Showing 216001 words to 219000 words out of 281271 words
ganin na shirya tsakanin yayana ne”
“Anjima nake son na tafi”
Waira ta fada, Ummi bata ce mata komai ba ta saki Ameer ta nufi hanyar dakinta. Ameer ya mike tsaye yayi serving dinta sannan ya zuba na kasa.
“Abiey yace be yarda ki tafi ke kadai ba, sai dai a rakaki kuma sai an sanar da jami'an tsaro ina ganin ya kamata ki hakuri har zuwa gobe saboda ayi komai cikin kwanciyar hankali, kuma Maleek da zai raka ki zai samu lokaci ya shirya kamin time din”
“Bana son kowa ya raka ni, a garin ba a karba baki, kuma za a iya cutar da wasu saboda ni, ko kuma ma laifina ya yafe su”
“No ba zan iya bari ki tafi ke kadai ba Waira, ko da kuwa kashe wanda zaku tafi tare za'ayi, i know baki sona a kusa da ke, shiyasa da Abiey ya ce na rakaki na zabi Maleek ya rakaki, saboda kin fi sonsa kuma hankalinki zai fi kwanciya idan yana tare da ke sama da ni”
Kamar tace masa kai ma ba tsanarka na yi ba, kawai da zancen aurena da kai ne bane so, sai kuma ta samu kanta da jin nauyin kasa furta haka. After sun gama breakfast din Ameer ya nufi dakin mahaifiyarsa wato Ummi, first tambayar da yayi mata is.
“Kin san abun da yasa Abiey yake son magana da ni?”
Sai ta girgiza masa kai.
“Ban sani ba, be fada min zai yi wata magana da kai ba ban san komai akan abun da zai tambayeka ba”
Ya juya ya fice daga dakin yana tunanin kondai Abiey zai roki wata alfarma a gurinsa ne akan Waira shiyasa yake masa magana kamar daman can babu wata kiyaya ko tsanar juna a tsakaninsu. Be san bangaren Abiey ba, dan haka yayi ta bude dakunan da suke corridor kamin ya isa babban falon dake cike da sanyin ac. Abiey yana hakimce saman kujera sanye da jallabiyar da ya saka tun safe sai wayar dake hannunsa yana duba yanar gizo.
“Bismillah Ameer shigo ciki”
Ameer ya cire talkamin kafarsa for the first time saboda zai shiga gurin wani. Ya isa cikin falon sai ya zauna a kujerar dake nesa da wanda Abiey yake zaune, zuciyarsa na raya masa abubuwa kala kala akan kiran da Abiey yayi masa, ko da yake hausawa sun ce karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifin da ka aikata. Shiru ne yayi ta wanzuwa a cikin falon na tsawon lokaci kamin Abiey ya dago ya kalleshi ya ce.
“Da gaske baka ra'ayin raka Waira garinsu?”
Yayi jimmmm kamar mai nazari sannan ya daga kai.
“Yeah akwai abubuwa da zan yi masu muhimmanci a nan, kuma zata fi jindadin tafiya da Maleek din dai”
“Okay, na yi magana da Imam na sanar masa komai tace zuwa 11pm na zo tare da yarinyar zai musuluntar da ita, kuma ya gabatar da ita a gurin mata yan'uwanta da za su nuna mata yadda zata yi addinin, su fada mata wasu abubuwan da suka kamata”
“Hakan yayi kyau”
“Abu na biyu ina son mu tattauna da kai ne akan ciwon mahaifiyarka, likitanta ya fada min tana bukatar a kwantar da ita a asibiti for now, ni kuma na san halinta bata son zaman asibiti maybe ma yana daga cikin dalilin da ya saka nmta boye mana ciwon tun farko, i know bata bukatar tashin hankali a yanzu shiyasa bana son takura mata cewar dole sai ta tafi asibiti, amman na san tana sonka kuma tana jin maganarka zaka iya lallaba mana ita ta yarda ta kwanta asibitin hakan ba yana nufin rasa rayuwarta ba, no saboda a samu damar bata kulawar da ta kamata, and ina tunanin ko da zata kwnata ba zata wuce sati a nan ba saboda ina tunanin fitar da ita waje, ko ba komai a can sun fi mu kayan aiki da kula da marasa lafiya yadda ya kamata amman me ka gani? Ban yi maganar da kowa ba, kawai na fi son na fara jin ra'ayinka ne”
Ameer ya dan yi shiru yana mamaki ace yau shi ne Abiey yake tambayarsa shawara akan Ummi, be tambayi yayansa ba.
