Showing 78001 words to 81000 words out of 281271 words
ne?”
“Eah”
Da sauri ta bi bayansa fitowar Ummi falon ta yi daidai da fitowar Dr Zainab a motar dake bayan ta su yayanta. Ummi ta nufe ta da sauri Dr Zainab ma ta nufo Ummi da saurinta abun ka da an dade ba a hadu ba, sai suka rumgume juna cikin farinciki.
“Sannu da zuwa Aunty Zainab”
Ummi ta fada idonta na cika da hawaye rabon data saka ta a ido yau shekara biyu kenan da watani, domin Abuja ba gurin zuwan Dr Zainab ba ne tun bayan da suka bar kasar.
“Zahra... Ya kike ya gida ya rayuwa bayan rabuwa”
Dr Zainab ta dago Ummi daga jikinta tana kallonta tare da aika mata tambayoyi a jere.
“Lafiya Kalau Aunty Zainab mun yi marmarinki sosai ku shigo ciki mana”
Ta riko hannunta suka nufi cikin gidan tana share hawayen dake zubo mata, rayuwar baya take tuna ita da Dr duka sun manyanta a yanzu, sai dai ita da sauki ba kamar Dr Zainab da tsufan ya bayyana karar a fuskarta ba. Kusan gaba daya suka shigo falon, Ummi da Sister in-law dinta agaba, Mahmood da Maleek na binsu sai yayan Dr biyu yan mata dake binsu kamin mazan su shigo daga karshe. Kamshin turaren wutar da Ummi ta kamsashe falonta da shi ya fara yi musu maraba, suka zauna a falon Ummi ta kira Hanne ta zo ta dauke kayansu da ďaya daga cikin yaran dake aiki gidan Rilwanu yake shigowa da su falon.
“Mommy Sannu”
Maleek ya gaisheta da sunan da yake kiranta kamar yadda yayanta ma suke fada, fuskarsa da murmushi kadan yana dan shafa kansa, ya ji yadda suka tararda shi yayi haje haje da gumi kamar wani mai aikin sharar gida.
“Maleek ya aiki? Kai ma Babanka ya koya maka zaman gida da son kwallo ko? Ko kai zaka gado Abiey ne”
“Come on Mommy na girma yanzu, idan za a fara ai da kananan shekaru ake farawa, ni yanzu aikin da nake na kai shi ina?”
“Hmmm 'Uhmm Mai Martaba ma ba zai bari ba, ko a wacan karon da ya bar Abiey saboda yana hannun Ammy ne, kasan jinin sarauta ba komai suke aikatawa a nan arewa sai ya zama abun magana ko abun kunya, musamman a gurin tsufin sarakuna irin Mai Martaba da suka rike al'adar iyaye da kankani”.
“Yana da gaskiya ai, yana da kyau mu rike al'adunmu da addinin mu a duk inda muka samu kan mu, Juwairiya ya karatu ko an gama”
Ummi ta karasa da dariya tana kallon yar autar Dr Zainab dake kokari cire dankwalin dake kanta tana murmushi. Namra ta kai mata rankwashi a kai.
“Yauwa ko shekaranjiya sai da Ummi ta yi zancen ki, muma yanzu muna da yar'uwarki a gidan nan da bata son dankwali”
Ta wara ido tana sosa kan kana.
“Asss Yaya Namra da zafi fa sabon kitso ne kaina, zuwan da zamu yi Mommy ta cilasta ni yinsa”
Kallo daya Maleek yayi mata ya nufi upstairs yana rike da ball dinsa a hannu. Hakan yayi daidai da saukowa Waira dake sanye da gown din data tsaya iya ƙwabrinta, kanta babu ďankwali sai dai ta faka gashinta a guri daya ta sake a bayanta. A hankali take saukowa domin har yanzu tana tsoron sulbin da tile din yake da shi, Maleek kuma na hawa da sassafar, kallonta yayi ya daga sama har kasa sannan ya dauke idonsa, ita kam tuni nata idon sun yi nisa gurin tantance bakin da suka shigo gidan. Ta fi kurawa Dr Zainab ido ganin Ummi ta zauna kusa da ita tana rike da hannunta. Bata sauko gaba daya ba sai ta tsaya jikin Stairs din har sai da Jabir ya tambaye wacece ita.
