Showing 231001 words to 234000 words out of 363274 words

Chapter 78 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2586

ya sa yaya Prince ya so ni ko da kwatan son da nake masa ne amma na sha wahala sosai a kan sa" "in Sha Allah zai so ki hiyana zai so ki sosai ma in dai yana da tausayi da imani to tabbas zai so ki in dai yana da ido kuma idan sa na gani da kyau to dole ya soki in dai yana da ilimin addini kuma yana amfani da ita to dole ya soki zan tayaki da addu'a"

taɓe baki Bgs yayi yana kallon su ta system nashi yana jin me suke faɗe abun ma har mamaki yake bashi "wai yanzu yar yarinyar nan ta san me so tab gaskiya Abba ya chucheni ya haɗa ni da wahala" dogon tsaki ya kuma ja tare da miƙewa ya fice daga office ɗin

Aɓangaren hiyana kuwa sosai ta bawa diyana lbr tun zuwar su Uk har yau sosai suka sha hira diyana ta jajan tawa hiyana akan wahalar da ta sha, ji suke kamar su haɗiye juna saboda so da kauna har sun yi sallama hiyana ta kuma chewa "diyana karfa ki faɗawa kowa hiran da mukayi" "ba zan faɗa ba hiyana na" godiya Hiyana ta mata sanna sukayi sallama ta ajiye wayar ta ɗauki hijabi ta sanya ta fito ta nufo part ɗin su Zahra


Kano Nigeria

Gaba ɗaya iyalan Abba suna zaune a palo suna cin abincin rana sai hira suke tsakanin su ban da Aryan da Aunty Amarya da suke zaune shiru Aryan na latsa waya Aunty Amarya na chin abincin ta
"Aryan gobe fa zamu wuce hope ka kammala abubuwan da zakayi" chewar Abba sai lokacin Aryan ya ɗago kai "Eh Abba akoi in da zanje yau idan na dawo zan zo muyi wata magana" Abba yana kokarin yin magana diyana ta rigashi da chewa Abba eyya ina son muje kauye ina son inje in kalli su yaya bello da innar sa" satar kallon Aryan Abba yayi dan yasan halin ƴaƴan na shi chike da zolaya yace "to my diyana an jima zakuje da mijin ki" a sukwane Aryan ya ɗago ido yana kallon Abba kashe masa ido ɗaya Abba yayi ɗaure fuska sosai Aryan yayi ya dubi diyana ya fara magana "ke idan kika sake yi mana Maganar wanchan ban... Haɗa ido da Ammi ya sanya ya mata kara bai karisa maganar ba ya miƙe chike da ɓachin rai zai bar palon Abba yayi saurin chewa "aa ba sai ka ɓata rai ba ai ba yadda za ayi na yanke wa diyana abun da zatayi yanzu dole sai da izinin ka zatayi komai" zama yayi saman sofa mai zaman mutun 2 a palon yana latsawa da alama wani sakon yake turawa "Abba yanzu ke nan duk abun da yaya Aryan yace na yi shi zan rinƙa yi? Chewar diyana tayi maganar tana kallon Ammi dan ta lura da Ammi tun ɗazu kamar tana son yi mata magana "eh my daughter yanzu duk wani abun da zakiyi sai kin nemi iznin sa idan bai yarda ba sai ki hakura" "to amma Abba in tambaye ka? Gyaɗa mata kai Abba yayi alamar Eh "Abba menene fyaɗe na tambayi yaya Aryan yaki faɗa min" a sukwane Aryan ya juyo yana kallon ta ita ko batama san yana yi ba hankalin na kan Abba "my daughter ai na ki kajiyo wanna kalmar? "Abba wata yarinya che tace zatayiwa yaya Aryan fyaɗe kuma tun da na kalli yarinyar batayi kalan mutanen masu hankali ba shi yasa nake son sanin manar maganar da ta faɗa" gaba ɗaya su Abba suka juyo suna kallon Aryan ɗauke kan sa yayi kamar bai san suna yi ba "my daughter ai na kuka haɗu da yarinyar? "Abba jiyane muna tafiya da yaya Aryan a mota shine wasu mutane suka kama mu suka kaimu wani waje wai zasu kashe mu shine wanchan mai kama da hiyana ya turo sojojin sa suka kashe su" tsaki Ammi taja kafin tace "wanna ɗan baki akoi magana wlh ke dai diyana ina ganin manne bakin nan naki zamu rinƙa yi" chikin sauri diyana tace "wai ni me baki na ya muku ne kowa sai ya rinƙa zagin baki na haka ma yaya Aryan yace sai ya shanye min ɗan baki na ɗin nan na dai na magana" kasa kasa Haidar ya sachi kallon Omar suna murmushi kasa kasa,

