Showing 132001 words to 135000 words out of 363274 words

Chapter 45 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2570

dan ba zai zauna damu waje ɗaya ba, shi ma Yusuf transfer zan masa ya koma, Us ko India duk kansu bazasu zauna kusa damu da mata a gefen suba"

"Gaskiya ko ni nayiwa Auta murna da samun Khalid a matsayin miji, chewar Aryan dake tsaye a bakin kofar toilet ɗaure da towel a ƙugun sa. Wani hararar Bgs ya wurga masa tare da miƙewa yace "idan ka gama shiri ka same ni awajen Ahmad, yana gama faɗin hakan yayi waje Aryan kuma ya juya ya koma chikin toilet

AUNTY AMARYA

Zaune take saman sofa mai zama mutun biyu tana waya da Aunty Maryam, yaya Umar da yaya Haidar suna zaune a gefen ta saman sofa mai zaman mutun 3, da gudu wata bigaggiyar budurwa ta shigo ko sallama babu tana sanye chikin wasu shaggun riga da wando, wadda kana iya ganin komai na tsurar jikinta, ta zuba gashin doki akai kamar wata aljana, ga wani dogayen gashin ido da ta sanya yarinyar tana da kyau ba laifi farache sosai amma farin mai ne, a shekara bazata wuche 21 year's ba

....... Da gudu ta tafi ta faɗa jikin Aunty amarya tana dariya "ke zulaihat menen hakan karyani kike so ki yi koh"? Chewar Aunty amarya "haba momy yanzu ni ɗin che zan karyaki ki ganni fa ko kiba bani dashi" "eh to naji yanzu dai ɗaga ni" "gaskiya aa mommy ni wlh a jikin ki nake son kwanchiya wani tsawa Umar ya daka mata wadda yasa sa ta miƙewa tsaye ba shiri "ke!! bazaki tashi ba"
"Haba Umar baka ganin yarinya che, wan nan irin tsawa haka ai ba ita kaɗai ka tsorata ba har dani" chewar Aunty amarya, miƙewa Umar yayi a fusache ya nufi waje

da sauri haidar ma ya miƙe ya bi bayan sa

"Maryan ki bari zamuyi waya anjima" chewar Aunty amarya batare da tajira amsar Aunty Maryam ba ta katse kiran ta ajiye wayar a gefe, san nan ta dawo da kallonta kan zulaihat dake tsaye tana taunan chingum.

"Dawo kiyi zaman ki my zulee kyale su Umar ɗin nan" "Allah mommy wan nan Umar ɗin bai da kirki ai naso na che masa bazan tashi ba, sai kuma na kyalesa" "kai zulaihat yayan naki zakiwa rashin kunya? "Aa mommy wlh Umar ba yaya na bane dan fa bai girme min ba, mommy na tace tare aka haife mu"
"Kai zulaihat aiko Umar ya baki shekara 4 dan yanzu wata uku ya rage masa ya chika 25 years" "to nidai mommy koma me gaskiya ba zan bari wani a chikin gidan nan ya takani ba, Ni mommy ina mijin nawa ma yake? Inane ɗakin sa naje na ganshi?

"A lallai zulaihat na yarda baki da hankalin kin san wanene muke son haɗa ku kuwa Bgs Brigadier General Safras, kuma prince yarima mai jiran gado shine mai rike da babban mukami na soja gaba ɗaya bayan mukamin sa ba wani mukami kuma duk wani soja da kike gani a duniyar nan to a karkashin Brigadier General yake, sai dai kowani kasa da nasu, ke bama shiba wlh ina rabaki da matasan gidan nan kibi kowa a sannu idan ba haka ba wlh inaga gawar kima zatayi wuyar ganewa kin dai ji na faɗa miki, yanzu ki wuche ɗakin tsakiyar nan kije kiyi wanka dan lokachin chin abin chin rana ya kusa, kiyi sauri inason in gaba tar dake wa kowa"

Shiru zulaihat tayi tana tunani "hmmm lallai wato masu girman kai ko to wlh nine nan zan gyara musu zama, ba Brigadier General Safras ba koma taɓa samane zanyi maganin sa, ni da na juya manyan manyan maza masu faɗa aji a kasar nan ma bare shi ɗan karami kwaro, ni wlh ba dan ma yana da kyau ba me zanyi dashi, kyau nashi ne kaɗai ke burgeni da kuma kirar jikin sa irin na jaruman maza ko in che sadaukin yaki amma ba komai zan dawo dasu kan saiti" ganin zulaihat tayi shiru alamar ta tafi duniyar tunani ne yasa Aunty amarya ta miƙe ta dafa kafaɗar ta tace

