Showing 330001 words to 333000 words out of 363274 words

Chapter 111 - Duk Karfin Izzata Hausa Novel Complete

12 Dec 2024

2583

kyau da ɗaukan hankali. Cikin dabara na kariso wajen sa domin na tabbatar Mutun ne ko ba mutun ba bayan wata bishiyar dalbijiya na ɓuye ina ta kallon sa ya tsaya shiru yana ta kallon shanun sa dake kiwo a ɗan nesa da shi ina da gata a gidan mu sosai ko waje ba'a barina na fita sai dai na saci hanya ba'a sani ba su yaya Abdussalam suna samin ido sosai da zarar na fita aka farga to za'a biyo baya na ina laɓe a bayan bishiyar dalbijiya na hango su yaya Abdussalam daga nesa suna nemana ganin su ya sa na kwasa da gudu na bar wajen ba dan na so ba ban gaji da kallon wanna mutumi mai kiwo ba na gudu na kutsa ta cikin masara na lallaɓa na koma gida ranar kwana nayi ina tunanin wanna mutumin. Washegari tun da sassafe na sake satar hanya na ɗauki abinci na cikin kula na gudu na tafi in da na ganshi jiya nayi Sa'a ina isa wajen shima ya iso ina ganin sa ban san lokacin da na saki wani cool murmushi cikin sauri na kari sa wajen sa cikin nitsuwa na masa sallama a zafafe ya ɗaga sandar kiwon sa zai buga min dan atunanin sa na miji ne da yake ta bayan sa na zo ihu na saki tare da sakin kulan abincin da na rike na runtse ido ina jiran saukan sanda a kai na. Ihun da nayi yasa ya dagata bai buga min sandar tasa ba zuba min ido yayi yana kallon na daga sama har kasa a lokacin sanye nake da dogowar riga mai kyan gaske ta kanti na sanya ɗan kwali karami a kai na a hankali na buɗe ido na na sauke su kan kyakkyawar fuskar sa sai na ga ashe jiya ma ban ga komai ba game da kayan sa kasan cewar nayi nisa da shi yau da na matso kusa da shi sai naga ashe kyan sa ya zarce tunani na murya na rawa nace masa "ina kwana?" Kallo na ya yi da kyau dan baya jin Hausa a hankali ya sauke sandar ki won tasa kasa yana faɗin "A yami Sa'a, a debbo on" (kin yi Sa'a ke mace ce) ba karamin ruɗewa nayi da jin zakin muryan sa ba muryan sa sak na Hiyana shi ta ɗauko a komai shi yasa idan na ganta sai na ji wani abu a rai na suna da murya mai sanyi mai daɗi.
ina jin fulatanci sosai dan haka sai na gane abun da ya faɗa cike da murna na mayar masa da magana da fulatanci nace masa "Ina kwana" shiru ya yi bai amsa ba kasan cewar bappan su Hiyana mutun ne ba mai yawan magana ba yadda kuka ga Hiyana haka yake bai da yawan magana kuma bai san hayani, wuce wa ya yi ya barni tsaye awajen cikin sauri na ɗauki kulan abincin na bi bayan sa ina faɗin "Hamma dan Allah ka tsaya ka ansa abincin" nayi masa magana cikin harshen fullanci bai kula ni ba ya kaɗa shanun sa suka bar wajen haka na koma gida da abincin kwana uku na ɗauka ina kawo masa abinci a sace amma bai taɓa kula ni ba tun ranar farko da ya min magana ban sake jin muryan sa ba na rasa ya zan yi da shi ina son jin muryan sa sosai dan tun maganar da ya min ta farko ta tsaya min a rai na ina tuna daddaɗar voice na sa.
