Showing 99001 words to 102000 words out of 281271 words

Chapter 34 - Wani Gari Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1242

Humaira ta rika masa ita suka fito yana gaba Nimra dake dafe da Humaira tana bayansa, sai da suka iso gurin motarsa da yayi parking sannan Ummi ta bude motar da facing din ta su ta fito tana kallonsa kamanin da ta gani a fuskarsa da jikinsa sun matukar daga mata hankali zuciyarta sai rawa, ita kadai take masa kallon tausayi da kauna, Abiey da Maleek kuma suna matsa kallon tsana daga cikin motar kamin su bude su fito. Nimra na ganin iyayenta sai hankalinta ya tashi ta fashe da kuka.

“Ameer kaika kira su?”

Ya juyo ya kalleta.

“Ba zan iya bari ki aikata kuskure nan ba Nimra”

“Ba kai ka fada min zaka iya mutuwa a kaina ba?”

“Hakan baya nufin na cutar da ke a yanzu, ba ki san abun da yake kasa ba”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un ”

Ta fada tana runtse ido. Maleek da Abiey suka iso gurin da suke tsaye Ummi kuma ta kasa karaso sao kallon Ameer take. Abiey ya kai hannu ya fisgo Nimra daga hannun Humaira ya tsinka mata mari sai da wutar kanta ta yi daukewar wucin gadi. Sannan ya kalli Ameer cikin bakar fuska ya ce.

“Babu kai babu jinina, babu kai babu zuri'ata, babu kai babu iyalina...”

Ya juya ya nufi motarsa yana jan hannun Nimra da karfi, ita kuma da yake bata da kunya sai kiran sunan Ameer take, har mutane suka fara lura da abun da ke faruwa. Allah ne kadai ya tsare Ameer be fadawa Abiey bakar magana ba, domin babu mai fada masa magana marar dadi be rama ba, sai dai tausayin Nimra da son nema mata sassauci ya saka be furta ma Abiey komai ba, sai kallon Ummi dake tsaye tana hawaye yayi daga inda yake yake fadar.

“Wata kila kin taba yin so a lokacin da kike da kurciya, ban sani ba ko kin san yadda yake da zafi da rikita zuciya, CIWON SO yana da wahala da dimauta mai yinsa, mutum kan fita hayyacinsa ya aikata abun da be dace ba, dan Allah ki dubi Nimra da idon rahma, wanda be taba so ba idan ya samu ba zai fita ďakin son da sauki ba, karki bari mijinki ya cutarta da ita dan Allah. Bata watsar da tarbiyar da kuka mata ba, duk abun da ya faru ba laifinta ba ne laifina ne...”

Each and every words da ya furtawa Ummi sai ta ji kamar magana yake jefa mata, gaba daya duniyar ta juye mata upside down. Maleek ya tabe baki yana kallon Ameer da tsarki.

“Nice one Ameer kai kake furtawa Ummi wannan maganar saboda da baka da kunya kuma baka da mutumci?”

Ameer ya matsa kusa da Maleek yana furzar masa da numfashi da karfi tare da saka hannayensa aljihu yana kallon cikin idonsa.

“Saboda bana da uwa a raye ba shi yake nufin van san darajar uwa ba, kai kuma baka san miye soyayya ba, baka san CIWON SO ba, saboda haka be kamata ka tsoma rubabben bakinka ba, baka san komai akan masoya ba dan haka karka sake karanbanin shiga a abun da ka zahilta, zan raga maka ne kawai saboda Uwa...”

Ameer ya daga hannunsa ya nuna Ummi dake tsaye, suna kallon kallo akuya kallon kura shi da Maleek. Maleek yayi kamar ya fada masa magana sai kuma wata zuciyar ta hana shi ya juya yana huci da jin ďacin maganar da Ameer ya fada masa ya nufi motarsu.

“Wayyo Allah zuciyata...”

