Showing 351001 words to 354000 words out of 363274 words

Chapter 118 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2555

kuka har da hawaye?" cikin kuka tace "Yaya Prince nima ina son in ga baby na an kwantar min da shi a nan, kaga babyn Lamrat kyakkyawa ne sosai mai kama da Diyana" rungumeta yayi yana faɗin "Karki damu ki ci-gaba da yi mana addu'a In Sha Allah, Allah zai bamu muma amma gobe zamuje muga dr kiyi shiru kinji" ya kai karshen maganar tare da sanya kyakkyawar hannun sa yana goge mata hawaye kwanciya tayi lamo a saman faffaɗar kirjin sa tana jin zafin rashin samun cikin ta gashi su Diyana duk sun kusa Haihuwa da haka har barci yayi awon gaba da ita. Shi ma bgs ɗin da tunanin rashin samun Haihuwar su barci ya ɗauke sa.

Washegari girjin su Aunty farida ya sauka gida ya kara cika sai murna suke fariciki wajen family nan baa magana a ranar da yamma sarki Abdullah wato Abbon Hajj Fateema ya iso shima da gaba ɗaya family sa tsabar farinciki Abbo kamar ya mai da su hiyana cikin sa dan murna haka Oumma ma taji daɗin ganin su barin ma su yaya Abdussalam murna awajen su ba'a magana sai murna suke.

After 1 week

Ranar suna yaron yaya Yusuf yaci sunan Bappa wato Ahmad wadda Abba da kan sa ya raɗawa yaron suna sunyi murna idan nace zan tsaya zayyana muku kyaututtukan da Lamrat da yaya Yusuf suka samu to sai mu kare book nan gaba ɗaya bamu kammala ba sun samu kyaututtuka ba na wasa ba dan shi bgs kyautan Company kayan sawa irin su jallabiya ya bawa baby yace a buɗe masa baby's Account ana zuba masa riba sarki Abdullah kuma ya bashi kyautan gokuna 10 su yaya Abdussalam dukkan su kyautan 1m suka bawa yaya Yusuf Aryan ya bawa Lamrat kyautan dankareriyar mota Roll-Royce boat Tail shi kuma Yusuf kyau tan kuɗi ya zuba masa a Account Abba da Uncle Aliyu kam na su kyau tan ma ba'a magana dan ya wuce tunanin mai tunan baby company guda aka buɗe masa a ɗakin sa na kayan sawar sa dan kayan sa sun cike ɗakin sa sosai. Duk in da Aunty farida zata je tana manne da baby kamar zata mai da cikin ta bata barin kowa ya ɗauka.

