Showing 51001 words to 54000 words out of 281271 words
mu tafi da ita a can”
“Hakan zai fi kam, domin abu ne mai wahala ta yardar ta bisu”
Shi ne abun da kowa ke fada, Dr ya daga kansa ya samu daker da cire hannunsa daga rikon da ta yi masa, sai ta kara kankanme jikinsa. Tana jin ya fara tafiya sai ta taka ita ma amman bata yarda ta bude idon ba, takawa take tana jin kamar tana taka ruwa saboda sanyin tile din bata taba tafiya a kansa ba, daker ya samu ya fita daga gurin, Office dinsa kam sai wani ne yaje ya dauko masa kayansa ya kawo masa, tana ta jin hayaniya mutane yayi yawa ta san sun fito guri mai mutane da yawa, a hankali ta bude idon ta kalli yadda gurin yake wasu na kallonsu wasu kuma na da hada hadarsu, dagowa ta yi ta kalleshi sai yayi mata murmushi sai ta sake rufe idon, sai da ya isa gurin motarsa ya bude sannan ta sake bude idon sokoko ta yi tana kallon motar at first bata ji tsoro ba sai mamaki tana kallon motocin da ba daya ba, ta kai hannu zata taba wani motar dake kusa da ta Dr yayi ma motarsa key karar da ta yi ya saka ta zabura ta dauke hannunta da sauri tana tasa motar a firgice, take hankalinta ya tashi ganin haka ya saka Dr ya ce.
“Mota zamu shiga”
Sunan mota ta fara rikewa, domin shi ta taba ji a bakin Eid.
‘Outarrr’
Ta maimaita sunan a ranta tana tuna yadda yake fada mata cewar wasu mutanen na dabam a wata duniyar suna hawanta su yi tafiya, bata taba sanin haka motar take ba sai yau, Dr ya kai hannu ya bude motar yayi mata alama da ta shiga da hannu, a take ta lake masa kafada alamar bata zata hau, he never thought da gaske take har sai da yayi unkurin sakata da karfi sai ta sake shi ta ruga zata fita daga gurin sai kuma ta rasa gurin waye zata tafi mutanen dake gurin sun mata wani iri da bata saba da su ba, ga gurin ababen hawan sun yi yawa ba mota kadai ba har da babur. Gudu take tana neman gurin boya ta rasa gurin wa zata tafi mutane sai kallonta ake kuka take sosai tana waige waige ta gudu nan ta dawo nan haka take har ta samu gurin wata fulawa ta boya ta nade guri daya kamar macijiya ga hannunta sai zafi yake mata zuciyarta na bugawa da mugun karfi kamar zata fado.
“Dole fa sai da karfi za a shigar da ita motar nan in ba haka ba, ba zata shiga ba kana ganin wannan yarinyar kasan daga wata duniyar ta fito”
Police din ya fada, Dr Shuraim ya sauke numfashi cikin damuwa yana kallon inda ta gudu ta boya.
“Ya za'a tafi da ita Abuja nan ne?”
“Ayi mata allurar bachi kawai”
Dayan ya fada yana ganin kamar hakan shi ne mafita.
“Ba'ayi ma mutun allurar bachi hakan nan kawai ba tare da lalura ba, da zaku aminta zan tafi da ita gidanmu for a while kamin ku tafi da ita”
“Aa ba zai yiyu ba, mu umarni aka ba mu kuma ba zai yi mu saba umarnin ba”
Ya nufi gurin ya risina ya leki inda take gaba daya a firgice take hawaye har sun gaji da ita a idonta sun kumbura mata idon fatar idonta ta yi masa ja, fuskarta ma ta yi kamar an mareta.
“Eid.... Eid... Eid...”
Shi ne kawai abun da take fada tana jin kamar ace yana jinta ya zo ta yafi da ita, a yanzu kan ta shiryar fuskantar hukuncin garinsu siye da wannan rayuwar da take bata tsoro, rayuwar da komai na su ya banbanta da nata, ina ma mafarki take ba gaske, bata da kowa a duniyar nan bata san kowa ba, ba su da abubuwa irin nata, zuciyarta kuma ba raya mata cutar da ita za su yi.
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:48 PM] My S Line: ©KHADEEJA CANDY 18
A hankali ya risina kusa da ita ya mika mata hannunsa.
“Zo mu tafi”
Ta kalli hannun nasa hawaye shar a fuskarta gashin kanta dake cinkushe ya kara watsewa ya baibaye fuskarta wani ya sauko har bayanta, kallo daya zaka yi mata ka san a firgice take. Na kurame yayi mata ya nuna ta ya nuna kansa sannan ya jikansa da hannun guri daya, ya sake mika mata hannunsa sai ta daga kai ta nuna mishi mota ta girgiza kai, alamar ba zata shiga ba ta hade hannayenta ta rufe kunnenta. Iskar bakinsa ya busar yana tunanin yadda zai yi ta aminta ta shiga motar.