“Oh Waira... Yata ce come here baby”
Ummi ta mika mata hannu, sai ta karasa saukowa a hankali ta tako zuwa gurin Ummi ta zauna a gefenta tana leken bakin Juwairiya da yar'uwarta Yesmin.
“Ko ita ce wanda Abiey ya fada min kuna riko yanzu”
“Definitely”
“Maa Shaa Allah kyakkyawa da ita tubarkalla, kuma har yanzu ba a samu iyayenta ba?”
Ummi ta dan juya ta kalli Waira sannan ta kalli Dr Zainab ta mike tsaye.
“Bari na hada miki ruwan wanka da kain Aunty Zainab, ku kuma sai ku shiga dakin Waira ko Namra ku watsa ruwa ga abincin can na dade da gamawa”
“Ina Nimra?”
Dr Zainab tambaya tana kallon tawainiyarta.
“Ta tafi gurin saloon”
“Okay, Namra aure har yanzu shiru? Ba ke ba ba yar'uwarki ba, ga Juwairiya ma da take karamar ku ana zancen yi mata baiko”
Namra ta rufe fuska tana dariya.
“Mommy muma soon za'ayi da yardar Allah”
“Haka kuke ta cewa saboda kun samu Abiey ya daure muku, da a gurina kuke ai da yanzu kun sha matsin lamba, shiyasa ya ki ya ba ni ko daya, idan na yi magana yace shi ma yaran ba su ishe shi ba idan sun min yawa na karo masa daya”
Duk suka saka dariya ban da Waira dake wasa da zara zaran yatsun hannunta. Dr Zainab ta nufi upstairs tana yaye mayafinta, Waira ta tashi ta koma kusa da Mahmood ta zauna, haka take idan ta ga bakuwar fuska bata da sakewa ko fita aka yi da ita ta tsawalla kenan har sai an dawo gida.
“What's her name again”
Jabir ya tambaya yana kallon idonta dake yawo a kasa. Sai Mahmood ya amsa masa.
“Waira”
“Waira.... What's that mean?”
Ya maimaita sunan tare da tambayar ma'anarsa, Mahmood ya daga kafadunsa.
“Just, but Ummi tace tana tunanin Nuwaira su kuma suke kiransa da Waira kawai”
“Oh okay har yanzu bata jin hausa?”
“Tana ji, and she can speak some, as well as English ana mata Evening lesson and tana zuwa makaranta”
Mahmood ya juya ya kalleta.
“Waira ki cewa Jabir barka da zuwa”
Sai ta dago ta kalli mutumen da Mahmood ya nuna mata, ta maida kanta kasa ba tare da ce masa komai ba.
“Yana ďaya daga cikin dalilin da ya saka na tsani yarinyar nan, sai ta rika abu kamar munafuka, ko kuma bata yarda da mutane ba Mtscheeeeee”
Waira ta kalli Namra wacce ta yi maganar ta sake maida kanta kasa. Mahmood yayi murmushi.
“Bata ga damar magana ba”
“Tau saboda ta ga baki ne ko? Kasan bata taba ganinmu ba sai yau”
Yesmin ta fada tana mika hannu ta karbi ruwan da Hanne take mika mata. Umar ya mike tsaye rike da wayarsa.
“Bari na fara ba cikina hakkinsa tukunna”
Namra suka saka masa dariya daman duk wanda ya san Umar ya san baya wasa da cikinsa ko kadan idan kuma zai ci ba kadan yake ci ba, wannan ya saka ya banbanta da yan'uwansa domin shi yana da jiki sosai kana ganinsa ka ga ďan lukuti ba kamar sauran yan'uwansa dake da kirar zaratan jarumai ba. Kusan lokaci daya Namra da cousin's dinta suka haura sama zuwa dakinta suna hira, Jabir kuma ya tashi tare da Mahmood sai ya rage falon babu kowa sai Waira dake zauna a cushion, da kuma Umar dake bawa cikinsa babban aiki, sai da yayi rabin plate sannan ya juyo ya kalli Waira dake zaune tana taba sarkar zoben dake wuyanta.