diyana na kokarin chi gaba da magana Abba yayi saurin chan za mata topic ɗin hiran da chewa "baki faɗa min ya akayi kuka kuɓuta daga hannun mutane da suka kamaku ba" dafe kai Aryan yayi Abba zai kara kwaɓe masa abubuwa yanzu idan diyana ta bada lbr abun ya faru tsakanin su da zulaihat ai ta rusa musu shiri gashi ita mutunce da bata karya bata iya ɓuye abu ba iya gaskiyan abun da ya faru take faɗe yanzu tana basu lbr ma Aunty Amarya zata tasa shi a gaba sai ya faɗa mata me ya faru,har Abban ma ba barinsa za suyi ba sai sun dame sa akan me ya faru kuma su waye mutane yanzu idan yace zai kira diyana su tafi ɗaki dole Aunty Amarya zata zargi wani abu zata tasa shi agaba sosai Aryan ya shiga damuwa akan surutan diyana gashi ya rasa mafita abun haushin ma shine biye mata da Abba ke yi wlh Abba ya chika shagwaɓa yara wlh yayi nisa chikin tunanin,diyana kuwa sai bawa su Abba lbr abun da ya faru take har da yi musu kwatan chen zulaihat

kamar daga sama Aryan yaji wayar sa na ringing picking call ɗin yayi tare da manna wayar a kunnen yana faɗin "hello my blood" daga ɗan ɓangaren Bgs yace "bata wayar" ba musu Aryan yace "my jidda zo ki anshi waya yaya ki na son magana da ke" make kafaɗa ta tana faɗin "wanchan mai kama da hiyana? Idan dai shine bana son magana da shi tun da yana azabtar min da yar uwa hiyana ta faɗa min duk abun da yake mata kuma wlh sai Allah ya saka mata tun da ba abun da ta masa wlh ni ban gama me yasa hiyana zata che tana son shi kamar ta mutu ba ita ma yar banza wlh rashin duka ke damun ta Allah ya sama ya mata dukan mutuwa ta yadda zata dai na son sa shike nan tana dai na son sa dole ya sake ta ta huta da ukubar sa mugu wlh da ina chan ba zan taɓa barinsa ya rinka bugun taba abun haushi ma har da wani chemin wai karna faɗawa kowa abun da ta faɗa min to me abun rufa masa asiri ni wlh na kusa barin gidan nan dan ba naso......bata kai karshen maganar ba Aryan ya daka mata gigitatchiyar tsawa "kimin shiru!!! wadda ya sata miƙewa tsaye ta rungumi Abba tana faɗin "kai ma yaya Aryan zaka dawo irin sa kenan? Mamaki ne ya kama Abba ita dai diyana ko zaa kashe ta bakin ta ba zai yi shiru ba ta wani gefen kuma albarka yake sa mata yau bakin ta yayi rana tun da sunji halin da hiyana ke chiki lallai ya zama dole a kai na a matsayina na uba na ɗau mataki chikin fushi Aryan ya tako ya kariso wajen da hannu ɗaya ya damko hannun ta ya jata suka nufi hanyar fita ko ajikin ta sai ma kallon sa da take tana faɗin "yaya Aryan ya naga da ka ɓata rai kafi kyau ne? Ba karamin dariya ta bawa su Abba ba wato ita batama damu da ɓacin ran nasa ba dogon numfashi Omar yaja kafin yace "tab wani abu sai soyayya idan ban da soyayya yadda yaya Aryan ya bata rai ɗin nan ai da yanzu ya tashi gidan nan da bom lallai yarinyar nan ta chiri tuta tun da har yaya Prince yace zai yi magana da ita awaya tab lallai samun irin ta akoi wahala" Haidar ne ya chaɓi zanchen da chewa "kai dai Omar bari ai wlh da da ne yaya Aryan ranshi ya ɓachi haka ai da gaba ɗaya gidan nan munji a jikin mu Sister fa tayi winning akan zafin zuchiyar yaya Aryan" "kai dalla ku mana shiru" chewar Ummi "miƙewa Abba yayi chike da ɓachin rai ya nufi bedroom nashi mikewa Ammi tayi chikin sauri ta bi bayan sa dan ita ma maganganu diyana sun ɗaga mata hankali duk tunanin ta yanzu Hiyana ta samu peace of mind a gidan Bgs amma ba komai za suyi maganin sa

