Showing 69001 words to 72000 words out of 281271 words

Chapter 24 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1227

question mark, kallo kawai take bata fahimci komai ba, tana ta kallon zanen bata gane me ake nufi ba, kamin ta juya gurin biron tana kallo bata taba ganin pen ba, domin a garinsu da feather suke rubutu, da ink na tawada ba irin wannan na zamani ba, pen din ta kai baki ta tauna ta ji ko zai karye sai ta ji shi da lauďi. Jefarwa ta yi ta sake lekawa sai ta yi arba da fuskar Mahmood, da sauri ta dawo bayan kujera da take boye gaabanta na bugawa da karfi. Tasowa yayi ya taka zuwa inda take yana kallonta da murmushi a fuskarsa saboda ya kwantar mata da hankali ta yardar ba cutar da ita zai yi ba ta, hakan be hanata rufe idonta jikinta ya fara rawa zaunawa yayi gabanta ya aje littafin ya dauki pen din da ya jefar ya zana mutum hudu ta, sannan ya saka hannunsa ya bude mata idon sai ta fara kokawar tashi gurin.

“Ke ba wani abun zan miki ba”

Ina bata saurara ba, har sai da ta ji ya sake ta sai ta kara matsawa can baya.

“Akwai matsala kenan kamin ki saba da mutane akwai aiki babba, wannan irin tsoro fa boya da kike yaushe za a gane yan'uwanki”

Ummi wacce fitowarta daga Kitchen kenan ta amsa masa.

“Ina tunanin wani mai fasahar magana zamu samu ko zai iya gane kanta yayi mata magaan ko da kurmancin ne, mu ga ko zai iya, idan hakan ya gagara we have no other choice but to put in school ta koyi hausa ko turanci ko kuma a daiko mai mata lesson nan gida ya koya mata, ta fahimci hausarmu ko kadan ne sai mu san yadda zamu iya gane iyayenta”

“Ko kuma a saka cigiyar iyayenta a can inda aka dauko ba”

“Eh kuma ka kawo shawara mai kyau zan yi ma Abieynku magana maybe hakan ya taimaka”

Jin muryar Ummi ya saka ta bude ido ta kalli gefen da take jin muryar Ummi ta tai yi arba da ita a tsaye tana kallonta, tashi ta yi ta koma kusa da Ummi ta tsaya ta juyo tana kallon Mahmood, littafin dazun ya dauko ya dawo kusa da su ya tsaya ya nuna zanen dake cikin hotom ya fadi sunansa.

“Mahmood”

Ya sake nuna kansa ya ce.

“Mahmood”

Ya nuna dayan zanen ya furta Ummi ya nuna Ummi ya furta Ummi, yayi haka ya fi a kirga sannan ya nuna dayan zanen ya nunata sai ta ce.

“Waira....”

Daga shi har Ummi kallonta suka yi da mamaki, jin ya yi magana.

“Sunanta ne ko kuma wani abun take nuna”

Ummi ta tambaya, Mahmood ya amsa mata shi ma yana mamaki.

“Ina tunanin sunanta ne”

Kamar ta san abun da suke tambaya sai ta kawar musu da zarginsu ta nuna takardar.

“Mamu...”

Ta nuna Mahmood

“Mamu”

Ta nuna dayan zanen.

“Oni”

Ya nuna Ummi ta furta.

“Oni”

A take farinciki ya cika kalbin Ummi tana ganin kamar hakan zai taimaka musu fahimce ta.

“Waira”

Ummi ta maimaita sunan tana jinsa wani banbaragwai, a take ta daga ma Ummi kai ta sake nuna kanta ta furta sunan. Suna haka Nimra ta sauko.

“Lafiya kike tsaye a nan?”

“Wata hikima ce Mahmood yayi har ta kai ga yarinyar nan ta furta sunanta”

“Sunanta kuma?”