“Zamu iya fitar da ita India ko Egypt suna da asibiti mai kyau da kwararun likitoci da suke kula da wannan bangaren kuma na ga ana yawan kai masu irin ciwonta kasashen, akwai kuma London can ma suna da asibiti mai kyau”
Abiey yayi murmushi yana jinjina kai.
“Good ni ma tunanina zuwa can zai fi, amman dai na yi shiru na ji irin shawarar da zaka yanke ne, zan yi magana da Maleek da kuma likitan sai mu ga inda ya kamata”
“Okay”
Ameer ya mike tsaye.
“Ameer, please feel free to talk to a duk lokacin da kake bukatar wani abu, ko da kuwa shawara ce, kuma ga yan'uwanka nan please ka manta da komai ka zauna lafiya da su ko dan saboda mahaifiyarka, ka dauke ni a matsayin uba, na san kana kallona a matsayin wani makiyinka no ba haka ba ne, akwai wadandansu dabi'u da bana so a cikin halayyarka, kuma ina ganin kamar ka dauko hanyar sauyawa, ina fatar hakan zai daure Allah ya kara hada kanku, su ma na yi magana da su, kuma zan sake yi sai na hadaku gaba daya na yi muku nasiha, and idan za a fita da ita waje tare za mu da kai, ko da sauran ba su samu damar zuwa ba”
“In Shaa Allah”
Ameer ya fada sannan ya juya ya fice daga falon.
[8/4, 9:57 PM] My S Line: 71
Misalin 11:30am Abiey da Ameer, Maleek da Mahmood har ma Namra da Ummi suka raka Waira gurin karbar shahadar shiga musulunci, Imam din ya gabatar musu da duk wasu abubuwa da suka kamata, ya fara da yi ma Waira shimfida yadda zata kara fahimtar addinin kuma ta natsu da shi, kana ya tambaye ta ko wane yayi mata dole ko kuma ya tsorata ya saka take son shiga addinin musulunci ta amsa da aa. Kanta a rufe da hijabin dake kara bayyana kyauta wato black hijab sai doguwar rigar abaya. Ya fada mata dokoki da sharudan karbar kalmar shahada ta ce ta aminta, zata daina bautar kowa sai Allah kuma zata bi duk wata doka da Allah ya kafa. Bayan ta gama sauraren dokikin ta amince ta gabatar masa da tambayarta.
“Akwai tsafi a jikina, ta yadda nake iya gane abun da ya faru da mutum a rayuwarsa ta baya, kuma zan iya wasu abubuwan na siddabaru idan ina so, amman ban taba yi ba, kuma ba zan iya fitar da tsafin ta hanya mai sauki ba, har sai na fasa jiki”
“Dole ne ki rabu da tsafin, ko da kuwa hakan na nufin tsare wani bangare na jikinki ne, a nawa ganin tsafi kaucewa Allah ne, a haka nake ganin be dace kina tare da shi ba, saboda haka nake shawararta ki idan har da gaske zaki yi addinin Allah kuma zaki karbe shi da zuciya daya ne, to ya kamata ki watsar da duk wani abu da zai kaiki ga shirka”
Ta daga masa kai. Sannan ya gabatar mata da kalmar shahada tana maimaitawa.
“Ashahadu Allah La'ilaha illallah”
“Ashahadu Allah La'ilaha illallah”
“Wa'ashadu ana Muhammadan rasullullah”
“Wa'ashadu ana Muhammadan rasullullah”
“Na shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma na shaida Annabi Muhammad Manzon Allah ne”
Ta nanata haka hawaye na sauko mata, Ummi ma hawaye take matan dake hidima dake sallamacin ma kallonta suke with emotional.
