Showing 267001 words to 270000 words out of 363274 words
nama ya shigo wajen kafin suyi wani yunkuri ya harbe su dukkan su ba wanda ya harba a in da zasu mutu dan yana bukatar su a raye,
wucewa Yusuf dake bayan sa yayi ya kwance Zahra sanna ya ɗaure jabir da igiyar da ya kwance Zahra
Da gudu Zahra ta tafi ta faɗa masan faffaɗar kirjin bgs tana kuka tana faɗin "yaya Prince wasu ne suka tafi da Aunty hiyana da yaya Khalid" yasar da gun ɗin hannun sa yayi ya rungumeta ta kyau tare da shafa bayan ta
da kyar ya iya buɗe bakin sa cikin matsanancin bacin rai kasa kasa yace "zaki iya gane fuskar ɗaya daga cikin su? girgiza masa kai tayi kafin tace "aa" ɗaukan ta yayi chak tare da yiwa Yusuf umarni akan su kwashe mutanen nan su kai su headquarter zai wai waye su,yana kai karshen maganar ya fice ɗauke da Zahra a kafaɗar sa
Suna shiga cikin mota ya ɗauki wayar sa ya fara kiran layin Aryan bugu ɗaya Aryan ya ɗaga yana faɗin "hello" "Aryan ka sanar da security kar wanda ya sake fita ko shiga gida ba tare da izini na ba" yana gama faɗin hakan ya katse kiran ya tada motar da kan sa da gudu suka bar wajen
"Me ya haɗaki da yaron nan da ya kamaki? Sanna me ya rabaku da su Khalid bayan Yusuf yace min tare kuka fita!? Kallon in da yake tayi kamar zatayi kuka ta fara magana "muna tafiya ne wasu suka tare mu suka ɗauki hiyana da yaya Khalid suka barni ni kaɗai shine ina tafiya shikuma jabir yazo ya kamani"
"Wanene shi jabir ɗin? Ai na kika sanshi? dan haka kawai dai bazai kama ki ba" "a makarantar mu na san shi shine wan da ka taɓa mari lakacin da yazo zai mari hiyana ka riƙe hannun sa ka buge sa har ya suma" a sukwane bgs ya taka birki motar har sai da kai zahra ya bugu da marfin motar "what are you saying!?" zaro ido waje Zahra tayi ta sake mai mai ta masa maganar da tayi da sauri ya fito da wayar sa ya fara kiran layin Yusuf
Bugu ɗaya Yusuf ya ɗauka "kai Yusuf kuyi sauri ku bar wajen wannan yaron wanna mutumin da muke nema ne ina da tabbacin uban sa zaizo kuyi saurin barin wajen" daga ɗayan ɓangaren Yusuf yace "to ko dai mu watsa sojojin awajen idan yazo sai mu kamashi" "no Yusuf ai ba zan taɓa zuwa wajen ba abun da ya sa nace maka zaizo,zaizo wajen mu neman ɗan sa dai amma ba zaizo wacan gidan ba matikar yasan munje gidan kuyi sauri kubar wajen ne dan kunga ba ku fito da kayan yaki sosai ba zai iya aiko muku da mutanen sa,yanzun nan ku kawomin yaron nasa gida zanyi magana da shi thank God da ban kashe shi ba wlh saura kaɗan daman na harbe sa a kirji,sai kuma na fasa kuyi sauri kwashe su" "okey"Yusuf yace tare da katse kiran.