"Zulaihat kar kiji tsoro fa dan nache maki shi Brigadier General ne mubi komai a sannu In Sha Allah zai soki kuma zai Aure ki, kinji" dawo da kallonta zulaihat tayi kan Aunty amarya san nan ta sheke da wani shu umin dariya tana faɗin "haba mommy karki damu nifa ba wani tsoron da naji yanzu dai bari naje nayi wankan" tana gama faɗin hakan ta ɗauki jakar ta ta wuche ɗaki, binta da kallo Aunty Amarya tayi har ta shiga ɗakin, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauke kafin tace "lallai zulaihat idan bakiyi hankali ba zaki koma da karyayyen kafa ko kuma daga nan ki wuche gadon asibiti dan na lura kan ki na rawa sosai, kuma kan naki ma ya rasa aina zai yi rawa sai a gidan Alhaji Abubakar Saraki gidan da yake da tarin matasa har rai 9 chikin su akoi manya manyan sojoji ga manyan likitoci, lauya engineer saurauta mulki dukka, hmmmm gaskiya rawan kan nan naki bai miki adalci ba, to Allah dai yasa ki wanye da kowa lfy, tana kai karshen maganar ta miƙe ta nufi ɗakin ta

Washe gari

Maiduguri

Zaune take a chikin Class nasu tayi shiru tana kallon kasa kamar mai tunani sauran students sai surutu suke.

buga belt ɗin fita breakfast da akayi ne yasa students ɗin su kayi ihu da karfi suka fara tururuwan fita waje.

gaba ɗaya kowa ya fice daga class ɗin sunyi waje dan zuwa yin breakfast saura diyana da wata yarinya dake zaune a kujerar bayan ta, chikin nutsuwa diyana ta miƙe tanufi hanyar fita har ta kai bakin kofar fita sai kuma ta dakata ta juyo tana kallon tarinyar dake zaune chikin Class ɗin, kallo ɗaya tayiwa yarinyar ta gane akoi damuwa atattare da yarinyar sosai, juyowa tayi ta dawo chikin Class ɗin kusa da yarinyar taje ta zauna chikin sanyin murya ta fara magana

"Sannun ki sunana diyana kefa" chikin sanyin murya itama yarinyar tace "Sunana Zainab" "wow amma Zainab me yasa ko da yaushe idan muka fita breakfast ke kike zama a class baki fita ko ina? "Babu komai Aunty diyana kawai Ni ban san me zan fita nayi awajen bane saboda ni bana zuwa da abinchi kuma ba'a bani kuɗin break"
"To Zainab me yasa baa baki kuɗin break ɗin? ko me yasa ba'a baki abin chi a gidan basu ganin har karfe 3 muke tashine?da baza su rinƙa baki abinchi ba, basa tunanin zaki ji yinwa? "Aunty diyana Ni fa bani da mama awajen matar babana nake shiyasa ita kuma bata bani abin chi kuma daddy na yana bani kuɗin break ai, amma Aunty na ɗin tache idan na sayi wani abu da shi sai ta kasheni sai dai na ajiye kuɗin na mai da mata" wani dogon tsaki diyana taja kafin tace "zanchen banza ke bazaki sanar da daddyn na kuba, to ina maman na ki take ko ta rasune? "Aa bata rasu ba tana raye rabuwa kawai sukayi da daddy na"
"Eyya to shike nan yanzu dai muje muyi break tare kuma daga yau tare zamuna chin abinchi na, kin zama friend ɗina kinji, ta karisa maganar tana miƙawa Zainab ɗin hannu, hannu Zainab ta bata suka gaisa san nan suka miƙe atare sukayi waje

Da mamaki yan class nasu kai gaba ɗaya yan school ɗin ke bin su diyana da ido mamaki suke yanzu duk jan aji da iyayi irin na diyana bata kula kowa a school ɗin nan shine zata kula wanchan kazamar Zainab ɗin, ita kuwa diyana bata ma san sunayi ba dan basa gaban ta daman ba ta yiwa kowa magana a school ɗin rike da hannun juna suke har suka isa wajen chin abinchin school ɗin.


KANO


Aban garen su hiyana kuwa

Kamar kullun ta fito daga class nasu kan ta na mata matsanan chin chiwo, ta nufi class nasu Zahra a hankali take tafiya kamar bata son taka kasa "ke ina zakije zo nan, chewar jabir dake tsaye a bakin kofar Class nasu" chikin sanyin murya hiyana tace "kayi hakuri jabir wlh yau kai na namin chiwo sosai bana son jin surutu ko kaɗan yanzu ma zanje na kira Zahra ne tazo ta rakani office na Hm, saboda ya saka a mai dani gida" chikin tsawa jabir yace "ke!! ni kike chewa baki son surutu na!? wato ma surutu kika ɗauki magana ta ko? Shiru hiyana tayi bata che komai ba "to ki wuche mutafi yau wlh har atashi muna tare kuma ke zakimin hira yau ni kuma in zauna shiru ina sauraron ki "gaskiya jabir ba zanje ba saboda bazan iya magana ba, ko ina da lfy ni ban iya surutu ba bare kuma yanzu da bani da lfy" a fusache jabir ya damko hannun ta ya fara jan ta da nufin sutafi