“Hey young lady zaki iya sama min wani lemun a fridge bana shan lemu mai kwakwa”
Ta dago sai dai bata juyo ta kalleshi, ta san da ita yake domin babu kowa a falon sai ita, Hanne ta fice tun bayan data mikawa Yesmin ruwa, sai dai hakan be saka ta motsa daga inda take ba balle ta yi alamar dauko masa abun da ya bukata.
“Bata san inda yake ba”
Ya sake juyowa jin wata kalar hausar bambarakwai.
“Ita wa?”
Sai a lokacin ta juya ta kalleshi ta idanuwanta masu matukar kyau da daukar hankali, sai ta nuna kanta.
“Waira... Bata sani ba”
Murmushi yayi mai kama da dariya ya juya ya cigaba da cin abincinsa. Ita kuma ya juyo da kanta tana cigaba da wasa da sarkarta, kusan ita da shi duk baki ne a gidan wata kila ma shi ya fita sakewa ya shiga yayi abun da yake so ita bata yi ba, har yanzu bata taba abu idan ba a Ummi ko wani ya bata umarnin yin haka ba, ta kayyadewa kanta abubuwan da take iya ci ko sha, wannan ya saka idan ka ganta kofar kitchen to Ummi ta kirata ta bata abun da ta sabawa kanta da ci ne, ko kuma ta shiga ta gada ma kanta kamar yadda Ummi ta nuna mata idan bata nan zata iya hadawa kanta tea ko zuba ruwa ta sha, ko kuma ta bude warmer ta zuba dankali ko dafaffen kwai domin bata cin soyayya, sai fruit da zallar madara, ko nama da aka dafa da gishi kawai ba tare da an sanka magi ko yaji ba, sai kuma cake da biscuits ko cookies da ake yi da kayan zaki wannan kan duk tana iya ci ko ta sha. Bayan shi bata da wani abinci da take ci. Wannan ya saka bata katsalanta a harkokin gidan duk kuwa da irin yadda Ummi take son ta saki jikinta da su ba komai ta san muhallinsa a gidan ba, kuma bata taba kokarin cilastawa kanta sani ba, domin komai yi mata ake idan Ummi bata yi mata ba, Mahmood ko Nimra zata su mata balle kuma Hanne da Ummi tace ta rika yi mata komai a gidan, Namra da Maleek kadai mutanen da bata taba shan inuwarsu a gidan ba, idan zata zillo ta fadi babu mai tareta a cikin, Namra dai saboda jin kai da ganin level dinsu ba ďaya ba, Maleek kuma saboda kyamar matan da yake, duk kuwa da kasancewar ya canja sosai ba kamar da yake baya iya zama a gurin da mata suke zaune ba, ko cin abinci tare da kanensa, a yanzu kam ya kan ci ko zama tare da su har ma ya dan tsoma baki idan suna magana amman ban da Waira, komai zata yi ko tace ba zai saka baki ba, duk yadda Ummi zata yi zancen wani abu daya shafeta ba zai ce komai ba, komai take ba zai yi magana ba sai dai ya kalleta.
