Showing 246001 words to 249000 words out of 281271 words

Chapter 83 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1199

tafiyarsa har ya shiga cikin falon, sai da ya zauna sannan ya gaishesu. Hajiya da kanwar mahaifinsa suka amsa suna karantar yanayinsa da ya canja.

“Allah yasa ba Ummi ce ta bato maka rai ba kuma Ameer”

Ya dago ya kalli Hajiya cikin yanayin damuwa.

“Hajiya idan kina son na so ki kuma na kaunace ki na girmamaki ki daina maganar Ummi marar dadi a gabana, duk wani abun da ta yi min ko zata yi min ita din uwata ce babu wanda ya isa ya canja wannan, kuma wannan damuwar tawa ba akanta ba ne akanta ba ne akan yarinyar da nake so ne”

Humairah ta zauna tana kallonsa.

“Wani abun ya same ta?”

“Ina fatar dai tana cikin aminci, domin Maleek ya bita sun shiga garin kuma police din sun ce mutanen sun fara dauka da zafi tun kamin su shiga da ita ma, ina ta kiran wayarsa kiran be shiga ba Abiey ma ya kira wayar bata shiga, and jiki na bani wani iri like kamar ba kalau ba akwai dai abun da yake faruwa”

“Da alama dai kana son yarinyar sosai Ameer”

Ameer ya kalli Bahijja ya daga mata kai yana kiranta da sunan da Humairah take kiranta.

“Sosai Mama ina son fiye da tunanin duk wani mai tunani”

“Allah ya zaba maka abun da ya fi zama alheri”

“Ameen thank you”

Ya kalli Humairah

“Ina list din?”

“Ko mu bari sai next time na ga kamar baka cikin yanayi mai dadi”

Sai ya mike tsaye ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi mai kauri ya duka gaban Hajiya ya aje mata.

“Ga wannan ko da zaku yi hidimar gida, zamu je da Humairah mu siyo wasu abubuwa sauran kuma ina tunanin sai dai na bada kudi a siyo dabam”

Hajiya ta mika hannu ta dauki kudin tana dubawa, farincikin ganin kudin ya kawar da damuwar maganar da ya fada mata akan Ummi a take ta washe da kau har ta fara hade fuska, ganin kamar baya son ana ganin laifin Ummi bayan kuma ita din a gurinsu babbar mai laifi ce.

“Ameer wannan duk hidimar gida? Maa Shaa Allah, Allah dai ya saka maka da alheri, ina ma ace mahaifinka yana raye ya ga wannan hidimar ace dansa ne yayi, Allah dai yayi masa rahma”

Ta karasa tana fashewa da kuka domin har ga Allah tana jin kewar danta, abubuwa da yawa tana yawan fata ina ma yana raye yayi mata, yau gashi kuma daga jininsa anyi mata amman bashi a raye balle ya gani. Maganar mahaifinsa da ta yi da kuma kukan ya saka Ameer kara shiga damuwa, sai ya ji abun ya ninka masa. Ajiyar zuciya kawai ya sauke ya fice daga falon. A mota Humairah ta same shi bayan ta saka hijabinta ta dauko takardar da suka yi list din. Be ce mata komai ba ya fara tuka motar, ita ma bata ce masa komai ba, kuma ta yi iya kokarinta ta dauke idonta daga gareshi har suka isa super market din. Ya faka ya ciro wayarsa yana gwada dialing number Maleek yana fadin

“Me zamu fara siya?”

A lokacin da ya kira wayar Maleek kiran ya shiga sai ya ji wani irin sanyi a ransa, har wani gyara zama yake yana kallon Humaira murmushi na bayyana a fuskarsa.

“Wayar Maleek ta shiga”

“Allah yasa ya daga”

Humairah ta masa addu'ar tana masa fatan samun jin muryar Waira domin bata son ganin damuwa a tare da shi, hakan ya saka take masa fatan samun Waira a yanzu domin ta gama fahimta yana sonta sosai. Rashin amsa kiran da Maleek yayi ya sake daga masa hankali hakan ya saka yayi ta kiran wayar ba adadi har da fita motar yayi yana yawo kamar wani tababben, a yanzu hankalinsa ya fi tashi fiye da farko da be san halin da take ciki. Da sauri ya dawo cikin motar yaja motar da sauri kai kace shi kadai ne a hanya haka ya rika tuki ba tare da ya fadawa Humairah inda za su je ba, ita ma tsoron yadda yake tukin ya hanata tambaya domin tuki yake bana arziki ba. Sai da ta ga sun fara ratso unguwarsu Ummi sannan hankalinta ya kwanta.