Ta da motar yayi da gudu suka bar wajen cikin kankanin lokaci suka isa gida,
kai tsaye part nashi ya nufa da Zahra suna tafiya yana faɗin "karki kuskura ki fito daga Part na dan kina fitowa hankalin su Ammi zai tashi zasu gane me ake ciki dan haka kiyi zaman ki har sai na dawo da su Khalid" "to" kawai tace
Suna shiga part ɗin ya nuna mata ɗakin hiyana shi kuma ya wuce wajen binciken sa ya fara tikan aiki
Da sallama Aryan ya shigo ɗakin kallon ɗaya yayiwa bgs ya fahimci yana cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa kusa da shi Aryan yazo ya tsaya
Ba karamin tashin hankali ya shiga ba lokacin da idon sa ya sauka kan desktop dake gaban bgs a sukwane yayi baya yana faɗin "what!? Me ido na yake gani haka Khalid sister to tayaya suka fita gidan nan ba tare da sojoji ba? Inannalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunallahu waniimal wakil" sai lokacin bgs ya juyo
kallon Aryan yayi da kyau kafin yace "Aryan komai ya kwaɓe na bibiyi na'uran jikin Khalid ya nuna min disconnected amma yana nunamin a hanyar abuja aka kashe na'uran ita kuma sister na yi kokarin tracking nata sai ya nunamin location na ɗaki na da alama ba ta tafi da shi ba kenan" durkushewa Aryan yayi awajen ya dafe sai tin zuciyar sa yana faɗin "innalillahi mu muka aikata laifi amma wayan da zasu karɓi hukunci daban wai yanzu ma ta ina zamu fara neman su?" Jin magana Aryan ya sanya bgs yace "muje Aryan" yana kai karshen maganar ya fice da sauri da sauri Aryan ya miƙe ya rufa masa baya
Kai tsaye wajen da aka kama su hiyana sukaje Aryan yana kokarin rufe kofar motar nasu a sukwane bgs yace "no karka taɓa komai domin ina da tabbacin wayan da suka kama su su suka buɗe kofar motar nan nasu" fasa rufe kofar motar Aryan yayi suka fara kewaye awajen suna dubawa
"Amma bgs me ya sanya baka duba nauran cikin jikin Khalid ba!?" Aryan ya jefo masa mubaya ba tare da ya kalli sa ba yace "No na duba kasan shi da network yake aiki to in da suka kai su babu network na waya sai dai na salulan mai aiki da tauraro ɗan adam hakan ya tabbatar min cikin manyan makiya nane ba karamin mutun bane ya kama su Khalid, ya katse duk wata hanya da zanɓi in same su ni abun da ya fi ɗaure min kai ma ya akayi suka san sister? Wannan ne dalilin da ya sanya bana son wata mace ta raɓeni, yanzu gashi bata san komai ba laifi na ya shafe ta" "amma bgs ya akayi suka san cewa kana da alaka da sister? dan haka kawai ba zasu kamata ba,Sannan ya akayi aka san su sister sun fita daga gida har aka kama su?" sai lokacin bgs ya juyo da kallon sa kan Aryan ɗin shiru sukayi kowannen su ya sanya ƙwaƙwalwar sa a tunani suna kokarin tuna waya makama
a fili bgs yace "ranar da nayi fitar sirri da sister a Uk an bi bayan mu ranar da na bar sister a shopping bayan Khalid yazo ya ɗauke ta an bibiye su ni kai na ranar da na fita ni kaɗai an bibiye ni ranar da Fahad ya fita shi da matar sa an bibiye su tabbas akoi abun da ya saɓa" matsowa Aryan yayi yana faɗin "amma bgs koma waye wanna makiyin namu mutun ne mai haɗari kuma yana kusa da mu amma wanna wanene gaskiya bgs awan nan karon munyi sakaci sosai" "no Aryan ba sakaci mukayi ba shigowar su sister