Showing 159001 words to 162000 words out of 281271 words

Chapter 54 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1211

dare, sa safe ma ka zo, da kai aka kaita makabarta, kuma shi ne zuwanka na farko, wannan shi ne karo na farko da wata ta yi hatsari ka tsaya ka dauketa ka kaita asibiti kuma har ka sakata a motarka, kamin ka zo nan kaje gurin wanki mota, sai ka yi tunanin za su yi zargin ka kashe wani sai ka fasa bada wanki ka zo da motar a haka, kana son ka tambaye ya aka yi na zama haka ya aka yi na iya hausa, ka taba ganina a school bus a lokacin da baka gane ni ce ba, ni kuma ban ganka ba..... ”

Haka ta rika zayyano masa abubuwan da suka faru da bata sani ba, da kuma wadanda ya san be yi maganarsu da kowa ba sai kansa. Tana fara maganar ya juyo yana kallonta da tsananin mamaki har ta kai aya.

“Ya aka yi kika san haka?”

“Wannan shi ne sirrina da ban taba fadawa kowa ba, ina ganin rayuwar da ta faru, ta haka ne na gane Ummi tana dauke da cutar leukemia, ba tare da ta fadawa kowa ba, ta haka na gano yadda take ta boye soyayyarka a zuciyarta, na gano damuwarta na son rayuwa da kai ni na fadawa Iyalanta tana dauke da cutar da take stage 3”

“Duba kike yi?”

“Bana duba, al'adar garinmu kowa yana irin baiwarsa ta tsafi ne, sai dai ni tawa ta sha banban da saura, saboda ana jiran na kai wasu shekaru ne a ba ni sarauta ta sarauniyar matsafa da garin, sai kuma gashi na gudu saboda an zarge ni da kashe kashe wani, alhalin ban aikata ba?”

“Me yasa ba ayi amfani da tsafin an gano ba ke kika aikata ba?”

“Ban tsaya jiran a gano ba, na gudu saboda bana son sarautar kuma a dokar da aka saka min idan na gudu kashe ni za'ayi”

Hawaye ya sauko idonta.

“Ina iyayenki suke?”

“ba ni da iyaye, duka sun mutu, ni kadai nake rayuwa a cikin wani daki, tare da beraye da zakaru, ban san wani abu dadi bachi ba sai da na zo nan, ban wani ya kira da ya ba sai da Ummi ta kira ni, ban san gatan da dadin dake cikin wanka kullum ba sai a wannan duniyar, ban san saka wani tufafin a kullum ba sai a nan, tun ana yi min da karfi, har na fara yi da kaina saboda na saba, a yanzu ko wane dare sai na yi wanka na wanke baki nake kwantawa, tsabanin can da ban san wani abu tsabta ba, ni da iyayena suka mutu sun tafi sun bar ni a cikin wata kazamar rayuwa, ni ce bana son tsabta bana son wanka saboda ina ganin hakan shi ya fi min, kuma ni zan iya mutuwa a kowane lokaci saboda na san ba za su kyale mu ba, ni da Ummi duk mutuwa muke jira, ita tana son ta gyara komai kamin ta tafi, tana son ta rabe ka ka kyautata maka, ni kuma bana son komai sai dai na san bana son mutuwa”

Be san lokacin da ya rumgume ta ba, ya lumashe ido hawaye suka zubo masa.
[7/11, 1:27 PM] My S Line: 52


Sai ta fashe da kuka sosai.

“I can take you back, zan maida ke inda na dauko ki, zaki nuna min hanyar garinku, zamu tafi tare mu roki yafiyarsu”

“Ba zan gane hanya ba, sun bata da komai a kaina, wanda ba dan garin ba, ba zai shiga garin ba, ba za su yafe ba, ba za su saurari kowa ba, ba zaka iya ba”

“Zan iya Waira i will do this”

Ya sumbanci saman kanta.