“A yanzu kin zama musulma, kin dawo jaririya kamar a yau mahaifiyarki ta haife ki, baki da zunubi ko daya, kuma kin zama yar'uwarmu muma mun zama yan'uwanki zumuncin da ya fi na jini karfi, Allah ya tabbatar da ke a cikin addinin musulunci”
Waira ta fashe da kuka tana jinta a wani irin yanayi na aminci da gamsuwa da natsuwar da bata taba kasancewa ba. Namra ta rumgume ta tana hawaye, Ameer ya ji kaunarta ta kara cika masa zuciya, Maleek ya ji ta cika ta ko'ina a yanzu bata da bukatar kari.
“Maa Shaa Allah, barka da zuwa addinin Allah addinin amincin da kyautatawa, yanzu kin zama yata baki da banbanci da Namra ko Maleek a gurina”
Abiey ya fada yana kallonta cike da burgewa.
“Ya sunanki?”
Imam din ya tambaya. Sai ta amsa masa tana kuka.
“Waira”
“Waira suna ne mai kyau, sai dai asalin sunan Nuwaira ne ba Waira zalla ba, saboda haka zamu iya kiranki da Nuwaira, ko kina sha'awar a canja miki sunan ne?”
Ta girgiza kai alamar aa, ta juyo ya rumgume Ummi.
“Allah ya miki albarka ya tsare rayuwarki da imaninki Nuwaira”
Duk suka amsa da Ameen. Matan da Iman din ya gayyato suka gabatar da Nuwaira yadda zata yi ibada, wanka tsarkin da zata yi na shiga addinin musulunci, da kuma dokokin da suka wajaba a kanta, suka tambayeta ko akwai wata matsala da take fuska ta musallin ko abinci ko kuma wata baraza ta amsa da cewar babu ko daya. Sai da aka fara tada Sallah azahar sannan Mahmood ya dawo da su Ummi gida, Ameer da Maleek suka yi sallah a masallacin tare da Abiey.
Ummi ce ta jagoranci Nuwaira gurin nuna mata yadda zata yi wankan tsarkin, bayan ta nuna mata a waya yadda zata yi a waya sai da ta tabbatar ta iya sannan ta fita ta bata guri, Nuwaira ta yi wanka da kanta ta fito tana daure da tawul ta rufe kanta da wani. Ummi dake zaune gafen gadonta tana jiranta ta mike tsaye ta mika mata sabuwar rigar abayar da zata sauko mata har kasa.
“Wannan kyauta ce daga gareni, farkon zuwana makka na siyo rigar nan amman ban taba sakawa ba, da na aje har sai idan daya daga cikin yayana za su yi aure na ba su saboda tsadar rigar, sai dai musuluntar da kika yi a yau, ya saka kin zama ďaya daga cikin yayana, zan iya miki komai fiye da yadda zan yi musu ma”
Nuwaira ta tara hannu ta karba tana kallon Ummi dake hawaye tare da murmushi.
“Na gode, ina ma ace zan iya saka miki da duk abun da kika yi min? Hakika ke uwa ce ta gari, kin cancanci ko wane irin Award na girmamawa da karanci”
“Idan kin shirya ki fito waje yan'uwanki suna kasa suna jiranki”
Ta gyada kai sannan ta karbi rigar ta aje saman gadon. Ummin ta juya ta fice daga dakin, Hannu Nuwaira ta kai ta taba rigar yadda ta sha stone tana kyali ga yadin sai walwalniya yake yana daukar ido, kana kallon rigar kasan an zuba guri gurin siyenta. Ta dade tana kallon rigar sannan ta mike tsaye ta cire tawul dinta ta dauki rigar ta zura, daman can bata mu'alama da birejiya dan haka bata damu da neman inda take ba balle ta saka. Tana zura rigar ta dauki mayafin abayar ta rufe kanta sai ta taka gurin madubi ta kalli kanta. Dan murmushi ganin yadda dark green din abayar ta yi mata masifar kyau kai kace sarauniyar Abuja ce, tsayin rigar 58 ne ita kuma tana saka 54 ne haka ya saka rigar ta yi mata fadi da tsayi, sai dai ko kadan hakan be rage komai daga kyaunta ba. Ta saka hannu ta rike rigar tana takawa a hankali har ta isa gurin kofar ta bude ta fita, tana fara saukowa stiars idon kowa ya dawo kanta, Ameer be san lokacin da ya mike tsaye yana kallonta kamin murmushinsa ya fara yi mata marhabun da saukowa. Maleek ya kalleshi ya kalli Abiey sannan shi da Mahmood suka kalli juna, Ummi ma kallonsa ta yi kamin ta dauke ido ta kalli Nuwaira. Tsaye ta fara yi a lokacin da ta sauko har sai da Namra ta mike tsaye ta isa gurinta ta riko hannunta.