rayuwar mu ne ya sanya muka sauya tun lokacin da ka fara son yarinyar nan gaba ɗaya ka sauya ba abun da kake sai shirme Yusuf ya dai na aikin sa sai shirme kuke min ni ka ɗai kuka bari da aikin abubuwa sun min yawa, na kula da gida ga uk ga Aunty farida Aunty mardiya ta ko ina ni kaɗai ne kuma 2 days da na biyewa sister shi ya sanya har aka samu damar shirya min wani abun wanna dalili ya sanya nace mata raunine koya kayi sai sun kawar maka da hankali kan wani abun" ya kai karshen maganar tare da jan tsaki "amma bgs waye kake ganin zai iya aikata wanna abun?" Shiru ya ɗanyi kafin yace "no ai ba makiyi ɗaya bane yanzu makiya uku zamu shiryawa domin masu neman sister a uku daban masu neman ta a nan daban ga wancan wawan da ya ɗauki auta" "to amma bgs me yasa sai sister kawai suke son kamawa" hararar gefen ido bgs ya masa kafin yace "saboda matata ce ita mana sun san cewa dole itace raunina kuma kowaye ya ɗauke ta idan nayi wasa zai iya galaba a kai na ya kai ni kasa" a sukwane Aryan ya duƙa kasa yayiwa Allah sujudur sukur da mamaki bgs ke kallon sa bayan ya ɗago daga sujjadar ya ɗaga hannu yana addu'a "ya Allah na gode maka daka nunamin wanna rana da bgs ya furta cewa sister matar sa ne da kan sa" jin hakan ya sa bgs jan dogon tsaki ya wuce ya cigaba da yan cinkiken sa
Miƙewa Aryan yayi ya bi bayan sa yana kara godiya ga Allah
dai dai in da wayan da suka kama su hiyana sukayi parking mota bgs yayi karo da agogon hannu,zubawa agogon ido yayi na ɗan lokacin kafin ya sanya hannu a aljihun sa ya ɗauko handkerchief ya duƙa ya ɗauki agogon ya miƙa wa Aryan yana faɗin "daga yau zuwa gobe a binciko min Company da suke buga a gogon nan dan ina da tabbacin wanna agogon ɗaya daga cikin mutanen da suka kama su Khalid ne idan na gane Company abun zai ɗan zo mana da sauki" ansan agogon Aryan yayi yana kallon agogon
ɗago ido yayi ya kalli bgs kafin yace "amma wanna agogon kamar akoi ajiya a cikin ta ai" "eh nima na gani akoi memory a ciki ka cire min memory idan mun koma sai muga menene a ciki" ya kai karshen maganar tare da duƙawa ya ɗauki wani hoton da ke kife awajen juyo da hoton yayi,wanna hoton ne da mutanen chan suka nunawa hiyana da Zahra zura hoton yayi a aljihun sa ya ɗago yana kallon Aryan.
Aryan yana kokarin yin magana bgs yayi saurin rungume sa suka faɗi kasa,ji kake tass arbin bindiga bullet ɗin ya wuce ya rusa glass ɗin motar su Khalid,
a zuciye suka miƙe dukkan su biyu suka ɓuya a bayan motar
shiru shiru har tsawon 10mins basu sake jin motsin kowa ba
Aryan ya ɗago ya kalli bgs yayi da shima bgs ɗin shi yake kallo a tare suka mike Aryan ya nufi motar su bgs kuma ya nufi motar su Khalid ya ɗauki bullet ɗin da a ka harbo musu yana dubawa kara waro idon sa wajen yayi yana kallon bullet ɗin tabbas wanna bullet ɗin na shine na gun ɗin sane lokacin guda kamannin sa ya sauya a zuciye ya juya ya nufi motar su cikin fushi yace wa Aryan "fita bari na ja motar ka koma gefen can" ganin yausawar da yayi ya sa Aryan bai yi magana ba ya fito ya koma ɗayan ɓangaren
Bgs ya shiga mazaunin driver da mugun gudu ya figi motar ya nufi hanyar gida da gudun gaske