a rana ta huɗu ne dana je yaki kula ni sai na ajiye masa abincin kusa da shi yana zaune kasan wata itaciyar mangoro ina ajiye masa abincin na nufi shanun sa dake kiwo ɗan nesa da mu na kutsa ta cikin su yana zaune yana kallo na ina zuwa na samu wata shanu da ake cewa bakolo mafaɗaci ne shanun sosai hannu nasa da karfi na murɗa bindin shanun, nan take ya yi kuka ya juya ya yo kai na a guje na juya na bar wajen, da gudun gaske shanun ya bini na shiga tashin hankali da dana sanin me ya kai ni gashi shanu zai kashe ni a banza ido na ya rufe gudu nake sosai kamar zan tashi sama ban san ya akayi ba kawai na ganni a saman kirjin sa ya ɗaga sandar sa ya bugi shanun da karfin gaske yana daka musu tsawa da gudu dukka shanun suka yo kan mu tsabar tsoro ban san ya akayi ba mumfashi na ya ɗauke na sume a jikin sa ban san ya ya kare da shanun ba kawai na farka na ganni a cikin wata yar bukka kwance saman gadon ciyawa. Da kyar na iya buɗe ido na tare da tashi zaune a hankali na mike na fito waje yana zaune kasan itacen ɓaure dake wajen ya sunkuyar da kan sa kasa kamar mai tunani gaban sa nazo na tsgunna ina faɗin "Kayi hakuri Hamma wall...ban kai karshen maganar ba ya wanke min fuska da mari cikin tsawa yace "Da yanzu kin mutu fa waya ce miki anan wasa da shanu haka" dafe kumatu na nayi na fara hawaye dan tun da nake ba wanda ya taɓa marina a rayuwata naji zafin marin sosai ganin ina kuka yasa ya sassauta murya cikin nitsuwa ya fara magana cikin harshen fullanci "Kiyi hakuri marin ki da nayi amma ki sani yau Allah ne ya cece ki ba'a yiwa shanu irin wanna gangancin shanu na da zuciya sosai kuma ki rasa wanne zaki takala sai bakolo shanun da ya fi kowa ni shanu faɗa shanun da ba shi da sabo ko ya kuke yanzu zai iya kashe mutun karki sake irin wanna gan gancin" ya kai karshen maganar tare da ɗago hannun sa ya fara goge min hawaye a hankali na ɗago ido na ina kallon hannun nasa nan naga hannun nasa sai zubar da jini yake alamar shanun ya ji masa ciwo waro ido waje nayi ina ganin yadda yaji ciwon sosai cikin sauri na cire abun da na ɗaure kai na na kama hannun nasa inason ɗaure masa fisge hannun sa yayi a kule yace cikin harshen fullanci "bana bukata!" ina kokarin yin magana ya daga min tsawa nan take naji zafafan hawaye sun fara bin kuncina ni da nake yar gata a gida ba wan da ya isa ya taɓa ni amma yau ga mutumin daji na sani kuka hawaye wani na bin wani a kuma tuna ganin hakan yasa ya sanya hannun sa kan face na yana goge min hawaye yana kokarin yin magana sai ga dogarawan Abban tare dasu yaya Abdussalam sun zo nema na kukan kura yaya Abdurahman yayi ya shake Bappa su Hiyana yana faɗin "me ka mata take kuka" basu bashi daman yin magana ba suka hau dukan sa yaya Abdurahman yaya Abdussalam dukkan suna da zuciya sosai duka sosai suka masa har ya faɗi kasa kamar ya suma nima sun ki bani daman yi musu bayani ina kokarin yi masu baya ni yaya Abdussalam sarkin zuciya ya wanka min wani gigitatchiyar mari abun da ba'a taɓa yi min ba ko da wasa cikin tsawa yace "Kin cuce mu wallahi!!" ni ban gane me suke nufi ba a lokacin saboda karancin shekaru a fusace yaya Abdurahman ya ɗaga hannu zai kara min mari kan na yaya Abdussalam na truntse ido ina jiran saukar mari sai naji shiru a hankali na waro ido na dake zubar da kwalla sai ganin nayi Bappan su Hiyana ne ya rike hannun yaya Abdurahman ɗin waro ido yaya Abdurahman ya yi ya kasa magana dan duk a tunanin su bappan su Hiyana ya suma. Cikin fushi Bappan su Hiyana ya fara magana cikin harshen fullanci "Duk wanda ya sake dukan ta wallahi sai na rama mata na bari kun dake ni a matsayin ku na yan uwan ta ban tan ka muku ba kasan cewar ni na neme ku da magana amma ita kuwa baku isa ku buge ta a gaba na ba idan kuma kun musa ku taɓa ta ku ga ikon Allah dukkan ku nan ba wanda ya wuce na masa bugu ɗaya ya suma" kallon juna suka yi a fusace yaya Abdussalam sarkin zuciya ya dungule hannu ya kai wa bappan su Hiyana duka a ciki da kyar bappa su Hiyana ya shanye yana faɗin "Sai dai ku dake ni dai amma ba ita ba" su da kan su sun san Bappan su Hiyana zai iya dukan su idan suka ce karfi za'a gwada dan haka cikin fushi yaya Abdurahman ya kwace hannun sa daga na bappan su Hiyana yana faɗin "ku ɗaure sa ku wuce min da shi kurkukun masauta ita kuma ku wuce da ita palon Hajiya ina zuwa" yana kai karshen maganar ya wuce ya bar mu, yaya Abdussalam ya tasa ni a gaba muka wuce gida shi kuma Bappan su Hiyana suka ɗaure sa kamar yadda ake ɗaure goro ga hannun sa da shanu ta ji masa ciwo na zubar da jini haka suka wuce da shi na sha kuka ina tausaya masa dan na san halin su yaya Abdussalam basu da imani duk wanda suka ce akai shi kurkuku tofa sai dai a masa addu'ar Allah ya kuɓutar da shi daga hannun su. Ko da mukaje palon Hajiya sun haɗu suna ta faɗa ni ko magana ɗaya da suke faɗa ban ji ba tunani kawai nake taya zan fitar da bappan su Hiyana daga wanna kurkukun masautan nan dan nasan cikin kurkukun nan yafi wuta zafi da horon azaba. Har su Hajiya suka gama taro ban ji komai da suka faɗa ba hankalina baya kan su.