“Ba zata shiga da arziki ba, kawai ka bari a sakata da karfi idan ta gaji dole ta hakura ai”
Daya daga cikin police din ya fada yana nufo inda take rakube, babu yadda Dr Shuraim ya iya sai hakuri ya kawar da kai, ko bata fada masa ba ya san bata taba ganin mota ba balle har yace ta saba shigarta, yanayin shigarta da kalamanta sun nuna ba a irin duniyar da yake rayuwa ta rayu ba, Allah kadai ya san daga wace duniyar aka fito da ita. Hakan nan ya ji ihun da take a lokacin da police din ya rika ta yana damunsa, wani irin fisga take kamar babu ciwo a hannunta musamman da ya danneta da karfi ya saka ta a motar Dr Shuraim sai ta rika yin wani irin abu kamar zata shide ta mutu gaba daya. Sai da Dr Shuraim ya rufe kofofin motar ta ko'ina sannan ya yi ma motar key madubin gaban motar ya saita baya da shi so that ya rika kallon fuskarsa da shi, sai dai me ta sauka daga kan kujerar baya ta zauna a kasa ta takure duk rashin fadin gurin ta takure ta zauna a haka ta boye fuskarta ta rufe ido, tsit ta yi kamar ba ita ce take ta ihu ba, a yanzu ta gane wani abun ake yi ma ihu wani tsoron kan sai dai ka boye kanka ka saurari sakamakonka. Each and every minute sai ya juyo ya kalli bayan motar domin ya tabbatar tana lafiya, motar police din tana gaba yana biye da su har suka isa, state CID dake Katsina, a nan ta zama abar kallo a gurin wasu police din da labarinta ya iso musu kamin a kawo ta gurin. Motar aka bude gaba daya ana kallonta dayan ya fara cika umarnin shigabansu na kokarin fitowa da ita a nan ta fara sabon ihu sai da ta kuka gurin tana lakewa ciki.
“Idan ba yanzu za a tafi da ita ba, a bar a motar har zuwa lokacin da za a tafi da ita please, saboda bata natsu da kowa ba a nan”
It's very unusual police su yarda su bar wani a hannun wani, sai dai yanayin fuskar kalama da mutuncin da Dr Shuraim yake da shi a fuska ya saka DPO ya aminta bayan ya duba id card din aikinsa kuma aka hada shi da wani police daya da zai bishi su je ganin muhallin da za'a ajeta, sun amince ne sanin babu inda gurin da za'a ajeta ta natsu kamar a gurinsa domin ihun da take ba karami ne ba, kuma abu ne mai wahala ta yarda ta zauna a hannun a yanzu, gaba daya ko idonta bata yarda ta bude ba tun da suka saka ta a motar balle kuma ta kalli inda aka kawo ta ko kuma mutanen da suke gurin, gashi ba a yau za'a tafi da ita ba sai gobe da safe za a tafi da ita Abuja, ba ita kadai ba tare da motar Nimra za a kai. A motar Dr Shuraim ya barta bayan sun isa gidan police ya shiga ya gaisa da mahaifiyar sannan ya fito yayi musu sallama. Mahaifiyarsa Hajiya Hajara ta fito waje tare da kanwar Dr Maimoon suna kallon motar kamin Dr ya iso har Maimoon ta ita gurin motar tana kokarin budewa.
“Maimoon karki bude, ku shiga ciki idan ta ganku ba zata yarda ta fito ma bata son mutane tsoro take ji”
“Ikon Allah”
Cewar Hajiya Hajara da gutun mamakinta domin bata taba jin mutumen dake tsoron mutane ba sai wannan bakuwar da aka kawo musu da ba zato babu tsammani, a kokarinta na kyautata masa ita da yarta suka fice daga gurin, shi kuma ya kai hannu ya bude motar ya taba ta, sai ta fara ihu.
“Shiiiiiiiii Baby Girl”
Ya kama dayan hannun mai ciwo ya rika mata a hankaloli, dayan hannunsa kuma yana rike da hannunta na hagu, yatsunta ya fara kallo sirara ne irin na mata akaifar mai kyau irin mao tsawon nan mai laushi, sai dai dattin dake ciki ya saka akafair ta yi mata kamar ta kwaba laka, ya sake hannunta ya mike tsaye ya cire key motar ya sake dawowa gabanta ya resina ya kama hannun a nan ma bata fasa halinta ba sai da ta yi masa ihu, sai dai be kula ba ya saka abun cire akaifa nails dake lake da keys din ya fara katse mata farcen, ko kadan bata jin ciwo amman sai ya mutsa fuska take tana.