“Ni dai ina son, kamin na mutu ka zauna lafiya da Ummi, ita tana sona sosai, ita ce ta zama min uwa, a gurinta na san abun da ƴa take ji idan uwarta tana raye, ta ba ni duk wani jindadi bata kyamata tun ina da kazanta, ina son ka yi rayuwa da ita lafiya, ina son na ga haka kamin na mutu ko kuma ita ta mutu, ina son farincikinta, Ameer ko wani dare na gani tana kuka saboda kai, tana kaunarka sosai tana son kasancewa da kai, kana da iyaye ai kai Ameer ba zaka taba sanin dadinsu ba har sai basu da rayuwa, na yi mamarin nawa, idan ina son ganinsu sai da na rumgume danginsu na ga hoton fuskarsu na ga rayuwarsu i miss them”

Ya dagota daga jikinsa ya sake hannunsa biyu ya share hawayenta.

“Ba zaki mutu ba, babu abun da zai same ki, na saka taimakonki a lokacin da ganki a daji, yanzu ba zan ki taimakonki ba”

Ta daga kanta tana kallonsa.

“I won't hurt anyone anymore, domin ban san ta inda zan fara neman gafara ba i regret what i did to Nimra i wash...”

“Then don't hurt your mother, karka dawo ita ma kana nadama a lokacin da bata nan, we're all making mistakes, kowa yana yin kuskure muna yin ba daidai ba to miyasa idan wasu sun yi ba daidai ba ba zamu yafe musu ba?”

Yayi murmushi yaja kumatunta.

“You're so brilliant”

Ta yi murmushi tana kallon cikin idonsa da blue eyes dinta.

“Zaka yafe mata?”

Yayi shiru.

“To zaka so ka zauna da mu?”

Wannan kam a take ya amsa mata.

“No no”

“Please bana son ka bar ni, ni bana da dangi a yanzu kai ku, mutumen da nake so rasa su nake, kuma ka ga ni ba dadewa zan yi ba idan na mutu sai ka tafiyarka”

“Wayo kike min Waira you're just building a room for Ummi”

“I'm building a room for all of us, ina son mu yi rayuwa a gida ďaya, kamar iyali daya a gidan nan Nimra ce kawai take so na sai Ummi da Mahmood, Ya Maleek baya so na, Abiey ma baya so na, na rasa Eid, da Sulem i don't want to lose you too”

“You wouldn't, idan kina so zaki iya magana da Ummi ki dawo gidanmu da zama”

“Me yasa kai ba zaka zauna a gidan Ummi ba? Why do you hate her”

“Saboda ba zan iya zama karkashin inuwa ďaya da Maleek ba, ba zan iya zama a gidan mahaifinsa ba”

Ta kama hannunsa.

“Please”

Ya rike hannun nata yana murzawa a hankali. Kamar daga sama suka ji muryar Maleek.

“Ke Waira”

Ta zabura ta juya da sauri tana kallon inda muryarsa ke fitowa, Ameer kam ko dago kai be yi ba balle ya kalleshi kuma ya ki ya saki hannunta duk kuwa da irin kokarin da take tana son kwace hannun. Ummi ta bude mota ta fito ta biyo bayan Maleek da ya nufo inda Ameer da Waira suke tsaye.

“Maleek Maleek bari na yi magana da shi”

Shi ne abun da take fada tana kokarin rikowa shi domin ta lura da yadda ransa yayi matukar baci.

“Daman na raya a zuciyata kai ka dauke ta, tun da muka je makarantar aka ce mana wani ya zo ya tafi da ita, na raya kai ne sai gashi ina duba details din abun kuma sai na ga kai din ne”

Ameer ya saki hannun Waira ya kalli Ameer fuska kamar bakin hadari.

“Me ye a abun kunya? Biyo yarinyar da ka tsana har makaranta da sunan daukarta, ko kuma tare abokinka a hanya kana fada masa maganar banza a lokacin da mahaifiyarka take kokarin hanaka?”

“Thank you ka ce Mahaifiyata ashe ka san bata cancanci zama uwar kazamin yaro irinka ba”

“Sai kuma gashi ta haife ni, ya ranka?”

“Fessss haihuwarka kawai ta yi bata amsa sunan mahaifiyarka ba”

Ummi ta dakawa Maleek tsawa.

