Showing 30001 words to 33000 words out of 281271 words
dakin a fusace har yana sakin kofar da karfi. Kalaman da yayi mata a yanzu sun kara tabbatar mata da cewar Ameer din ta ne, sai dai ya shata mata layin da bata isa ta tsallaka ba, kamar yadda ta yi ma kanta kataga tsakaninta da shi da bata isa ta rusata a yanzu ba. Ba tayi mamakin kalaman mijinta ba domin ta san ba shi da makiyi kamar Deen, hakan ya saka a duk lokacin da ta nuna damuwa akan Ameer sai ransa ya bace ya ce saboda yana ďan Deen ne, a kullum ikirarinsa bata son Maleek saboda jininsa ne sai Ameer da yake ďan makiyinsa.
‘Gaskiya ne, Ameer ba ďana ba ne a yanzu, ďan wasu ne, yana da family da iyaye yana da rayuwarsa ta dabam’
Da zuciyarta take magana tana kokarin ganin ta kawar da tunaninsa a ranta ta cire shi daga zuciyarta, ko ba komai yanzu dai ta san yana a guri mai kyau kamar yadda take buri, ta san Mr Bashir ya ba shi gata da kulawa kamar yadda yayi mata alkawari tun da har ya hana police su kama shi saboda abun da ya aikatawa ďanta Maleek, ya girma a yanzu ya zama babban Saurayi rayuwar baya ba ita ce a yanzu ba, ya kamata ta manta da komai. Hakan ya saka ta tashi ta shiga bandaki ta wanke fuskarta ta fito ta zauna bakin gadonta dafe da zuciyarta, har yanzu bata daina jin wannan mashin da ya tsoki kahon zuciyarta ba, a yanzu kam ta yarda ta rasa Ameer har a bada, sai dai idan ta tuna bata bashi kulawa yadda ya kamata ba, sai ta ji wani iri a ranta, ga cutarwa da ta yi ma iyayen Deen na raba su da ďan Deen tilo da zai iya zame musu sanyin ido.
“Hakki ba zai bar ni ba, na cutar da yaron nan na cutar da kananinsa na cutar da kaina, miyasa ban yarda na karbi hukunci tun a wacan lokacin ba?”
Ta fashe da kuka sosai tana tsananin nadamar abun da ta aikata, ina ma ace da halin gyara da ta gyara komai a yanzu, yanzu ta kara tabbatar da hakkin ne yake bibiyarta shiyasa Maleek baya kaunar matsowa kusa da ita, kuma baya son ko muryar mata ya ji, ita kuma ta kasa manta abun da ta aikata hakan ya hana ta farinciki. Mikewa ta yi tsaye ta dauki wayarta ta yi clearly din searching din da Namra ta yi mata na Ameer, a kokarin na engaged din kanta da wani abu ya saka ya canja tufafin jikinta zuwa wasu marar nauyi ta sauko falo, Mahmood kawai ta samu zaune yana lasa wayarsa, dagowa yayi yana kallonta har lokacin idonta be cire kumburi ba.
“Abiey yace mana Bachi kike”
“Yanzu na farka”
Ta fada tana kokarin ta yi murmushi amman ta kasa, haka ta wuce Kitchen suna da masu aiki, sai dai ta sabawa kanta ita take girkawa mijinta abun da zai ci da kanta, hakan ya saka ta fara shirye shiryen girka masa abin da ya fi kauna saboda ta san ransa ya bace, sai dai me tana kai hannu ta bude fridge sai ta fashe da kuka.
AMEER POV.
Be isa Katsina ba sai 11pm na dare sai da ya fara tsara dajikan garin ya fara tunanin me ma zai kawo shi garin? Miyasa ya zo nan?
“To ina zan je idan ba nan ba?”
Ta tambayi kansa domin ya san barin kasar a yanzu ba abu ne mai sauki a gare shi ba, idan ma ya bar kasar duk inda zai je zai samu kansa cikin bacin rai ne da damuwa. Ya cika bakinsa da iska ya busar tare da kai hannu ya dauki wayar Nimra da sakonta na uku ya shigo domin jin lafiyarsa tsoron kiransa take kar ransa ya kara baci wata kila be huce ba har yanzu.
Kai tsaye ya aika mata da kira ringing daya ta daga kamar daman can jiran kiransa ake, sai dai yayi mamakin jin wata muryar wacce ta girmi ta Nimra ta daga wayar tare da sallama, da gangan yaki amsa sallamar domin ya san ba Nimra ba ce, kuma shi tun da ba wanda yake son waya da ita ce ta daga ba be ga amfanin yin magana ba, sai kawai ya kashe wayar. After like 3 minutes Nimra ta kira shi sai ya daga ya saka ta a speaker.
“Ka kira na je na daukowa Ummi abu, ka isa Lafiya?”