Kwana uku Bappan su Hiyana ya yi a kurkukun masaurata ba abinci ruwa ma sau ɗaya a rana ake ba shi nayi ƙoƙarin na fitar da shi amma ban samu dama ba kullun ina satar hanya in je in bawa shanun sa abinci in kwance su su je yawo haka da yamma ina zuwa in ɗaure su.
A rana na huɗu ne karfe biyu na dare na tashi na nufi wajen da aka tsare sa Allah ya bani iko mai gadi ya yi barci a hankali na saci key daga aljihun sa na buɗe Bappan su Hiyana ya jigata sosai ya kasa tafiya baya iya gane komai ya fita hayyacin sa saboda wahala da ya sha kasan cewar bai da kiɓa bai da nauyi sosai yasa na goya shi a bayana muka fita ta kofar baya na masautan kai tsaye wajen shanun sa muka nufa na ɗauki wani yar roba a dakin sa na ɗebo masa ruwa a ɗan ƙaramin rafin dake wajen na ba shi ya sha sosai har lokacin baya gane komai amma ya ɗan samu karfi daya sha ruwan haka na goya shi na kwance shanun sa kusan shanu 550 lokacin haka na kaɗa su gashi a bayana da kyar nake jan kafata.
munyi tafiya mai nisa kafin gari ya fara haske, hasken da gari ya fara yi ne yasa ya fara dawowa hayyacin sa lokacin kuma munyi nisa da cikin sudan. Bayan ya dawo hayyacin sa ya nuna rashin jin daɗin sa akan abun da nayi da kyar ya iya ce min "Ban san sunan ki ba amma koma me bai ka mata na gudu ba kama ta ya yi gaskiya ta ta fitar da ni, ni bana guduwa idan nasan bai yi laifi ba koma nayi laifi bana guduwa bare ban yi ba" ya yi kokarin mu koma dan ya mai da ni amma na nuna masa idan muka koma kashe ni zasu yi jin zasu kashe ni yasa ya yi shiru ni kuma na faɗa masa hakane saboda dalilai biyu na farko ina son kasan cewa da shi ko ma ai na ne na biyu kuma nasan ko zan mutu a gida ba za'a aura mi shi ni ba shi yasa naki yarda ya mai da ni.
yaso tafiya ya bar ni awajen ya kama hanya ya kaɗa shanun sa ya fara tafiya da karfi na sa masa kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro hakan yasa ya tsaya ya juyo yana kallona ganin da gaske nake kukan ya sa ya min nuni da hannun sa akan nazo mutafi da gudu na karisa wajen ina murna haka muka cigaba da tafiya bana taɓa manta lokacin da muka zo wajen wani babban rafi mai cike da ruwa ya ɗaga ni ya ɗaura ni saman shanu ɗaya tsoro ya kamani gani nake kamar zan faɗin na sa masa kuka ina faɗin "Ni ba zan iya ba zan faɗi" lokacin har murmushi sai da na sa shi har gobe ina kallon wanna murmushi na sa a fiskana mussam idan Hiyana na murmushi sai in ga kamar shi. Ganin na tsorata sosai ina kokarin fara yi masa kuka ne yasa ya hau bayan shanun ya rike ni ta baya naji daɗi sosai na saki jiki na ina kaɗa kafata a cikin ruwa haka shanun nan suka kutsa cikin ruwan babban rafi ne sosai. Muna cikin tafiya daddaɗar voice na shi irin na Hiyana ko in ce irin na Ammi ya daki dodon kunnen na yana faɗin "Menene sunan ki" ya yi maganar cikin harshen fullanci cikin sauri nace masa "Amina" shiru ya yi bai sake magana ba har muka wuce ruwan cikin dabara ya tsai da shanun ya sauka a hankali ya sauke ni ya wuce bai ko kalle ni ba.