Zaune bankin gado ta samu Abba gefen sa ta zauna chikin sanyin murya tace "ranka ya daɗe menene abun yi yanzu dan ka san dai maganar diyana gaskiya ne bata faɗen magana idan ba gaskiya ba" ɗago kai Abba yayi yana kallon ta ya fara magana "ni ba wanna ne damuwa ta ba babban damuwa yadda diyana tayi maganar bakiji me take faɗe bane ta tsani Safras bata son sa kuma sai ta chusawa hiyana tsanar sa" "bai kamata ka ɗauki zanchen diyana na chewa ta tsane sa da sauran su ba dan yarinya cen yanzu dai kamata yayi mu nemi mafita akan zaman hiyana da yaron nan" "no Aisha ni na san ya zaman su yake dan ba wani motsi na ƴaƴa na da ban sani ba ni damuwa na kalaman da diyana ta faɗa ne kin san fa fulanin daji basu iya tsanar abuba idan sukace miki basu son abu tofa tabbas basu sone kuma zasu iya yin komai dan suga sun rabu da wanna abun yanzu damuwa ta a nan kar diyana ta juyawa hiyana tunani dan shi Safras ya fara sauya wa yanzu haka maganar da nake miki ina da tabbacin yana son hiyana sai dai shi bai fahimci hakan ba ina gab da shirya masa wani tarko da shi da kan sa zai furta yana son ta to amma kalaman diyana sun kashemin hiki" "to menene abun kashe maka jiki kuma diyana fa yarinya ce kuma idan ka auna ka gani hiyana tana da hankali bazata ɗauki zanchen diyana ba" "aa Aisha ina raba ki kin san fa yaran nan suna matikar kaunar junan su to kinga ɗaya zata iya sadaukar da abun da take so domin ɗayan ke baki bibiyar sune shiya sanya bazaki gane abun da nake gudu ba wlh tsab hiyana zata iya hakura da Safras saboda diyana" shiru Ammi ta ɗan yi kafin tace "karka damu daga yau zan sanya Aryan ya dawo min da diyana domin na faro tarbiya daga farko diyana na bukatar abubuwa da yawa" shiru Abba yayi bai sake magana ba miƙewa Ammi tayi ta fice daga ɗakin Ammi na fita Abba ya gyara kwanciyar a saman gadon


A ɓangaren Aryan kuwa yana fita tare da diyana part na shi ya nufa kai tsaye a tsakiyar palon kasa ya tsaya tare da sakin hannun ta chikin fushi ya fara yi mata faɗa sai magana Bgs yake masa ta chikin wayar amma Aryan baya ji kasan chewar ya chire wayar daga kunnen sa katse kiran Bgs yayi ya sake kiran sa kamar ba zai ɗauki kiran ba dan ɓachin rai amma sai ya danne ya ɗaga kiran tare da manna wayar a kunnen sa "mika mata wayar" abun da Bgs ya faɗa kenan ba musu Aryan ya miƙa mata wayar ganin ransa ya ɓaci sosai ne ya sanya ta ansa wayar a kule ta fara magana zuba mata ido Aryan yayi yana kallon yadda take matana a nitse kamar ba ita ba kome Bgs ya faɗa mata oho sai gashi ta kwashe da dariya har da dukawa kasa shi dai Aryan ya zubawa sarautan Allah ido almost 30mins suka kwashe tana hira da Bgs tantama Aryan ya shiga yi anya ba da hiyana take magana ba dan Bgs ba zai tsaya yayi hira mai tsawo da diyana haka ba mutumin da magana ma wahala take masa kai ina akoi dai wani abu sai da diyana ta kwashe 1h tana magana da Bgs sanna sukayi sallama sai mamaki Aryan yake tana katse kiran ta tsugunna kasa tace "yaya Aryan kayi hakuri namaka alkawarin ba zan sake faɗin abun da baa tambaye ni ba kuma ko da an tambaye ni ma ba zan faɗa ba har sai ka bani izinin" Aryan ya rasa bakin magana tunani yake to wa'azi Bgs tayiwa diyana yasa ta sauya kome dan dai ya san halin diyana idan kace zata mata tsawa wlh bazata taɓa yimaka abun da kake so ba sai dai ma ta kara yi maka abun da baka so ɗin to me Bgs ya faɗa mata haka kai dole na san ya akayi irin wanna sauyi lokacin guda haka yau Bgs ya shafe 1h yana hira da mutun akoi alamar tambaya

ganin yayi shiru bai tan ka taba ya sanya ta miƙe ta rungume sa tana faɗin "yaya Aryan fushi kayi da ni" dawo da kallon sa yayi kan face nata ya rungumeta da kyau yana faɗin "aa my jidda akan me zan yi fushi da ke?" Hannun ta chusa chikin gashin kansa tace "to yaya Aryan muje yau ma na maka kitso" chikin sauri yace "aa kije wajen Ammi tana neman ki ni ma akoi in da zanje idan na dawo sai muje shan ice cream" murmushi tayi tare da sakin sa tana kokarin juyawa kara kankame ta yayi kasa kasa yace "my jidda tafiya zaki ba tare da kin bani hot kiss ba? Saukar da idon ta kasa tayi chike da jin kunya tace "yaya Aryan ni kam ban iya kiss ba" ɗaukan ta yayi chak suka haura sama


