Showing 27001 words to 30000 words out of 363274 words

Chapter 10 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2524

ita komai ba sai ma ɗaga glass ɗin motar datayi ta bada umarnin sutafi da sauri suka tada motochin suka bar kauye kai tsaye Airport suka nufa.


Innar bello kuwa ta juya ta koma chikin gidan su hiyana ta ɗebo ruwa ta zubawa inna a fuska, a'razane inna tafarka tana faɗin zanga uban da zai hana auren nan idan an isa ache menake, innar bello tache "to ni dai natafi sai anjima tajuya tayi fichewarta, inna kuwa tafara waige waige taga bakowa a gidan duk sun watse mikewa tai ko mayafi babu tayi waje kai tsaye gidansu buba tanufa

Zaune suke dukkansu a tsakar gida har da bello inna tashigo ko sallama babu nan tasamesu ga buba sai faman ihu yake yana fadin aradun Allah bazan barsuba nine zanzama ajalin hiyana indai baayi auren nanba to aradu saina mata asiri ta mutu saina mata sanda
Inna tache meyasamishi
Inna larai maman buba tache mutanen dasuka zo din nanne dasukache kowa yawatse bazaa daura aurenba shine shi buban yache basu isaba sai wani daga chikinsu ya daga buban yabugashi da kasa kana ya kama kafarsa ya karya
" karaya tayi maganar tana zaro ido
Inna larai tache "karaya kuwa shine yanzu malam yatafi kiran mai dauri

Mikewa inna tayi tana faɗin "zomuyi magana tana tana kai karshen maganar tashige ɗakin innar buba, inna larai tatashi tabi bayanta tana shiga inna habiba tache "kinji meyake faruwa koh kuma kinsan idan yaran nan basu mutuba a dokar kauyen nan ban isa intaba koda kafar kazane a chikin dukiyarsu bakoh
Inna larai tache kwarai kuwa yanzu me abunyi
Inna tache wajen malamin chan na bayan dutse zamu sake komawa mana yasan yadda zaiyi ya kashemanasu a chan ko dai a haukata manasu komaidai me ma amusu dan wlh bazan barsuba
Inna larai tache to kina da kudine " Inna tache zannemo ai zuwa nan da sati mai zuwa sai muje
Inna larai tache yauwa kiyi kokari dan allah
To kawai inna tache mata kana tafito daga dakin tayi waje


Kano ta dabo

Aunty amarya zaune take a gefen gadanta ita da hajj sadeeya
"sadiya yanzu tafiya Enugu ya kamaki dan bazan taba barin wani yayi mulkiba idan ba danaba
Sadiya tache gaskiyakam amma bayanzu zanjeba sai wata mai kamawa dan kuwa wlh inada tafiya dayawa a gabana
Aunty amarya tache wata daya baiyi nisaba kinfasan bayan sallah za'a dorasa a mulki nikuma danaga wan nan rana gwanda namutu
Sadiya tache karki damu ai da dan sauran lokachifa abunda idan najema sha yanzu magani yanzu zaamin dankuwa a wajen zansa gagara ba dau ya kashe Safras din kowama yahuta
Aunty amarya ya tache amma sadiya bansan bakida kwakwalwaba sai yanzu kifadamin idan muka kashesa muna da gadansane kina ganinfa yafi kowa kudi a gidan nan ai bakashesa zamuyiba sawa zamuyi gagara badau ya chusa mashi sun yar wajenki kinga dayafara san zulaihat shike nan insunyi aure sai sun haihu sai mukashesa inmun kashesa kinga a lokachin muke da gado
Washe baki sadiya tafarayi tana fadin ashe kinasona har haka bansaniba wayyo allah tayi maganar tana kokarin rungumar aunty amarya
Aunty amarya tache inasanki mana sosaima ai fin hakama yanzu dai kiyimana kokari akan afasa bashi sauratan nan daga nan kuma sai muzo muyi aikin zulaihat da murna hajiya sadiya tamike tana fadin to shike nan ai dolenema ayi aikin nan da gaggawa yanzu dai kawo kudi zanwuche
Wani akwati aunty amarya ta bude ta zaro rapa rapan yan dari biyar biyar 300k tamukawa hajiya sadiya tache inbasu isaba saiki min magana sai nakaro
Karba sadiya tai tanafadin saikinjini kana tafiche daga dakin tai waje
Aunty amarya kuwa kwanchiya tai tana fadin ai dukkanku sai nayi maganinku wlh shima yusuf din ba kyalesa zanyiba aiyana da kudi sosai shima dan haka yarinyar hajiya binta zansa gagara badau ya hadasu dan mukwashe kudin dukka haka dai aunty amarya tai ta surutanta har barchi ya daukesu