an sha shahalin bikin suna. Ranar da aka yi suna da safe da yamma Abba ya tara gaba ɗaya family a harabar gidan yasa aka zuba kujeru na alfarma kowa ya hallara nan Abba ya ciro kuɗi mai tarin yawa ba tare da ya kirgaba a gaban kowa ya miƙa wa Abbo yana faɗin "Sadakin Fateema ina son yanzu a ɗaura Aure" da fara'a Abbo ya amsa ya miƙa wa yaya Abdussalam san nan shima ya ciro kuɗi dayawa daga aljihun sa ya miƙa wa Abba yana faɗin "Sadakin Aisha ina nema wa Abdussalam Auren ta" a sukwane yaya Abdussalam ya ɗago kai yana tunanin wayace wa Abbo yana son ta kallon yaya Abdurahman yayi, Yayin shi ma yaya Abdurahman ɗin shi yake kallon ita kuwa Aisha yar Sadiq miƙewa tayi zata gudu Hiyana ta riko ta tana faɗin "ina zaki je" ɓuye fuska tayi a jikin Hiyana tana dariya kasa kasa.
Miƙa wa Ammi kuɗin sadakin Abba yayi yana faɗin "Ki miƙa wa mahaifiyar ta san nan ku tambayi yaran suna son junan su dan karmuyi abun da zamu yi dana sani" shi dai Abba yayi auren haɗi nasu Hiyana daga farko bai ji da daɗi ba shi yasa yanzu sai ya tambaya kafin ya yanke hukunci. A nitse Abbo yace "Abdussalam na san kana son Aisha amma zanso ka faɗa da bakin ka kowa yaji" kasa yaya Abdussalam yayi da kan sa kafin yace "Hakane Abbo tun randa muka shigo kasan nan naganta na fara son ta ban ɓoye mata ba na sanar da ita kuma ta anshi soyayyata muka fara soyayya da ita" "Alhadulillah Alhadulillah" Abba ya furta kafin ya kalli Aisha dake ta faman ɓoye fuska a jikin Hiyana yayi murmushi kafin yace "A'isha ina son ji daga bakin ki shin kina son shi ko kuwa?" kasa kasa tace "Eh Abba ina son shi" guntun tsaki bgs yaja a ransa yana faɗin "Ni gaskiya Abba ka takura min wallahi dama dan wan nan abun yasa ka taramu" yana son mikewa ya tafi amma yana tsoron ɓatawa Abba rai haka ya daure ya zauna ya sunkuyar da kan sa kasa tare da ciro wayar sa ya fara latsawa. Ci-gaba da magana Abba yayi "Yanzu Ahmad Omar ku kawo sadakin ku duk a nan zamu ɗaura auren ku tare dana su Aliyu shi kuma Haidar sai muje gidan su yarinyar ko? Sai lokacin bgs ya ɗagi kai a nitse yace "Omar kaje ka ɗauko kuɗi a ɗaki kazo ka bada sadakin naku na ɗau nauyin komai na bikin ku" da sauri Aryan yace "A'a ko yaushe kai kake ɗaukan nauyin komai ya taso a cikin mu gaskiya a wan nan karon kam ni zan ɗauka nauyin bikin nan Omar kaje drawer mirror ka ɗebo kuɗi ka kawo a biya sadakin naku san nan duk wani abun da za'a buƙata ka ɗauko kuɗi a ɗaki idan ma wayan can ba zasu isa ba ga ATM card na ku ciri abun da kuke bukata" ba karamin daɗi Sarki Abdullah yaji ba yana kara yaba wa haɗin kai irin na family Abba addu'a yake a ransa "Allah yasa shima nashi family su kasan ce haka masu haɗin kai da kaunar juna". Haka ko akayi Omar ya miƙe ya wuce ɗakin Aryan ya ɗibo kuɗi dayawa wadda shi kan shi bai san nawa ya ɗiba ya dawo ya miƙa wa Abba ansan kuɗin Abba yayi ya kalli Ammi san nan ya kasa kuɗi kashi biyu ya miƙa mata ɗaya yana faɗin "A matsayin Zainab da bata da kowa kin zama mahaifiyar ta daga yau ga sadakin yar ki" da fara'a Ammi ta ansa tana sa wa bikin albarka sauran kuɗi kuma Abba ya miƙa wa Yaya Bello yana faɗin "Already an riga an banu Hajjo so zamu ɗaura Auren a nan ga sadakin ta ka rike idan mun koma Nigeria sai muje kauye mu kai musu sadakin mu musu godiya" hannun biyu yaya Bello yasa ya ansa kuɗi yana sawa bikin Albarka. Shi dai uncle Aliyu mamaki ya hana shi magana ya kasa ganewa yana son tambaya ina Auren Hajj Fateema amma ba dama sai kawai yayi shiru ya zuba musu ido.

Nan family Abba da Abbo suka shaida ɗaurin Auren Aliyu Khalid saraki da matar sa Amina Abdullahi sai Abdussalam Abdullah da matar sa A'isha Omar Farooq sai Ahmad Usman saraki da matar sa Hajara Husaini sai Omar Abubakar saraki da matar sa Zainab Abubakar farinciki wajen Angwaye da Amare da family gaba ɗaya ba'a misaltawa Aunty farida uwar gayya bakin ta yaki rufuwa saboda farinciki sai Addu'o'i da fatan alkhari familys ke wa angwaye da amare. Da haka taro ya watse suna masu farinciki bgs shi ne first parson da ya fara barin wajen dan ya gaji yana jin Abba ya shafa fatihar Addu'ar tashi ya mike ya bar wajen daman kamar a kan kaya yake.