mun yi tafiyar kwana biyu da shi amma bai taɓa ɗaga ido ya min kallo mai kyau ba ni har mamaki ma yake bani kamar baya kallon mutane kuma yana da manya manyan idon masu kyau kaman nin sa ɗaya sak da Ammi da Hiyana da Safras da Zahra duk kaman nin su ɗaya wanna kwana biyu da muka yi da shi tun kafin in ce ina jin yinwa yake shiga daji ya damo min abinci ya kawo min wani lokacin su apple yake kawo min wani lokacin kuma ayaba ko gwaiva ko mangoro wani lokaci ya kama kifi ya gasa min abun mamakin shi ne idan ya kawo min in nace muci tare baya ci ban taɓa kallon in da yaci wani abu ba alokacin har tsoron sa ya fara kamani na fara tunanin ko dai ba mutun ba ne? Da ga lokacin na ɗan fara ja baya da shi daya lura da na fara tsoron sa sai ya fara sake min fuska idan na yi magana ya fara amsa min sama sama saɓanin da dako kallo ban ishe shi ba haka muka yi ta tafiya idan dare ya yi baya barci yana haɗa min ganye na kwanta a kai shi kuma ya zauna shiru ku sa da ni yana gadi na a hanka mukayi sati da shi a hanya dai dai da lokacin guda ban taɓa neman wani abu na rasa ba a satin da muka yi da shi. Cikin dare muka shiga garin su na yi barci ya goya ni a bayan sa ka san cewar dama wani lokaci idan bai son mu tsaya da tafiya in nayi barci yana goya ni a bayan sa mu cigaba da tafiya ban san lokacin da muka shiga garin su ba ina cikin barci na ji daddaɗar voice na sa ya daki dodon kunnen yana faɗin "Boɗɗo ummu" (Kyakkyawa ki ta shi) da kyar na iya buɗe ido na saboda gajiya gashi nayi datti sati na ɗaya ban yi wanka ba abun mamaki ina buɗe ido na yi arba da kyakkyawar fuskar sa ya yi wanka yana sanye cikin farar jallabiya kyan sa ta kara bayyana hasken fatar sa ta kara fita hannun sa rike da fitilla mai haske ta haske ɗakin hakan ya bani damar kallon sa da kyau miƙewa na yi zaune ina kallon sa na kasa kawar da ido na ganin haka yasa ya sanya hannun sa ya ɗan tsorata ni cikin wasa kamar zai tsokale min ido cikin sauri na runtse ido na cool murmushi ya saki yana faɗin "Matsoraciya ta shi ki yi wanka kici abinci yau zaki yi barci mai daɗi, inna ta zata kawo miki abinci da duk abun da zaki buƙata idan ma akoi abun da bata kawo miki ba kuma kina buƙata ki tambaye ta zata baki ni zan tafi ɗaki na sai da safe" mamaki ya hana ni yi masa magana dama yana magana haka nasha ruwan mamaki jin yadda yau ya yi magana mai tsawo haka daman haka muryan sa ke da daɗi sosai shi yasa bai san yawan magana ashe, dan a baya kafin muzo gidan su ciki ciki yake magana ba zaki taɓa cewa ga kalar muryan sa ba. Ganin na yi shiru na kasa magana ne yasa ya mike tare da a jiye min fitillar hannun sa yana kokarin juyawa ya fice nayi saurin riko rigar sa ina faɗin "Hamma ina jin tsoro wallahi" dawowa ya yi ya tsugunna yasa kyawawan fararen hannun sa mai ɗauke dogayen yatsu ya riko hannaye na cikin sanyin murya ya fara magana "Buɗɗo kar ki ji tsoro komai nan gidan mu ne inna ta tana zuwa tana kitchen ne zata zo ta kawo miki abinci kin ji? yanzu kije ki yi wanka ki ɗauki fitillar ki fita waje zaki ga bayi kusa da ɗakin nan na kai miki ruwan wanka yana ciki kinji ko?" Shiru na ɗan yi kafin nace "To kai kuma ina zaka je?" Yana kokarin yin magana Kyakkyawa mata ta shigo fara tas kaman ta ɗaya da shi cikin sauri ya sake hannu na ya mike ya nufi hanyar fita "Ahmadu ina zaka je? Kazo kuci abin cin mana" cewar Innan sa tayi maganar cikin harshen fullanci ƙasa na yi da kai na dan naji kunya yadda Innar su ta same mu da shi a rai na ina mai mai ta sunan da Innar sa takira shi da shi Ahmadu daman sunan sa kenan suna mai daɗi.
Cike da jin kunya shi ma yace "Na koshi Inna" tsabar tausayin sa ban san lokacin da nace "A'a Inna wallahi bai koshi ba tun da muka fara tafiya ban ga yaci wani abu ba na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login