Yayi shiru kamar ba zai amsa mata ba.
“Ina na je?”
“Ban sani ba, amman ina fatar kana wani guri mai aminci”
Ya faka motar gefen titi ya sauke gilashin Motar yana kallon titi.
“Ina KT in the middle of the road i think”
Nimra dake zaune a dakinta ta mike tsaye cike da damuwa.
“I know be kamata ma saka kaina a cikin matsalarka ba, Amman da zaka yi hakuri ka dawo gida ina tunanin zai fi domin a yanzu zaka jefa kanka a cikin wata matsalar ne kawai kuma..”
Sai kuma ta yi shiru..
“Mahaifinka yana bukatar ka Ameer”
Ya juyo ya kalli wayar kamar ance masa ita ce a gabansa.
“How do you know my father? Taya kika san shi?”
“Abiey mu yayi magana da step mother dinka”
“Ke ki fito fili ki yi min magana yadda zan fahimta, what do you know about me?”
Bata son ta fada masa cewar ita din kanwar abokin hamayyarsa ne duk kuwa da ta san dole zai sani, sai dai tana ganin kamar be dace ta yi hakan a yanzu ba.
“I'm talking to you”
Ya daka mata tsawa kamar tana gabansa, a dole ta fada masa abun da ya faru da yadda aka yi ta gane cewar shi din ne ciki har da hotonsa da Mahmood ya nuna musu.
“Wow... So Maleek duk shi yayi planning wannan? Shiyasa kike ba ni shawarar yadda zan yi masa? Shi yake fada miki ko?”
Ta girgiza kai da sauri.
“No no no Wallahi ba shi yayi ba, ba shi ya saka ni ba, taya zan baka shawarar yadda zaka yi masa haka? Wallahi ban san akwai alaka tsakaninku ba sai dazun ka yarda da ni Ameer”
“Idan na yarda dake duniyarki zata gyaru ne? I don't trust you karki sake kirana, and mark my words ke ma sai na koya miki darasi kamar yadda zan koyawa ďan'uwanki”
Rasa ta yi ta inda zata kamo zaren balle har ta fara sakar yadda za 'ayi ya yarda da ita.
“Mahaifinka yana bukatarka Ameer He's Unconscious, Step Mother dinka tace be ma san an kai shi Asibiti ba”
Yanke watar yayi ya bude motar ya fito yana jin wani bakinciki na karuwa a ransa, Ameer wani irin murdaden mutum ne da bashi da fahimta cikin sauki, abu kadan ya bata masa rai. Ji yake gaba daya Maleek ya gama da shi.
_Da gaske mahaifinka na asibiti Ameer ba karya nake maka ba, kuma ka yarda da ni ban yi komai saboda na bata maka ba, dan'uwana ma be san muna da alaka ba_
Ta aiko masa da sako, yana gama karanta sakon ya koma cikin motar ya danna a wata hanyar da ke gefen inda ya faka motar, daman can be san tsoro ba tun yana karami baya shakkar kows bata shakkar komai, musamman idan ransa ya bace babu abun da ba zai iya aikata ba, Ameer irin mutanen nan ne da idan ran su ya bace hankalinsu ke gushewa su aikata komai sai dai daga baya ayi nadama, tun yana karami haka ya tashi ko mutuwa aka aje sai ya taba ta sai dai ya mutu, idan kuma aka ce idan yaje can zai mutu ko wani abun ya same shi to sai yaje sai dai komai zai faru ya faru.
Ba ma kamar yau da yake jin kamar ya kashe kansa, miyasa ya yarda da yarinyar da be sani ba, why ya kulla alaka da kanwar makiyinsa? Duk wannan plan din Maleek ne haka zuciyarsa ke raya masa, be taba sani shi din wawa ba ne dai yau. Gudu yake sosai cikin jar kasar da babu titi sai kura da turda dake tashi saboda gudun da yake komai ya ci karo da shi bugewa yake babu ruwansa da bata motar da zai yi ko kuma ya jiwa wani ciwo, yo a gari ma Ameer ai gudu yake da mota yana kade mutane balle kuma a wannan dajin na Allah da babu kowa a hanyar. Karshe gudu ya kai motar har sai da ya kai karshen hanyar sai ya tsara ta inda ransa yayi masa dadi domin ba hanya da ke bullewa cikin gari ba, da gangan yayi ta buga motar a jikin wasu manyan duwatsu da ya samu daker da wahala motar ta karaso gurin, sai da ya tabbatar ya lalata gaban motar sannan ya bude ya fito ya jefar da wayar a cikin daji. He rather die here da ya sake amfani da wani abun da ya shafi Maleek.