“Maleek ina ganinka kamar mai hankali? How could you say those words to your own brother?”

Ameer yayi murmushi yana kalleta.

“Karki damu, Maleek be taba zama ďan'uwana ba and he wouldn't be, he is just a friend shi ma kuma a can da”

Ameer ya maida dubansa gurin Waira.

“Shiga mota na kai ki gida”

Ta girgiza kai da sauri hawaye na mata zuba, jikinta sai rawa yake ita dai daman can bata son ta ga ana tashin hankali balle kuma a yanzu da take ganin kamar saboda ita ne komai ya faru. Da ido Maleek yayi mata alama da ta wuce zuwa gurin motarsa. Ta fara takawa Ameer ya fisgota ya dawo da ita.

“You should know your limit kai ba ubanta ba ne da zaka rika juyata yadda kake so she's under no one control but me”

“Saboda kai ne ubanta kenan?”

“Saboda ni ne silar zuwanta nan”

Maleek yayi murmushi da ya fi kama da dariya.

“Yarinyar da ka ce baka sani ba? Yarinyar da ka bari a mota saboda kana tunanin ta mutu? Yarinyar da ka wulakanta? Ashe dai ka santa kenan Maleek what a shame”

“Okay that's enough, kuna kunyata kanku ne kawai a gaban idona, ku daina saka ta a cikin matsalarku you guys have no idea what she's going through”

Ummi ta kama hannun Waira dake ta kuka ta nufi motar da suka shigo da ita ta barsu a tsaye idan ma cinye junansu za su yi sun dade ba su yi ba. Ganin ran Ummi ya bace ya saka Maleek bin bayanta ya bar Ameer tsaye a gurin yana kallonsu. Ummi da Waira baya suka shiga shi kuma ya shiga gaba yaja motar suka kama hanya.

“I warned yarinyar nan, Ummi do you plan this?”

“Yanzu kuma ni ce bar zargi ka gama da da zaka dawo a gurin uwarsa?”

“Ummi ta ya aka yi ya san lokacin da suke tashi? How ma ya zan makarantarsu? Kuma ke kika ce kar school bus ta dawo da ita, secondly tun dazu nake cewa mu taho amman baki fito ba sai da kika tabbatar ya dauketa”

“Idan ma daukarta yayi me ye matsalarka? Shi ma yana da iko da ita kamar yadda kake da, babu ubanta a cikinku”

“Ba shi da iko da ita Ummi, be san cinta da shanta ba be san gurin bachinta da karantunta, be san damuwarta da kukanta ba, be san farincikinta ba dan haka ba shi da wata isa ko iko akanta, a gidanmu take Under my father control, ba zan taba bari yayi iko da ita ba he's late, yana son iko da ita ya barta a daji ta wahala har ta kusa mutuwa, no one ba zan ba shi wannan damar ba”

“Thank you”

Ummi ta fada masa, sai ya juyo ya kalleta.

“I'm sorry bana nufin bata miki rai, ki yafe min please”

Ummi bata ce masa komai ba ta maida hankalinsa gurin titi, hakan ya saka shi juyawa ya cigaba da tukin, suna hada ido da Waira ta madubi gaba ya dalla mata harara, sai ta yi hanzarin rufe idonta ta kife kai jikin Ummi. Ko da suka isa gidan Jabir na tsaye harabar gidan tare da Juwairiyyya, Dr Zainab kuma tana tsaye bakin entrance da alama magana suke. Maleek ya fara fita sannan ya budewa Ummi ta fito Waira ma ta fito ta kama hannun Ummi ta rike saboda tana ganin kamar Maleek dukanta zai yi.

“Ba ku tafi ba?”

Ummi ta tambaya. Dr Zainab ta kalleta tana fadin.

“Yanzu za su wuce, na ce masa da ma yayi cancelled flights din gobe mu tafi tare”

“Mommy ni fa yadda kika san ina kam kaya haka nake, kara dai na tafi kawai sai kun iso”

“Da Juwairiyyya za a tafi?”

Ummi ta tambaya. Juwairiyyya ta amsa matada kanta.