Aban garen su Ammi kuwa suna barin kauye airport suka nufa nan suka hau jirginsu sai kano
Suna isa kowa yanufi part Ammi ma ta kama hannun amrat tache su hiyana su biyota part nata suka nufa suna shiga Ammi ta kira zahra a waya tache tazo tasameta a dakinta san nan tachewa su hiyana su zauna
Zama sukayi a kasa Ammi tache aa kutashi ku zauna a kujera bamusu suka tashi suka koma kan kujerar Ammi tache amrat tazo ta zauna kusa da ita ba musu amrat taje ta zauna kusa da ita su diyana kam sai kalle kalle ake
Da sallama zahra tashigo da gudu tatafi tafada jikin Ammi tana fadin harkundawo
Ammi tache tashi ajiki nikam mutun ne sai shegen san jiki " turo baki zahra tayi tache kai Ammi to niba yar auta bache Ammi tache duk bawan nan yasa nakirakiba
Kibani hankalinki da kyau kinutsu ki saurareni wayan nan dakike gani yayan kawunkine damukaje wajensa a yola sai yanzu zahra ta dago ido tana kallonsu dan shigowarta bata lura da mutane awajenba
Tache laaa Ammi kingasu kyawawa dasu wlh wanchan tana kama da yaya prince sosai
"kinga zahra bansan shirme ki saurari abun da zanfada miki yanzu a gidan nan zasu zauna
Zahra tabuga tsalle tache wayyo allah dadi Ammi dan allah kusasu a school namu danna na nunawa freinds dina su tunda suna da kyau sosai Ammi dai baki sake take kallan zahra mikewa zahra tai takoma kusa da Hiyana tamika mata hannu wai suyi musabaha
Bamusu hiyana ta mikamata nata hannu zahra ta kama hannunnata sukayi husabaha tache sunana zahra kefa " hiyana chikin gurbatatchen hausarta tache nikuma sunana Hiyana " zahra ta mai mai ta sunar Hiyana tache nice name kekumafa tayi maganar tana mikawa diyana hannu
Itama diyanar hannu tabata suka gaisa tache nikuma sunana diyana zahra tache hiyana an diyana wow su nan yayi to dayanfa tayi maganar tana nuna lamrat " diyana tache sunata lamrat zahra tajuyo da kallanta kan amra dake kusa da ammi da sauri tamike takoma kusa da Ammi tana fadin kai kaga yar india a naija gata karama da ita ga kyau kamar me to amma itakuma wlh da yaya haidar take kama amma tafishi kyau gaskiya
Ammi dai yau taga ikon allah wajen zahra mutunne sai kaudin tsiya tache zahra'u zakizo kizauna kiji abun da zanfada mikine kodai sai na batamiki rai
Sai lokachinma zahra tatuna ashe magana ammi kemata komawa tai wajen zamanta ta zauna
Ammi tachigaba da chewa yanzu dake da hiyana da diyana dakinku ɗaya ammi zata sake magana taji Zahra na fadin eyeeeee wayyo dadi Ammi ta daka mata tsawa zaki tsaya ki saurarenine ko saina saba miki shiru zahra tayi tanitsu
Ammi tachigaba dachewa lamrat da amrat dakinsu daban dakin dake kusa da nakin nan shine nasu yanzu abun danakeso dake kitashi kuje dakin ki suyi wanka kibasu kayanki susa san nan suyiwa su amrat ma wanka zansa a kawomusu kaya tunda su naki yamusu yawa kuyi sauri dan inasan muje wajen mai martaba mikewa zahra tayi da sauri tache kuzo muje wani dan korrido suka shiga san nan suka dan tafi kadan sai suka shiga dakin zahra
Nanfa zahra ta nunamusu toilet hiyana ne tafara shiga saikuma tafito tache aunty zahra bansan yazanyi amfani da abubuwan chikin toilet din ba " zahra tache dukkansu su biyota san nan tamike tanufi chikin toilet din nanfa tafara nunamusu yadda zasuyi amfani da abubawan dayake suna da kwakwalwa sosai nan take suka gane zahra ta nunawa hiyana towel dake makale awajen tache tayi amfani dasu san nan taja hannun amrat sukayi waje
Diyana da lamrat ma sukabi bayansu " hiyana kuma tafara kokarin chirekaya danyin wankar
Suna fitowa Zahra tafara kokarin fiddo musu kayan hadaddun dogayen riguna abayas tafitar musu masu kyau ta ajiye a kan gado san nan taje ta daukoh musu plat shoe masu kyau
Hiyana nafitowa wanka diyana tashiga nanfa zahra tache saitawa hiyana make up hiyana bata hanataba
Zahra tafara yimata make up mai kyan gaske bayan ta gamane tachewa hiyana ta dubi kanta a mirrow
zubur hiyana tamike lokachin data ga kanta taba fuskarta tashiga yi tana fadin anya aunty zahra niche kuwa kodai chanzamin fuska kikayi
Zahra tache aa hiyana kedai zauna bari nabaki kaya aike din kyakkyawa gaskene kyankine kawai aini simple make up ma namiki dan na lurama make up din rage maki kyau zaiyi shiyasa banmiki dayawaba
