Showing 96001 words to 99000 words out of 281271 words

Chapter 33 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1235

mutuwa idan har aka rabata da love of her life, bata ta inda zata rayu ba idan har iyayenta suka zabi raba soyayyar da Ameer. Daker ta tashi ta tsaye ta nufi inda ta nefar da key din mota da wayarta ta dauka idonta daya a rufe saboda dukan da Maleek yayi mata ya same ta a dayar idonta ne, bakinta na a kumbure yake har lokacin yana jinin naushin da Abiey ya kai mata a baki, bata ko iya taka kafarta da kyau sai dingishi take, ko'ina na jikinta tsami yake duk inda Maleek ya same ta da bulalar ya kumbura mata jiki, yayi mata ja. Idonta har ya canja kala saboda kuka har wani jiri take gani. Sai da ta fara lekowa ta ga babu kowa a saman sannan ta sauko nufo downstairs tana tafiya dake tana sauri ta sauka, kanta babu ďankwali balle ayi maganar mayafi, haka ta sauko falon ta nufi kofa ta fita babu talkami da faduwar gaba ta fito falon ta nufi gurin motar da Ummi ta bar mata tana hawa tun bayan da Ameer ya ci uban tata motar. Ta bude ta shiga ta yi mata key kamin ta yi reverse kamar zuciyarta zata fado ta ji, masu gadi na ganin ta kunna mota sai suka fara kokarin bude mata gate, kamin ta iso har sun gama budewar ta nan ta samu sa'ar ficewa da sauri tana wani irin gudu. Fita ta yi daga unguwar amman hankalinta be kwanta ba har sai da ta ganta a bakin gate din gidan Ameer, tana faka motar bata tsaya kashewa ba ta bude ta fito ba dan tana da tabbacin Ameer yana cikin gidan ba ta nufi kofar falonsa ta tura kofar tana budewa sai ta fadi cikin falon saboda babu kuzari a jikinta kanta ma kamar zai tsage gida biyu take jinsa saboda ciwon da yake. Ameer dake rike da gorar ruwa da waya a kunne yayi saurin yanke wayar ya aje ruwan ya nufota.

“Nimra wooo what happened?”

Ta dago ta kalleshi tare da kai hannu ta taba fuskarsa.

“Ameer. Abiey, Ummi da Ya Maleek ba za su bari na aureka ba, ba za su bari mu zauna a tare ba, Ameer idan suka ba ni da kai mutuwa zan yi, ni kadai na san yadda nake ji a raina, Ameer guduwa zan yi, mu tafi wani gurin har sai iyayena sun sauka daga fushinsu, zan iya daukar komai amman ban da rabuwa da kai, ina sonka Ameer...”

Lokaci daya aka jefo masa digon tausayinta a ransa, yadda aka yi mata jina jina da jiki kuma har ta baro gidansu a irin wannan yanayin babu mayafi babu talkami hawayen da take zubar kawai sun isa su sosa masa zuciya.

“No Nimra ba zaki aikata haka ba”

“Ba zaman ban za zamu yi idan muka gudu ba Ameer aure zamu yi, mahaifina ba zai saurareni a yanzu ba, kalli yadda Ya Maleek yayi min da jiki”

Ta nuna masa jikinta, duk sai ya ji wani iri domin saboda shi komai ya faru, a kuma manufarsa ta daukar fansa ba dan yana sonta ko son aurenta da gaske ba. Ya saka hannunsa ya daga ta daga kasa ya zaunar da ita kan kujera ya rumgumeta.

“Ba zamu aikata hakan ba Nimra, ni ma da kika ga na gudu saboda Mahaifina ya kore ni da kansa ne, ke kuma mace ce hakan zai iya janyo miki matsala ba ga iyayenki kadai ba”

“Ameer ba ka ce kana kaunata ba? Zaka iya yin komai akaina?”