“Gurin Ummi zamu tafi?”

Ya kalleta a firgice domin ya manta ma tana cikin motar.

“Oh my God kina nan still”

Bata sake cewa komai ba har ya faka harabar gidan, yana bude mota ya fito Mahmood ma ya bude tasa ya fito.

“Ina Abiey?”

“Yana falom Ummi”

Mahmood ya amsa masa yana kallon Humairah da ta fito a front seat din. Ameer ya nufi kofar falon Ummi da gudunsa, Humairah ta rufa masa baya tana tafiya a hankali ganin Mahmood na kallonta ya saka ta gabata masa da kanta.

“I'm Humairah ni Cousin dinsa ce ta bangaren mahaifinsa”

“Oh... Oh.. O... Nice Sannu Humairah”

Ya fada yana jin kamar ya santa, ita da shi a tare suka shiga falon, sai suka samu Ameer a zaune yana kallon Ummi dake kuka. Ameer ma be san dalilin kukanta ba and he don't want to ask shiyasa ya samu guri ya zauna kamar yan'uwansa Namra da Mahmood sai kuma Abiey dake zaune kujera daya da ita.

“I'm sure Maleek yana lafiya Ummi dan Allah ki kwantar da hankalinki”

Namra na fadar haka ya fahimci saboda Maleek ne hankalin Ummi ya tashi. Abiey ya ce.

“Na yi magana da police din yau za su kuma sun tabbatar min ba za su dawo ba sai da ďana”

“Na kira shi yanzu wayar ta shiga yana ringing amman be daga ba”

Ameer na fada hakan Abiey ya dauko wayarsa da sauri ya gwada kiran Maleek and suka yi sa'a yayi picking sai Abiey ya saka a speaker saboda hankalin Ummi ya kwanta. Kamar wanda aka daga sama aka buga da kasa aka mikar tsaye haka Ameer ya ji bayan ya gama sauraren wayar Maleek da Abiey, kasa cewa komai yayi ya mike tsaye yana hade wani abu mai daci a makoshinsa ya nufi kofar fita, duk binsa suka yi da kallo har ya fice. Ummi ta share hawayenta ta kalli Abiey ta ce.

“Me yasa Maleek zai fadi magana irin wannan a gaban Ameer?”

“Be fada dan ya san Ameer yana nan ba, please don't blame him bari dai ya zo mu ji whole story”

Abiey ya fada a kokarinsa na kare dansa. Humairah ta mike tsaye

“Bari na duba shi”

Ta fice daga falon daman jin take kamar tana kan kaya, tana fita ta ga babu Ameer babu alamarsa. Sai ta juyo ya dawo cikin falon ta tsaya daga bakin kofa

“ban ganshi ba ina ganin ya tafi”

“Zo ki zauna zan kira shi ya zo ya dauke ki”

Ba musu ta dawo ta zauna kamar yadda Ummi ta bukata, Ummi ta dauki wayarta ta yi ta kiran wayar Ameer be daga ba.

“Maybe yayi fushi, ki jira zuwa anjima na san zai dawo ko dan ya duba Nuwaira”

Bata son musawa Ummi haka ya saka ta amsa ta toh. Ta zauna a falon ta maida hankalinta gurin tv dake kunne Namra kuma ta tashi ta rika Ummi suka nufi Upstairs Abiey ma ya fice daga falon zuwa bangarensa aka barta ita kadai sai Mahmood dake zaune yana buga game da wayarsa.