“Ash ash ash ash ash ash ash...”
Kamin ta fisge hannunta ta bude ido domin ganin abun da yake mata, ta duba hannunta sai ta ga an yanke mata farce, ta kalleshi kamar za ta yi kuka sai yayi saurin nuna mata nasa hannun da babu farce ko daya. Bata yarda ba sai ta nade hannun ta maida baya, ko kadan be tirsasa kansa cewar sai ya yanke mata ba, sai ya saka abun a aljihunsa ya mika mata hannu alamar ta fito, a nan fa tace masa bari na duba inda nake, kallon iya inda idonta zai kai take a cikin motar tana mamakin a ina ya kawo ta? Kuma me zai mata? Ta san ba gurin dazun ba ne da take jin jama'a da yawa, duk kuwa da bata bude ido ba amman ta ji alama hakan kuma ta ji anyi motsi da abun da take ciki kamin a kawota nan. Jin kamar ta aminta da shi ya saka ta fara kai hannunta ta taba interlock din dake gidan so take ta ji idan bashi da sanyi kamar na asibitin da suka baro, sai ta samu wannan ta dumi sosai saboda zafin ranar da ake a Katsina, ganin haka ya mika hannunsa ya fito da kafarta waje, sannan ya riko hannunta ta fito a hankali tana kallon gidan da yake da girma sai dai ba irin matsiyacin girman nan ba, sai dai an kawata shi da shuke shuken itace kala kala a jikin ginar gidan har zuwa gate haka ta rika bin itacen ta kallo kamin ta maida ga harabar gidan, ba mamakin yadda aka zagaye gidan take ba, domin ko a duniyarsu akan zagaye gida da wadanda suke iyawa ko kuma suke da Sarautar a garin, wani da kasa za ayi wani da itatuwa, fenti da ginin bulu suke abun da bata taba gani ba, yanayin ginin gurin yayi kama da na inda aka fito da ita wato asibitin sai dai kamshin nan ya banbanta da can, kamar wacce ta yi arba da abun tsoro haka ta rike shi da sauri da kuma karfi tana raya cewar idan ma ya kawota a irin gurin da aka fito da ita ne ba zata yarda ta sake shi ba, haka kuma ba zata yarda ya cutar da ita ba. Sanin zata bashi wahala gurin shiga gidan saboda rikon da ta yi masa ya saka ya duka ya dauketa cak kamar yar baby, sai ta saka hannayenta ta zagaye wuyanta tana murmushi idonta a rufe, tana matukar son a dauke ta a haka sai dai bata samu domin Eid baya mata haka saboda gudun fushin Sarki ko fadansa, kusan tun da take a rayuwarta sau biyu ko uku kadai ya taba yi mata irin wannan daukar. Yayi mamakin ganin murmushi a fuskarta domin be tsammanci haka da wuri ba, gashi murmushi ya kara mata kyau dattin dake jikinta yayi kadan ya boye kyauta gaba daya. Sai a yanzu yake jin karnin da take na datti har wani tsami tsami take irin na Shugaban kazaman garinsu, kai kana jin warin kasan ta dade bata ga ruwa ba kuma ruwa be ganta ba, sai dai ba kawowa kansa cewar bata son wanka ba a tunaninsa bata samun wankan ne wata kila a inda aka boyeta ko aka fito da ita a rufe take ba a barinta fita. Ba karamin jihadi ta yi ba na amincewa ya shiga da ita har cikin gidan, tana jin karar bude kofa sai ta bude ido domin bata saba jin irin sautin ba, a nan fa ta zama na daji a makka idonta kamar za su fado tsabar kallon labulayen falon da kujeru ba ka kamar lokacin da idonta ya sauka a gurin TV dake kashe ta kalli guluf da fankar dake aiki sai ta kankameshi ta rufe ido. A tunaninsa ta fi bukatar wanka da komai a halin yanzu hakan ya saka be direta ko'ina ba sai bathroom din kanwarsa. Tana jin sanyi tile din sai ta dage kafafuwanta tana son ya dauke ta.