A zuchiye hiyana ta ɗaga hannu ta sharara masa mari chikin tsawa tace "idan ka sake taɓa jikina wlh duk abun da na maka kai kaja" a zafafe jabir ya ɗaga hannu zai zabga bama mari charab yaji daga baya an rike hannun sa, a fusache ya juyo da karfi ganin.....✍️


Amin afuwa bana update ranar Sunday amma na muku yau ba yawa dai, ina busy sosai ne sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu akoi fa chakwakiya



💖NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)



More comments an share
*💫STAR LADY💫*34

💖The Talent Troupe Writer's 💖


*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*


Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai



*Episode 3️⃣7️⃣*




........A fusache jabir ya juyo da niyar yayiwa wadda ya riƙe masa hannu rashin mutunchi, wani haɗaɗen guy idon sa yayi tozali dashi, ya haɗu iya haɗuwa sosai ga green eyes nashi sai kyalli yake saboda ya zaro su waje sosai akan wayar sa,ya riƙe hannun jabir da hannun sa ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma yana rike da waya yana latsawa da alama wani sakon yake turawa, sai dai kash duk wannan haduwar tashi fuskar nan tasa babu annuri ko kaɗan babu alamar dariya fuskar aɗaure take tam kamar hadiri,sauko da kallon sa jabir yayi izuwa kan surar jikin guy ɗin dogone sosai ga faffaɗar kirji, ɗamtsen hannun san nan kamar zasu fasa riga saboda chika dam dam da sukayi,ga wani lallausan bakin gashin mai kyau da sheki a kansa wadda ya tara ya ɗure a baya ya zuba jelar gashin nashi har tsakiyar baya, kallo ɗaya zaka masa kasan ya karɓi horar wan sojoji sosai.

A hankali hiyana ta ɗago blue eyes nata ta sauke a kan guy ɗin,chikin tsoro da tashin hankali har lips nata na kerma, a hankali ta mutsa lips nata ta furta yaya prince kuma a school namu ko me ya kawosa? Bata gama rufe bakin ba, Bgs ya murɗe hannun jabir da karfi ta baya ji kake kas, kas, kashin ta balle, a guje hiyana ta juya ta bar wajen dan kar ya gama da jabir ya juyo ya haɗa da ita.

Wani gigitachen ihun azaba Jabir ya saki, bai gama ihun nasa ba Bgs ya sauke masa wani wawan nushi a gefen chiki nan take jabir ba ɗauke dif kamar an ɗauke wuta nepa alamar ya suma, sakin sa Bgs yayi ya zube kasa wanwar tsallake ta kansa yayi wuche ya nufi office ɗin Hm, da sauri rundunar jibga jibgan sojojin sa suka rufa masa baya.

gaba ɗaya jama'ar dake waje daga kan malamai har ɗalibai, kowa murna yake da bugun da Bgs ɗin yawa jabir.

Bgs

Yana kokarin shiga office na Hm shi kuma Hm na kokarin fitowa karo sukayi Hm yayi baya kamar zai faɗi, da kyar ya iya sai ta tsayuwar sa, Bgs kuwa yana tsaye kamar wani sadaukin yaki ko motsi bai yiba "sorry sir ban san kana shigowa bane chewar Hm

Bgs dai bai tankashi ba sai ma raɓawa yayi ta gefen sa ya wuche chikin office ɗin saman sofa ya zauna jibga jibgan sojojin 4 ne suka bishi chikin office ɗin hannun su ɗauke da manya manyan bindigu (gun) suka tsaya a kanshi suna bashi tsaro,sauran Sojojin kuma suka tsaya a bakin kofar shigowa

"Sir naji ka bugi wani awaje me ya haɗa ku? Hm ya tambaya yana ƙarisowa chikin office ɗin, dogon tsaki Bgs yaja kanfi yace "kawai naga zai bugi wata yarinya ne shiyasa na bugeshi dan na lura bai da hankali bai san me yake ba" "to wan to kuma wace yarin yace kuma wani yaro ne!? Hm ya tambaya yana kokarin zama a kujera "kai Ni ban sani ba domin duk kansu daga yaron har yatinyar ban ga fuskar ko ɗaya daga chikin suba, ni ba shine ya kawo niba, Abba ne ya aiko Ni, ya karisa maganar yana ya mutse fuska

tunani Hm ya shigayi "ko wani mai karan kwanne yau kuma ya haɗu da Bgs domin ina da tabbacin duk wan da Bgs ya buga to fa in bai mutu ba zai yi fama da doguwar jinya ko da ya tashi kuma ba lallai ya koma kamar da ba.