Haihuwar Lamrat da sati biyu yau Zahra ta tashi da nakuda mai zafi tun asuba ta farka daga barci ta fara yiwa yaya Khalid kuka yana cikin barci ya jiyo kukan ta a firgice ya farka tare da kunna wutar ɗakin can kasan gadon ya hangota tana juyi tana kuka a sukwane ya sauko ya kariso wajen ta ganin alamar nakuda take tun da yaga na Lamrat hakan yasa ya fita da sauri ya nufi part ɗin su Ammi tsabar rudewa yasa ya manta bai yi sallama ba ya faɗa bedroom na Ammi, Ammi na zaune tsakiyar gado idon ta biyu ga Lamrat da babyn ta a gefen ta suna barcin su cikin kwanciyar hankali ya sha ruwan mamakin ganin Ammi bata yi barci ba ganin ta haka sai yasa yaki faɗa mata meke tafe da shi ya danne yace "Ammi lafiya bakiyi barci ba?" da sauri Ammi tace "Kai nake jira dan nasan Zahra na gab yanayin dana ganta jiya ya hana ni barci bana son takura mukune yasa bance ka dawo min da ita nan ba" ta kai karshen maganar tare da mikewa tazo ta wuce sa ta fita ta nufi ɗakin Ummi abun mamaki itama Ummi zaune take tsakiyar gado ta kasa barci ga Ayaam a gefen ta yana barci ganin Ammi yasa ta miƙe tana faɗin "Auta na nakuda ko ai daman na san hakan zata iya faruwa dan yanda na ganta jiya da daddaren nan ban tuna zata kai yanzu bama bata Haihu ba" ta kai karshen maganar tare da dirowa daga gadon. A tare suka nufi waje suka wuce part ɗin Khalid.
Nan suka isko shi har ya dawo ɗaki ya rungume Auta yana ta mata sannu kallon Ammi Ummi tayi kafin tace "To oga bamu waje" da sauri ya ɗago kai yana faɗin "Ammi mu wuce Asibiti ko?" Karisowa wajen su Ammi suka yi dai dai lokacin baby ya kawo kai ihu Zahra ta fasa ta ƙanƙame Khalid dake kokarin tashi, shi bai san ihun me take ba a tunanin sa tana ihun karya tafine dan haka sai ya koma ya rungumeta yana faɗin "Sorry Auta" da sauri su Ammi su anshe ta daga hannun sa Ummi na faɗin "Ka bamu waje" miƙewa yayi ya fice da sauri ya nufi part ɗin bgs. A nan Zahra ta haifo ɗan ta namiji kato da shi kyakkyawan gaske fari tas kamar Bature kaman sa ɗaya da Khalid Ammi da Ummi su suka mata komai suka gyara ta ita da baby kafin gari yayi haske sun yi iya dube duben su a matsayin su na iyaye sai da suka tabbatar da Zahra da babyn ta dukkan su lafiya lou san nan suka wuce da Zahra bedroom ɗin Ummi. Sai da safe family suka samu labari Abba yayi murna over yau ga jinin autar sa da Khalid wow murna awajen family nan ba'a magana. Ranar suna yaro yaci sunan Bappa Usman wato babab su yaya Khalid suna kiran sa da khalifa nan Abba yace to su tattara su koma Ammi tace aa idan ma zasu koma to sai dai su koma da Diyana dan cikin tan nan ya girma ya kusa shiga watan Haihuwa yanzu cikin 8 month 2 weeks nan fa Aryan ya kafe yace aa a nan itama zata Haihu sai dai su Abba su kara koda wata ɗaya ne suma su ɗan huta da farko Abba yaki amma da bgs yasa baki sai Abba ya hakura akan zasu kara 1 month amma zasu je saudiya ɗaurin Auren Haidar tukun nan su dawo bgs bai ce komai ba sai ma basu jet ɗin sa da yayi aka kai su.
Gaba ɗaya mazan sun je ɗaurin Auren Haidar amma ban da bgs shi ɗai ne bai je ba yaki zuwa a mata kuma Ummi ita da Aunty farida da Hajj Fateema suka je suka bar Ammi da kula da masu jego wato Zahra da Lamrat da yanzu ta kusa gama wanka.