“Eh wai Waira”

“Waira”

Ita ta maimaita sunan duk da kasancewar ba shi ne a gabanta yanzu ba, damuwarta yana gurin abin da ta kwama da shi a ranta wato sarewar Ameer yadda zata yi ta fito da sarewar a motar ne ya fi komai tsaya mata a rai tana matukar jin son kyautatawa Ameer fiye da kowa a yanzu. Ummi ta juya zata koma kitchen sai Waira ta fara kokarin binta tana daga kai ta kara kallon gurin.

“Idan kika rike ni ba zan yi saurin gama aikin nan ba, so nake da zarar na gama aikin sai mu tafi asibitin tare likita ya duba ki idan ma kwantarwa ya kamata sai mu ji”

“Daga can Ummi ke ma zaki kai kanki”

Mahmood ya fada yana mata kallon da ita kadai zata fahimci yarensa, domin ita ta san salon karon halshensa.

“Eh”

“Baki da lafiya ne Ummi?”

Nimra ta bukata tana dubanta.

“Lafiyata kalau kai ne kawai yake dan ciwo”

“Sosai?”

“Aa da sauki wata kila damuwa ce na san ina ganin likita zai warware”

“Okay Allah ya kawo sauki bari na rika miki ita”

Kamar wata yar yaye haka Waira ta zama sai da dabara da wayo sannan Nimra ta sami rabata da jikin Ummi ta dawo da ita jikinta ta rumgumeta kamar yadda Ummi take mata, da murmushi Ummi ta bar gurin ta nufi Kitchen. Mahmood kuma ya nufi kofar falom dake kara ya budewa Hanne ta shigo tana gaishe shi.

“Mahmood why not a duba motar ko za a samu wata shaidar da zata taimaka a gano inda yarinyar take?”

Mahmood ya juyo yana kallonta ta kawo magana mai kyau, sai dai baya tunanin police din ba su duba ba, wata kila da sun samu wani abin tun kamin a kawo ta nan.

“Ina tunanin police sun bincike motar da akwai wani abu da sun garamu gani, Allah kadai ya san duniyar da wannan yarinyar ta fito kuma ya akai ta shiga motar shi ma Allah kadai ya sani”

Bata son zafafawa kar a gano manufarta hakan ya saka ta yi shiru, Mahmood ya koma dakinsa ita kuma ta zauna da Waira a falon har Ummi ta gama shirya komai. Ta dauki na mijina ta nufi bangarensa da shi, Nimra kuma ta saka Hanne ta zuba mata nata ita da Waira ko kadan bata kawowa ranta cewar Waira ba zata iya cin kalar abincin da suke ci, kamin Hanne ta kawo abincin Namra ta sauko da shirinta na office domin bata wasa da zuwa office a ko wace rana, ba kamar Nimra ba da bata damu da neman aiki ba. Wayar salula ce makalle a kunneta tana dan murmushi kadan domin mace ce mai kasaita kusan ita kadai ce jinin sarautar da suka gada daga gurin mahaifinsu yake ratsa jininta har yanzu tafiyarta ma da kasaita take Namra mace ce mai matukar ji da kai. Jakarta ta fara ajewa a kan cushion sannan ta zaune wayar tana zaunawa.

“Don't d tell me ke ma irin na Ummi kike mata? Kuna rumgumar yarinyar da bakusan inda ta fito ba, ke kina ganin yanayin yarinyar nan kin san hankali be wadace ta”

Namra ta yi murmushin da ya fi kama da dariya.

“Aljana ce, kika mata iskanci sai ta makure ki da dare”

“Sai dai ke da kika dauko ta, ko kuma kika yi dalilin zuwanta a gidan nan”

Ta yatsina fuska ta tashi ta nufin dinning table, da kanta ta shiga hada ma kanta abubuwan da take son karyawa da su even though ba komai da komai da suka saba karyawa da shi Ummi da dafa tare da Hanne ba. Farfesun kayan cikin da plate din dankali da ruwan zafi sai kayan hada tea, sannan ta koma ta dauko bread for Waira domin Nimra bata damu da shan tea tare da bread ba, ta fi son ta zuna dankali enough ta saka masa miyar farfesu ta ci ta koshi ta dora da tea sama, sauran kam basa haka sai dai kowa ya ci farfesun da dabam wani lokacin ma basa ra'ayin cin komai sai kayan kwalama.