💋Duk Karfin Izzata 💋



💖The Talent Troupe Writer's 💖


💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*




Book 2

Page 27



saman katafaren gadon sa ya kwantar da ita tare da yi mata runfa da faffaɗar kirjin sa yana kokarin yin magana massage ta shigo wayar sa chikin jin haushi ya anshi wayar nasa daga hannun ta sakon Bgs ne murmushi ne ya kubche masa lokacin da yake karanta sakon "kai zaka kashe Cameran ɗakin ne ko dai zaka nunamin ka isa" kwafa Aryan yayi a fili yace "wlh ba zan kashe ba idan mutun ya isa yayi hakan da matar sa" "yaya Aryan kai da wa kake magana? Shafa kan ta yayi tare da ajiye wayar a saman bedside drawer yana faɗin "my jidda ba kowa ni da waya ta ne" zatayi magana ya ɗaura hannun sa saman lallausan lips nata yana faɗin "shiiiiiii" shiru tayi tana kallon sa hannu ya sanya ya rufe mata ido ya matso da fuskar sa dai dai sai tin nata face ɗin haɗe bakin su yayi waje guda ya fara bata hot kiss hannunta ta kewayo da shi ta saman bayan sa tana ɗan bubbuga shi alamar ya sake ta

da kyar ya iya zame bakin sa daga nata chikin sarkewar murya yace "my jidda menene kuma? Turo baki tayi tace "yaya Aryan ba kai ne kake danne min hanchina da wanan dogon hanchin naka ba idan kana min kiss bana numfashi ko kaɗan" jan dogon hanchin ta yayi yana faɗin "ni baby ma zan baki yau ba kiss ba" waro ido waje tayi kafin tace "kai yaya Aryan ni bana son baby yanzu sai hiyana ta samu baby sai ni ma ka bani" "aa my jidda ba yanzu hiyana zata samu baby ba sai gaba ni kuma yanzu nake son baby gaskiya" "waya ce maka ba yanzu zata samu baby ba ai yaya Prince ya...sai kuma tayi shiru bata karisa maganar ba "me ya faru my jidda me yaya Prince ɗin yace? Girgiza kai ta shigayi tana faɗin "yace kar na faɗa wa kowa kuma karna kuskura na sake faɗin abun da bai dace na faɗa ba"murmushi Aryan yayi tare juyo da ita ta dawo saman kirjin sa yana matikar farinciki ko ba komai Bgs ya ɗan sai ta masa jiddan sa tun da har tana iya danne magan bata faɗe lallai Bgs ba iya aikin soja ya iya ba har da aikin gyara mutane irin su diyana ko me ya faɗa mata oho kuma tun da tace bazata faɗa ba komai Aryan zai mata bazata taɓa faɗe ba

"My jidda nifa yanzu ki faɗa min sai yaushe zaki ansa baby" "sai yaya Prince ya sayawa hiyana baby tukun nan ni ma zan ansa" ɗago ido Aryan yayi yana kallon Cameran dake jikin kwan wutar ɗakin yana gararar Bgs lokacin Bgs baya ma wajen ya fita sabgan su tun sa yace Aryan ya kashe Cameran yaki sai shi ya fita ya shiga wani Aikin

rungumota yayi a jikin sa ya fara shafa ta suna yar hirar su mai daɗi da haka har barci ya ɗauke ta chikin dabara ya kwantar da ita ya miƙe cikin sauri ya nufi toilet a gurguje yayi wanka ya fito ya shirya zuwa gidan su zulaihat

bayan ya gama shirin sa tsab ya hauro saman gadon ya manna mata kiss a saman ɗan karamin bakin ta kasa kasa yace "ina matikar kaunar ki my jidda ina son ki fiye da yadda nake son kai na ya Allah ka kulamin da ita kara manna mata kiss yayi ji yake kamar ba zai iya fita ya bar ta ba ji yake kamar ya ɗauke ta su tafi tare amma sai ya daure ya sauko daga gadon har ya ɗauki wayar sa sai kuma ya fasa ya ajiye mata dan ya san ta da son buga game chire sim ɗin yayi ya ɗauko wata wayar daga chikin drawer mirro ya sanya sim ɗin ya fice daga ɗakin chikin sauri

Shi da Shahram kawai suka tafi gidan su zulaihat mota ɗaya suka ɗauka suna isa unguwar basu sha wahala ba suka gane gidan wani katafaren gida ne na alfarma horn ɗaya sukayi a bakin gate mai gadi ya wangale musu gate ɗin kasan chewar an san da zuwar su kallo ɗaya Aryan yayi wa gidan ya gane akoi tsaro sosai a gidan akoi manya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login