Suna shiga gida tun bai gama kashe motar ba ya fito a zuciye ya ɗauko piston gun daga gefen kujerar motar ya nufi wajen security dake wajen gate ɗin kai tsaye ɗakin Abdol ya nufa
Kwace ya sami Abdol saman gado yana mai da numfashi, ba tare da ɓata lokacin ba bgs ya harbesa a kafar dama,ihu Abdol ya saki tare tare da miƙa wa zaune ya dafe wajen da bgs ya har besa damko wuyar sa bgs yayi ya jasa zuwa waje zawa tsakar gida
Wani wawan naushi ya kai masa wadda ya sashi faɗuwa kasa da gudu Aryan ya kariso wajen yana faɗin "bgs me kake yi ne? Abdol ne fa ko baka lura bane? Yana kai karshen maganar ya riko hannun bgs,hakaɗe sa bgs yayi gefe yayi baya baya yana kokarin faɗuwa
da gudu sauran jibga jibgan sojojin dake gidan suka karaso wajen cikin tsawa bgs yace "Abdol why? Me na maka me ya sanya kake neman kashe ni da family na?" da kyar Abdol ya iya miƙewa tsaye cikin raɗaɗin ciwo yace "kayi kuskure Safras kayi sake ɗan zaki ya girma ni nasan daman ba zaka kyaleni ba zaka gano ni amma kasani ko na mutu ka kashe macijine baka sare kan sa ba" yana kai karshen maganar ya ciro piston gun daga aljihun jaket ɗin jikin sa kafin suyi wani yunkuri ya harbi kansa da kansa a goshi nan take ya faɗi kasa wanwar
Allah sarki Shahram lokaci guda yaji jikin sa yayi mugun sanyi yanzu duk yadda Abdol yake da bgs ba abun da bgs baya masa amma sai da yaci amanar sa lallai duniyar yanzu mutun ba abun yarda bane tunani yake anya Aryan zai sake yarda dashi kuwa? Tun da ga abun da ya faru tsakanin Abdol da Bgs
A fusace bgs ya juya ya nufi part nashi, umarni Aryan ya bawa sojojin su akan su yiwa Abdol abun da ya dace da shi yana gama faɗa musu hakan ya wuce yabi bayan bgs
ɗakin binciken su ya isoko bgs kusa da shi yaje ya tsaya yana faɗin "amma bgs ya akayi ka gane Abdol yana ɗaya daga cikin masu shirya mana tuggu!? dogon numfashi bgs yaja tare da sauke ajiyar zuciya lokaci guda idon sa sukayi jaa kamar wuta
Furzar da iska mai zafi yayi daga bakin sa kafin yace "Aryan Abdol ya cuceni tun last 2 weeks na fara zargin sa lokaci da mukayi fitar sirri ni da sister ba wanda ya sani bayan munjeka kayan mu da ruwa ne na kirasa awaya akan ya kawo wa sister kayan sawa dan zazzaɓi ya kamata
bayan yazo wajen ya tafi kenan aka kawo mana hari,tun lokacin na fara zargin sa amma ban bari zargin nasa yayi yawa a zuciya ta ba dan ina ganin kamar idan na zarge sa ban masa adalci ba gani nake kamar ya riƙe min amana sannan yanzu da mukaje binciken nan na samu hoton sister a kusa da in da muka sanu agogon nan kuma hoton nata bata sani ba aka ɗauke ta sanna a Uk aka ɗauke ta ba a nan ba, lokacin da na kalli hoton sunan Abdol zuciyata ta kawomin domin su Khalid dai ba zasu ɗauki hoton sister su bawa wani ba amma duk da haka na kore zargin sa a rai na dan ban son hakan bayan harin da aka kawo mana Allah ya tsare naje na duba bullet ɗin tabbas bullet ɗi nane wadda na bawa Abdol nauran kuma ta nauran ya harbe mu amma ni na bashi yar nauran ne kasan cewar yana tare da ni akowani lokacin zaa iya farmakan sa tun da yana da kusan ci da ni ban san cewa na bashi abun da zai nemi kashe ni da shi bane,da Abdol bai kashe kan sa ba wlh Aryan ba zan iya kashe shi ba sai dai