“Aa rakiya zan yi ni sai gobe zamu tafi”

Jabir ya kalli Waira dake tsaye kusa da Ummi tana kallonsu.

“Waira kawata babu sallama?”

Ta kalli Maleek dake tsaye ya saka hannayensa aljihu.

“Zan masa sallama”

Da kai yayi mata alama da tafi, sannan ta saki Ummi ta nufe shi da gudu ta rumgume. Maleek ya yamutsa fuska kamar wadda yayi arba da abun kazanta.

“Haka ake good bye ke kowa abokin rumgumarki ne what's wrong with you?”

“Bata iya banbance halal da haram it's not her fault”

Cewar Mahmood yana kokarin rufe kofar falon Ummi. Jabir yayi murmushi sannan ya dagota daga jikinsa.

“Me zan siyo miki idan zan dawo?”

“Wata kila ba zaka dawo ka tararda da ni ba”

“Me yasa kika saka tunanin a ranki Waira? Idan kuma an yafe miki fa?”

Ta yi shiru tana kallon kasa. Maleek ya sauke ajiyar zuciya a sirrance sannan ya ce

“Waira shiga ciki, Jabir muje na sauke ka”

Ta matsa baya tana masa waving sannan ta nufi kofar falon Ummi.

“Allah ya kiyaye Jabir”

Ummi ta fada sannan ta bi bayan Waira. Jabir ya amsa da Ameen sannan ya karaso gurin Maleek yana fadin.

“Please don't be so harsh to her, idan abun da take ikirari ya faru abun da kake mata zai yi ta damunta”

“Ku ne dai kuke ganin kamar ina matsa mata, amman ni na san ina daga mata kafa sosai”

Ya fada sannan ya bude motarsa ya shiga. Sai da
Maleek da Jabir suka bar gidan tare da Juwairiyyya da zata masa sallama sannan ya Dr ta koma ciki tare da Yesmin, Mahmood kuma ya shiga tasa motar ya fice.

Ummi ta raka Waira har dakinta ta dauko mata tawul din da zata daura tana tambayarta.

“Waira ta Ameer ya ci cake din da na hada miki”

“Eh ya ci”

“Da gaske?”

Waira ta daga mata kai tana murmushi kamar yadda Ummi ma take murmushi kamin Waira ta gusar da murmushin sakamakon amsar da ta bata.

“Amman da na ce ke kika yi sai ya zubar”

“Wata kila zai dauke ni lokaci kamin Ameer ya fuskanci abun da nake nufi ya yafe min, zan jira har lokacin da zai fahimci gaskiya, har zuwa lokacin da zuciyarsa zata bude ya fahimce ni, sai ban sani ba ko rayuwa zata ba ni aron lokaci”

Waira ta karbi tawul din ta daura.

“Ummi school bag dina da ragowar cake din yana can a motarsa mu kira shi mu ce ya kawo”

Ummi ta girgiza mata kai.

“Zamu bari sai gobe da safe sai mu kira, kin ga yanzu ransa a bace yake”

“Okay Ummi”

Ummi ta shafa fuskarta.

“Allah ya miki albarka”

“Ameen”




AMEER POV.

Binsu yayi da kallo sai da suka wuce sannan ya shiga motarsa ya mika hannu ya rufe motar, zuciyarsa na mugun tafasa, a yanzu ya fahimci abun da take fada cewar Maleek baya sonta, daman can ya san halin Maleek baya son mata ko yan'uwansa ne balle ita da ta fado daga sama. Ba ma abun da ya bata masa rai kamar gadarar da Maleek din yake nuna masa.

“Zan gyawa yaron nan zama, sai na bashi mamaki”

Ya juya ya kalli jakarta da cake dinta dake cikin motar, sai ya daki sitiyarin motar da karfi, yana jin haushin yadda take tsoron Maleek.