“Kamar na sanki”

Yayi maganar kamar ba shi yayi ba, domin be kalleta ba kuma be fasa game din ba. Dan juyowa ta yi ta kalleshi

“Maybe”

Sai a lokacin ya kalleta daman shi be iya munafurci ko shan mur ba, he's straight forward yana da wayayya da kowa even if ace yau kuka fara haduwa, balle kuma ita da jikinsa ke bata ya taba ganinta ko saninta.

“A ina?”

“I don't know, ko Maybe restaurant na yi siyar da abinci a can before”

Ya sake dubanta da kyau from head to toe be ga ta yi masa kama da wadda ke siyar da abinci ba.

“Wasa kike min?”

Ta yi dariya.

“Baka yarda ba?”

“Babu wanda zai yarda ai”

“Haka mutane suke cewa idan na fada, ban san me yasa ba”

“Yanayinki be bada haka ba”

“Abun ba daga yanayi ba ne, amman ba zan maka karya a farkon ganinka da ni ba”

Ya dan tabe baki feeling comfortable with her.

“Ba zan iya shaidar baki ba”

“Ni ba bakuwa ba ce, na taba zuwa gidan nan sai ko idan ka manta ko kuma baka nan”

“Na miki kama da wanda kika taba gani? And when kika taba zuwa gidan nan don't lie”

Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba

“Da girma zan yi karya? Idan baka yarda ba ka tambayi Ummi, ita ta gayyatoni a gidan nan ma”

“How are you? Kin girma ki fadi karya ne? Karki cece ni da innocent face din nan, ni at first ma na dauka ko wata sabuwar budurwa Ameer ya kawo mana”

“Kai Ameer a yanzu ai be jin yaren kowa sai na Nuwaira, ni kuma yanzu I'm not ready na fada son wanda be shirya so na ba, ita kanta Nuwaira na fada masa ba zai same ta da sauki ba idan ma ya samu”

“Why? Ba ki masa fatan samunta kishi kike?”

“Why would I be jealous? No I'm not ni ba budurwarsa ba ce, just his cousin”

“Don't you have feelings for him?”

Wannan karon Mahmood har da kanne ido daya yake yana tambayarta sai ta yi murmushi ta girgiza kai.

“Da alama dai kai ne mararjin magana gida nan”

Ya mike tsaye yana murmushi.

“Na bar miki falon ma karki ce na cika ki da surutu”

Humairah dai ban da murmushi babu abun da take ta bishi da kallo har ya fice, sannan ta samu damar baza idonta a falon tana karewa komai na cikin falon kallo, tana jin motsin daukowar mutum ta yi saurin yin kasa da kanta.

“Sannu Humairah an barki babu ko ruwa, Wai shi nake sake kira ko zai daga”

Jin muryar Ummi ya saka ta dago ta dubeta Ummi da rama da ciwo ke kara bayyana a jikinta.

“Hello.. Ameer...”

“Ba Ameer ba ne, Ameer din yayi accident ga mu a hanyar zuwa asibiti yanzu”

“Ameer kuma?”

Ummi ta sauke wayar daga kunnenta ta duba line da ta kira sannan ta mayar da wayar.

“Ameer ko dai Maleek?”

“Toh ban san sunan shi ba mai wannan wayar dai, ya samu hatsari jaction din Hird da ake bada hannu”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Ameer yayi hatsari, Innalillahi Ameer”

Humairah da tun da Ummi take wayar hankalinta ya tashi ta nufo Ummi da sauri ta rike ta, sai kuma ta sake ta ta nufi kofar fita falon da sauri ko zata samu ganin Mahmood da ya fita ba jimawa. Bata ganshi ba ta dawo da sauri a daidai lokacin ne Namra ta sauko kamakon kukan da Ummi take tana tambayar me yake faruwa.

“Ameer yayi accident kar ďana ya mutu please janyo mota ki kai ni gurinsa yi sauri Namra, ďa”

“Waya fada miki wannan maganar Ummi kina cikin wannan hali?”

Ta rika Ummi tana kallon Humairah dake girgiza kai alamar ba ita ba ce.