Ita ma kuma bata taba kokarin son yi masa magana ba, tana kokarim kiyaye iyakarta da shi tun a lokacin da ta fahimci yadda rayuwarsa take, ko a kitchen ta shiga idan ta ga shi ne a ciki fitowa take sai yayi abun da zai yi ya gama sannan ta shiga, Ummi ta sha mata fadan hakan har ta fara gajiya, domin so take shi kanshi Maleek ya dawo kamar kowa, wannan ya saka tun tana cilastawa kanta da yayanta da shi kansa zaman a cikin yana takura har ta fara sabawa yana sakewa, domin kullum addu'a take shi ma kuma be fasa ba, azkar din safiya da yamma basa wuce tun a wacan lokacin da yayi mata alkawari. Haka ma idan zai kwanta zai yi addu'a tare da alwala sannan ya kwanta. Duk wani mataki na neman kariya da kuma mafita na halin da yake ciki Ummi ta bi, kuma tana kan bi, addu'ar da Abiey yace zai saka ayi masa bava fasa ba, an roka masa sauki har gaban Ɗakin Allah, tare da kyautata zaton addu'ar ta fara karbuwa domin kaso 50 na rayuwar da yake a baya ta barshi a yanzu, kyanar matan da yake ya ragu yanzu ba kamar da ba, sai dai har yanzu baya jin wani hauki ko ko burgewa a game da mace, har yanzu bata iya hada jikinsa da mace ko da kuwa Ummi ce balle kuma wata macen dabam da be taba kawowa kansa zai iya son wata mace balle har ta kai ga ya aureta ba, balle kuma ace wata mu'amala ta shiga tsakaninsu idan ma ya tuna da wannan sai ya ji baya bukatar auren gaba daya, ba dan kuma ba shi da lafiya ba, sai dai halittarsa data kasance haka.
Sai da Umar ya gama cin abinci tsab sannan ya tashi ya shiga kitchen ya dauko kalar lemun da yake yana gyatsa ya zuba a cup ya sha sannan ya nufi upstairs. Ana kiran Sallah La'asar suka sauko gaba dayansu a tare, wato Umar da dan'uwansa Jabir sai Maleek dake warware hannun rigarsa Mahmood na gefensa, har suka sauko kowanensu da kalar kamshin turaren da yake, suka fice daga falon Waira bata dago ta kallesu ba, ta mike tsaye ta nufi upstars tana takawa a hankali har ta haye sama ta nufi dakin Ummi ta kwankwasa kamar yadda Ummi ta koya mata ta ja ta tsaya har sai Ummi ta bata umarni shiga sannan ta kai hannunta ta murda kofar ta shiga, suna hada ido da Ummi sai ta nufi Ummi da sauri ta zauna kusa da ita saboda ganin Ummi na kuka.
“Ummi tana kuka?”
Ummi ta yi murmushi ta rumgume Waira ta share hawayenta, tana kwaikwayar yadda take hausarta.
“Ummi ta daina kuka Waira... Ta yi shiru...”
Dr Zainab ta sauke ajiyar zuciya cike da damuwa take kallon Waira.
“Waira ba zaki iya tuna yan'uwanki ba? Garinku? Danginki? Da rayuwar da kike?”
Waira ta kalleta sai kuma ta yi saurin sauke idonta kasa ta kama hannun Ummi ta rike tana kara kwantawa jikin kamar Mage.
“Haka take min a duk lokacin dana tambaye ba, bata son fada min komai akan garinsu, al'adarsu ko addinninsu, ko wani abu daya danganci rayuwarta ta baya, kuma saboda mu san ina yan'uwanta suke ya saka muka saka a makaranta kuma ake zuwa har gida ana mata lesions da yamma kullum saboda ta iya Hausa da English, ta fada mana komai amman ta ki ba mu hadin kai har yanzu”
Cewar Ummi cikin damuwa tana kallon Waira.
“Kuma tana jin hausar da kyau?”
“Duk wani abun da zaki fada da hausa ko turanci tana ji, sai dai gurin maidarwar wani lokacin yakan gagareta ko kuma ta yi ba daidai ba, wata kila shiyasa bata son yawan magana, ta fada min makaranta ma idan ta yi magana dariya suke mata”
“Waira ina babanki? Da Mama?”
“Uhmm-hmmm ai idan zaki shekara kina tambayarta wannan ba zata amsa miki ba, ba zata ce miki komai ba, kuma har kwakwalwarta sai da aka duba mana lafiya wai ko ta manta wani abu ne, amman aka ce mana lafiyarta kalau, sai dai idan asiri aka yi mata aka rabata da yan'uwan har ya saka bata son maganar su, ko kuma wanda ya saka a motar wata kila wani abun yayi mata daya danganci sihiri saboda ta manta komai kar ta fada”
“Toh... Allah ya baku kenan, sai ku rike ta har ta yi aure”
Ummi ta yi tare tana shafa gashin kan Waira.