Doguwar riga sky blue zahra ta dauko daga kan gadan tamikawa hiyana hiyana ta karba zatasa " zahra tache to aibakisa bra ba
Hiyana tache me kuma bre " zahra tache breziya mana
Hiyana tache bansanshiba zahra tache to kina nufin baki taba sawaba kai to aiyakamata kirinka sawa bari na daukoh miki nawa
Lokachin da zahra ta daukoh bra ta mikawa hiyana damamaki hiyana ke kallan bra din tache to aunty zahra aina akesa wan nan kuma taya zansashi
Zahra batasan sanda dariya ya kubche mataba saida tayi dariya sosai san nan tashiga yiwa hiyana bayani akan bra
Hiyana nagane menene bra nantake taji kunya yakamata tayi kasa da kai zahra tache aa karmufara haka dake nidakefa kinganmu kamar yan biyu shekarunmu ma ƙila dayane dan haka karkisake chewa zakiji kunyata juya na daura miki bra
Hiyana tache nifa shekaruna 15 zuhara tache kai shekara 15 kuma shine breast naki sukayi girma haka kinfini komaifa nikuma shekarata 16 amma kingani kam bawani auki tako ina
Hiyana dai shiru tai bata sake magana ba har zahra tagama taimaka mata tasa kayan Zahra tache yabaki wanke kanki ba ingani
Chirewa hiyana dankwalin kanta zahra tai a rude tache kai inna lillahi kinga gashinki har baya wayyo dama niche amma yanaga kannakima ba datti
Hiyana tache jiya anwankemin kai din ai zahra tache mamanku hiyana tache aa makwanchiyar mu che innan bello ta wankemin mukam bamuda mama da baba duk sun rasu
Zaro ido waje zahra tayi tache allah sarki sannu kinji allah yajikansu da rahma
Hiyana ta amsa da ameen
Ribons da mayuka masu kanshi na gashi zahra ta daukoh tazo tafara gyarawa hiyana gashin kannata da kyar ta tara gashin nata ta daure mata a tsakiyar kanta zuba mata gelar gashin tabaya wadda yakai har kan boos din ta san nan zahra ta daukoh mayafin rigar ta mikamata kana tasamata manya manyan dankunne masu raun sai kyalli suke
Diyanama tana fitowa zahra ta dau yimata kwalliya saidata gyarasu tsab san nan tache ita zatayiwa amra wanka dan daga yau amrat yar tache
Kama hannun amrat zahra tai sukashiga toilet tamata wanka san nan tache lamra tazo tayi wanka da kanta
Sungama shiri tsab Ammi ta kawowa su lamtar blaus mai shegen kyau black colour
Zahra ta karba tasamusu bakaramin kyau sukayiba
A palo suka samu Ammi " Ammi ita da kanta ta tsorata daganin kyan da sukayi dan sunhadu tache to kuzo muje palan mai martaba dan mukadai ake jira sukache to zahra ta kama hannun amrat Ammi kuma tarike lamrat sukayi gaba su Hiyana na binsu abaya
Da sallama suka shiga palan gaba daya mutanen gidan suna palan har da mai martaba ma yana zaune shiru wajen babu mai magana kowa da abun dayake sunajin sallama suka dago kai amma banda Don Aryan Fahad Yusuf Aiman duk sauran su dago suna kallan Ammi
Wuchewa Ammi tai ta zauna kusa da mai martaba zahra kuwa taja hannunsu sukaje suka zauna kusa da aunty farida " kasa kasa aunty farida tachewa diyana tazo kusa da ita ta zauna mikewa diyana tai ta koma kusa da aunty faridan ta zauna
Mai martaba yayi gyaran murya saida kowa yadago kai amma banda wayan nan jarumai guda 5 din sudai har yanzu suna duke da kai suna daddan na wayoyinsu
Mai martaba ya nuna amrat da hannu yache tashi kizo mikewa tai tanufi wajensa gyra zama yayi san nan ya dorata a gefensa ta zauna yana shafa kanta yache yasu nanki
Shiru amrat tayi bata amsaba mai martaba yasake mai mai ta mata tambayar
Sai sukaji diyana tanachewa chikin gurba tatchen hausarta tache itakam batajin hausa mune kawai mukeji
Dukka palan saida sukayi dariya banda Don, Aryan,Aiman,Fahad,Yusuf "
Khalid ne yache to kema kina ganin kinajin hausake nan
Ummi tache yata rabu dasu hai ai kinyi kokarima dakika iya wan nan hausar abunda ba yarenkaba kuma katasowa kayi a inda ake magana da yarenba kuma a haka har kika iya fadin hakan ma ai masha allah
Zahrane ta matso kusa da diyana tafara mata magana da fullanchi dayake zahra najin fullachin sosai Ammi ta koya mata
Magana take mata a kan idan mai martaba yana nagana baa magana har saiyagama wani mugun kallo umar ke wurgawa Zahra hakan yasa tayi shiru ta daina magana