“Ita ta kira waya sai aka dauka aka fada mata”

Namra ta saki Ummi ta nufi bangaren Abiey da gudu. Duk yadda Abiey ya so Ummi ta zauna a gida, shi da Mahmood su tafi asibiti bata yarda ba, ganin take kamar ma ya mutu ne gaba daya, ko kuma zai mutu idan bata kusa da shi. Abiey ya karbi wayarta ya sake kiran number Ameer din police din da suka yi jagorancin kai shi asibiti suka amsa wayar suka fada masa asibitin da suke. Ummi gaba daya hankalinta a tashe yake son kawai take ta ga Ameer a dole tare da ita suka je asibitin. Ko da suka isa asbitin har likitoci na masa dressing guraren da ya samu rauni, kirjinsa sai kafarsa sai kuma gefen kafadarsa. Sai dai ba abar Ummi ta ganshi ba sai da aka gama masa komai aka ware masa dakinsa sannan Ummi ta shiga tare da Namra da Humairah Mahmood da Abiey. Tana ganinsa ta isa gurinsa da sauri ta kama hannunsa ta rike tana ta kuka.

“Haba Ameer miye haka? Police sun fada mana gudu kake yi sosai ana daga maka hannu ka tsaya amman baka yi ba har ka bugu wasu motocin? So kake ka kashe kanka? Saboda me Ameer”

Cikin wani yanayi na rashin lafiya da azababen ciwon kai Ameer ya kalli Ummi yana murmushin karfin hali ya ce.

“Ba haka ba ne, jikina ne yayi nauyi burki kuma ya cige”

“Gudu yake sosai ni ma dazun har tsoro ya ba ni, baya duba kowa idan hankalinsa ko ransa ya bace”

Humairah ta fada tana share hawayenta ganin babu ko riga a jikinsa sai bandeji. Abiey ya ce.

“Rayuwa guda ce dai, kuma yanzu girma kake yi ya kamata ka rage wasu abubuwan ko dan mahaifiyarka da ka ga yadda ta tashi hankalinta a yanzu nan muma yadda hankalinmu ya tashi da baka aikata haka ba, Alhaji Bashir ma yanzu na kira na fada masa da sauki amman hankalinsa duk ya tashi, kana da mutane masu son rayuwarka ya kamata ka tausaya musu ka kula da kanka”

“Zan kiyaye gaba Abiey i promise”

Ya fada sannan ya kalli mahaifiyarsa da har lokacin hawaye take yayi murmushi.

“Ummi I'm fine kin gani, dan Allah ki daina kuka”

“Ka yi alkawari ba zaka sake irin wannan abun ba? Idan ma kashe kanka kake son yi ka bari sai na mutu, amman a yanzu babu abun da nake bukata sai rayuwarka”

“Hakan ba zai sake faruwa ba Ummi na miki alkawari”

Namra ta masa hannu ya amsa Mahmood ma yayi masa kamin ya amsa Mr Bashir ya shigo dakin hankali tashe baya ganin kowa sai Ameer Mommy tana bayansa ita kan sai hawaye take kasancewarta mace bata iya rike kuka ko damuwa. Abiey na gama fadawa Mr Bashir abun da police din suka fada masa ya zabura ya rufe Ameer da fada kamar zai doke shi har sai da Ummi ta shiga tsakiya ta tare Ameer.

“Ni ma na masa fada, ai that's enough”

“No it's not enough duk wani iskanci da yake ina jurewa ina dauka amman ban da wasa da rayuwa, idan kuma ka ce haka zaka yi to sai mu saka kafar wando daya da shi”

“Daddy I'm sorry it wasn't intentionally”

“Na dai fada maka”

Daddy ya fice a fusace, Abiey ma fita yayi domin ya san Ummi ba zata yarda ta bishi su tafi gida a yanzu ba. After like 5 minutes Doctor ya shigo ya bukaci kowa ya fita a bar Ameer shi kadai ya huta suka saka masa drip tare da magani sannan suka fice within seconds bachi yayi gaba da shi.
[8/12, 8:57 PM] 🦋-🦋: 78

Skylines Hospital aka kwantar da ita shi da abokin aikinsa Dr George suka dubata duk wani abun da ya kamata ayi mata suka mata sannan ya fito daga asibitin ya nufo gida. Yana fakawa harabar gidan ya ji wata mahaukaciyar yunwa ta sako shi gaba, kusan haka ya wuni kamar mai azumi sai da ya shigo falon Ummi ya nufi kitchen dinta ruwan zafi ya fara zubawa ya sirka da na sanyi zafin ya ragu ya dauka ya sha be ko iya jira ya hada tea ba.