“Tashi kije BQ ki kira min Hanne ta zo ta yi serving din baki”
Waira ta ďaga daga jikin Ummi ta fice daga dakin zuwa kiran Hanne. Ummi zata yi magana wayarta ta yi ringing sai ta kalli wayar tare da kai hannu ta dauka.
“Nimra kina ina?”
“Ina gurin Saloon Ummi”
“Tun zafe har yanzu da La'asar?”
“Eh akwai jira ne, ban ma samu Saloon din ba sauran mutun ďaya akai gareni”
“Gwaggonku ta zo tana ta tambayarki”
Daga can cikin wayar ta kwala ihu tana zumudi.
“Oyoyo Mommy ta iso, gani tafe na ma fasa Saloon din Ummi ki ce in amata barka da zuwa”
“Toh sai kin iso”
Ummi ta sauke wayar tana murmushi.
NIMRA POV.
Ameer na rike da hannun Nimra dake waya da Ummi hankalinsa kuma yana gurin wakar da Humaira take rerawa.
“Idan ka biye ta kan saurayi, sai ya kai ka ya baro, samarin yanzu yan shan minti ne, yar'uwa ki yi hankali 🎶 Duniya budurwar wawa yarinya ki yi hattara... 🎶 iyeee yaraye nanaye Humaira.... 🎶”
Kusan kullum idan ya zo gurin sai ya ji tana rera wannan wakar tun yana daukar abun nata shirme har ya fara tunanin ko da shi take, domin yana yawan zuwa gurin a yanzu kasancewar gurina da babu mai saka maka ido saboda privacy na gurin, idan har yana son ya fita ya shakata da Nimra to nan ne kadai gurin da yake zuwa da ita, saboda bata yarda su fita wani gurin gudun kar wani daga cikin familynta su ganta tare da shi, har gobe tana gudun labarin da zai je kunnen mahaifinta akan alakarta da Ameer. Duk kuwa da irin shakuwar da suka yi da juna a yanzu, da kuma irin yadda sonsa yake da tasiri a zuciyarta, Kullum da kalar karyar da take saboda ta samu ta fito daga gida ta hadu da shi, idan zata shigo a nan sai ta rufe fuskarta ruf da mask da glass saboda kar a ganeta, haka ma idan zata je gidansa. And kullum idan suka zo gurin Humaira ce kadai Ameer ya yarda ta yi serving dinsu, yanayin yadda kullum yake jinta da kamshi ya tabbatar zata yi kokarin tsabta, kuma yana mata haka ne saboda ya takura mata, duk yadda zai bi ya tsallawala rayuwarta idan ya shigo gurin sai yayi, ya kasa korarta ko sakawa a koreta tun bayan rokon so called Kakarta ta yi masa, sai dai ya saka mata ido da yawa ta yadda da zarar ta yi kuskure kadan sai ya mata hukunci mai tsauri, I sauran jama'ar dake aiki gurin tun basa kula har suka san irin takun sakar dake tsakansu. Ita kuma takan yi kokarin ganin ta yi avoiding ko wane kalar mistake saboda ta ba shi kunya.
A kullum idan ya shigo gurin tare da Nimra sai ta rare masa wannan wakar, saboda yadda yake hugging dinta ko ya rike hannunta a gaban Humaira, ko kuma mutanen da suke kai da kawo wato ma'aikatan gurin, daman can Ameer be san wani abu kunya ba, ko da ba halinsa ba ne zai zabi yin haka saboda ya zubar da kimar Nimra duk abunda yake yana yi ne da ganganta, ita ma kanta Nimra da farko ba son hakan take ba sai dai tana kyalewa ta jure saboda farincikin Ameer, zuwa yanzu kam ta fara sabawa kanta da rabar jikinsa har abun da ya fi wannan ma. Idan shi kadai ya zo gurin ko da wani daga cikin abokansa tana da kalar wakar da take rara masa idan tana zirga zirga a gurin ko kuma ta zo kawo musu wani abun. Idan kuma da Nimra ya zo da kalar waka da take musu, zuwa yanzu dai ya haddace duka wakokin saboda yawan rarewar da