na bashi horo dan ya faɗa min waya ke wa aiki ina kaunar Abdol har cikin raina wlh ba zan iya kashe shi da hannu na ba yanzu ya mutu ban san da suwaye yake aiki ba ban san su nawane a cikin mu suke aiki da Abdol ba ban so Abdol ya tafi wutar jahannama ba banso ya kashe kan sa ba" yana magana idon sa na kara jaa kamar jini sai zufa yake gaba ɗaya jijiyoyin kan san nan a tsai tsaye kasa kasa ya furta "Khalid my sister" yana faɗin sunan su yaji wani kwarin guiwa lokacin guda
bincike ya farayi a system nashi kai tsaye ya shiga sunan Abdol ya fara bincike dan yaga da suwaye Abdol yake aiki
tsaki ya ja yana kokarin wurgi da system ɗin Aryan ya tare yana faɗin "lfy bgs? pls ka kwantar da hankalika ka saita ƙwaƙwalwar ka dan mu samu muyi aikin da ya dace yanzu ba lokacin da zaka sawa kan ka tension bane yanzu ne muke bukatar ƙwaƙwalwan Brigadier general Safras ka nitsu kayi tunani ni nasan zaka iya tun da ka iya gane in da su anwar suke ba tare da wani evidence ba wanna ma idan ka nitsu zaka iya" "Aryan wanna case ɗin daban da ko wanne dole kai na zai ɗau zafi my sister Khalid kai ai dole na shiga tension dole nayi tunanin su" "duk da haka daurewa zakayi yanzu dai me ya sanya zakayi wurgi da system ɗin kuma!?" "Aryan Abdol ya rufe komai na shi yanzu na kara tabbatar wa ba da karamin mutun zanyi yaki ba domin duk wan da Abdol yake wa aiki ba karamin mutun bane babban kwaro ne yanzu dai ka kara jaddawa security karko wa ya sake shigowa gidan nan ba tare da izinin na ba haka fita kar su bar kowa ya sake fita ka sanya mana memory cikin agogon nan a cikin system ɗin mu gani ko zamu samu wata makama" ba tare da yayi magana ba ya fito da agogon daga aljihu sa ya fito da memory ya sanya a system ɗin suka zauna saman kujera suka fara bincike a cikin memory.
Video manya manyan maka mai da kwayoyin maye suka fara cin karo da shi a memory zubawa wajen ido bgs yayi shi bama kwayar ko makaman yake kallo ba wajen da akayi video yake kallon,bai taɓa kallon wannan wajen ba amma koma inane wanna tabbas a cikin Nigeria ne sunyi shiru suna kallon video Yusuf ya shigo ɗakin bakin sa ɗauke da sallama
Kusa da su yazo ya zauna yana faɗin "ya zamuyi da wancan yaron? sai ihu yake wa mutane" cikin bacin rai bgs yace "ku har besa dashi da mutanen nasa duk ku kashe su dan basu da wata amfani mugun iri ne idan an barsu ma karawa kasa criminals zamu yi" "wani yaro ne kuma? Cewar Aryan tsaki bgs yaja kafin yace "ɗan wancan wawan mutumin mana wadda muke nema" "no kar ku kashe sa this time ka barni zanyi aiki a kansu kai kuma kaji da wayan da suka kama su sister kai Yusuf ka kai min shi ɗaki horo bari nayi wanka zanzo nayi bincike akan sa amma sauran yaran nasu duk ka harbesu bana bukatan su" to Yusuf ya amsa da shi tare da miƙa wa ya nufi hanyar fita har ya kai bakin kofa Aryan yace "yauwa Yusuf ka saki wancan Ahzan ɗin dan ya karɓi horo yadda ya kamata ita kuma wancan matar ka kawo min ita dan inason in haɗa ta da yaron nan akoi tambayoyin da zan musu dan tace min yarinyar ta ɗaya ce a duniya kuma wanna mutumin ne baban yarinyar yanzu kuma ga yaron sa mun samu shi kuma daga ina? ina maman sa take?"
tun da suke