“Zo na nuna miki wani abu little Sis”
Gurin wata Laptop dake aje kan kujera Namra ta nufa da ita, suna isa ta saki hannunta ta bude laptop din ta shiga whatsapp din ta kunna video call, few seconds Shuraim yayi picking fuskarsa da murmushi, Nuwaira na ganinsa ta durkusa a gaban laptop din tana kallonsa da murmushi a fuskarta.
“Sulem...”
“Baby girl Welcome to World Of Islam, na yi matukar farinciki na jidadi a lokacin da na Namra takw fada min hukuncin da kika yanke, na yi bakinciki da bana kusa da ke, da yanzu da ni za a samu wannan ladar, amman a haka ma ina farinciki yanzu kin kallama komai duk wani abu da ake so a mace a yanzu kin hada shi”
“I miss you”
Ta fada hawaye na sauko mata.
“I miss you too baby girl, idan zan zo zan kawo miki tsaraba mai yawa kuma mai ban mamaki”
“Maybe ba zaka same ni ba, zan tafi gida gobe”
Shuraim ya dan yi jimm for some seconds sannan ya kalli Namra dake gafenta.
“Why? Akwai matsala ne Namra?”
“No ita dai take ra'ayin zuwa”
“Ina fatar ba za su cutar da ke ba”
“Nima ina fatar haka”
“Zan tare a Katsina, sai na ganki i miss you so much”
“Ina da labari da yawa da zan baka”
“Ni ma ina da labarai da yawa Baby girl ”
Ta taba hancinta ta kai hannunta ta taba jikin computer sai yayi dariya shi a ya taba hancinsa ya taba computer.
“See you”
Namra ta rufe computer, Nuwaira ta juya ta kalli Namra tana murmushi.
“Nuwaira ga wannan na san zai taimaka miki gurin Sallah saboda yanzu kika fara, yana magana kuma yana fadar duk wani tasbihi da ya kamata ki yi a cikin Sallah”
Nuwaira ta karasa kusa da Abiey ta tara hannu biyu ta karbi prayer mat din.
“Na gode”
Ta shafa carpet din dake cikin wani jacket mai kyau kamar ba prayer mat. Ameer ya tashi ya fita, Namra kuma ta shiga dakinta sai gata ta fito da katon akwaiti ta sauko da shi.
“Ban san me zan baki ba, kuma na san kayana ba su miki, so shiyasa na zabi baki tufafin da ban danka ba gasu na hada miki guri daya a akwaiti, akwai turarukan jiki da na fesawa, kuma akwai mayuka da sabulai masu kyau”
“Na gode”
Nuwaira ta yi mata godiya tana kallon madaidaicin akwatin. Kamin ta juyo ta kalli Ameer da ya mika mata box, ta karba da hannu biyu ta bude sai ta yi arba da kur'ane mai kyau. Ta bude ido ta risina kasa ta saka hannu biyu ta ciro kur'anen ta sumbanceshi sannan ta kalli Ameer idonta na cika da hawaye.
“Na gode”
Ta sakar mata murmushinsa mai matukar tsada ta warware wata yar karamar sarka ya daura mata a hannu a yayin da take rike da kur'anen, abun hannuna ne mai kyau fari mai kamar azurfa.