Mai martaba ya dubi diyana chikin harchen fullanchi wanda bai taba magana dashiba yache to yasu nanta ai basu aunty amarya kawaiba harda jarumai 5 saida suka dago suna kallon mai martaba hankalinsa kwanche yake fullanchinsa
Ammi kam ko ajikinta dan tasan ita ta koyamasa fullanchi
Chikin harche fullachin diyana tache su nanta amrat
Mai martaba yafa ra bayani nan yafadawa yan gidan matsayinsu Hiyana yakara dachewa daga yau sunzama yayansa kuma a nan zasu zauna bayan yagama maganarne yache koh akoi mai magana
Aunty farida tadanyi gyaran murya alamar tanada magana " mai martaba yache to ina jinki
Aunty farida tache dan allah Abba inasan abani wan nan natafi da ita ta zauna awajena tayi maganar tana nuna Diyana
Mai martaba yache aa bazaki rabasuba ki kyakemin yayana anan babu inda zasuje

Nantake aunty mardiyama ta hadiye maganarta jin amsar da mai martaba yabawa Aunty farida daman itama tanasan taroka abata lamrat amma jin Aunty farida da kanta an hanata yasa tai shiru

Aunty amarya kuwa tunani tashigayi ta yadda zata bullowa al amarin dan wlh bazata taba yarda su Diyana su zauna a gidan nanba dan kuwa yaddasuke kyawawan nan karsu Safras sufara sansu domin Safras zulaihat kawai zai aura

Mai martaba yache to kutashi kutafi Khalid kai kuma ranar monday kaje kamusu registration a makarantar su Zahra
Khalid yache to da ɗai ɗai mazan suka fara fita daga palan

Ummi ne tachewa Ammi yamukaji da hakuri
Ammi tache hakuri yazama dole " Ummi tache allah yajikansa Ameen Ammi tache san nan su Aunty farida ma kowa yafarayiwa Ammi taziya