Yayi shiru kamar mai tunanin amsa mata, ba kansa yake ji ba, ita yake ji idan har ta aikata abun da zuciyarta ta raya mata zata jefa kanta a matsala ne kawai ne.

“Hakan ba yana nufin na sake jefaki a wata matsala a yanzu ba, Nimra I'm ever to fight for you now i can't let your family hurt you again, I'm serious this time”

“I think I'm losing my mind now, please don't let me down Ameer ina matukar kaunarka, dan Allah mu gudu idan mahaifina ya san na sake zuwa gurinka kashe ni zai yi”

Ta saki jikinsa ta mike tsaye jikinta na rawa. Sai yayi saurin mikewa shi ma ya rumgume ta.

“Shikenan zamu gudu, amman yanzu akwai wanda ya san kin zo nan?”

Ta girgiza masa kai alamar aa.

“Amman za su iya zuwa nema na a nan, Abiey zai iya kashe ni idan ya zo ya gan ni a nan”

Ya saketa ya nufi inda ya aje wayarsa ya dauka ya dauki key dinsa ya dauki wayarta ya rika hannunta ya fito da ita da sauri, a motarsa ya saka ta, sannan ya nufi motarta ya kashe ya dawo gurin motarsa ya shiga mazaunin direba ya tashi motar, ana bude masa gate ya fice da gudu, sai da yayi nisa sannan ya faka ya kwantar mata da kujerar motar yana kallon idonta dake rufe fuskarta har ta fara canja kammani. Tunanin inda za su je su boya ya fara yi kamin ya mike hannu ya rike hannunta shi dai ya san har ga Allah baya son ta a zuciyarsa sai dai kuma tausayinta ya cika masa zuciya a yanzu, domin ya fahimci ta gama haukacewa kansa.
[6/17, 10:49 PM] My S Line: 32

*W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*


Jin ya faka ya saka ta bude idonta daya domin ďayan ya rike ya rufe a yanzu ya like, tana kallon gurin ta dube shi.

“Me mike yi a nan?”

“Dole zamu zauna mu yi tunani inda zamu tafi mana, kuma kin ga muna bukatar kudi mai yawa da zai wadace mu a iya zaman da zamu yi, and dole mu tsara komai kamin mu tafi, kin ga babu wanda ya san muna zuwa nan balle ya saka mana ido ko a fada cewar an ganki”

Ta fashe da kuka.

“Ban tana tunanin zan iya aikata haka ba Ameer dan Allah karka ci amanata, karka bar ni dan Allah”

Ya saka hannunsa ya rike fuskarta.

“Ni na janyo miki wannan abun Nimra, so i promise you ba zan kyale ki ki sake aikata kuskure ba, kuma ba zan kyale ki sha wahala ke kadai ba”

Ya sumbanci hannunta, tun da yake a rayuwarsa be taba jin tausayin wani mutum lokaci daya kamar yadda ya ji tausayinta a yanzu ba. Yarda da ta yi da shi ya saka ta amince da kalamansa har ya bude motar ya fita ya zagaya side dinta ya bude mota ta sauko sai yayi mata side hug domin bata iya tsayuwa da kyau kuma ba zai yiyu ya dauke ta a public guri kamar wannan ba, haka ya shiga da ita a gurin ya nufi gurin da suka saba zama ya zaunar da ita sannan ya koma ya dauko wayarsa da tata wayar ya dawo ya zauna, yana kallonta sai ta miko hannunta ta rika hannunta. Humairah dake gefe tana kula da wasu wata abokiyar aikinta ta tabo ta ta nuna mata shigowarsu domin kowa a gurin ya san Humaira ce kadai take kula da su idan sun zo gurin. Sai da ta gama da wandanda suke serving sannan ta nufo gurin da Ameer yake zaune tana rare wakar da ta tanadar musu. Kusan a yanzu ya haddace wakar dan haka tana fara rerawa sai ya tayata suka kare wakar a tare.