“Hanne akwai cake a bridge please ki dumama, ko zata iya ci”

“Toh ranki ya dade”

Ta koma kitchen ta dauki cake din kamar yadda Nimra ta bukata ta saka a oven. Nimra ta zaunar da Waira kasa ta matsa dayan gefen ta zauna ta fara hada tea Waira nata kallon yadda take zuba wani abun cikin wani tana juyawa kamin a gama kamshi mai dadi ya cika mata hanci, daman yawunta ya dade da tsinkewa ganin farfesun dake wani kamshi na dabam ba kamar na su ba. Sai da Nimra ta gama hada tea tsab tana kokarin karbar cake din da Hanne ke mika mata Maleek ya soma saukowa without making any sound daman baka jin saukarsa ko hawansa idan yana tafiya, yana sanye da material ash colar wanda yayi matukar yi masa kyau ya haska fatarsa da bakin gashin kansa sai dai rama ta samu muhalli a fuskarta kadan hakan kuma ya karawa goshinsa haske, kamar ance daga kai ki kalli stairs haka Waira ta yi tana ganin Maleek ne sai ta mike tsaye da sauri kafarta ta kifar da tea da da Nimra ta hada, ta taka bread din da Nimra ta aje mata a gabanta bata ko tsaya gurin Nimra ba sai ta nufi dinning ta kwanta kasa taja kafafuwanta ta shiga da jikinta karkashi ta boya. Maleek kam tsaye yayi yana kallonta ya san tsoronsa take kuma ya cancanci ta tsorata idan ta ganshi saboda marin da yayi mata ba kadan ba ne, shi kansa ya ji ba dadi a dazun da ta ganshi ta yi ihu yanzu kuma ta nemi gurin boya, be dace ya mareta ba from first place sai dai idonsa ya rufe a lokacin baya iya gane hakan sai a yanzu da ya aikata. Nimra ma kallonta take bayan ta mike tsaye domin kadan ya rage tea ya bata mata tufafi.

“Ikon Allah ke kuma haka kike?”

Namra ta fada tana leka karkashin table din da mamaki. Juyawa Maleek yayi ya koma dakinsa, daman ba a falon zai karya ba, idan be yi breakfast a bangaren mahaifinsa ba to ya kan sauko ya debi abun da zai iya ci ya koma sama ta karya ko kuma Ummi ta kai masa da kanta, domin baya cin abincin tare da yan'uwansa mata, kamar yadda baya zama a falon idan suna nan.

“Ya wuce fito Hajiya”

Namra ta fada tana mikewa tsaye ta dawo kan cushion da tea dinta tana sha. Nimra ta nufo table din ta leka karkashi sai ta hangota tana ta kuka jikinta na rawa. Hannu ta miko mata sai ta kama hannun hakan ya bata damar janyota a hankali har ta fito. Ta koma da ita gurin da suka zauna dazun daman tuni Hanne ta gyara gurin, dankali Nimra ta fara dauka ta mika mata, sai ta karba ta kai bakinta tana taunawa a hankali shi kam ba laifi zata iya cinsa duk kuwa da kasancewar ba wani dadinsa ta ji ba sai dai abu ne da aka soya da mai da sai gishi kuma ta saba cin gishiri a garinsu. Karamin plate Nimra ta cika mata da dankali ta aje mata gabanta, sannan ta dauki karamin bowl ta zuba mata fesfesun kayan cikin ta saka mata spoon ta aje mata. Waira na ganin mai nama sai ta aje dankalin hannunta ta dauki bowl din wani abun kallo ne a gareta domin a garinsu da akushi suke cin abincin sai kuma abun da aka yi da wood itace kenan, tabawa ta yi ta murza sai ta ji shi da sulbi, ta mika hannu ta taba plate din da aka zuba mata dankali shi ma ta jishi kamar wannan, ta daga spoon din da Nimra ta saka mata sama tana kallo ta matsa shi ta murza tana ta mamakin yadda ake iya cin abinci da shi gashi har wani haske yake kamar zinari.