“Waye a kitchen?”

Namra ta fada a lokacin da take saukowa stairs domin ga ga wulgawar mutum amman bata tantance ko waye ba, kai tsaye ta nufi kitchen din ta leka sai ta yi arba da Maleek with surprised ta ce.

“You...? Yanzu ka shigo?”

Ya daga mata kai kawai ya dauki plate ya fito daga kitchen din ya aje plate din a dinning.

“Zuba min abinci kamin na sauko”

Ya nufi upstairs, dakinsa ya shiga ya tsabtacen jikinsa ya canja tufafi ya fito ba tare da ya shafa komai a jikinsa ba, domin yunwar cikinsa ta kusan firgitashi. Spoon ya dauka da sauri ya fara cin abincin hannu baka hannu kwarya.

“Baka ci abinci ba since?”

“Gaba daya yau banci komai ba, sai yanzu ma nake jin yunwar Ina Ummi?”

“Tana asibiti?”

Ya kalleta da sauri.

“Nonono ba ciwonta ba ne, Ameer ne?”

Har yanzu ma kallonta Maleek yake domin jin ba'asin. Namra bata yi kasa a guiwa ba ta karanta masa komai a take ya tsayar da cin abinci yana yawo da idonsa a falon.

“Abiey fa?”

“Yana cikin gida, ina ita Nuwaira?”

“Tana asibiti bata da lafiya, shiyasa na fara aje ta can”

Ya zuba ruwa ya sha ya tashi ta dauki wani cup din ya hada tea ya dauki cup din ya nufi bangaren Abiey rike da cup din tea. Abiey na yi arba da dansa farinciki ya lullube shi ganin dansa lafiya kalau babu rauni a tare da shi sai gajiya da yunwar da ya kwaso har ta saukar masa da rama na wuni daya. Maleek ya zauna cikin jindadin abubuwan da suka faru ya fadawa Abiey komai, take dadi ya lullube Abiey jin yadda dansa ya zama Jarumi cikin birnin matsafa ya rinjayesu da karfin ayar Allah da tsaronsa, kamar wanda ya samu tv haka Abiey ya rika kallon Maleek yana alfahari da shi. After ya gama bashi labarin ya dauko maganar Ameer Abiey ya girgiza kai.

“Namra ta fada maka ko? Umminku ma tana can asibiti ance bachi yake amman tace ba zata dawo ba sai ya farka”

“Daman na yi tunanin haka, shiyasa da yayi ta kirana na ki na daga, saboda ba zan iya masa karya ba, kuma na san gaskiyar zata yi effecting dinsa, and i san Ameer irin mutanen nan da idan rai ya bace basa iya controlling kansu, and zai iya facing komai ba”

“Na dai fada masa, ya kamata ya kiyaye ko dan mahaifiyarsa”

“Yes”

Maleek ya amsa sannan ya mike tsaye ya aje cup din.

“Bari na leka asibitin daga sai an fada mata halin da Nuwaira take ciki, saboda a samu wanda zai kwana a tare da ita asibitin”

“Okay ka cigaba da rike addu'a fiye da da Maleek”

“Dole ai Abiey, ni na ga tasirin addu'a a zahirinta kuma hakan ya kara min kwarin guiwar rike ta da hannu biyu”

“Good Allah ya kara tsarewa, bana shakkar ka shiga ko'ina Maleek I'm proud of you”

“Thank you”

“Idan ta farka Cp yace min za su dauki statement dinka da nata saboda gaba, kuma tsarin haka yake dole san komai ya faru”

Daf da zai fice Abiey ya fada masa haka, sai ya amsa da.

“Okay”

Sai da ya sake komawa bangaren Ummi ya shiga dakinsa ya dauko keys da waya sannan ya dauko ya fice daga falon. Wata motar ya dauka ta dabam ba wadda ya dawo da ita ba, sai da yayi warming

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login