“Ni na jefaki a wannan halin, zan rabaki da gidan nan soon”

Ya fada daidai lokacin da ya faka motarsa a harabar asibitin Hikima domin hankalinsa ba zai kwanta ba idan be je ya duba tsohuwar da ya kade ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya mika hannunsa ya dauko jakar makarantar ya bude ya ciro littafanta yana dubawa, da textbook ya fara kamin ya duba notebook, ba laifi tana rubutu yadda xa a fahimta even though bata gwane sosai ba rubutun yan primary 4 take yi. Yana dubawa maganar da suka yi a dazun tana dawo masa, tausayinta ya cika masa zuciya. And she's right shi be rasa gata ba, kuma matar da take ikirarin ita mahaifiyarsa ce tana dakun zuwan ranar da zai karbi hakan, and he would ko dan abun da ta fada masa cewar Ummi tana dauke da cutar Leukemia, ba sosai ya san komai akan cutar ba, amman ya san cuta ce mai hatsari dake farautar rayuwar ďan adam. Ya aje mika hannuna ya dauko box din cake din da ta bari ya dauka ya bude, kallon shape din cake din yake yana, kamin ya fi karfin zuciyarsa ya kai hannu ya dauki spoon din dake gefe ya gutsiri cake din ya ci.

“Da hannu yafi dadi mu bama ci da spoon”

Maganar Waira ta fado, masa sai ya aje spoon din a muhallinsa ya zari tissue ya saka ya dauki cake din yana ci. Sai da ya ci kusan rabi sannan ya rufe mata saura ya saka mata a jakarta ya aje jakar gefe ya kwanta jikin kujerar yana sauke ajiyar zuciya, duk wata magana da Waira ta yi masa sai da ta dawo masa a lokacin, ta fada masa kusan abun da mahaifinsa Mr Bashir ya fada masa amman be fahimta ba sai a yanzu. Bude motar yayi ya fito nufi cikin asibitin, ya isa Emergency ya nufi dakin da aka ya barta sai ya tarar wasu ne ba ita ba. Nurses din dake gurin ya tambaya ta fada masa cewar an canja mata daki. Wani ta saka yayi masa jagora har dakin da aka maidata, Mutumen na nuna masa dakin ya juya yayi tafiyarsa. Ameer ya kalli room number din dakin sannan ya murda kofar ya shiga, first abun da ya fara arba da shi is Humairah tana tsaye gurin kan tsohuwar idonta yayi ja har ya kumbura, kana ganinta kasan ba kadan ta yi kuka ba. Tsayawa yayi yana kallonta da mamaki ita ma kallon mamaki take masa, Mamarta kuma ta mike tsaye tana kallonsa domin ta gane shi ne mai gidan yarta Humairah ta rike fuskarsa tun a ganin farko da ta yi masa, shi kam ba dan ganin Humairah ba da ba zai iya shaidar fuskokinsu ba daga ita uwar har kakar.

“Me kik.... Kakarki ce?”

Ta daga masa kai.

“Kai ka kadeta?”

“It wasn't intentionally, zan wuce ne ita kuma zata je karbo sadaka”

Ya karasa gurin gadon.

“Ya jikinta?”

“Da sauki amman har yanzu bata dawo hayyacinta ba”

“Ba zata dawo hayyacinta da wuri ba, tana bukatar lokaci”

“Ina wuni ranka ya dade”

Mahaifiyarta ta gaishe shi kamar zata risina.

“Lafiya kalau”

Ya amsa yana jin wani iri. Sannan ya kalli Humairah ya ce.

“Za'ayi muku komai a nan, zan tafi gida yanzu anjima kadan za a kawo muku abinci tare da kudi ku siye wani abun, kuma idan akwai abun da kuke bukata ki sanar da ni”

“Okay”

Da ok kawai ta amsa mahaifiyarta ta dora da godiya da addu'a, shi kuma ya juya ya fice bayan yayi ma tsohuwar fatar samun sauki. A lokacin da yake kokarin bude motarsa ya shiga ya ji muryar Humairah bayansa.

“How are you Ameer?”

Ya juyo ya kalleta.

“I'm fine”

“Ban ga haka a fuskarka ba”

“I will be fine”

Ta rumgume hannayenta.

“Ka yi magana da ita?”

“No maybe tonight idan zan kai jakar Waira”

“Who's Waira?”

Ya daga kansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login