Hudun yayi masa yawa domin ya lalata na Motar kuma ya jefar da wayar a inda be saka ran ganinta ko da ya duba, tsaye a gurin yana kara jin tsanar Maleek a ransa musamman idan ya tuna shi yana can kwance a guri mai kyau tare da iyayensa shi kuma ya hada shi da nasa iyayen kuma ya bashi da inda ya fi jindadin kwanciya. Ya dade yana tunanin yadda zai yi ya rama abun da Maleek yayi masa kamin ya bude motar ya dauko Carpet dinsa da ya siya ya saka hannu aljihu ya ciro ATM din Nimra ya karya shi, ya cire kudin data bashi ya saka a motar ya rufe motar. Da taimakon farin wata dake haska dajin mai kama da tarkon mutuwa ya karasa gurin fakon dake gabansa mai kamar an share ya shinfida ya kwanta a gurin ba Aljannu ba ko Uban gidan aljannu ne a gurin sai ya kwanta ko ma kashe shi suka yi shi daman mutuwar yake nema, yadda ka san wani dan shaye shaye haka yake zama idan ransa ya bace.
Kasa bachi yayi hakan ya saka shi tashi ya zaune idan ya gaji da zaman yayi tsaye, ba bacin ran abun da Maleek yayi masa ne kadai damuwarsa a yanzu ba, har da ta mahaifinsa da aka fada masa baya cikin hayyacinsa, sai dai duk da hakan Maleek yake dorawa laifin. Sai da sanyin Asuba ya fara sauka sannan ya fara jin bachi na son daukarsa daukar Carpet din yayi ya nufi wata hanyar da be san inda ta nufa ya fara tafiya kamar ana kiransa.
Gaban manyan duwatsu sai ya tsaya nesa da su kadan ya shimfida Carpet din ya kwanta, wata kila ya fi jin natsuwa a nan fiye da inda ya zauna a dazun, rairai ya kwanta ya yayi matashin kai da hannayensa ya hade kafafuwansa guri daya yana kallon sama ya runtse idonsa, sai dai babu abun da yake gani sai mahaifinsa ko ba komai ya san shi kadai ya rage masa tun da mahaifiyarsa ta rasu tun yana jariri kamar yadda Daddynsa ya fada masa, idan kuma ya rasa Daddy ya rasa komai kenan.
‘Wait... Da gaske take ma ko kuma wani sabon plan din ne?’
Da wannan tunanin bachi yayi gaba da shi.
WAIRA POV.
Gudu take sosai ba dan ta san inda zata je ba, sai dan ta tsira da rayuwarta domin ta san tabbasa za a biyo sawunta ko da kowa be biyo ba Eid zai yi kokarin yin haka, a zuwa yanzu ta san laifinta ya karu a gurin Sarki hukunci da za a mata wata kila sai yafi na mutuwa kai tsaye, a tunaninta sai an azabtar da ita sannan a kashe ta ranta kila na wulakanci.
Tana jin ta taka abu amman bata damu ta tsaya ta duba kafarta ba, tana jin zafi sosai amman tsoro ya hana ta tsaya ta yi tafiyar tsanaki balle har ta duba abun da ta taka a kafarta, tana kokarin tsallaka wasu duwatsu bata ankara ba wani dutsen ya tadeta ta fadi bakinta ya bugu da dutsin dake gabanta a take jini ya balle, a rikice ta tashi zaune tana kuka ta koma bayan duwatsun ta boya ta rumgume hannayenta tana tausayawa kanta, domin bata san inda zata je ba kuma ba zata iya komawa garin da suka shar'anta mata doka ta karya ba. Sosai ta lafe jikin duwatsun ta yi zamanta a gurin da baka jin motsin komai sai ruwa dake gudana babu komai a gurin sai ciyayi, duk yunwa da kishin ruwan da ta ji bata yarda ta fito daga gurin ba ganin take idan ta fito za a iya ganinta, tsoro da rikicewar da ta yi ya saka ta manta cewar suna da tsananin tsafin da za su gani ko sanin inda take, a gurin ta wuni har dare yunwa ta hana ta bachi sai da dare ya raba sosai sannan ta samu yin bachi shi ma daker domin yunwa take ji sosai, saboda bata saba zama da yunwa ba, idan ma bata da abun da zata ci a gida taje take zuwa ta hau itacece ta ci yayan itatuwa sai ta koshi sannan ta dawo wani lokacin har sai ta yi guzuri.
*⚜️ ...WANI GARI... ⚜️*
_Na Khadeeja Candy_
1️⃣2️⃣
Ganin yana kokarin saka babbar rigarsa ta kalleshi tana karasa bude abincin.
“Abun da ka fi so ne na girka”
“Eh na ji kamshi ai, akwai abun da ya taso min na na gaggawa, zan ci abinci a waje”
Ya fada ba tare da ya kalli inda abincin yake ba, da fuskar mamaki ta sake kallonsa.