Ummi ta fada tana kai hannu ta dafe zuciyarta, Maleek ya rikata da sauri ya saka a back seat inda Nimra take zaune ya rufe motar sannan ya bude front seat ya shiga domin Abiey ne yake tuka motar. Daga Humaira har Ameer tsaye suka yi suna kallon motar har ta fice daga gurin sannan Humaira ta cire hannayenta biyu da suke dafe a fuskarta tun a lokacin da Abiey ya mari Nimra ta ji kamar ita aka mara ta dafe kumatunta bata dauke ba sai da suka wuce. Sannan ta kalli Ameer tana hawaye ta ce.

“Baka kyauta ba, kalli yadda ka saka ƴa da uwa kuka saboda selfishness dinka, ka san yadda uwa take ji idan aka lalata tarbiyar ƴarta? Wallahi kana da hakki da yawa akanka”

Ya juya zata koma ciki, ya saka hannunsa ya rika dantsen hannunta ya fisgota ya dawo da ita daf da shi har tana iya iya jiyo numfashinsa ya kalli cikin kwayar idonta ita ma ta kalli tasa...





©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: 𝐖𝐀𝐍𝐈 𝐆𝐀𝐑𝐈

33

Sun dauki tsawon lokaci a haka ya kasa ce mata komai.

“It hurt...”

Ta fada slowly, sai ya kalli hannun nata ya sake.

“Ban yafe ba”

Ta fada da muryar da zai iya ji bayan ta wuce shi, yawu kawai ya hade ya nufi motarsa, ya bude ya shiga sai a lokacin ya kalli wayar Nimra dake hannunsa, samun kasan yayi da rashin sukunin abun da ya aikata, ya daga kujerar ta daya kwantar a dazun yana kallon gurin kamar tana nan, kamin ya kwantar da tashi kujerar ya kwanta a gurin gaba daya ya rasa ta inda zai dafa ya wanke Nimra, halin da ya jefata a yanzu ya matukar daga masa hankali, yana kwance cikin motar har la'asar sannan yaja motar ya fita daga gurin ya faka a gurin wani masallaci dake bakin hanya yayi sallah la'asar nesa da mamu.


*** *** ***

Har suka isa gida Nimra bata daina kuka ba, Abiey na faka motar ya fita ya nufi gurin masu gadi yayi musu gargadin cewar kar wanda ya kuskura ya bar Nimra ta sake fita daga gidan. Sannan ya dawo ya bude gefen da Nimra take ya fito da ita ya jefar a kasa kamar wanda be san inda ta fito ba, Ummi ta juyo da sauri ta kalleta sai dai bata da kuzarin da zata iso gurin domin zuciyarta a rike take. Abiey ya sake rika hannunta ya nufi cikin gidan da ita kamin ya isa falon Namra da Mahmood sun fito Waira ma tana bayansu, sai kowa ya kasa bawa Abiey hakuri ganin yadda fuskarsa take a hade kamar bakin hadari, tun da suke a rayuwarsu Abiey be taba saka hannu ya dakesu ba kuma ba taba yardar wani ya taba masa yara ba domin yana matukar kaunar yayansa, sai dai a yau shi da kansa yake yi ma Nimra hukunci. Sama ya hau da ita ta saka ta cikin dakinta ya janyo kofar da karfi.

“Kar wanda ya bari ta sake fita a gidan nan”

Waira na ganin zai saukowa ta yi saurin guduwa ta boya bayan kujera jikinta na rawa gani take kamar ita aka yi ma jina jina a jiki, a zatonta Abiey ne yayi ma Nimra wannan dukan daya canja mata kammanin. Tsoron kar ya hukuntata da laifin data aikata a dazun ya saka ta fashe da kuka tana rufe bakinta, dazun ma ba karamin fada yayi mata ba balle kuma yanzu da ya doki yarsa ita ma zai iya dukanta. Namra ta rika Ummi ta karasa shigowa falon ta zaunar da ita saman kujera.

“Ummi are you okay? Please kar ki saka abun da Nimra ta aikata a ranki”

Ummi ta juyo ta kalli Mahmood dake maganar tana kallonta cike da kulawa. Ta lumshe ido ta bude so take ta cika rokon da ďanta yayi mata na ganin ta bawa Nimra kariya.