"Yallaboi Abba yace na karɓawa su Zahra transfer later, da sauri Hm ya ɗago ido yana kallan Bgs chikin rawar murya ya fara magana "lfy Abba yake son chan zawa su Zahra school? Mikewa tsaye Bgs yayi yana faɗin "Ni ma ban sani ba idan ka gama ka bawa Abdol later ya kawo min ina mota yana kai karshen maganar ya fice daga office ɗin.

Yana fita jibga jibgan sojojin sa masu ji da karfi da lfy kallo ɗaya zaka musu kasan sun samu training mai kyau suka rufa masa baya

Daga malamai har students din dukka kallon Bgs da tawagar sa suke kowan nan su tambayar kan sa yake wanene wan nan? Ko dai ɗan shugaban kasan American ne, dan wan nan bai yi gama da ɗan naija ba, awani ban garen kuma murna students keyi an musu maganin jabir yau dai kam an samu wadda ya tanka shi har ma ya sumar dashi, bangaren yan matan school ɗin kuwa kowanche mutuwa take akan Bgs da bai ma san sunayi ba, ko wacce fatan samun sa amatsayin miji take ba karamin rikitasu kyan shi yayi ba

Taku yake irin na manyan jarumai har suka kai in da sukayi parking motochin su da gudu wani matashin soja ya sha gaban sa ya buɗe masa kofar motar, shiga yayi ya zauna ya zuro kafafun sa waje ya sunkuyar da kai kasa yana latsa waya, da alama jiran Abdol suke



Aɓangaren hiyana kuwa

Da gudu ta nufi class ɗin su Zahra sai numfashi take sama sama, Zahra na ganin ta ta miƙe ta nufeta tana faɗin "hiyana lfy kike numfashi haka!? Me ya saki gudu kuma!? "Aunty Zahra yaya prince a school namu kuma ina da tabbachin ya bugi jabir" waro fararen manya manyan ido ta Zahra tayi ta dafe kirji chikin tsoro tace "mun shiga uku hiyana me kuma ya haɗa shi da jabir!? Allah yasa dai ma bai kashe shiba ya tsaya a iya bugu" "wlh Aunty Zahra ai jabir dinne ya rikemin hannu ni kuma na mare shi, shima ya ɗaga hannu zai rama kenan sai yaya prince ya rike hannun sa"
"Wayyo hiyana munshiga uku yanzu kina nufi a akan ki yaya prince ya bugi jabir!? Kuma ya ganki yasan dake jabir yake faɗan!? "Aa Aunty Zahra bai ganni ba domin lokachin da ya riƙe hannun jabir ɗin latsa wayar sa yake da alama wani sako yake turawa shiyasa ai na gudu dan karya ganni, yace nima zai hukun tani dama ni kam ya tsane Ni" ta karisa maganar kamar zatayi kuka rungumeta Zahra tayi tana faɗin "ki dena chewa ya tsaneki kin ji Allah yaya prince bai tsane ki ba kawai shi dai haka halinsa yake ne"

"Wai ma me ya fito dake daga Class naku ne? Har kika haɗu da jabir ɗin" "daman kai nane yake min chiwo nache bari nazo ki rakani office na Hm dan yasa amai dani gida ina tafiya a hanya ya tareni" "to shike nan yanzu muje wajen Hm ɗin sai amai dake gida koh?

"Kai Aunty Zahra ni wlh idan ki kaga na fita daga class nan to sai naji fitar motochin su yaya prince daga school nan kuma ma ai kan ya warke ya daina yimini chiwo" dariya Zahra tayi tare da raba jikin su tace "kai hiyana sarkin tsoro In Sha Allah ke che zaki zama matar yaya prince ɗin nan sai naga karshen tsoron" "dan Allah Aunty Zahra ki dai na yimini mugun fata kinji wlh ko da wasa naji an kira sunan shi ji nake zuchiya ta na bugawa da karfi" hannu ta Zahra ta riƙe suka koma wajen zaman ta suka zauna suna yar hiran su, yammatan class ɗin sai kallon su suke, kamar wasu tagwaye domin kamin nin Zahra sak yaya prince haka itama hiyana kamannin ta ɗaya da shi shiyasa suke kamar ta gwaye gashi yanayin jikin su ɗaya yan sirara sai dai hiyana ta ɗara Zahra tsawo kaɗan, Zahra kuma ta girmi hiyana da shekara 1.

Maiduguri

Kyau iya kyau diyana tayi kyau har ta gaji da kyau idan ka ganta zaka che yarinyar nan da madara take wanka saboda sabulan da Aunty farida ta haɗa mata ba karamin gyara ta yayi ba gata da iya ɗaukan wanka da make up ta chanza sosai ta kara haske fatar ta tayi luwai luwai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login