“Ba ala'adarka ba ce cin abinci a waje, na san na bata maka rai amman ka yi hakuri”
Ya juyo ya kalleta irin duba na manya yana tambayar abun da ta yi masa kamar da gaske be san abun da ya faru ba.
“Akwai abun da kika min ne? Zan tafi sai na dawo”
Ya nufi kofa yana daidaita tsayuwar hularsa. Ganin haka ya saka ta mike tsaye.
“Ranka ya dade a gafarce ni, idan ba fushi kake da ni ba, me zai saka ba zaka ci abinci ba? Baka yi min irin haka sai idan shaidan yayi galaba akan mu”
Be amsa mata ba be kuma juyo ya kalleta ba har ya fice, komawa ta yi ta zauna ta rufe abincin tana jin wani iri a zuciyarta, ko kadan bata son ganin bacin ran mijinta kamar yadda shi ma baya son ganin bacin ranta, wannan na daga cikin abun da ya karawa rayuwar aurensu karko da dadewa. A bangarensa ta zauna tana ta jiran dawowarsa zuwansa har aka yi magariba aka sauko daga Sallah Isha'i Abiey be dawo gidan, tun abun na normal a zuciyarta har ya fara daga mata hankali, gurin karfe 1 na dare ta kira wayarsa ta shiga tana ringing amman be daga ba, a nan hankalinta ya tashi sosai ba na tsoron halin da yake ciki ba, sai na fushin da yayi da ita, domin be taba fushi ya kaurace mata ba, iyakar fushinsa da ita ya shareta ko ya kauracewa abincinta ko shimfida amman ban da kauracewa gida kuma ta kira shi ya ki dagawa, ba abu ne mai kyau ga namiji mai iyali ya kwana a waje ba, balle kuma shi da yake da manyan yayan da idan suka aikata hakan zai yi musu fada. Sai a lokacin ta fito daga bangare, daman ban tunanin rayuwarta ta baya babu abun da take gaba wunin yau ta ji shi wani iri. Bangarenta ta shigo sai ta samu wutar falonta a kunne Nimra na zaune saman kujera ta rumgume hannayenta, da sauri Ummi ta nufi gurinta domin duba lafiyarta, kusan wannan shi ne karo na farko da ta samu yarta Nimra a farke kuma a falon ba a dakinta ba, ko da tana kaiwa wannan lokacin ita dai bata taba gani ba, Namra ce mai dade wani lokacin bata yi bachi ba, tana kallon ko wani abun na dabam, sai kuma Maleek dake kwakwayar aljannu domin shi daren ne yafi jindadinsa fiye da rana.
“Nimra...”
Ta juyo ta kalli Ummi da idonta dake nuna alamar ba su shirya bata hadin kan yin bachi a yanzu ba. Ummi ta zauna kusa da ita tana fahimtar damuwar dake bayyana a fuskarta.
“Miya hana ki bachi a wannan lokacin Nimra?”
“Ummi ban sani ba, kawai kaina yana dan ciwo kuma bana jindadin rai na”
Lamari irin na uwa mai kula, sai ta danne nata damuwar ta fuskanci yarta.
“Akwai abun da yake damunki Nimra? Karki boye min”
“Ban sani ba, ina jin kamar akwai damuwar na tsoron rasa abun da ban riga na samu ba”
“Are you in love?”
“No, ban ce ina son sa ba, shi ma ba so na yake ba, amman shakuwar da muka fara ne bana son na rasa”
Ta fada idonta na cika taf da kwalla.
“Wani abun kika masa?”
“Shi yana kallon abun a matsayin laifi, amman ni a gurina ba laifi ba ne domin ban aikata dan na bata masa rai ko na cutar da shi ba, shi ya juya min baya yanzu ina ta kiran wayarsa be daga ba”
Be like a best friend to your kids, shi ne abun da Ummi ta yi har ta san damuwar Nimra, sannan ta fara kokarin kwantar mata da hankali.
“Ban san waye wannan Saurayin ba Nimra, amman na san yana da muhimmanci a gareki, domin duk wani abun da zai hana yata bachi a wannan lokacin to abu ne mai muhimmanci, kaurace miki da yayi da kuma fushi hakan na nuna cewar shi din mutum dan'adam wanda ke ma zaki iya yin abin da yayi, saboda haka ki daga masa kafa har sai ya sauko daga fushin, wani lokacin nisantar juna yana da amfani domin mutum zai gane muhimmancinka, kuma zai yi kokarin kiyaye laifin da ya saka aka yi haka agaba, kamar yadda zai bawa wanda aka cutar ko yayi fushi damar hucewa kuma yayi tunani, ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita”
Ta kwantar da kanta a kafadarta, maganar take wani sashe na zuciyarta na tuna mata da abun da mijinta ya aikata a yau, ko ba komai dole ta kiyaye maganar Ameer a gabansa kamar yadda take ta kokarin yi shekaru masu yawa baya, shi kuma