“Yau ta fara ganin plate ne?”

Tambayar Namra.

“I don't think so, jiya ba Ummi ta bata fruit a plate ba, sai dai wata kila bata samu natsuwar tsayawa ta kula da plate din ba sai yau”

Dukansu kallonta suke, har ta cire spoon din ta aje kasa ta saka hannunta tana dauko kayan cikin a hankali ta kai bakinta ta fara taunawa, ďanďannon farin maggi da kuma species da seasoning bata taba cin irinsa ba, wannan ya saka yana sauko a kanta ya kaiwa kwakwalwarta sako, sai ta ji kanta ya dauki wani ziza tana hadewa ya shiga cikinta sai hanjinta suka bata no a matsayin amsa domin sun ji bakon abun da ba za su iya dauka ba, a take ta dawo da naman ba shi kadai ya zo ba har da fruit din da ta ci da safe sai da ta amayar da shi tas a gurin. Namra ta jefar da cup din tea ta ita ma ta fara amai domin kazantar wani tana daga ta wani ne da zuciyarsa bata da nisan tashin.




©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: *W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*

24

“Fita da ita waje please mun shiga uku, Nimra kin janyo mana fitina”

Cewar Namra tana fashewa da kuka domin rabonta ta ganin kazanta irin wannan ta amai har ta manta, and the most annoying thing is tana cin abinci Waira ta yi amai.

“Hanne ki fita da ita waje na ce, gaskiya ba zamu zauna da yarinyar nan gidan nan ba”

Ta fada a tsaye tana jin kamar ta fashe da kuka, Nimra kam kasa magana ta yi sai dai ta ji babu dadi kuma kazantar aman ya daga mata hankali. Hanne taja hannun Waira da sauri ta fitar da ita falon ta kaita can kusa da Garden ta tsayar rai a mace tana ta mata masifa domin ta san ita zata kwashi aman.

“Idan ba shegen kwadayi ba, kin ga abincin da ba irin na ku ba kuma sai kin ci, gashi nan yanzu kin janyo min aiki, Wallahi ba dan Hajiya ba da sai dai ki saka hannunki ki kwashe amanki da kanki mahaukaciyar yarinya kai”

Ta dangwari goshinta har sai dai Waira ta yi baya kamar zata fadi, ta ja tsaki ta juya ta koma tana jin kamar ta yi ma Waira duka. Waira ta saka haka hannunta ta share bakinta sannan ta duka ta zauna a gurin hawaye na sauko mata, gaba daya sai ta ji rayuwarta ta baya take marmari ta saba da can da acan ta yi amai sai dai Eid ya wanke mata baki ya zaunar da ita ba ya nuna mata kyama haka ba, ta kalli hannunta dake zugi ta fashe da kuka, can kuma ta mike tsaye ta nufi hanyar Garden din tana leken gurin da take ganin yayi mata yanayi da garinsu saboda itatuwan da suke gurin da shuke shuke, da sauri ta karasa tana jin kamar ace akwai wata hanya da za a bulle a gurin ta tsinci kanta a garinsu. Cikin Garden din ta shiga ta daga kanta sama tana kallon itatuwan sai gata tana murmushi da hawaye a lokaci daya, bayyana yadda ta yi marmarin hawan tsauni da icen bata lokaci ne, ta taka har gurin swimming pool tana kallon ruwan da aka tara a gurin sannan ta nufi gurin da tsuntsaye suke kebe tana kallonsu fuskarta fes kamar ba ita ce ke kuka dazun ba, dawowa ta yi gurin itacen ta kama dayan da hannun daya tana tunanin hawa saboda dayan ciwo yake mata, duk yadda zata yi ta hau icen sai ta kasa saboda hannu daya kawai take iya aiki da shi, a nan ta rumgume icen abarbar ta fashe da kuka ta taba kanta tana jin kamar ace beranta yana nan dake cire mata kewa, kamin ta sulale kasa ta zauna a hankali, ta cire ribbon din da kanwar Dr Shuraim Maimoon ta saka mata a kai gashinta ya watse ya sauko gaba daya a bayanta, sai ta kwatanta irin zagen da Mahmood yayi mata dazun ta zana mutane biyu, ta zana beranta da wani irin zane mai ban dariya ta zana zakara iya yadda ta ga ya iya, sannan ta nuna na farkon idonta na tara hawayen da suke daf da zubo mata