“Idan ka biye ta kan saurayi, sai ya kai ka ya baro, samarin yanzu yan shan minti ne, yar'uwa ki yi hankali 🎶 Duniya budurwar wawa yarinya ki yi hattara... 🎶 iyeee yaraye nanaye Humaira.... 🎶”

“Na haddace wannan wakar sai wace kuma?”

Ya tambaya a tsawa yana kallonta sai ta daga kafadunta tana kallonsa ita ma.

“Wakata ce kawai”

“Nice song”

“Thank You”

Ganin kamar tana kokarin raina masa da wayo ya saka ya daki teburin gabansa da karfi, har sai da ta zabura.

“Don't you ever singing that song again”

Ta hade yawu tana sauke ajiyar zuciya domin ta lura ba da wasa yake ba.

“Me za a kawo muku?”

“Ba ma bukata go back to your work”

Ta juya ta fice daga gurin tana ta mamakin dukan data gani a jikin budurwarsa yau, fada suka yi yayi mata wannan dukan ko kuma dai wani ne yayi mata, idan har wani yayi mata zata fi kowa jindadin musamman ace iyayenta ne sun san halin da take ciki, domin dai alakar dake tsakanin yarinyar da Ameer ya isheta sai ka ce a kanta suke zaune.

“Dear shiga ki wanke fuskarki a restroom i will make a phone call na yi mana booking flight”

Ta daga masa kai ta fara kokarin mikewa tsaye ta kasa sai Ameer yayi kiran Humairah da hannu, ta zo gurin daman idonta yana kansu, ya nuna mata Nimra.

“Taimaka mata ta shiga bandaki”

Humaira ta kalli Nimra tsab sai kuma ta kalleshi da alamar tuhuma, da ido yayi mata alama da lafiya? Bata ce komai ba ta rikata Nimra ta mike tsaye suka nufi hanyar shiga bandakin. Sai da suka wuce sannan Ameer ya ďauki wayar Nimra dake aje a gabansa saman teburin da suke zaune ya bude security wayar, domin ya dade ta sanin password din ya shiga calls dinta ya duba number da yake kyautata zaton ta mahaifiyarta saboda an yi saving dinta da My Lovely Ummie and saka heart emoji da rose flower, number ya kwashe ya saka a wayarsa da danna kira. Sai da ya kira kira har sau uku ba a daga ba ya sake gwadawa ana biyar aka yi picking.

“Assalamu Alaikum”

“Wa'alaikussalam...”

“Who's this?”

“Ameer saurayin Nimra”

Wani deep Ummi ta yi ta nemi guri ta zauna kunnuwanta na sake saka mata sautin muryarsa, wasu zafafan hawaye suka kwankwaso mata kofa.

“Na san be kamata na kira ba, amman ina son mu yi magana ne ta fahimta, ina son ki duba ďakin Nimra ki gani tana nan?”

Ummi ta tashi da sauri ta fita dakinta ta isa kofar dakin Nimra ta tura kofar sai da ga babu kowa a ciki, ta leka bandaki bata ganta ba, a take ta girgiza kai.

“Bata ciki”

“Tana nan tare da ni, ta gudo ta zo inda nake tana son mu gudu ni da ita, saboda tace ba za ku yarda na aureta ba, ita kuma zata iya mutuwa idan kuka rabata da ni, sai dai ba zan iya bari ta aikata hakan ba saboda kuskure ne da zai kara mata tsana a idonku, please ki zo ki tafi da ita zan aiko miki da address inda muke yanzu nan. Ke uwa ce Ummi ban san dadin uwa ba domin na tashi ba tare da na santa ba, tawa uwar ta rasu tun ina jarari saboda haka ban san dadinta ba sai rashinta, amman ke yanyanki sun san dadinki kuma ke ma kin san ďadin yaya, be kamata ki bari Maleek yayi mata wannan dukan ba, da nine mahaifiya ba zai yarda wani yayi min haka ba, balle kuma uwa ta da na tabbatar zata iya hada yakin duniya saboda ta kare ni daga wani ya yi min jina jina a jiki haka, balle kuma Nimra da take mace ce, idan ba ku san alakarta da ni, ku fahimtar da ita cikin hikima da soyayya ba ku yi mata horon da fadan da tunaninta zai gushe har ta bar gidansu ta zo gurina ba, and i want to clean this doubt to you ban taba aikata zina da yarki ba, tsawon lokacin da muka dauka a tare tana boye soyayyata a gareku ba mu aikata abun da kuke tunani ba, i know I'm a bad person but ban taba yarki ba. For now zaki iya zuwa ki tafi da ita kamin mu bar gurin”