“Nooo a nan zaki tsaya Maimoon zata taimaka miki ki yi wanka”
Ta bude idon kamar ta san abun da yake fada, a nan ma ta shiga bawa idonta abinci, tun daga kan kofar bathroom din take kallo har zuwa tube da karamin madubin da yake lake, kamin ta daga kanta sama, sakinta yayi a hankali ganin su biyu ne kawai a gurin babu wani ya saka bata yi yunkurin yin ihu ba ko roke shi, ya nufi durum ya bude ya zuba ruwa a bokiti sannan ya dauko soso da soap ya aje a gurin, ya bude gurin da kanwarsa take aje kayan amfaninta ya dauko sabon brush ya dauko brush and toothpaste ya zuba a kai ya mika mata, ta dade tana kallon abun sannan ta karba sai ta saka yatsanta ya kwashe toothpaste din da yake kai ta saka a baki ta lashe abun ta, ta hade sannan ta saka halshe ta lashe dan zaki zakin da take ji ya hana ta ji makakin da yake tare da toothpaste din, sai ta mika mata tana tande baki, abubuwa biyu suka zo masa a lokaci daya mamaki da kuma tausayinta a lokaci daya, ya mika hannu ya karbi brush din ya saka zuba mata wani sannan ya zuba wani a hannunsa yana nuna mata yadda zata yi, a maimakon ta saka brush din a bakinta sai ita ma ta saka yatsanta ya lakaci man ta saka a baki tana gogawa kamin ya goga yadda ya kamata har ya nuna mata ta zubar ita kan har ta hade nata, yana zubarwa sai ta tofar da yawu.
“Oh Allah”
Ya fada yana furzar da iskar bakinsa ya daga kansa sama, sai ita ma ta kwaikwayeshi sai dai ita bata ita furta abun da ya fada da kyau saboda ba yarenta ba ne.
“Oww Allah”
Ta furzar da iskan ta daga nata kan sama, zatonta yana nuna mata komai ne, be san lokacin da dariya ta subuce masa ba, sai ita ma ta yi murmushi, karbar brush din yayi ya aje sannan ya nuna mata ruwan dake cikin bokiti tana ganin ruwan sai ta bata fuska ta lake kafada domin ta yi arba da makiyinta. Sai ta matsa can baya ta rakube ta bata rai sosai. Ganin haka ya saka shi nufar kofar ya bude ya fito, a falo ya samu mahaifiyarsa a tsaye tana jiran fotowarsa.
“Ni kam ina cewa Allah yasa dai ba wanka zaka mata ba”
Yayi murmushi.
“Aa Maimoon zata taimaka mata ta yi wanka”
Maimoon ta nuna kanta cikin rashin jindadi.
“Ni kuma?”
“Haba ki tausaya mata mana, bakonka Annabinka kuma iya yau ne kawai tun da gobe wucewa za'ayi da ita”
Ba dan ranta ya so ba ta mike tsaye sai daj Mamanta ta saka baki kuma yayanta ya hade fuska.
“Ki wanke mata kanta sosai, kuma ki kula da ciwon dake hannunta”
“Yaya kamar wannan yarinyar za'ace ba zata iya yi ma kanta wanka ba?”
“Wanka na ce ki mata? Ki taimaka mata ta yi nake nufi, idan kin wanke mata kanta sai ki fito ki barta ta yi wankan, kina ganin yanayin yarinyar nan kin san bata saba irin rayuwarmu ba, yanzu ba Brush na bata da man wanke baki sai ta lashe man”
Cikin Mamaki Hajiya Hajara ta ce.
“Ni ai tun da ka fada min cewar tana tsoron mutane na san akwai matsala, anya ba memory kanta ya samu matsala ba”
“Bata yi yanayin da irin wadan nan mutanen ba, kuma ba su barta a asibitin ba balle a abincika kwakwalwarta ba, sai son tafiya suke da ita Abuja, ni tsorona daya idan ba tsafi za'ayi da ita ba, wata kila an ajeta a wani gurin ne aka koya mata rayuwar ta dabam, ko kuma an satota daga wani gurin ne, a yadda na fahimta su police din suna kokarin rufe maganar ne kawai, wata kila akwai manya a ciki, in ba haka ba mi zai saka a dauke ta a kaita can ba tare da ta ji sauki ba, idan har nema mata yan'uwa za'ayi ai sai a nema mata a inda yan'uwanta suke a nan ba tufafin jikinta ma irin na fata ne da aka ce a can da arna suna sakawa...”
Kamin Hajiya Hajara ta sake magana Maimoon ta fito tana fadin.
“Ihu take min kuma bata bari na taba kanta kuma Wallahi yayi datti da yawa sai an saka mata Clean”
Dr Shuraim ya juyo yana mata wani kallo mai kama da harara.
“Ina kika taba ganin an sakawa kan mutun clean? Sai kace kayan wanki”
Hajiya ta yi murmushi.
“Kar a taba mata kayana ko sai ka ce ke kike siya? Je bathroom dina ki dauko min shampoo and conditioner sai na rika miki mu wanke mata”
Ba musu ta juya ta koma sai Hajiya ta bi ta a baya, kamin ta kawo har Hajiya ta shiga Bathroom din ta tsaya tana mata kallon tausayi a kalaman Dr Shuraim cewar wata kila tsafi