Kwana biyu suka yi aka ɗaura aure suka dawo da Fariza amarya a nan yaya Abdurahman ya samu wata balarabiya mai suna Samha shima a ka haɗa auren sa da Haidar akayi Abba ya musu waliyi aka ɗaura aure suka juyo Us da amaren su. Sai farinciki family Abba da Abbo suke ita dai Hiyana kullun sai ta ɓuya tayi kukan rashin Haihuwa yanzu sun shiga shekara na biyu kenan da aure duk da cewa da farko basu yi zaman daɗi da Bgs ɗin ba, sun je wajen dr yace dukkan su lafiyan su kalau Allah ne kawai bai kawo lokacin Haihuwar ba shi kan sa bgs yana damuwa sosai dan yana bala'i son yara yana son ganin jinin sa shima.

After 3 week

Labour room

Tun karfe 1 na dare Diyana ta fara nakuda gaba ɗaya family suka wuce hospital da ita banda wayan da ke jego an barsu a gida da Aunty mardiya tun 1 na dare take nakuda amma har karfe 3:30am bata Haihu ba Aryan ya shiga tashin hankali da bai taɓa shiga ba, ba shi kaɗai ba har bgs ya shiga damuwan ganin halin da Aryan da Diyana ke cikin. bgs Aryan Fahad Khalid Yusuf ango Ahmad yaya Abdussalam yaya Abdurahman suna tsaye daga ɗan nesa da labour room ɗin su Ammi kuma suna tsaye a bakin labour room ɗin Ummi Ammi Aunty salma Aunty farida Hajj Fateema Oumman Hajj Fateema Innar yaya Bello sai Hiyana da ta kafe sai ta biyo su dukka matan dai suna tsaye a bakin Labour room ɗin suna jiyo ihun da Diyana ke yi tana ɗurawa yaya Aryan zagi kasan cewar su Aryan suna ɗan nesa da labour room ɗin shi yasa basa jiyota.
Shi dai Aryan ya kasa jurewa gani yake kamar likitocin nan basu san aikin su ba cikin zafin nama ya nufi labour room ɗin su Ammi nace masa ina zaka je bai bi ta kan kowa ba ya buɗe kofar Labour room ɗin ya shiga ya rufo kofar. Ba shiri yaja birki a tsakiyar ɗakin jin irin zagin da Diyana ke masa tana kuka tana faɗin "Wayyo zan mutu yaya Aryan ka cuceni wlh Allah ya isana Ammi na kizo ki taimake ni yaya Aryan bakin mugu azzalumi kamin ciki ka barni da azaba har da yau darata kace min Haihuwa ba'a mutuwa to gashi yanzu zan mutu shi yasa tun farko nace ban son cikin nan bakin mugu kace min ba komai ba zan mutu ba yanzu gashi nan zan mutu na bar su Hiyana wayyo Allah jinina ya kusa kare wa shike nan na mutu na lalace Abba na wlh ban son ƴaƴan, sun ci uwar su suma ƴaƴan ni wlh rayuwata nake so wayyo Allah Hiyana ta" ba yadda doctors ɗin nan basuyi ba akan tayi shiru amma taki sai fama suke taki yin shiru a fusace ɗaya daga cikin su ta ɗaga hannu zata buge mata baki ko zata yi shiru cikin zafin nama Aryan ya kari waje rai a bace ya rike hannun dr cikin tsawa yace "Ku matsa min awajen nan baku san aikin ku ba ke kuma da kinyi kuskuren marinta da baki sake marin wata ba a rayuwar ki" ya kai karshen maganar tare da yin wurgi da hannun Dr ya sanya hannun sa ya tallabo kan Diyana idon ta a rufe cikin masifa tana kuka tace "Wayyo Allah yaya Aryan ya gama cutata ni gashi yanzu zan mutu shi kuma ko ajikin sa zai iya kara Auren sa ma wayyo Allah Ammi na innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allahumma innni a uzubika minal kubsi walka ba isi" Aunty farida dake tsaye awajen suna jiyo Diyana basu san lokacin da dariya ya kubce mata ba su Diyana anji wuya har da addu'ar shiga bayi ita kuwa Ammi idon ta ya cika tab da kwallah tana tausayin Diyana.