“Je ka fito min da Nimra”

“Amman Ummi ba zaki hakura har zuwa anjima ba?”

Ta girgiza masa kai. Sai ya mike tsaye ya nufi upstairs ya tura kofar dakin Nimra ya shiga, kwance ya same ta a kasa tana kuka kamar ranta zai fita.

“Ta so Ummi tana kiranki ita ma kin saka ta kuka idan haka shi ne burinki, sakamakon da zaki yi mata kenan”

Nimra ta dago ta kalli Mahmood ta koma ta kwanta ita kadai ta san abun da take ji a zuciyarta, ganin ba zata tashi ba ya saka ya iso gurin ya rika hannunta yana janta da karfi domin shi ma a yanzu haushinta yake ji, sanin zata wahala ya saka ta fara rarrafe tana bin bayansa daker da sauko downstairs din, sai dai wani abu mai kama da kunya da jin nauyi ya hanata karasa inda Ummi take zaune, Maleek ya gurin dinning tsaye ya rumgume hannayensa yana harararta kamar zai cire.

“ƴa ta taso mana”

Ummi ta fada kamar ba komai tana kallon Nimra, kalaman da Ameer yayi mata a dazun ya dawo mata da tunanin rayuwarta ta baya, a yanzu tana iya fahimtar halin da Nimra take ciki. Bacin rai ya saka Maleek da Mahmood bari falon, sai Namra ce ta tashi ta riko hannun yar'uwarta tana kuka ta kawo ta gurin Ummi, Ummi ta rika kanta ta kwantar a kan cinyarta.

“Ya isa haka, wannan kuka ya isa Nimra ki kwantar da hankalinki ki saka ranki a inuwa, komai zai wuce kin ji? Karki sake kokarin guduwa ki bar ni saboda wani, kina tunanin uwa zata rayu idan babu yayanta a kusa? Ke kika da saurayi kika kasa jurewa balle ni da na haife ki? Kamin ki aikata wani abu ki rika tunawa da Umminki, kuma kin ga da acw guduwa abun kirki ne da wannan saurayin na ki be barki kin dawo ba, bude baki ki yi ta Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, ki yi sallah ki fadawa Allah damuwarki ki roki sasauci da zabi na alheri, Abiey zai sauko amman dole ne a yanzu sai yayi fushi sosai kin ji”

A hankali ta daga kai tana jin kaunar Ummi a ranta da kuma tausayin kanta.

“Kalli yadda kika saka ni kuka ni da yar'uwarki, karki sake yin haka kin ji? Ke musulma mai tarbiya, na yardar ba ki watsar da tarbiyar da na baki ba, tun da har baki bashi mutuncin ba, yadda kika oya yakar zuciyarki ta hana ki aikata zina, ya kamata ki yake ta ta hana ki batawa iyayenki rai, domin bacin ran iyaye yana tare da fushin Allah, idan kika bata mana rai ko da kin gudu kin tafi wani gurin ke da ahi ba zaku taba ganin haske ba, amman idan kika bi komai a hankali sai a samu maslaha”

Ummi tana fadar tana shafa kanta, kamin ta kalli Namra ta ce.

“Je ki kira Maleek ya zo ya bata magani”

Namra ta share hawayenta ta mike tsaye ta fice daga falon zuwa gurin nemansa a wajen bangaren Ummi. Ummi ta kalli gefen kujerar da Waira ta boya ta ce.

“Baby Waira Yata fito mana me kike yi ma buya? Wa kike tsoro”

“Abiey...”

Ta fada daga can inda take boye.

“Abiey ya tafi bangarensa Umminki ce kadai a nan sai yar'uwarki Nimra fito”

Ta fara lekowa ta karewa falon kallo ta ga babu kowa sai Ummi da Nimra sannan ta fito da sauri ta nufi gurin Ummi ta zauna a kasa dayan side din da Nimra take zaune tana kallon Nimra da idonta yake rufe tana zubar da hawaye.