Amrat na zaune kusa da mai martaba suna ta hira dashi da harchen fullanchi
Aunty amarya kuwa afusache tamike tafita daga palan kai tsaye part nata tanufa
Tana shiga ta kira hajiya sadiya tache ke aiki yakarufa domin kuwa mai martaba yana neman rusa mana shiri
Hajiya sadiya tache mekuma yafa " Aunty amarya tache Aisha che taje kauyensu ta daukoh wasu yara wai yayan kaninta daya rasu to wlh idan kikaga yaran nan kamar susukayi kansu dan kyau gasu da diri da komai kuma biyu daga chikinsu yan matane,yanzu fargabana ɗaya a nan shine kar matasan gidan nan sufara sansufa
hajjiya Sadiya tache wayache maki zasu fara sonsu
Aunty amarya tache ke wlh koke kikaga yaran nan sai kinsosu saboda kyau ni tsoran danake jima karfa Safras da Aryan su fara son su idan hakan yafaru wlh angama dani
Hajiya sadiya tache angama dakene kokuma angama dani nida har na fadawa zulaihat Safras zata aura yarinya sai murnatake ai yazama dole mutashi tsaye
Aunty amarya tache to yanzu me abunyi
Hajiya sadiya . tache aiki gagarabadau zai mana ya koresu daga gidan kokuma ya haukata mana su kowa yahuta
Aunty amarya tache wlh hakan kawai za'ayi zankaramiki 500k achikin account naki yanzu ayi aiki mai karfifa wanda idan suntafi suntafi ke nan sufita daga rayuwar kowa sukoma rayuwa a bula
Hajiya sadiya tayi dariya tache karki damu aikinsan aikin gagarabadau badaga nan ba kedai kawai kizuba ido watan nan nakarewa muka shiga wata zanje enugu
Aunty amarya tache ai shiyasa nake sanki kawata sai munyi waya kekam anjima da daddare zan kiraki bata jira amsar Hajj sadiya ba ta katse kiran ta ajiye wayar a kan gado tanufi toilet

Pls more comments an like

*💫STAR LADY💫*



*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star Lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai


*Episode 8*



Tana dago kai suka haɗa ido da yusuf," chikin kuka take faɗin dan allah hamma kayi haku...bata karisaba yadora hannunsa a kan lips nata yana faɗin to ya isahaka kiyi shiru bamai sake bugunki"
"Zahra'kam Mutuwar zaune tayi tashiga duniyar tunani, wai shin daman yaya yusuf haka voice nashi yake, allah yasa dai bawani aljani bane yazo musu a siffar yaya yusuf
Zahra, tayi nisa a chikin tunaninta kawai " "saitaga yusuf yamike tsaye yana rike da hannun hiyana saida sukamike," yache
Yakamata kirinka banban'chemu ni sunana yaya yusuf, wanda yamareki jiya su nansa yaya prince kinji, " cikin shesshekar kuka take faɗin to amma zan iyache muku hamma ," Yusuf yache meyasa kikesan kirinka chemana hakan "
"ai kunada yawane idannache dukkanku yaya zanrinka chewa bazan ganeba, amma idan ina hadawa da hamma abun zanmin sauki "
"Murmushi yayi san nan yache to shike nan nikirin'kachemin hamman kinji " to Kawai hiyana tache," dawo da kallansa yayi kansu diyana, kutaso muje mana, ba musu suka saukoh daga kan gadan "
"Zahra ma saukowa tayi suka jera yusuf narike da hannun hiyana saida suka fito palon Ammi, batare da yasaki hannun hiyanaba, yasa ɗayan hannunsa ya kamo hannun lamrat yache ke yasu nanki "
"Dawani gurbatatchen hausarta tache lamrat," jinjina kai yusuf yayi yana faɗin gaskiya lamrat yamin nisa awajen kira gashi su nan naku nada wahalar kira sosai dole na chanza muku suna ni bazan iya kiran sunan nan nakuba"
"Shiru sukayi kawai suna jinsa, yanuna hiyana ke daga yau su nanki sweet sis, yanuna diyana kekuma little sis, yanuna lamrat kekuma baby yanuna amrat yache my little baby ,"
"Zahra dai binsu kawai take dan ita duk tunaninta aljanine yazo a saffar yaya yusuf dan tun da take wlh bazatache, ga kalan voice na yaya yusuf ba, amma yau shine har da magana mai tsawo, kai to kodai umarnin mai martaba yabashine dan nasan mai martaba bazai tabarinsu hiyana a kunchiba

Dasallama sukashiga palan mai martaba," kowa yadago ya zubamusu ido amma banda don da tager Aryan"
"Umar'ne ya taba haidar kasa kasa yake faɗin kai anya kuwa yaya yusuf ne, kadubafa har


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login