“Welcome to the peace”
“Thank you, duk wannan saboda kai ne Ameer”
Abiey ya mike tsaye yana fadin.
“Ameer ka yi abun a yaba, ka kyauta kuma na jidadin haka Allah ya baka lada, ya saka maka da alheri, ina fatar a yanzu ba za a sake samun matsala ko tsabanin tsakaninka da yan'uwanka ba, Allah ya hada kanku”
“Ameen”
Ya amsa yana kallon Nuwaira da ta aje kur'anen tana ta taba abun hannun da ya saka mata cikin farinciki da jindadi.
“Yayi kyau”
“Do you like it?”
Tambayarta yake tana kallonta kamar daga shi sai ita ne a falon, gaba daya ta dauke masa hankali baya ganin kowa. Ta daga alamar yes she like it kamin ta dago ta kalleshi wannan karon hakoranta a waje yake, can kuma ta juya ta kalli Mahmood da ya mika mata chocolate da carbin hannunaa yar maroko, wato counter.
“Ga wannan zaki iya yin tasbihi da ita ko salati, zata kirga miko ko adadin guda nawa kike son yi, kuma ga chocolate kowa ya baki komai ban san me zan baki ba”
“Thank you”
Ta karba ta dora saman jikinta sannan ta kalli Maleek, shi kam be roko mata komai ba domin ba sa ran su ma za su mata kyauta ba, idan ma zai bata be san wace kyautar zai bata ba. Hakan kuma ba karamin dadi yayi ma Ameer ba daman shi so yake ya zama shi kadai ne yake burge Nuwaira baya son abokin takara.
“Maybe next time ni ban riko miki komai ba”
Ta yi murmushi ta maida hankalinta gurin abun hannun da Ameer ya daura mata, ita dai tana kaunar ayi mata kyauta wani abun da ya danganci sarka ko abun hannu.
“Ameer kai ka katse min sarkar da Sulem ya ba ni ka tuna?”
“Gashi nan ai na baki wani”
Ta yi dariya ta mike tsaye ta rufe kur'anen ta dauka ta rumgume.
“Na gode All”
Ta nufi stairs duk suka bita da kallo, Ummi na ji kamar tace mata kar ta tafi.
“Har a yanzu da ta musulumta tafiya zata ti Ummi?”
Namra ta tambaya. Sai Abiey ya amsa mata.
“Tafiyar zata fi zaman, ko ba komai zamu san yan'uwanta kuma tafiyarta ba yana nufin mu barta a can shikenan ba, no zamu bibiyeta ko dan sanin halin da take ciki, shiyasa na ce ba zata tafi ita kadai ba sai tare da jami'an tsaro, kuma Maleek zai rakata kamar yadda Ameer ya bukata, zuwa gobe zamu shirya komai jibi sai ta tafi”
“Haka ne, Allah yasan hakan ne alheri a gareta da mu gaba daya”
Addu'ar da Mahmood yayi sai duk suka amsa da ameen. Duk a cikin kyautukan da suka mata babu wanda ta fi so kamar abun hannun da Ameer ya daura mata, da kuma alkur'anen da ya bata, domin ta dade tana sha'awar kur'ane yawan sauraren da take idan Maleek na karantawa da kuma abubuwan da Ameer yake fada mata sai yace akwai a ciki kur'ane sai dai bata san yadda zata yi ta karanta ba. Sai dai ta zuba masa ido ta yi ta kallo tana shafawa, Prayer mat din da Abiey ya bata kuma sai ta taimaka mata sosai gurin yin ibadarta yadda ya dace tana fadar duk abun da nau'urar dakw ciki take fada, kana kuma ta bi yadda take nunawa. A kowa ce Sallah. Abiey yayi magana da Cp dake Abuja ya fada musu tafiyar da Nuwaira zata yi har ma da dansa Maleek da zai rakata, sai aka basu police biyu da za su raka su, bayan sun zo har gida sun yi mata tambayoyi sai ta fadi iya inda zata iya ganewa a kofar garinsu, daga inda ta fito zuwa gurin da ta hadu da Ameer, domin nan kadai gurin da