“Kalli wacce ta rasa iyaye da yan'uwa da abokai da gari, ta rasa abinci da masu jin kalar yarenta ta bata mutu ba ta rayu tare da mu, sai ke ce zaki mutu dan kin rasa saurayi? Karki bari shaidan ya sharin zuciya su rinjaye ki Nimra”

Nimra ta bude ido ta kalli Waira take leken fuskarta, murmushi karfin hali Nimra ta yi mata sai Waira ta saka hannu ta fara share mata hawayenta, ta mika hannunta ta kama hannun Nimra ta rike ba dan komai ba sai dan ta san abun da yake faruwa, ta kwanatar da kanta a jikin Ummi kamar yadda na Nimra yake kwance. Ummi ta girgiza kai tunanin Ameer da kalamansa sun hanata sukuni, furucinsa na cewar saboda be san dadin uwa ba shi ke nuna be san muhimmancinta ba ya matukar tsaya mata a rai. Me aka fada masa? Uwarsa ta mutu? Shigowar Maleek ya saka ta share hawayenta ta kalleshi sa'insar da sukayi a dazun da Ameer take ta gani a idonta.

“Treatment zaka mata ka bata maganin da ya kamata”

“Ban taba mata treatment ba”

“Ka fara daga yau, kuma ban ce ka fada mata ko da kalma matar dadi ba balle har hannunka ya sake kaiwa a jikinta, Namra rikata ku tafi dakinta ki hada mata ruwa ta gasa jikinta zan hada mata wani abun ci a yanzu”

Ummi ta karasa tana kallon Namra wacce ta amsa mata da kai ta rika yar'uwarta suka mike tsaye. Waira ta bude ido da sauri tana kallon Nimra.

“Ta sanshi i know him... Waira ta san shi ta gane shi ta san shi”

Haka take ta fada da sauri tana nuna Nimra, daga Ummi har Maleek dake tsaye ba su fahimci abun da take nufi ba, Ummi kuma bata da lokacin tsayawa ta fahimceta a yanzu balle har ta gyara mata abun da take furtawa. Da ido Maleek ya harare a tunaninsa zata fara ba bada labarin abun da ya faru a school dinsu ne a yau, sai ta yi tsit kamar bata gurin.

“Bari na je na siyo magani”

Maleek ya fada sannan ya juya ya koma ta kofar falon da ya shigo. Waira ta bi Nimra da kallo har sai da suka haye sama gaba daya sannan ta dauke idonta ta dawo da su gurin Ummi.

“Ummi...”

Ummi ta kalleta wasu hawayen suna tarar mata a ido.

“Ummi miyasa Ummi ba zata bari Nimra ta aure shi ba”

“Saboda wani abubuwa da yawa tashi ki je ki cire uniform dinki”

Ta tashi ta nufi upstarts, sai kuma ta juyo.

“Ummi... Meyasa Ummi ba zata fadawa Abiey tana son mijin Nimra ba?”

Ummi bata bi ta kan maganar ba, domin tana cikin damuwa a yanzu.

“Na ce ki tafi ki canja uniform dinki”

Waira ta juya ta karasa hayewa sama, Ummi kuma ta cire hijabinta ta kwanta akan kujera tana ta addu'ar samun saukin zuciya. Waira na shiga dakinta wanka ne abun da ta fara yi sannan ta fito ta saka wando da riga ta sauko kasa bata samu kowa a falon ba sai motsin da take ji a kitchen, hakan ya saka ta nufi kitchen kai tsaye ta leka sai ga ta samu Ummi a tsaye.

“Ummi ta canja”

Ta fada tana shafa tufafin jikinta, Ummi ta juyo ta kalleta tana jin kamar zuciyarta zata tsage.

“Ummi. Meyasa Ummi ba fada fadawa Abiey bata da lafiya?”

“Lafiyata kalau tafi falo ki zauna zan hada miki tea yanzu ke da Nimra”

A maimakon ta juya ta fita kamar yadda Ummi ta bukata sai ta rugo da gudu ta rumgume Ummi ta fashe da kuka.

“Waira tana son Ummi”

Ummi ta shafa bayanta..