Tun da ya fara maganar har ya kai aya Ummi bata ce masa komai ba, sai sauraren muryarsa take wani bakinciki na bude mata sabon feji, hannu ta mika ta taba ginin dake bayanta ta jingina a hankali ta lumshe ido. Can kuma ta bude idon tana ta kallon number da ta yi appearing a truecaller da sunan Ameer. A yau ďanta ya kirata, amman ba kira na sanin cewa ita mahaifiyarsa bace, ba kira nw irin an ďa da uwa ba.

Sakon address inda suke ne ya biyo bayan kiran da yayi mata, ta mike tsaye har lokacin hawaye take, ta kasa tsayar da kuka kuma ta kasa saka hannunta ta share, saukowa ta yi downstairs ta nufi gurin mijinta, tana shiga falon sai ta samu Maleek da Abiey zaune da alama wani abun suke tattaunawa, sai dai shigowarta ya saka sun maida hankalinsu a gurinta.

“Nimra bata gidan nan”

“Kuma..?”

Maleek ya fada da mamakin wani irin hali yar'uwarsa ta daukarwa kanta.

“Ta gudu ta tafi gurin Ameer, ya kira ni a yanzu ya fada min inda zan same ta”

Abiey ya hade wani kwalolon bakincikin da ya tsaya masa a makoshi.

“Ina daf da yafe yarinyar nan...”

“Ba zaka iya ba Abiey, ka fi kowa sanin yadda ake ji idan iyaye suka juya baya, ko ka manta abun da ya faru tsakaninka da Mai Martaba? Ba zaka aikata hakan ga marainiyar da uwarta ta tafi ta bar mana amanarta ba, da ace ta saba aikata maka hakan sai ka ce ka gaji amman bata saba ba, kuskure aka samu ya kamata ka duba mata Abiey, ni bazan iya juyawa yata baya ba”

Ta juya ta fice daga dakin, da gudu ta iso bangarenta tana kuka ta shiga ta dauki hijan dinta ta saka ta dauki makullin motarta ta fito da saurinta ta sauko kasa. Tana fitowa waje sai ta samu Abiey Maleek sun data mota ita kawai suke jira.


AMEER POV.

Ameer ya aje wayar yana matukar jin tausayin halin da ya jefa Nimra, be taba sanin abun da yake aikatawa be kyautu ba sai a yanzu da ya firgita yar mutane ta fita daga hayyacinta. Bama kamar data fito daga bandakin yana kallon fuskarta ya san samun damar kebe kanta ta yi kuka ne kawai ta yi amaimakon wanke fuskar da yace ta yi, yana ta kallonta har Humaira ta zaunar da ita a kujerar da take zaune a dazun, wannan karon tausayine a fuskar Humaira ba kamar dazun ba, bata san abun da ya faru ba, amman yadda ta ga jikin Nimra da kuma kukan da take ya saka jikinta yayi sanyi tana jin tausayinta.

“Zaki iya cin wani abu na kawo miki?”

Humaira ta tambaya, sai Nimra ta girgiza mata kai alamar aa. Humaira ta kalli Ameer dake kallon Nimra.