Wani ihu Diyana ta saki tare da yin nishi mai karfi sai ga baby boy ya faɗo cikin sauri dr ɗin suka dawo kanta suka ɗauki baby suna kokarin yanke masa cibiya sai kuma me? sai ga Diyana ta fara sabon murkusoso tana juyi ta fara sabon kuka kallon dr Aryan yayi yace "Me kuma ke damun ta" dr tana kokarin yanke wa jariri cibiya tace "Ai Twins ne a cikin ta yanzu nakudan na biyu zata fara" waro ido waje Aryan yayi yana kokarin yin magana Diyana ta katse sa cikin ihu tace "Wallahi bana son baby kuyiwa Allah ku cire min na baku shi kyauta na mutu na shiga uku wallahi bana so na yafe baby dan Allah kuce kar ya fito ya zauna a ciki ni bana son shi" cikin muryan rarrashe Aryan yace "My jidda kiyi hakuri kunji? Yanzu zaki haihu" kamar jira take daman taji muryan Aryan nan ta kara ihu tana faɗin "Bakin mugu da ka gama yi min mugunta shine zaka ce nayi shiru yanzu ko bakin azzalumi wallahi ba zan ya fe maka ba ko na mutu sai na ɗau fansa ka rabu da ni na tsane ka Allah ya is... Bata kai karshen magana ba ya rufe mata baki yana mai tausaya mata dan shi duk wanna surutu da take basa shiga kunnen sa da kyau tausayin halin da take ciki kawai yake. Da iya karfin ta ta cire hannun sa daga bakin ta tana kokarin mikewa Doctors ɗin suka danne ta dan karta kashe baby dake neman hanyar fitowa runtse ido Aryan yayi yana jin zuciyar sa kamar zata fashe ta fito waje ihu ta fara mai tarwatsa kwakwalwa ta cigaba da surutan ta.

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu












[8/23, 10:58 AM] Maman Aslam: 💋Duk Karfin izzata 💋




By
Star Lady


Page 64


.....dafe kai Aryan yayi yana karanto mata addua'o'i yana tofa mata Dr dai yau sun ga abun mamaki duk da basu san wanene yaya Aryan da take kira ba kuma basa jin hausa amma sun fahimci zagi take kuma tabbas Aryan da ya rike ta shi ne Aryan da take zagi sun sha ruwan mamaki kuma sun yabawa kokari irin na Aryan in da wani ne daga cikin su turawa ai bata isa ba. Haka ta rinƙa ihu dr suka danne ta har Allah yasa ta haifi yaro ɗayan. Yaron na faɗowa ta saki jikin ta ta koma ta kwanta tayi shiru still idon ta a rufe cike da zolaya Dr tace "Oga saura baby ɗaya fa" waro idon sosai Aryan yayi zai yi magana ɗayan Dr tayi saurin cewa "Sorry Oga it's a joke" kallon face ɗin Diyana yayi sai yaga alamar tayi barci a hankali ya mai da kan ta ya kwantar saman gadon yana sauke ajiyar zuciya ya ɗago kai ya zubawa baby's ɗin dake hannun Dr suna gyara


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login