“Ya isa, bana son jin kuka kowa a yanzu je ki zauna zan kawo miki tea kamin mai lessons dinki ya zo kin ji? Ni ma ina sonki”

Ba dan ta so ba ta bar jikin Ummi ta fito falo ta zauna ta takure guri daya kamar bakuwa, tana kallon Maleek ya shigo ya haura sama zuwa dakin Nimra, aka sake bude kofar Dr ta shigo tare da Jabir hankalinta a tashe.

“Ina Zahra take?”

Ummi na jin muryar Dr Zainab ta fito daga kitchen din ta nufota ta rumgume tana jin wani sanyi sanyi a ranta. Jabir kuma ya nufi Waira dake ta sharar kwalla.

“Waya taba ki?”

“Ummi zata mutu...”

Yayi saurin rufe mata baki, a zatonsa kuka da ta ga Ummi tana yi ne ya saka ta tsorata har take furta haka.

“Subhanallah, ki dina fadar hakan ba abubuwa ne akwai suka faru kuma komai zai wuce kinji?”

Ta girgiza kai ta fara magana da karfi cikin kuka.

“Ummi tana kuka, Ummi tana da ciwo Ummi zata mutu, Ummi ba zata fada ba, Ummi tana son mijin Nimra, Ummi ta haifi Mijin Nimra”

Ta ta saka dayan hannunta ta share hawayen fahimci abun da take nufi bata iya fadar da kyau ba hakan ya saka ta kalli Ummi dake kallonta ta ce

“Ummi talk, tell them ki fada musu”

Kusan kowa kallonta yake daga Maleek dake saukowa rike da syringe a hannunsa har Mahmood da ya turo kofar falon ya shigo da zimmar sanar mata mai lessons dinta ya zo, balle kuma Ummi data tsorota da abun da Waira take fada, Jabir kuma be fahimci zancen da kyau ba as well as Maleek sai dai kalmar Ummi zata mutu ta daga musu hankali, Dr Zainab ma bata fahimcin yaren nata ba.

“Me take fada ne? Ni ban fahimta ba”

Jabir ya tambaya yana kallon Ummi.

“Ummi tana da ciwo mai mutuwa Ummi zata mutu Waira tana son Ummi”

Ta sake fada tare da fashewa da wani irin kuka mai karfi, a wannan karon Mahmood ya fahimcin inda ta dosa, Maleek kuma ya shiga hudu sai idonsa suna akan mahaifiyarsa.

“Waira ki tafi dakinki yanzu nan?”

Ummi ta fada, sai Mahmood yayi karaf ya ce.

“Mai lessons dinta ya zo yanzu nan”

“Okay wuce ki dauko jakarki ki tafi gurin lessons dinki”

Ta sauka daga kan couch din ta nufi upstarts haka ta raba gefen Maleek da ya gagara saukowa ta wuce dakinta ta dauko jakarta ta sauko ta fice daga falon.

“Me yarinyar na yi take fada ne Zahra?”

Dr Zainab ta tambaya.

“Shirmenta ne mana, da ma kin tafi gurin Abiey kun tattauna zai fi”

Maleek ya sauko ya nufi kofa ya fice daga zuwa gurin motarsa ya bude ya dauko wata ledar sannan ya dawo ciki ya haura zuwa dakin Nimra zuciyarsa da tunani kala kala. Dr Zainab ta nufi hanyar da zata sadata da bangaren Abiey, Jabir da Mahmood kuma suka zauna a falon Mahmood na labarta masa abun da ya faru a game da Nimra da kuma rashin mutun Ameer da ya sani. Ummi kuma ta koma kitchen din ta cigaba da abun da take tana tunanin inda Waira ta samu wannan labarin, hausawa suka ce sawun giwa ya batar da na rakumi, gaba daya sai tunaninta ya koma gurin Waira.


WAIRA POV.

A inda suka saba zama su yi lessons ta zauna akan kujerar da aka siya mata da karamin tebur din da take dora littafan karatunta, dattijon da zai yi shekara 50 yana ta zuba mata karatu amman hankalinta baya guri, tunaninta ya tafi akan dalilin Ummi na boyewa kowa ciwonta da kuma burinta akan Ameer, a yanzu kuma ta rasa gane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login