurin har sai da Ummi ta aiko mai aikinta Hanne kiransu, sannan suka fito Waira na fada masa yadda take iya saffara kowane kalar itace ta hau, har tana fadar ba dan Ummi ta aiko kiransa ba da sai ta hau itacen ta nuna masa.
Tare suka shigo falon yana rike da hannunta ya san haramun ne but he don't mind ya aikata hakan a gaba kowa, domin dan boko ne da ba dan zuwan Waira ba wani abu da ya shafi addini be dame shi ba balle har ya tattauna kuma ba dan be sani ba, sai dai be damu da wannan bangarenba, but one he doesn't want to miss is pray, baya wasa da sallah da duk wani abun da ya shafeta.

Maleek na zaune a kujerar dake fuskarta kofar fita da shiga falon Ameer ya shigo, wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login