“Eid...”

Ta nuna na biyu.

“Sulen”

Ta nuna berata.

“Bulat”

Haka ta yi a gurin zanen zakaran shi ma ta fadi sunansa hawaye na sauko mata sosai su ne kadai mutanen da ta yi marmari domin su ne kadai take jin sanyinsu, ta taba zoben dake wuyanta ta rumgume kanta kuka sosai marar sauti. Duk abun da take Maleek na tsaye jikin Window dakinsa hannayensa zube a aljihu yana kallonta, kamin ya juyo ya fito daga dakin ya sauko downstairs gaba daya a daidai lokacin da Ummi ta shigo falon tare da Abiey domin Namra ta kai karar Waira gurin mahaifinta wai ba zata iya zama da ita gida daya tana musu ihu da kazanta ba.

“In that case sai a maida ta BQ ta zauna tare da Hanne”

Abiey ya fada domin yana goyon bayan abun da yayansa suke so. Ummi ta gigiza kai domin hukuncin be yi mata ba sam.

“Haba ya za'ayi yarinyar da muke son ta sake jiki mu fahimce ta ta fada mana danginta a maidata cikinsu zamu barta gurin Hanne ta zauna gashi ko lafiya bata da”

“Ummi ji ihun da take mana idan an kunna Plasma, ga kazanta kuma bata saba cin irin abincin mu ba, kuma Wallahi bata da hankali, ni dai gaskiya ba zan iya zama guri daya da ita ba”

Namra ta fada, ita dai yar'uwarta Nimra kanta a kasa yake domin bata son hada ido da Abiey musamman a yanzu da ya zama ita ce silar faruwar komai.

“Zan ta iya zama a dakinta, for now asibiti zan kai ta a duba lafiyarta”

“Har da kwakwalwarta a duba Ummi kar wata rana ta kashe mu muna bachi Wallahi, Nimra kin ja mana masifa Wallahi”

Abiey yayi saurin tarewa yarsa domin ya san tana cikin damuwar rashin magana da yake mata yanzu kuma suna son kara mata wani.

“Haka Allah ya kaddara stop blaming her”

Nimra ta dan dago a hankali ta kalli Abiey tana jin sanyi a ranta. Maleek dake rumgume da hannayensa yana kallonsu ya ce

“Tana Garden tana kuka”

Ummi ta kalleshi da sauri.

“Waya kaita waje?”

Ya daga mafadarsa alamar be sani ba, sannan ya karasa saukowa ya nufi hanyar da zata sada shi da bangaren mahaifinsa.

“Ni na ce Hanne ta kaita waje”

“Haba Namra”

“Madam idan yaranki basa son abu don't force them please, ba ina nufin a waulakanta yarinyar nan ba, no zai fi kyau a barta ta zauna a BQ saboda su samu sukuni”

“Dan Allah ka barta ta zauna a nan, ina son yarinyar jin ta nake kamar yata ina son na taimaki rayuwarta, tana cire min kewar abubuwa da yawa, ko ba komai ina bukatar wanda zai zauna da ni idan Namra ta fita yar'uwarta ta fita Mahmood ba shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login