“Ban san miya faru ba, ban san damuwarta ba, amman ka sani idan kai ka cutar da ita Allah ba zai barka ba”

Ta fada idonta na cika da hawaye, kallonta Ameer yayi yadda take iya fada masa magana ba tare tsoro ko fargabar abun da zai mata ba abun har mamaki yake ba shi, shi kam a rayuwarsa be taba haduwa da tsagera ba irin wannan yarinyar, ba dan ta samu damarsa ba har yaushe zata kalli tsabar idonsa ta fada masa cewar idan shi ya cutar da yarinyar da bata da alaka da ita Allah ba zai barshi ba, sai dai ta ďayan bangaren kalaminta ya sanyaya masa jiki domin duk wani mai imani da tausayi idan ya ga yadda Nimra take zubar da hawaye dole ya tausaya mata, musamman ma shi da ya san silar kukanta da kuma halin da ya jefarta.

“To yar iya na gode sai ki koma gurin aikinki”

Ta watsa matsa harara kasa kasa, tana zaginsa a ranta dan dai ba zata iya fada a fili ba.

‘Bakin Azzalumi macuci, shaidane mai karyar arziki, Allah kadai ya san abun da ya kullawa yarinyar ya yaudare, ita kuma ta fi kyau da kudi ta cutar da kanka, waya sani ma ko ciki yayi mata, dan iska dan kasan wuta... Da wani shegen hanci na shi kamar tattasai, kai kamar ganwon albasa’

Tana tafiya tana zaginsa a ranta, tana ayyana da ace ita ya cuta sai ta karya masa kafa ya zama gurgu.

“Ameer mu tafi yanzu”

“Okay amman akwai wanda nake jiran ya kawo min sako zan dan jira shi minti kadan”

Sai a lokacin ta fara jin ta tsargu sboda babu mayafi a jikinta kuma babu talkami. A da idan zata shigo gurin sai ta saka mask da glass saboda kar wanda ya santa ya ganeta. Dan karamin veil Humairah ta kawo mata tare da gorar ruwa mai sanyi.

“Karbi wannan ki rufe kanki”

Ta kalli Humaira sannan ta mika hannu ta karba, ta lulluba, Humaira ta mika mata gorar ruwa.

“Ba zan iya sha ba, bakina ciwo yake”

Ta nuna mata bakinta dake kumbure.

“Wayyo sannu Allah ya isar miki”

Ameer ya kalli Humaira da sauri ganin tana zakalkalewa.

“Ga wa?”

“Ga wanda ya cuceta mana, daman mace rauni ne da ita wasu mazan suna amfani da haka su cutar da ita, kuma idan mutum ya san be yi cuta ba miye ruwansa da Allah ya isa”

Wata uwar harara Ameer ya watsa mata, ba dan yana a yanayin da baya son biye mata ba, da sai ya gaura mata mari a gurin ko ta shiga hankalinta, domin ya kura bata tsoronsa sam kuma bata kunyar fada masa magana, sai dai baya a cikin yanayin da zai biye mata su siyar da hali a gurin, dan haka ya dauke idonsa yana kai zuciyarsa nesa ya tattara hankalinsa ya maida gurin Nimra. Ganin hakan ya saka Humaira ta juya rike da gorar ruwanta ta koma a iyakar gaskiyarta take neman Allah y isarwa yarinyar da zuciyarta ke raya mata Ameer cutar da ita yayi, ko da yake ta ďayan bangaren tana ganin kamar har da laifinta taya za'ace duk wakar nan da take mata idan suka zo gurin bata dauki haske ta gane Ameer yaudararta zai yi ba, saboda yawan taba ta yake ta kyale shi yana shiga jikinta gashi yanzu har ta kai yayi mata duka kuma ya dauko sun ta zo gurin babu ko mayafi a jikinta babu talkami.

Ameer na ganin kiran number da ya kira ta Ummi dazun ya fahimci sun iso gurin, sai ya yanke kiran ya aika mata da sako daidai inda zata tsaya ta jira shi. Sannan ya kalleta ya ce.

“Tashi mu tafi”

Gudun kar ya rikata su fita tare mahaifiyarta ta gani ranta ya bace sai ya nemi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login